Sashe 88
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Harararsa tayi cikin wasa "kasan dai ba'a son magana ana cin abinci ko"
"Gani nake yi idan nayi shiru kamar zaki bace na dena ganinki" ya bata amsa kai tsaye yana kallon idanunta da suka cicciko da kwalla.
Hannunsa ta kama ta rike gam da hannun hagunta ta cigaba da bashi da daman.
"Babu inda zani Sojana"
Murmushi suka yiwa juna basuyi aune ba ya cinye leda daya madaidaiciya harda karin rabi na tuwon. Nama ma ba kadan ta bashi ba sai da yaji cikinsa yayi masa nauyi don kansa yace ya isa yana dariya.
"Kada na kasa tashi daga wurin nan fa Fillo. Ina zaune kina ta zuba abinci a tumbin da yunwa ta cinye shi."
"Inda kake horon yunwa suke yi maka? Dubi yadda ka rame sosai ko da dai ba kiba gareka ba amma yanzu ana ganinka za'a gane rama ce ba siranta ba" tayi maganar yayin da ta soma hade kan kwanukan zata kai kitchen.
Da wata irin murya mai sanyi Zayyan yace "Mairama...ki kira min su Major muyi magana kafin na saka hakarkarina a makwanci."
"Ka huta don Allah"
"Yadda kuke matse da son jin me ya sameni nima haka na damu da son jin yadda kuka rayu ke da 'ya'yana da aminai na. Kirjina yana son amayar muku da nauyin da yayi ta dako ko zanji sauki"
Wani irin tausayinsa take ji tana gama kai kwanukan ta wanko hannunta ta dawo ta kira Mami ta sanar da ita.
Su Major so suka yi ya huta ko zuwa gobe ne amma yasan shi dai bazai iya hakurin nan baiji me ya sameta ba.
Har wannan lokaci Baban Arifah yana gidan tare suka dawo falon Zayyan yace a kira masa duka yaran domin su ma sun cancanci sanin ina mahaifinsu ya shiga tsahon lokacin nan. Falon yayi tsit Awwab ne kawai babu. Radhiya dama tana dawowa ta sake komawa gabansa yana daga kan kujera tana kasa. Zayyan ya dube su daya bayan daya ya jinjina kai domin yasan wannan labari yanzu ya fara bada shi har sai duk wanda ya kamata ya sani ya sani. Sojansa ya koma rikakken namiji ma'abocin cikar zati kafin ya fara magana.
"Kwanaki kadan bayan rabuwarmu da Baban Arifah zuwa wuraren karfe daya da rabi na jiya sunana 3810 mazaunin gidan yari da ake yiwa zargin dan tawaye a Liberia"
Major da Baba Hadir sun ji kadan daga labarin daga wurin Baban Arifah amma sauran matan musamman Ummi da Alheran sun dimauce matuka.
Daga lokacin da ya rabu dasu Hadir kawo ga haduwa da rabuwarsa da Baban Arifah da zamansa a wannan prison din ya sanar dasu mahimman abubuwan da suka same shi. Wahalhalun zaman kurkuku da tsananin begen komowa gida garesu. Kuka duka matan suke yi wurjanjan. Ummi saboda tsananin kaduwa tsigar jikinta har tashi take yi ta kasa zaman falon ta tashi tayi ciki sai sautin rufe kofar daki aka ji.
Murmushi yayi yana kallon kofar da ta bi "banda abin Fillo komai ba ya wuce ba"
Jikkuna sunyi sanyi. Girma, kima da darajar wannan bawan Allah ta ninku a cikin idanun duk wanda yake zaune a wurin. Ga su Daddy dadin ciwon abun duka su ukun fa a garin ceton rayuwarsu ne ya fadawa wannan kaddara mai radadi da sosa zuciya. Idanuwa sunyi kuka ba babba ba yaro shiyasa Mami ta cewa yaran dukkansu su tashi tunda sauran labarin ba bakonsu bane. A sanyaye suka fice zuwa gidan Mama ita kuma da Maman suka shiga wurin Ummi. Dama kuma tun zuwan su Zayyan din bayan anyi zaman gabatar da juna sallah suka yi shine Daddy ya jagoranci addu'a da suka yi. Emzee da Ibrahim gidan Mami suka wuce su.
Da kyar bayan fitarsu Major yace "Zayyan ka ga rayuwa ni bani da wani bakin magana ko baka hakuri. Nauyi da girmanka nake kara gani ina jin inama ban biyo motar da taje camp dinku ba ranar. Da bazan biku wurin ba kai kuma babu dalilin da zai sa ka koma daukoni har wannan abu ya faru. Nine silar komai Zayyan ka yafeni" ya kare muryarsa tana rawa sosai.
Idanun Zayyan sai suka kada suka yi jazur "ashe ni din ba kaninka bane kamar yadda nayi zato. Matsayin da muka baka ni da Hadir ba shi ka bamu ba"
Sai ga hawaye ya saukowa Major da sauri yace "a'a Zayyan ba haka bane. I feel so guilty"
"Saboda kaninka yayi rayuwar da ko da babu kai ita Allah Ya zaba masa? Hadir kace wani abu mana ka barni inata babatu ni daya"
Wani mashahurin shiru yaji ya ratsa falon ya kalli Hadir ya kallesu duka a dan tsorace yace "kada kuce min wannan mutum-mutumi ne ba Hadir dan uwana ba"
Hadir din ne ya fara dariya kafin sauran su biye masa da kyar ya iya cewa "Zayyyyyan ko" yana kada masa yatsa. Abokin nasa bai chanja hali ba. Suna cikin damuwa sai da ya saka su dariyar dole.
Tashi yayi yaje yana dan dukan kafadar Hadir din a hankali "tun zuwana banjin kayi min magana ba dole na tambaya."
