← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 157

Sashe 115

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan magariba Radhiya ta dora girkin da Tante tace tayiwa Awwab Emzee da Ibrahim suka zo dauka. Farar shinkafa ta dafa masa tayi shar da ita sai dai baifi minti biyu ya rage ta kwashe ba ta juye mata alayyahu madaidaici a ciki. Gyareshi tayi amma bata yayyanka ba a haka tayi amfani dashi bayan ta cire shi. Ba kuma tsigar nan ta ganye kawai ba, ta hada ne harda itacen inda yayi karfi da yawa kadai take yankewa. Yau dai tayi kamar na mutum biyar ne tunda tasan su Yousuf na gidan. Miyar kuwa farfesun kaza ne da ta barshi ya danyi kauri an yanka dankali amma da girmansa a ciki da caras shima da dan girma sai koren wake. Rahima, Zayyana da Hibbah suna makale wurin koyon girki tayi ta gama. Sai da ta dibar musu suka sama mata lafiya. Ibrahim ne ya fara zuwa kitchen din yace Zayyana tazo ta bashi labarin Khaleel. 

Radhiya da bata gano komai ba tace "ashe dai zatona ya zama gaske da nake tunanin ko saurayinta ne kusan kullum sai ya kirata sai ta gudu don kada muji me ake cewa"

Kashewa Zayyana ido yayi da take ta jin kunya Hibbah da Rahima sun san komai shiru kawai suke yi "zan binciko mana shi Adda Amarya muna zuwa"

Bai yarda ya fita ba sai da ya sakata a gaba. Rahima ce take ta yiwa Radhiya tambayoyi suna tsaye ita da Hibbah ita kuma tana wanke kwanukan da ta bata Emzee ya shigo. Bata ganshi ba sai alama ya yiwa Rahima da suyi shiru. Ido ya rufe mata ta baya sai dai jini baya buya tuni ta gano rabin jikinta ne Zayyan dan Zayyan. Rungume juna suka yi tana ihun murna don har ta fitar da ran zai zo saboda tasan tsananin makarantarsu.

Ya wani kara budewa ya kereta tsaho sosai yana mata dariya ya dan duku kansa "ashe nayi missing dinki Addata yau gaskiya kwanan hira zamuyi kafin Hamma ya daukeki, na fasa bin Ibrahim ma"

"Ka manta ko an daura ina gida har sati biyu?"

"Eh to idan ya bani damar hirar kenan. Muje dakina kiga wani abu"

Suna juyawa Hibba tace "Ya Emzee ina wuni"

"Lafiya kalau mai tale baki number two"

Dariya tayi za ta fita taji Rahima tayi mata wani irin riko tabi bayanta da sauri. Radhiya tayi saurin cewa Emzee ga Rahima tana dakatar da ita su gaisa.

Haba Rahima idanu tuni sun raina fata ashe tunda ya shigo ta tabbatar shine sojan taji cikinta ya kulle saboda girmansa da ta gani. Sai yanzu ya kula da ita a zatonsa 'yar uwar Hibbah ce ko wata dai cikin bakin biki ya saki fuska zai amsa gaisuwar da tayi masa a tsorace suka hada ido. Wani irin yanayi ne da bai taba zato ko tsammani ba ya fizge shi a take a lokacin ya fadada murmushinsa gareta yanayin idanunta tamkar wani maganadisu ya zame masa.

"Kinyi kama da matsorata, yaya sunanki?" Ya tambayeta a kasalance.

Yawu ta hadiya tace "Rahima"

"Rahima zaki zama kawar soja?" ya sami kansa da cewa babu wani tunani.

Duka Radhiya ta kai masa a baya ganin idanun Rahiman sun kara girma duk ta firgice "kada ka tsorata min kanwa dama har yanzu bata sakewa idan Daada ya shigo."

Tana ganin Radhiya ta dauke masa hankali ta fita da sauri ta riga Hibbah zuwa daki. Sai da ta rufe kofa ta soma sauke numfashi da sauri da sauri. Tunda take bata taba ji ko ganin wani abu da ya kwashe mata nutsuwa kamar wannan bawan Allah ba. Danganta abin tayi da tsoron sojoji da take yi ta kai hannunta kirji tana jin yadda zuciyarta ke bugawa.

A kasa kuwa kafin su bar kitchen din Ibrahim ya shigo yana kiran Emzee dreban da zai dauko Awwab motar ta lalace a hanya Raji kuma da yake gida bai san gari ba shine Ummi tace suje su dauko shi. Shi dai Emzee so yayi ya zauna a kira masa yarinyar nan mai idanu bai gaji da kallonta ba.

Da abincin da Radhiya tayi a motar suka je dauko shi. Ibrahim kasa hakuri yayi sai da yace masa yayi jiki saboda aikin nasa yafi yawa a zaune gashi babu inda yake zuwa daga gidan da ake basu kamar hostel idan baka da ra'ayin kama wani ko kana da naka sai office din nasu. Murmushi kawai yake yi yana jin kewar Radhiya amma dare yayi ana neman shabiyu gashi jirgin safe zasu bi zuwa Jos saboda karfe biyu ne auren kuma suna tare da ango. Wanka kawai yayi da sallah yaci abincin nan sosai tare dasu Raji suka kwanta a gajiye bayan ya tura mata text din godiya tunda taki daukar wayar tasa. Ya dena damuwa don ya ma fi son haduwarsu ta gaba da amsa sunan matar Awwab. 

