← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 157

Sashe 29

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mairama ta fusata ta fara wawurarta "Karami dauko min yayarka ko ka janyo min ita. Yau tambotsan nata harda iyayena kuma"

A guje ta tashi "Ardo don Allah ba Innawuro ce ta fada ba."

Innawuro ta dauko muciya "bari na mulmule ki kema sai aji dadin kiranki jikarta"

Hanyar waje tayi tana gudu wai ita gidan Malamijo zata koma.

Mairama ta daure fuska "da ya fi miki mu ma mu huta. Kuma karatu ki ma fara shiri sai kinyi"

Dawowa tayi da baya tana murza yatsan kafarta a cikin kasa tana tura baki "to don Allah ki kaini soja irin na babana indai kina so nayi karatu"

Gaban Mairama ne ya fadi ba shiri sai ga hawaye. Innawuro da ta dauki abin wasa tana biyewa Radhiya ta shiga bata hakuri tasan bazai wuce mijinta ta tuna ba.

Radhiya ma sai ta soma kuka tana cewa tayi hakuri zata yi karatun ko wanne ne.

**********

Alheran Radhiya Zayyan Tureta irin fitinanun daliban nan ne marasa tsoro ga kin ji. Duk inda akace 'yan aji daya sunyi laifi to in sha Allahu Radhiya tana cikinsu. Kan kace kwabo tayi kaurin suna tsakanin dalibai da malamai. Kirikiri tace sunanta 'Yar soja haka babanta yake kiranta daga Mairama ta bata labari. Shikenan makaranta suka santa da wannan sunan. Anyi sa'a tana dan taba karatun babu laifi. 

Wata rana suna layin dibar ruwa suna ta hayaniya irin ta 'yan makaranta ta dage tana ta zuba.

"Allah Ya kaimu siniya wallahi zan warwasa a makarantar nan. Duk wasu jiniya a lokacin sun shiga talatin a hannuna"

Kawarta Ruqayya tace "ke 'Yar soja so kike yadda muke tsinewa su senior Jummai kema a tsine miki?" 

"Ke baki gane ba. Lokacin kannen su senior Jummai mai tafiyar agwagwa ne a makarantar. Ramuwa zan zauna yi"

Wata tace "ai kuwa nima zan so, rannan fa kwai tace nayi mata a karkashin gadonta"

Radhiya ta daka tsalle "inama nice wallahi, na samu na sassaka mata kashi mai waaaaaari"

Dariya suke duniya sweet kampo sai ga senior Jummai ta taho da tafiyar catwalk dinta da su Radhiya suke yiwa lakabi da tafiyar agwagwa. Ta gama jinsu tsaf suna bayan ginin da famfon yake.

Idonta ya kyallo mata ita sai kawai ta canja hirar amma saboda tsoro muryarta har rawa take yi.

"Allah Yasa senior Jummai tace in zama daughter dinta a makarantar nan. Daga ranar wanki da debo ruwanta duka zan rinka yi"

Sauran sai suka fara mamakin me take nufi tunda dai haduwa suka yi ana zaginta. Yadda tayi  maganar ne idanu har sun ciko da hawaye yasa Jummai da sauran seniors din dariya. Kawayen Radhiya ciki ya duri ruwa. Ita kanta a tsorace take. Jummai ta dafa kafadarta kamar ta saki fitsari don tsoro sai ji tayi tace daga yau kada wani ya sake ko da aiken daughter dinta ne.

Kowa yayi mamaki harda kawayenta tace Radhiya tana burgeta saboda ko me za'ayi mata sai ta aikata abinda tayi niya. Idanunta kawai zaka kalla kasan fitina da rigima suna dawainiya da ita.

Wata kungiya da aka bude a makarantarsu SS wato School Soldiers a nan aka samu kanta. Da jikinta da zuciyarta take wannan aikin na kare hakkin dalibai. Gashi da kayan makarantarsu riga da zani ne amma an basu hula irin ta sojoji mai lankwashewar nan suna sakawa akan hijabansu. Radhiya jin kanta take kamar sojar gaske. An kamanta gaskiya da amana sannan an gurji seniors masu hana sababbin dalibai sakat. Idan kaji ana Officer 'Yar soja a makarantar zaka rantse wani babban soja ne saboda yadda ake shayin shiga tarkonta. Zaman SS shine babban jindadinta a makarantar.

A haka aka yi karatun cikin ikon Allah tayi nasarar fita da credit bakwai. Emzee kuma duka taran ya haye. Sai dai ko kadan a yadda ilimin ya tabarbare bazaka hada makarantar gwamnati dake kauye da wadda take birni ba.

***

Tana jin shigowarsa dakin nata tayi saurin rufe ido kamar mai bacci. Murmushi kawai yayi yana kada kai. Zainab bazata taba canjawa ba indai tare dashi ne. Shekarun da suka yi a matsayin ma'aurata bai sa ta canja komai daga yadda ta faro ba. Akan doguwar kujera irin ta hutawar nan ta dakin ya zauna sannan ya soma yi mata magana.

"Tashi magana zamuyi"

Kin motsawa tayi sai da taji yace bari ya hawo gadon ya tabbatar ko idonta biyu.

Juyowa tayi a hankali tana jin kunyar ya gano karyarta. Bata son yadda take yiwa Musa amma zuciyarta ta kasa rissina.

"Shawara nazo nema"

"A wurina?" Ta tambaya mamaki yana bayyana a fuskarta.

"Eh, aure nake son karawa sai dai na kasa tsayar da shawara akan na dawo da mamansu Aisha ko na auro wata daban"

"To ni me kake so nace? Ka auri wadda tafi kwanta maka"

Fuskarsa ta nuna ba haka yaso ba kuma shima bai boye ba yace "zan so kiyi min rigima irin wadda kowace mace take yiwa mijinta a lokacin da ya tashi yi mata kishiya"

Cikin yanayin rashin damuwa don har ranta ita bata ga abin rigima ba tace "saboda me?"

