← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 157

Sashe 70

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kamar yadda kuka sani sati biyar da suka wuce an sami gobara a daya daga cikin hostels dinmu sanadiyar konewar socket. Babu wanda yaji ciwo duk masu 'ya'ya a wannan hostel din sun sani. To amma abinda da yawanku baku sani ba shine waye ya yi sanadiyar ceton rayukan mutum sama da hamsin single handedly. Nafi kowa mamakin jarumta da kaifin tunani na wannan yaro da yake shekararsa ta farko a makarantar nan. A lokacin da kowa yake gudun ceton nasa ran wannan Cadet din ya koma ya rinka buga kofofin dakunan wadanda basu sani ba saboda abin ya faru cikin dare ne. Bai tsaya a nan ba duk da kiran da abokansa da malamai keyi yaje inda fire extinguisher take da zafin wuta da hayaki da komai ya cirota ya tsaya a kofar dakin da wutar ta fara ci yana kokarin kashewa yana kuma commanding sauran 'yan uwansa cadets da su bi dakuna su tabbatar kowa ya tashi." Yana kaiwa nan yayi musu alama da hannu "Please lets all stand in honour of Cadet Muhammad Zayyan Tureta"

Baba Hadir ne ya fara tashi zumbur da yaji an kira sunan dansa. Ummi kam tamkar ta saka ihu duk da ance sati biyar kenan da yin gobarar. A tunaninta Karami ya dena miskilanci ashe abu irin wannan zai faru ya boye mata? Bata san lokacin da ta soma hawaye ba. Major bai tuna kowa ba sai nasa Zayyan din. Karin maganar bahaushe ya tuna da ake cewa barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba. Duka duka Emzee shekarunsa da yasan ya koma ceton rayuwar wasu.

His Excellency Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ji yayi tamkar an saukar masa da guduma a tsakar kansa. Kunnuwansa sun jiye masa da kyau kuwa? Ya san  nasa Zayyan Muhammad Tureta din yau kuma yaji ana kiran Muhammad Zayyan Tureta. Me yake shirin faruwa ne? Bai karasa tsinkewa da lamarin ba sai da kyakkyawan matashin mai dauke da fuskar da ko yasha giyar wake baya jin zai taba manta ta ya taso cikin shigarsu da dalibai wato cadets da hularsa a karkace yayi matukar kyau ya hawo kan stage din inda Minister of defence zai bashi kyautar Cadet of the Year.

Emzee kenan, yasan da award din shiyasa ya matsawa Umminsa dasu Daddy akan su zo domin yayi surprising dinsu.

Excellency fa sai yaji tsayuwa tana neman gagararsa ya lalubi kujera ya zauna kansa ya daure gabadaya. Masu hoto suka yi caaa akansu lokacin da Minister yake baiwa Emzee award din. Da murmushi a fuskarsa ya rinka baza idanu har Allah Ya bashi ikon hango iyayensa. Daga kambun da aka bashi yayi ya nuna shi saitin inda suke yana kara fadada murmushinsa.

Sosai ya burge Minister ya dafa kafadarsa suna tsaye a gaban loudspeaker yace "Cadet baka da abin cewa?"

Wadanda suke kusa zasu iya ganin kunyar da ta bayyana a fuskar Emzee. Duk da haka ya dan saita bakinsa a jikin speaker din yayi godiya ga Commandant dinsu, dukan mutanen academy din sannan ya kare da cewa "I dedicate this award to my late father LT. ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"

Ummi kuka Mama kuka suka rungume juna. Kukan farinciki, famin ciwo da kuma tsantsar godiya ga Allah akan kowane yanayi take yi.

Emzee zai sauka daga wurin har lokacin baiyi nisa da speaker din ba ga mamakin dumbin jama'ar da suke wurin yaji hannu ya sauka a kafadarsa an damke shi. Da sauri ya juyo ya ga mutumin da aka kira da gwamnan Plateau ne sai yaji ya firgita.