Da safe kuwa ba a nutse suke ba anata shiri. Duka  kayan da zasu saka na daurin auren a jaka suka saka su. Suka wuce airport mota mota sai Jos. Karfe biyu da 'yan mintuna bayan sallar azahar Major General Zayyan Tureta ya karbi sadakin Arifah daga hannun kanin Alh Mousa naira dubu dari da dalleliyar mota. Nan da nan jama'a suka shaida auren Yousuf da Arifa abinda wata uku da suka wuce ko sanin juna basuyi ba bare suyi tunanin wannan rana. His Excellency the Executive Governor of Plateau state Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ya tara jama'a sosai 'yan siyasa manya a wannan taro mai dumbin tarihi. Ansha hotuna a ranar biyar na yamma suka sake dagewa sai Birnin Shehu. Ga gajiya an dauko ga wata za'a sake dauka gobe. 

Hotel da wani guest inn Zayyan yasa yayunsa kama dakuna da dama saboda yayi mamakin jama'ar da suka zo wannan aure. Da wuri ya biya kudin masaukin saboda haka basu sami wata matsala ba. Mutanen Katsina gayya guda sai kayi mamaki kamar ba su bane masu cewa dole Awwab ya auri 'yar uwarsa don duka kakanin Awwab sunzo su ukun. Malamijo da 'ya'yansa maza kananun ne kadai babu amma ya dauko kowa ga kannensa suma motoci suka ciko da mijin Nene. Ga jama'a guda daga Nijar wadanda suka halarci auren Yousuf jiya. Daga Rugar Barkindo Ardo, Baffa Gide, Baffa Habubakari da su Zakari kusan kowa yazo shaida auren 'yar soja. Mutanen Tureta da su Alh Salisu da duk wanda ya kamata sun zo. Chibuzor dashi aka daura na Arifah kuma yau ma yana tare da babansa Zayyan shima zai shaida. Karfe goma na safe aka saka saboda masu komawa a ranar su iya tafiya. Kusan ma dai kowa juyawa zaiyi suna sa ran da an daura anci abinci a fara tafiya.

Zuwa lokacin Zayyan ya ciko sosai don Mairamansa ba da wasa ta tasarma fito da mijin nata ba. A babban masallacin juma'ar unguwarsu da yake bakin titi za'a daura auren. Wata hadaddiyar mota ce ta tsaya a harabar masallacin sojoji suka yi dafifin kare shugabansu. Mutum uku ne suka fito daga motar wata shadda suka saka iri daya ruwan zuma mai dan karen tsada. Dinkinsu da komai hatta hula da takalmi basu bambanta ba. Suna fitowa aka fara daukarsu a hotuna tun kafin su karasa ciki. Uban gayya ne Major General Zayyanun dan mutan Sakkwato yana ta murmushi kamar shine angon. Har yau da yake shirin aurar da 'ya bai dena tafiya da hankulan mata ba. Daga gabansa rike da wata sanda mai kyau domin samun balance din jiki Daddy Rtd Major Mustapha ne mutumin Katsinan Dikko kunya gareku ba tsoro ba. Kamilin mutum msi tafiyar da komai cikin tsari da haiba. A bangaren damansa kuwa aminin kwarai ne wanda abotarsu ta zame musu 'yan uwantaka Rtd Lt Hadir gaisuwarsa daban take jinjina ga dan mutan Kanon Dabo mai dutsen Dala da Gwauron dutse, Kano ko da me kazo an fika. Hadir Murtala abokin da Zayyan Tureta wadanda sukayi zamani a matsayin zaratan jaruman samari kyawawa. Su ukun nan tarihin rayuwarsu abin duba ne domin kada duniya ta manta da soyayyarsu da sadaukarwa domin kasarsu domin abotarsu. Taku suke maza 'yan uwansu na waigensu domin sun isa a dube su din. Cikin masallacin suka shige ana ta gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.

Daga waje mintuna kadan bayan shigewarsu wata motar ta iso Awwab ya fito rike da waya a hannunsa yana sanye da shadda fara kal wadda aka yiwa aiki da zare ruwan toka msi duhu. Hula da takalminsa kalarsu daya da zaren sai agogo da links din hannun rigar duka silver masu kyau. Saboda kurewar lokaci ranar da zai taho yayi aski saisaye aka yi masa wani irin gyaran fuska da ya fito da gajeren kwata miliyon dinsa. Matashi ne ajin farko mai tattare da nutsuwa da kamala. Kallo daya za ka yi masa  kasan cewa yau din ta dabance a wurinsa ranar aurensa da Alheran dinsa. A gefensa angon jiya ne Yousuf bayansu kuma Emzee da Ibrahim sanye da wani ubansun yadi da Mama ta dinka musu. Su dinma kamar iyayensu daga sama wato hula har takalmi babu ta inda su ka bambanta komai. A tare dasu Halifa ne shima ya fito fiye da zato. 

A cikin masallacin kuwa wakilan ango da amarya aka nema Hadir da Zayyan su ka matso gaban limanin suka zauna a kusa dashi.  Yadda yake a tsarin musulunci haka aka gabatar da komai inda Hadir waliyin amarya ya karbi sadakinta naira dubu dari daga hannun Zayyan waliyin ango. Addu'a aka yi aka shafa Captain Muhammad Awwab Mustapha ya zama mijin Alheran Radhiya Zayyan Tureta. 
Chapter 115 · 0% Book details