Sashe 109
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cameraman din sai da ya kawar da fuskarsa ya goge ido. Haka Darakta Bigman, Assistant dinsa, Arifa da Radhiya kowa ya zubar da kwalla.
"Kin taba nadamar auren Soja"
"Ko kadan, bana fushi da aikin mijina don nasan ba kowa bane jarumi kamarsa. Damuwata bata wuce yadda rayuwa ta koma mana ba bayan ransa. Mata da yawa da muka rasa mazajenmu ance za'a bamu wani abu to amma lokacin wai babu kudi. Shekaru ashirin da biyu kenan tun ina zuwa Sokoto har na hakura na dena."
Radhiya tace "abu na karshe, kina da wani sako da kike son mikawa ga gwamnatin kasar nan?"
"Ina dashi....KU DUBE MU 'yan Nigeria!....a kullum kwanan duniya ana mutuwa kuma muma din mazajenmu kwanakinsu ne suka kare. Sai dai abin dubawa shine umarnin kasarsu da son kare rayuwar miliyoyin jama'ar cikinta ya kaisu ga rasa rayukansu, su bar iyalai babu gata. Ku tuna da marayu da zawarawan da sojoji suke bari, ku tuna da su kansu sojojin domin damu dasu babu abinda za'a biyamu ya maye mana gurbin kewar da muke kwana mu tashi da ita idan suna bakin aiki. Abu daya kawai nake so shine kasarmu ta dena mantawa damu da sadaukarwar mazajenmu. Bakunan al'umma su rinka yi musu addu'a a duk inda suke domin su sake samun kwarin gwiwar yin aikinsu."
"Maman Dolapo mungode"
"Mune da godiya"
Ana dauke camerar daga kansu Radhiya taje ta rungume Maman Dolapo tana hawaye. Wai a haka ma don matar ta sakaya wasu abubuwan ne.
Kafin su tafi envelop ta dauko a cikin jakarta. Sakon Ummi ne a ciki na dubu hamsin ta mikawa Maman Dolapo da kuma katin da aka buga da wuri na walimar da suka shirya ta dawowar Zayyan domin ta bawa matan wadanda suka zauna tare. Dubu dari dama Ummi ta ware musu ita da Christie saboda idan ka cire su Mami bata da tamkarsu kuma a zamansu na barrack din.
Washegari gidan wani soja mai konanniyar fuska suka je. Duka duka bai fi shekaru talatin da biyu ba. Nasa labarin ma ya tabasu inda yace an tura shi aiki ne cikin garuruwan da ake yawan rikici. Wataninsa bakwai ya dawo gida bayan wata biyar da dawowar tasa matarsa ta haihu. To ba shiba kusan kowa ya tabbatar jariri ba nasa ba. Mata da ta ga an ganota tace laifinsa ne baya bata kulawar da ta dace. Tun aurensu sau nawa ya taba yin wata guda tare da ita. Yayi bakincikin abinda tayi masa iyayensa suka raba auren ya sake tafiya aiki. A can kuma wuta ta kama a wani ginin maaikata bayan rikici ya balle suka je kai dauki. Nan ya kone sosai da kyar aka samu ya rayu amma rabin jikinsa da fuska sun kone. Aikin da yake ji dashi dole ya hakura sannan shekara biyar kenan duk inda ya nema ya rasa saboda munin halittarsa. Babu wanda yake tunawa da cewa mutum shida ya tseratar daga gobarar nan kafin zuwan motar kwana-kwana. Lokuta da dama ji yake inama ya mutu ya huta da kyamar da al'umma suke nuna masa.