Idanun Excellency sunya ja sosai hankalinsa tamkar baya jikinsa yace "sunan mahaifinka Zayyan Muhammad Tureta?"

Emzee ya gyada kai a dan tsorace. Ummi tashi tayi daga seat dinta tana jin me yake fada tana kuma tsoron ko dan nata yayi laifi ne.

Kwalla ce Emzee ya tabbata ya gani a idanun Gwamnan sai kawai ya rungume shi a bainar jama'a. Commandant din yana ganin haka ya kira wasu da zasu jagoranci taron shi kuma ya duka kadan yadda Excellency din zai ji yace "kana bukatar kebewa tare da yaron ne"

"Kwarai kuwa dan kanina ne, zaku iya bashi pass na kwana daya? Shekaru sama da shabiyar nayi zaton sun mutu"

Sai da Commandant din ya girgiza da jin wannan magana daga bakin Gwamnan yace su tafi. Emzee yaji mamaki matuka da furucin mutumin nan. Yana rike da hannunsa motocin suka yo gaba aka fara sakin jiniya suka sauka Arifah tana take musu baya itama mamaki ya kamata. Da sunan Zayyan Tureta a bakin mahaifinta ta girma yau ace ga dansa bayan Dad din da kansa yace mata iyalinsa sun mutu. 

Kafin su shiga motar Ummi tayi gaba hankalinta a tashi Gwamnan garin da ba nasu ba kuma basu da mahadi dashi yayi mata gaba da danta. Major da Baba Hadir suka nufo stage din aka nemi hanasu hawa. Daga murya yayi yace "danmu ne aka tafi dashi kuyi mana bayani."

Commandant sai ya zaro waya ya nemi PA din gwamna ya sanar dashi ga iyayen yaron fa.

"Fada musu guest house din da zamu je. Ina bukatar magana dasu privately."

Ibrahim ke jan mota daya dreban Daddy yana jan dayar suka bi bayan motocin. Dakatawa ma akayi suka shiga tsakiyar convoy din sannan suka wuce cikin garin Kaduna. Wata unguwa da ta yi nesa kadan da hayaniya ga maka makan gidaje suka je. Emzee ya dena tsoro sai mamakin yadda tunda suka shiga motar Gwamnan yake rike da hannuwansa yana kallonsa yana murmushi ya kasa cewa komai. Abin ne da matukar mamaki da daure kai. Dan Zayyan dinsa ne yake gani a gabansa.

Sun shiga harabar gidan aka fito daga motoci. Excellency yana rike da Emzee su Ummi suka firfito daga mota yana jiransu. Kan kace meye wannan an bude gidan da ya wadatu da kayan alatu. Arifah da PA dinsa ne kadai suka bisu cikin wani wawakeken falo. PA din yace su zauna amma duka hankulansu basu kwanta ba sai da gwamnan da kansa yace su zauna. Tambayar farko da ya fara watso musu ita ce "ina Alheran?"

Idanu ya ga sun dora masa kawai yayi dariya sosai ko ya tsorata su ne? Farinciki ne ya cika masa ciki da zuciya tamkar kirjinsa zai fashe.

"Bari na faro muku daga farko dai. Sunana Nasiruddeen Aliyu....." bai dire labarin ba sai da ya kai zuwa lokacin da aka harbe Zayyan yana rike da hannunsa bayan ya sauko ya taimaka masa "duk abinda na zama a rayuwa wallahi Zayyan ne sila, ina kuka shiga aka ce min kun mutu? Ina matar Zayyan da yace min yana kiranta Fillo, ina 'yarsa Alheran Radhiya...kada kuyi mamaki ban taba manta Zayyan ba. Da Allah Ya sake bani haihuwa babu makawa idan namiji ne sunan da zai amsa kenan" yace idanunsa na fitar da kwalla.

