← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 157

Sashe 94

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kuwa falon ya kaure da dariyar yadda yayi har ya tashi zai bar musu falon da Ibrahim yace "irin jaririn samudawan nan kawai zaka koma".

"Dawo ka zauna in karasa...Zayyanatun Daada kema ba'ayi miki suna ba"

Zayyana sai ta rasa inda zata saka kanta don dadi Zayyan ya fasa mata kai yace ita tashi ce. Ibrahim ya dan kalleta yadda take dariya ta tashi ta koma kusa da Zayyan ta zauna tana narkewa "Daada ba'ayi min ba, ko kayan barka fa bana jin an kawo"

"Kiji tsoron Allah" Mami tace tana dariya.

"Ai kuwa duk wanda bai kawo ba muna binsa bashi. Su Ummi da Mama kowa ta kwance bakin jaka"

Anata dariya ta hada ido da Ibrahim wanda ya kasa gane mata tun ranar da yayi maganar tale baki. Abin ya dame shi sosai ya kasa fadawa Emzee. Yanzu suna hada ido yayi murmushi ita kuwa ta murguda masa baki ta kawar da kai, babu wanda ya kula sai shi.

Zayyan ya dago Daada Karami "kaima bakon duniya nazo na tare hanya ba'ayi maka taro an kawo kayan barka ba. Saboda haka in sha Allahu za'ayi taro na musamman idan komai ya natsa na Zayyan, Zayyan, Zayyanatu da Zayyan."

Hayaniyar murnar da suka cika falon da ita ba arziki Mami tace su tashi su fita. Zayyan ya yafito Awwab da hannu. Tun shigowarsa dama baiyi magana ba sai ma dukufa da yayi yiwa abokin aikinsa text akan abinda zasu yi idan ya koma.

"Idan an gama suna sai mu fara shirin bikin dana. Kunyi min komai daidai amma an bar min yaro ba aure. To mu dai yarinya ko 'yar waye tunda yana so idan ta kama na sato ta ne zanyi na kawo maka kaji ko"

Idanu suka koma kansu shi da Radhiya lokacin suna rige rigen arcewa daga falon. Shi hanyar waje yayi ita kuma tayi kitchen. Su Major ma sai da suka yi dariya.

"Kunga kama kai, yanzu don Allah waye yaji na ambaci suna?"

Da dariya suka fita harda ta kitchen ita ce karshen tafiya. Major yace masa ya fara tara jikoki ya kamata ya rage chalikanci.

"Idan na dena so kake su rinka guduna? Kuma dai shekarata nawa ina danne Zayyan Tureta ta karfin tsiya. Yanzu kuwa lokaci yayi da zai fito yayi kara'i"

"Aiki ya sameki kanwata kiyi a hankali kada mu fara ganinsa da kitso da dankunne irin na matasan zamani" Baba Hadir ya rubuta ya mikawa Mama ta bata. 

Zayyan yana ganin tana dariya yace sai ya gani. Daga nan dai hirarsu ce da bata karewa suka dasa. Sai sakon text Alh Salisu ya yiwa Baba Hadir zai zo suyi sallama gobe zasu koma Kano da yaran. Ya kara da dan korafin wai ko basu hakura bane yana ta sa ran zuwansu gidansa ko su ko yaransu amma shiru. Baba Hadir sai yaji babu dadi ya mikawa Daddy wayar. Kiransa Daddy yayi bayan sun gaisa yace

"Hadir yana mai baka hakurin rashin zuwan nasa. Wani abu ne ya taso amma idan babu takura kuma kana da lokaci kafin ka tafi goben me zai hana ka shigo ka ga uzurin nasa?"

"To Allah Ya nuna mana Yasa lafiya. A gaida yaran don Allah"

Da haka suka yi sallama. Matan na daki suna tsokanar Ummi amarya babu lalle babu gyaran gashi ta ce laifinsu ne. Mama tace ba don jego ba da idan ta fara gyarata sai sun biya mata Hajji da Umra.

