← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 157

Sashe 84

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Awwani hudu bayan dauko shi Awwab da Excellency suka saka Zayyan a tsakiyarsu suna zaune a cikin jirgi domin komawa Nigeria. Sai da aka hadu so da takardun neman afuwa kuma mataimakin shugaban kasa yace zasu zo Nigeria officially bada hakuri. Sun kama hanya cikinsu babu wanda zai iya bacci a wannan kasar idan basu ga kafafun Zayyan sun sauka a kasar haihuwarsa ba. Babu wanda ya damu da wata tafiyar dare ko nisa. A lokacin da suke hawa jirgin Zayyan ji yake kamar ana zare masa wata kaya mai tsini daga cikin zuciyarsa.

"Baban Alheran" Excellency ya kira shi ganin idanunsa sun kasa daina zubar hawaye. Kukansa kuwa kara raunana Awwab yake yi suke ta yi tare. Kallonsa yayi suka hada ido yaji mugun tausayinsa ya mamaye masa zuciya.

 Har yanzu kyakkyawan mutum ne da ya wadatu da arzikin kyakkyawar zuciya, amma yasha wahalar rayuwa fiye da zato da tsammani. Ciwon da yake tattare da rabuwa yafi karfi a gareshi domin shi yasan ya baro iyalinsa da rai ya azabtu da begen sake ganinsu sabanin su da suka dangana saboda tunanin ya rasu. Akwai lokutan da yake jin kamar zai zauce saboda kewarsu. Wani zubin kuma hakuri yake sakawa ransa, wasu lokutan kuma yayi kuka har sai yaji kamar bashi da sauran hawaye.

"Baban Alheran kayi hakuri shine abinda zanyi ta fada maka har muje gida. Ni dasu Hadir da Mustapha duka zaton mutuwa muka yi maka"

"Ka dena bani hakuri domin Allah Ya riga Ya warware min ciwon da yake raina. Ku bani labarin me ya faru daku da matata"

"Bazaka jira mu koma ka nutsu ka huta ba?"

"Labarin ne kadai zai sa na cigaba da dauriya har mu sauka. Idan ban manta ba ana cewa aski idan yazo gaban goshi..." yayi murmushi.

A takaice Excellency ya labarta masa dalilin tunaninsu na cewa ya rasu, ya kare da cewa "sauran bayani zaka ji idan mun isa gida ka huta yanzu"

Ruwa da abinci aka kawo musu amma shine ya fara daga hannu domin dakatar da air hostess din daga ajiye masa.

"Daadaa kaci wani abu mana. Kafin mu taho ma ko ruwa baka sha ba duk wannan lokacin da aka bata" Awwab yace yana rokonsa.

Murmushi yayi sai ka rantse Emzee ne a wurin yace "babu abinda zan sake ci ko sha sai naje gida in sha Allahu Mairama ta bani."

Yana so ya tambayi Awwab ko tayi wani auren amma baya tunanin zuciyarsa zata iya daukan nauyi irin wannan komai kankantarsa a yanayin da yake ciki shiyasa ya ja bakinsa yayi shiru suka cigaba da tafiya kowa yana murmushin farinciki da jindadi.

A awa uku mintuna kalilan ne babu a tafiyar suka iso Nnamdi Azikiwe International Airport na birnin tarayya Abuja. Jirgin yana sauka Zayyan sai ya soma jin kamar mafarki yake yi. Anya shi din da ya yi bacci ya farka a kuntataccen dakin kurkuku dazu da safe wanda suke sharing shi da mutane shida kowa akan katifa mara kyaun gani a wata kasar da ko sunanta baya son ji shine yake sauka a kasa mai dimbin daraja kamar Nigeria? Ana bude kofa ya hango hasken lantarki na ciki da harabar filin jirgin saboda dare sai yaji wasu zafafan hawayen da suka fi na dazu.

Excellency ya nuna masa kofa da murmushi a fuskarsa "ka fara fita".

Sannu a hankali yake takowa ga wasu sojoji kowa da bindiga a hannu suna jiran saukowarsa. Sojijin da suke da alaka ne da binciken dawowar dan uwansu bayan shekaru masu yawa a prison. Babu abinda yake kallo sai kwaltar dake shimfide a makeken filin da jiragen suke sauka da tashi. Kafarsa na taka kasa ya sake fashewa da kuka.

 Wani soja ya daga murya yace "Atteeeeention!"

Sauran suka jeru a layi guda kowanne ya gyara daga bindigarsa sai kuma suka sauke suka sarawa jarumin jarumai mazan fama Lt. Zayyan Tureta domin duk da sai an sake ji daga bakinsa amma basu sami wani dalili na karyata komai nasa ba a bisa bincikensu. Ayya, sake karyar da zuciyarsa suka yi ya daure ya kame shima cikin kayansa na kurkuku ya sara musu sannan kawai ya fadi ya kai goshinsa kasa domin nuna tsantsar godiya ga Sarkin Sarauta wanda MulkinSa shine cikakken Mulki Allah Azza wa Jallah. Sujjada yayi ya rinka kwararo kirari ga Ubangijin sammai da kassai yana hamdala da ganin wannan rana. Shi shaida ne akan kansa cewa ba don Allah Ya so shi ba da tuni ya sami tabin kwakwalwa a prison dinnan saboda yawan tunani. Sumbatar wannan kasar da muka raina, muke zubar da jini, zina, sata da manya manyan laifuka akai yayi saboda shi uwa ya dauketa wadda idan 'ya'yanta sun lalace ba ita bace ta lalace sai dai a kawo mata gyara. A yayin da daruruwan mutane suke fatan budewar kofar da zasu bar Nigeria idan suka tafi ko ta halin kaka bazasu dawo ba mutane irin Zayyan da dama zasu iya fansar da rayuwarsu domin suyi yini guda da iyalansu a cikin wannan kasa. Tabbas Nigeria bata lalace ba sai dai a cikin 'ya'yanta akwai bara gurbi. Ya Allah Kayi mana maganinsu Ka shiryemu baki daya.