"Saboda nasan cewa ko yaya Zainab ta damu dani kamar yadda na damu da ita. Sai dai nafi kowa sanin zaman hakuri kike yi a gidan nan. Na tauyeki na hanaki walwala da jindadin zama da wanda kike so"

An tabo inda yake mata kaikayi sai hawaye sharrr tana gogewa da bayan hannunta. 

Musa yana jin kukan har ransa amma yasan ba nasa bane na wani ne "kinyi hakuri sosai Zainab, naso ace mun haihu don in samu abinda zan cigaba da garkuwa dashi in ki rabuwa dake amma Allah bai kawo ba. Sai nace zan barki ko don su Aisha. Yanzu kuma gashi suna shirin aure nan da watanni kadan. Ina ganin kamar bani da sauran dalilin cigaba da zama sanadin kuncinki"

Kukan Zainab sai ya koma mai sauti. Tana tausayin Musa bisa soyayyar da yake mata. Tayi iya yinta amma zuciyarta taki amsarsa a matsayin masoyi. 

"Kayi hakuri da dukkan bata maka da nake yi, zanyi kokarin gyarawa"

Murmushi yayi mata yana mika mata takardar hannunsa "ni na gyara mana matsalar ina fata Allah Yasa nayi abinda ya dace. Zainab na sakeki saki daya"

A gigice ta kalle shi hawayenta yana karuwa. Idan ya saketa fa kenan babu sauran shamaki tsakaninta da Hadir. A gaggauce ta bude takardar sai ta kula guda uku ne a hade da stapler. Daya takardar saki, daya check na miliyan biyu, dayar kuma takardar mallakar wani gida ne a Kano da ya saya mata dan madaidaici. Dago kai tayi sharbe da hawaye harda majina.

Cikin nutsuwarsa yake magana daki-daki "tukwicin kulawar da Aisha da Anisa suka samu daga gareki ne. Bana son fada amma yabon gwani ya zama dole. A kanki na yarda ba sojoji bane kadai jaruman kasata harda matansu. Soyayyarki ga baban Ibrahim ita tafi komai kara miki kima a idanu na. Nayi zaton kudina zai sa ki manta da wanda yake talaka mai nakasa amma bakiyi ba. Kin so zama da mutumin da bautar kasa ta nakasa farincikinku domin cikar soyayya. Nagode da lokacinki da kika ara min muka zauna tare"

Maganganun sunyi mata tsauri sun taba mata zuciya. Tashi yayi zai fita Zainab ta taho da sauri ta rungume shi tana kuka. Bata taba yi masa haka ba idan ba shi ya nema ba sai yau.

"Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min Abban Aisha. Ka yafe min duk laifukan da nayi maka a zamanmu tare"

Dago kanta yayi kana ganin damuwa a cikin idanunsa "yanzu dai ki soma hada kayanki kafin na chanja shawara"

Da hawayen take murmushi "nagode"

"Nima nagode" yace ya sa kai ya fita yana jin a ransa kamar an sauke masa wani kaya mai nauyi. Ya dade yana tsoron hakkinta kada ya kama shi saboda son zuciyarsa yau Allah Ya bashi iko ya rabu da ita ba don yana so ba.

Ajiyar zuciya ta saki bayan fitarsa ta mika godiyarta ga Allah sannan cike doki ta kira Ibrahim.

Labaran tara na NTA ya kunnawa Hadir yana gefe game ya dauke masa hankali a wayar kiranta ya shigo. Murmushi yayi ya dauka.

"Hello Mama"

Hadir ya juyo ya kalle shi sai kuma ya dauke kai. Ina ma zai iya tambayar lafiyarta da yayi. 

Daga daya bangaren tace "Ibrahim yaya su Umma?"

"Lafiya kalau, ya su Anti Anisa da Baba?"

"Su ma lafiya kalau. Ibrahim nace me kake so gift din graduation ka ki fada min kamar wata surukar ka ko, na kula ko hira baka son yi dani" tayi karamar dariya.

"Ina naga fuskar" yace a zuci. Ita da bata sakin jiki da kowa bare ayi batun hira. Daga gaisuwa sai ta fada kogin tunane tunanenta ta bar mutum zuru. Yana mamakin yadda idan yaje hutu take hira da su Anisa duk da ba wata hirar kirki suke yi ba.

"Ya kayi shiru ne?"

"To kiyi hakuri zan gyara"

"Shikenan, ina babanka?"

Hadir ya kalla suka hada ido. Anya Mama ce kuwa yace a ransa. Bata taba tambayarsa babansa ba sai su Umma kawai.

Kara kashe shi tayi da wani mamakin ta hanyar cewa ya dora masa wayar a kunne "saura ka sani a speaker"

Bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba. Wai dama Mama ta iya wasa haka? 

Hankalin Hadir gabadaya yana gare shi sai kawai ya dora masa. 

Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta da taji sautin numfashinsa. Soyayyar da ta dade tana dannewa ce ta taso mata. Da suna tare yanzu shekararsu goma sha tara da aure.

Cikin wani yanayi na shauki da begen da yake nuna soyayya bata tsufa tace "Hadir"

Allah Sarki rayuwa, yaji sunan har tsakiyar kansa amma bazai iya amsa mata ba.

"ASTAGFIRULLAH" tace da sauri ta katse wayar. Shaf ta manta cewa har yanzu tana karkashin Musa har sai ta gama iddah. Tashi tayi ta bude wardrobe ta dauko akwatunanta.
Chapter 29 · 0% Book details