A tsukin kwanaki goma su Radhiya sunyi yawo a garuruwan Nigeria lungu da sako suna hira da sojoji ko iyalansu. Kuka kam ba'a cewa komai. Darakta Bigman ya ga wani salon rayuwa da basu taba sanin akwai ba. A irin yawon sun hadu da matan da suka yi sa'ar samun wani abu na kyautatawa daga daga dangi ko abokai ko kuma cikin abinda ake bawa mazajensu daga wurin aikin. Sai dai da yawansu babu abinda yake daga musu hankali kamar kewar mazansu na bakin aiki ko wadanda suka rasu. Abin da ban tausayi matuka. Masu nakasar dole a dalilin rashin wata gaba da suka yi a bakin aiki su ma tasu rayuwar yana cikin garari. Da dama cikinsu kuma sai su kasa rungumar wani aikin saboda tsaro suka sani shi su ka fi iyawa. Tafiya ce irin wadda ake kira mabudin ilimi suka yi.
Wuri na karshe da suka je shine garin Onitsha (Onicha) wurin Christie. A wata makarantar kwana ta 'yan mata suka sameta inda take aiki a matsayin malamar Geography. Christie tayi kukan sake ganin Radhiya sai da ta hadasu a waya da Ummi kamar yadda ta hadasu da Maman Dolapo. Ta amsa tambayoyin da Radhiya tayi mata inda take tambayarta yadda ta sami kanta a aikin koyarwa.
Sa'arta daya sai da ta hada NCE dinta sannan tayi aure. Bayan labarin mutuwar mijinta ta koma gida ashe tana da ciki. Da Radhiya da camera man suka bita cikin gidanta da tace su shigo. Kofar wani daki ta bude yarinya budurwa na kwance tana bacci ga kafafunta a lankwashe.
"Rebecca sunanta. Kashinta bashi da kwari bata tafiya ga matsalar kwakwalwa. Saboda ita ban sake aure ba ga rashin kudi da kyar na sami wannan aikin na koyarwa. Matsalar farko da na fara samu shine rashin mai kula min da tunda bani da kudin da zan biya mai raino. Wurin aikin suka ce na dena zuwa da ita a bayana lokacin tana da shekara goma na fara. Nasan wasu zasu daukeni mara imani amma bani da yadda zanyi. A gida nake kulleta naje aiki na dawo in tarar tayi kashi da fitsari. Ko ta mirgina inda zata iya jin ciwo daga baya na soma daureta idan zan fita shima da kaina naga rashin dacewarsa. Shine fa nake takura mata na hanata baccin dare har ta saba sai da safe tayi har naje na dawo. Albashina dashi muke cin abinci da sayan magungunanta duk sati. Rayuwarta akwai tsada sosai shiyasa na kasa daukar mai aiki har yanzu"
Dole mai imani ya zubar da hawaye idan ya ga rayuwar Christie da 'yarta. Itama dubu hamsin Radhiya ta bata inji Ummi da katin gayyata.
An sha wahala amma ana fatan bukata ta biya. Tare suka koma Abuja harda Darakta Bigman saboda zai duba video din gabadaya bayan an gama editing. Arifah da Radhiya kamar kada su rabu ance sabo turken wawa. Gashi dai suna gari daya amma saba su kwana daki daya suyi komai tare. Kafin ayi bacci kuwa kowacce zata raba lokaci da masoyinta idan an kare su koma hirar samarin nasu suna dariya. Kwanaki bakwai ya rage mutan Nijar su zo kawo gaisuwar Arifah. Yousuf kuwa jiransu yake yi su dawo dama ya taho domin kara gina kansa a zuciyarta.
Kowacce ta shiga motar da mahaifinta ya turo daukarta. Cameraman da Bigman motar su Arifah suka bi za'a saukesu a hanya sai jibi idan sun kammala aikin hadawa zasu je gidan Major General Zayyan.
A guje Radhiya ta shiga gida ta kwakume Ummi tana murna. Itama Ummin tayi kewarta sosai gidan kamar ba shi ba. Zayyan da taya bera bari kuwa dagata yayi yayi juyi da ita ai kuwa yasha nishi. Ummi ta rinka dariya. Abinci taci sosai Zayyan yana ta tausayinta wai ta fada tana gamawa tace bacci zata je tayi sai jibi da safe a tasheta.