Wani irin kuka Ummi take yi wanda duk mai sauraronsa zai tausaya mata matuka. Kirjinta kawai ta dafe tana jin wannan sabon al'amari. Emzee bai san komai akan mahaifinsa ba sai hoto sai labari amma ya tayata kukan saboda girman abinda suka ji.

Daddy da Baba Hadir sai suka ji abin kamar almara. Daddy ya kada baki yace "kana nufin kace min Zayyan bomb bai tashi dashi ba?"

Excellency yayi ajiyar zuciya ya sake yi musu bayanin ainihin abinda ya faru na binne landmine din karya da 'yan tawayen suke yi "tabbas bomb ya tashi domin har zuwa lokacin rasuwarsa Zayyan yana ta fargabar bomb din ya shafi 'yan uwansa Hadir da Major Mustapha ko kuwa Allah Yasa sun tsira. Kamar yadda na fada muku ni da Zayyan munyi wata irin rayuwa ne da bamu da sirri ga junanmu. Zayyan was my last patient daga kansa ban sake iya duba wani mara lafiya ba."

Hawaye ya gani sharkaf a fuskar wanda tun zuwansu baiyi magana ba. Mai yin maganar kuma wato Daddy sai sunkuyar da kai yayi ashe shima hawaye yake digarwa. Kaddara ta riga fata. Ashe da rabon Zayyan zai sake ceton rayuwar wani shiyasa suka yi masa zaton mutuwa. Yau gashi mutumin ya zama gwamna bayan yayi dan majalisa da sanata.

"Kunyi shiru ina Fillo na manta ainihin sunanta"

Mama ce tayi karfin halin nuna masa Ummi wadda kuka ya hanata katabus.

Abin ya taba Excellency sosai ya sake cewa ina Alheran ita yake son gani.

"Tana karatu a France" Ibrahim yayi karfin halin bashi amsa.

Murmushi ya sake "Alhamdulillahi rayuwarku bata lalace ba kamar yadda Zayyan yayi ta jin tsoro. Ko sati banyi da dawowa ba naje har gidan iyayensa wani da yace min shi yayansa ne yace matarsa ta haifi da babu rai kuma sunyi hatsari sun rasu ita da Alheran"

Gyaran murya Major yayi da kyar ya iya tattaro kuzarin cewa "nine Major Mustapha, wannan kuma shine Hadir"

Tashi yayi yazo inda suke ya tsaya "daya daga cikinku kafarsa ta fita a ambush din Liberia?"

Kafar damansa Major ya taba yana kwankwasata "katako ce"

Hannunsa Excellency ya kama ya damke sosai "nice to meet you Major" sannan ya koma ga Hadir "dan uwan Zayyan baka ce komai ba"

"Maganarsa ta dauke tun ranar da abin ya faru....." Major bai dire ba shima sai da ya bashi labarin tashin hankalin da suka fuskanta da rayuwar da suka yi su duka har tasu Mairama. Yau din sai ta zama wata rana ta tuna baya da kuka a garesu. Sannan kuma rana mafi farinciki ga His Excellency Nasiruddeen na haduwa da mutanen da baisa rai dasu ba. Sai dai wani tunani da ya darsu a zuciyarsa ya sanya shi dagowa kana iya ganin fushi mai girma a idanunsa.

"Who the hell is Maikudi? 

"Yayan Zayyan ne amma ba uwa daya ba. Ina tunanin kaina dashi kuka hadu"

"Sai yayi nadamar kallon tsabar idanuna yayi min karya. Na dawo da hope na daukar nauyin komai na rayuwarsu mutumin nan yace min sun rasu" yace cikin bacin rai da jin inama dai yayi ido hudu da Maikudi yanzu.

"Your Excellency mun riga mu sa an kama shi. Gidan magada an karbe sannan wanda ya gina da kudin da na turo da kudin hayar gidan shima yanzu haka mun saka a kasuwa saidawa za'ayi. Family dinsu na Nijar sun shigar da kara sai da yayi wata shida a rufe sannan yana kan biya tara" Major ya sanar dashi.
Chapter 70 · 0% Book details