Baban Arifah Excellency yace "ka zauna Mustapha zaiyi maka duka bayanin da ya dace"
Haka ya koma ya zauna yana sauraron Major wanda ya fara da labarin tasa rayuwar sannan ya gangaro dawowarsu Nigeria da sake haduwa da Hadir. Jikin Zayyan wata tsuma yake yi da tashin hankali da yaji rayuwar da suka yi. Wane irin ciwo ne PTSD yake ayyanawa a ransa da ya nemi haukata Major mutum mai dauriya da karfin zuciya? Yanzu Hadir dinsa ne yayi shekaru baya iya motsa komai nasa kuma baya magana...kai rayuwa shine mutane suke kwallafa rai da neman haram bayan idan Allah Yaso sai Ya dauke maka komai Ya barka da ranka. Hadir mutuwar zaune fa yayi kuma aka raba shi da nasa iyalin alhalin yana cikinsu. Sai yaji yafi tausayin aminin nasa akan tasa rayuwar.
Bayan ya gama jin komai ya kalle shi
" To gaskiya shawarar da zan baka shine ko ka bude baki ka fara magana ko kuma kaf tarihin 'yan matanka wadanda zan iya tunawa da wanda ban tuna ba in dora nawa zan kaiwa Zainab mu koma gefe ni da Fillo musha kallo" Zayyan yace a yayin da yake ta kore kwalla da yatsansa. Dariya Baba Hadir yayi ya taso suka sake rungume juna.
Excellency yaji suna kara burge shi "ina zaune ana nuna min wariya. Ai shikenan ba fushi zanyi ba bare na barku. Nema kuke ku nuna min ku ukun kunfi shakuwa ni dan karo ne"
Major ya kwashe da dariya saboda yanayin muryar da Excellency din yayi magana da ita ta ban tausayi.
"Dama ka dena damuwa nima ana nuna min amma ya na iya they are my Ladies"
Aka sake yin dariya musamman da Baban Arifah yace shima dole zumuncin nan ayi dashi mai karfi. Kuma da yake shine babba don har Major ya girma a shekaru yace "na dauki matsayin babban yaya mai fada a ji. Idan kuma aka ki ji to fa na iya displine"
Zayyan yana dariya yace "Ka tuna min da 'yan gidanmu Yaya Babba. Ina ta tunaninsu wallahi. Ko yaya Maikudi don yafi kowa baudadden hali a gidan"
Dariyar da suke yi yaji dif ta dauke har ya soma zargin ko rasuwa akayi a gidan nasu.
"Maikudi ya rasu ne? Ku fada min dama nasa rai da ba kowa zan samu a raye ba"
Major ya sake kallon Excellency "to Yaya Babba ai sai kayi masa bayani mu dai babu ruwanmu ko Hadir"
Excellency ya dan dake "wato zamewa zaku yi? Kada ku manta ku kuka fara naku ma harda duka. Ni me nayi Allah na tuba banda dan tsare shi kuma ba ya fito ba last month"
"A fada yadda zan gane ni dai"
Major ne ya soma bashi labarin yadda ta kasance da Mairama bayan an tabbatar da rasuwarsa a wancan lokaci. Maikudi ya handame abinda ya bar musu kuma don karfin hali yayi ta musu kazafin mutuwa ya rabasu da masu taimaka musu.
Iyakar kulewa da bakinciki Zayyan ya kwasa ga tashin hankali da suka ce masa a makance suka dawo suka sami matarsa. Ashar yake nema da zai turawa Maikudi sai dai takaicinsa daya bai ma san wanda ake yayi ba yanzu.
"Kiyayyar da yake min har ta kai ya cutar min da iyali irin haka?" Yace a raunane. "Kuma meye dalilinsa na yi maka karya kaima" yayiwa Baban Arifah tambayar.
"Barni da karamin dan iska, da yaci uban duka cewa yayi fa wai dan firit ya ganni ya zata buzu ne."
Shi ya bada amsa da seriousness amma dariya suka saka ganin yadda yake kosasshen dan siyasa. Ya kuwa hade rai saboda dariyar da suke yi masa.
Su Mami suna ta bawa Ummi baki a daki su kuma a falo sun cigaba da tattaunawa.
***********
Kiran sallar la'asar da aka soma daga masallacin wani gida a nan kusa da estate din inda suke zuwa jam'i shine ya farkar da Awwab da yake baccin wahala a falon Mami. Yunwa yake ji kamar yaci babu, idanunsa suka sauka akan plate din da Radhiya ta rufe akan centre table bayan yayi bacci. Daukowa yayi ko kuskure baki bai iya tashi yayi ba ya shiga ci da sauri. Ko rabi bai ci ba sai amai kamar zai fitar da kayan cikinsa. Ibrahim da Emzee kakarinsa suka ji daga toilet din da yake cikin falon suka fito. Emzee ya tafi zai taimaka masa shi kuma Ibrahim ya tafi gidan Mama dauko mukullin motarta idan abin zuwa asibiti ne su tafi.
Yanayin yadda ya shiga falon da sauri shi ya tada hankalin Radhiya tana gyara hijabin jikinta tayi alwala.
"Ibrahim ya?"
Shima gwanin rudewa ne yana ta bincike a falon yace "Hamma ke amai ban san me ya same shi ba"
"Amai?" Radhiya tace a tsorace tana fita da sauri.
Da shigarta gidan Mami ta hadu da Emzee a falo yana gyara wurin amma bata ga Awwab din ba.
"Adda fita ki koma gidan Mama" Emzee ya umarceta saboda baya so Awwab din ya leko ta ga yadda ya jigata lokaci guda.
"Don Allah Emzee ka barni na gamshi minti daya kawai" kuka yazo mata.