"Ni dai naga ranar da zaki girma Zainabu. Ina jin halinku ne Sakkwatawan nan. Daga ke har Zayyan sai ku sa cikin mutum ciwo da ban dariya."

"Cewa zakiyi suyi abu su daure fuska ki rantse ba daga bakinsu magana ta fito ba" Ummi ta fada da dariya.

"Baki ji ba wai zai satowa Awwab Radhiya ya kai masa ita. Uban amarya zai saki layi."

Kowacce ka gani tana cikin walwala da annashuwa suna jindadin zama da juna sai fatan Allah Ya kade shaidanu Ya kara hada kawunansu.

**********

Tun dawowar Zayyan yau ce rana ta farko da su ka kebe su kwadai da 'ya'yansu a bangaren Ummi. Ba kowa ne da wannan tunanin ba kuwa sai Mama Zainab. Bayan sun fita ta tura musu Radhiya da Emzee da sunan su je ko babansu yana son hira dasu. Babu wani boye boye tace ya kamata su bashi lokaci yaji matsaloli da cigaban rayuwarsu kamar yadda kowane uba yake yi. Radhiya taji kunya sosai ganin da su Zahra a wurin. Amma sai ta kula babu wadda abin ya dama sai ma goyon baya da su ka baiwa Mama aka korasu yau su kwana a gidansu.

Ummi da Radhiya ne suka yi girki yayin da Zayyan yake sake jin daukakar da Emzee yake samu a NDA tun shekararsa ta farko. Ya yaba kwarai da dan nasa yana jinjinawa a ransa wannan wai magajinsa ne wanda bai barshi ta ko ina ba...suna da aiki.

A kasa Radhiya ta ajiye musu abincin Zayyan yace ta dauko babban plate yau a kwano daya zasu ci ya ga girman lomar kowa. Da dariya aka soma ci sai gashi su hudun sun buge da zubar hawaye lokacin da ya kallesu daya bayan daya yace "ko yanzu mutuwa ta riskeni zan tafi ina mai farinciki da cika godiyata ga Allah."

Ummi ce ta fara hawaye sai Radhiya ta kama harda shessheka. Emzee ma duk dauriyarsa sai da yayi "don Allah ni dai a dena kukan nan abincin da dadi amma zaku sa ya fita daga raina"

Dundu Ummi ta kai masa "acicin kawai"

"Zancen gaskiya Ummi. Ba abin nayi fuska na gama ci sannan nayi nawa kukan ba na rasa me tayani"

"Ashe haka kake Zayyan? Shiyasa Malamijo yace yana nemanka kaje da bindiga ko ta katako ce"

"Nemana kuma Daada?"

Ummi ta amshe da fada musu sakonsa na dazu "sai ku shirya zamu tafi tare. Zamu barku a can mu wuce Sakkwato daga can muje Nijar"

Radhiya ta rike baki "Ummi wai ni din da gaske yace ko dai kin fada ne kawai don kada nace baya sona"

"Kaniyarki" ta kai mata duka Zayyan ya tare yana cewa babu mai taba masa uwa.

"Da gaske nake Daada, cewa fa yake yi idan yaji muryata gabansa faduwa yake yi" ta turo baki da takaici.

"Gonarsa take zuwa tace wai dabba ta kasa tasa a yanka. Ka kuma sanshi da dabbobinsa sarai" Ummi tace tana murmushi.

"Amma anya lafiya kuwa yake nemanmu?" Emzee yaji abin ya daure masa kai. Malamijo fa ko waya baya kiran kowa sai dai a kira shi.

Kowa da tunaninsa amma sunfi kawowa da gaske akwai matsala. Ko ma dai meye jibi da wurwuri zasu bar Abuja. Gara suyi su dawo da wuri Radhiya ta fara aikinta. Zayyan yaji dadin wannan program da zata yi yace idan tana bukatar bayani game da halin da sojojin suke riskar kawunansu a filin daga a shirye yake. Basu ankara ba suna wannan hira sai gani suka yi daya da rabi na dare. Dole aka tashi ba don sun so ba saboda hirar tayi musu dadi. Suna jindadin yadda iyayensu ke zolayar juna. Ummi tace mijinta dan saurayi ne wanda ya tafi yanzu an kawo mata wanda ya fara furfura.