"Ana la'asar zaki ji bugu idan baki tashi ba" cewar Ummi
"A tasheni sallah amma banda cin abinci. Na gaji sosai Ummi"
Tana sauke hakarkatinta akan gadon sai bacci kamar an jibge kayan wanki. Da kyar take tashi tayi sallah ta koma. Bayan isha ne Daada yace Ummi ko kunu ne ta dama mata baya so ta kwana da yunwa.
"Sai kace wata jaririya..idan taji yunwa zata fito ne"
"Ni dai ki dama don Allah. Baki ga yadda tayi zuru zuru ba kin kuma san meye a gabanta. Ni bazan kai 'yata gidan miji a bushe ba azo ana mata gori"
"Oh ni Mairama, waye zaiyi mata gorin?"
"Awwab mana. Yanzu tana murmurewa a gidansa zai ce kamar ba ita ya dauko a bushe ba."
Tafa hannuwa ta shiga yi tana dariya "Wannan uban amarya mun ga ta kanmu."
Lallabata ya koma yi saboda da gaske yake dan wuya ya gani ta fara yi saboda rashin hutu "taimaka kinji 'yar albarka Mairama baiwar Allah"
Ba yadda ta iya haka taje ta dama kunun gyada ta tafi dakin. Wata irin kwanciya Radhiya tayi a wargaje tsabar ta tara gajiya a jikinta. Ummi kuwa ta sakar mata duka a cinya ashe Zayyan ya gani "A'a Wallah ki bari fa. Daga cewa ki bata kunu sai cin zali"
"Dubi yadda ta kwanta fa"
Murza idanu Radhiya take yi ta tashi tana tura baki "Ummi me nayi?" tace cikin magagi.
Zayyan karasa shigowa yayi ya zauna a gefen gadon kusa da ita "tashi kisha kinji Innata kada ki kwana da yunwa"
"Na koshi" tace da kyar idanunta na rufewa.
Allah Sarki ji yayi bazai iya bari ba yana tausayin 'yar tasa. Da tare dashi suka girma Allah kadai Yasan irin yadda zai shagwaba kayarsa. Gyara zama yayi ya dora kanta a kafadarsa idanunta a rufe "rinka bude bakinki kinji Alheran sai Ummi ta baki"
Baki Ummi ta wangale ta ma rasa me zata ce masa. Wannan sangarta har ina. Shi kuwa kiss ya hura mata wai ta rufe bakin ko ya matso. Daure fuska tayi tana nuna masa Radhiya dake zaune kanta a kafadarsa ido a rufe.
"To ki bata ko yanzu..."
"Naji, naji. Ke bude baki ko na kwara miki kowa ya huta"
Da rarrashi Zayyan ya samu take bude bakin Ummi na bata yana shafa mata baya har ta shanye. Ta bude na karshen Ummi tace "ai sai ki rufe bakin ya kare"
Zamewa ta soma yi zata kwanta Zayyan yace ta dan yi hakuri ko yaya cikinta ya sassauta. A daddafe tayi minti biyar sannan ya gyara mata kwanciya ya kashe fitilar dakin sannan ya rufe kofa yana dariya shi kadai.
"Kalau kuwa Sojana"
"Lafiya kalau...yau dai mafarkina ya tabbata. Kin tuna na taba ce miki ina son komai na Alheran ayi dani. Ko wanka kike kyuyar yi mata ni zanyi saboda bana son missing komai na rayuwarta tun kafin cikin Zayyan. Na rasa abubuwa da dama amma kafin ta koma hannun Awwab sai dai ku rufe ido"
"Sojana ba fa babyn da ka tafi ka bari bace. Kaima duk ka wani tsufa shine zaku yi mana kara'i"
"Ba don kada abin nawa yayi yawa ba har goyata sai nayi"
"To ni a goyani mana" suka ji Emzee yace yana hawowa saman saboda bai ga kowa kasa ba.