 Zayyan yace "ko kiyi shiru ko na tona miki asiri su san cewa a wurin bin kwalaben mutane a gidan biki kina shanye ragowar mirinda muka hadu"

"Bonono rufe kofa da barawo...ai ka gama tonawa"

Emzee da Radhiya dariya harda hawaye. A zahiri idan kewarsa ta ishi Mairama tana bawa yaranta wannan labari amma yadda ya fada yana kwatanta yadda tayi da ya kamata dole suyi dariya. It was a time well spent a tsakaninsu.

**********

"Ikon Allah jama'a dama Zayyan yana da dan uwa da suke mugun kama banda wadda na gani a wurin Zayyan karami?" Alh Salisu yayi magana a lokacin da suke shiga gidan Baba Hadir shi da yaransa ya kasa dauke ido daga kallon Zayyan din.

"Nine dai Salisu ba kama bace" 

Gabansa yaji yayi wata irin faduwa ya shiga kallonsu yana jira wani yace wasa suke yi amma shiru kake ji. Radhiya ce tayi dabarar kiran su Halifa da kannensa su ka bita wurin Ummi.

Zayyan tasowa yayi ya kama hannun Alh Salisu wanda jikinsa ya fara rawa sai kuma ya soma hawaye "kai din ne don Allah? Hadir Zayyan nake gani. La ilaha illallahu....Zayyan dai nake gani."

"Nine Salisu Allah Ya dawo dani"

Mamaki da al'ajabi ne ya kama shi sosai da aka yi masa bayanin dawowar Zayyan. Wannan al'amari da daure kai yake. 

"Gashi a hanya muke ina da taro gobe da sassafe na 'yan kasuwa. Don Allah ku tsaya a gidana idan kun shigo goben." Ita ce abinda ya fada musu karshe lokacin da suka gama hira ya tashi. 

Aka tura kiran yaran sai ga Halifa tare da Emzee yace a tafi a barshi zasu taho gobe in sha Allahu shima yana son zuwa Sumailan. Alh Salisu yace babu matsala a turo 'yan matan. Kusan minti goma suna jiransu suka taho da Zayyana za'a rokawa Hibbah itama ta kwana. 

Yayi dariya "Kuna tsareni da ido na isa na hana ne" 

Kananan ma sai suka hau rigima saboda kaunarsu dasu Jawad da Femi.

"A'a kuma kada abin yayi yawa. Ku wuce muje su ma zasu taho gobe"

"Ka kyalesu mana nan da can duka gida ne. Dama su Alheran zamu ajiye a Sumaila mu Kanon zamu kwana sai a kawo su gida"

Alh Salisu yaji dadi da Zayyan bai nuna fushinsa ba da ya fada masa laifinsa na rashin kula masa da iyali. Dreban motar yaran ya roka arzikin ya koma can gidan nasa ya kwana gobe sai yazo su tafi shi kuma ya shiga mota suka tafi.

Ga alamu Halifa ya damu kwarai da Radhiya komai ya kira ta ko ya sakota a ciki. Yanzu ma hira suke yi take tambayarsa yaushe rabonsa da zuwa wurin Malamijo yace ya dade sosai.

"Gaskiya kazo muje ka ganshi. Kila ma har Gwaggo Salame ba ka zuwa gidanta ko?" Ta dan dage gira.

"Bazan miki karya ba ita ma bana zuwa yadda ya dace da ya ziyarci mahaifiyarsa. Gidan nata ne ko hadiyar yawu bana iyawa ga yaran nan nata ko sunayensu ban rike ba sai azabar roko"
Chapter 94 · 0% Book details