Baso wani bata lokaci a airport din ba motocin mai girma gwamna dana sojoji zuga guda suka rankaya zuwa ga babbar headquarter dinsu. Dare ya riga yayi ana neman goman dare amma ga mamakin Awwab sai yake ganin baban nasu da kuzari babu alamun gajiya ko yunwa. Shi da yayi shekara ashirin da biyu yana jiran wannan rana ba karamin abu bane zai sarar masa da gwiwa bayan isowarta.

Excellency ne yake masa bayani da cewa zai amsa tambayoyi ne domin keeping record da binciken da ba'a rasa ba kamar yadda aka yiwa Chibuzor. Idan yana so zaiyi magana a barshi ya wuce wurin iyalinsa gobe ya dawo.

Wani irin kallon anya kana tausayina ya yiwa Excellency din yana komawa Zayyan dinsa na da "idan akace maka zan fito gobe sai ka yarda?"

Dariya yayi "ina zan yarda kuwa Baban Alheran....to muje in sha Allah ba dadewa zamuyi ba"

"Suna Sumaila ne ko ta zauna a Sakkwato?"

"Duka muna nan Abuja Daadaa, ka shiga ku gama mu tafi gida" Awwab yace yana dauko wayarsa daga aljihu.

"Mu gani Awwab" Zayyan ya mika hannu zai ga abin mamaki. Juya wayar ya rinka yi yana shafawa "Allah mai Iko, a prison dinmu na kan hango su a hannun wasu maaikatan sai aka ce wai cellular ce. Ni dai nayi mamaki sosai ace 'yar wannan abar ita ce waya yanzu. Kuma kamar nawa take?"

Maimakon amsa kuka ya sake sake Awwab. Duniya ta cigaba sosai amma Zayyan bai sani ba saboda a prison da yake na masu manyan laifuka ne sosai wadanda gwamnati bata musu sassauci. Musamman ake kai firsunonin yaki da 'yan tawaye wadanda suka kawo asarar rayuwa da dama da dukiya a kasar.

"Yi hakuri na dena magana tunda kuka nake saka ka" suka rungume juna sannan Awwab yace ya tsaya tare da Excellency da Chibuzor Zayyan a tsakiya ya mikawa wani soja wayarsa ya daukesu a hoto fuskar kowa cikinsu a sake. Ai da ya nunawa Zayyan sai ga dariya yana kada kai "kara mana daya dai na sake gani"

Awwab ya yi dariya a ransa yana ayyana irin abinda Alheran zata aikata ne idan abu ya burgeta. Wata matsananciyar kewarta ta soki zuciyarsa ya fara matsuwa da su tafi gida haka. Hoton Chibuzor ya daukesu su biyu dashi da Zayyan sun sakala hannuwa a kafadun juna sannan aka shige dashi wani daki da manyan sojoji aka rufe kofa.

Tambayoyi ne dai kamar bazasu kare ba daga manya manyansu da aka hada comittee na bincike akansa. Komai nasu anayi ne bisa tsari daki daki. Da ya gama bayani a dauko wani.  Suna yi suna duba takardun da aka basu daga can Liberia da kuma information da suke dashi akansa saboda har file dinsa sai da aka binciko wanda aka buga masa KIA wato killed in action. Sai gashi suna bin komai da kyau aka gane gaskiyarsa daga kwanakin wata da abubuwan suka gudana.

Babu wanda ya iya tafiya saboda su ma takaitaccen lokaci Mr President  ya basu su hada komai. Ga Excellency shima nasu ne tsohon soja ya roki alfarma shima. Lokaci ne da siyasa ta gabato zabe saura wata uku. Dawowar Zayyan wata gagarumar sa'a ce da dama da ta fadowa shugaban kasa mai ci a lokacin zaiyi amfani da ita wurin karkafa kamfen dinsa. A matse yake da ya samu a fito da komai fili domin duniya ta shaida irin kokarinsa da jajircewa. Su kansu sojojin yana son samun hadin kansu ne. Da farko ranar da aka ce masa gwamnan Plateau na son magana dashi kamar bazai amince da wuri ba saboda dan jam'iyyar hamayyarsu ne wanda suka tsayar da wani jajirtaccen tsohon soja a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sai da yaji me yake faruwa shine fa ya sako kansa ayi dashi. Shine fa tun daga saukar jirgin da ya dauko su zuwa yanzu ana ta daukar komai a video ne da hoto. Idan komai ya tafi daidai a saki al'ummar Nigeria ta shaida. 

Karfe uku na dare ranar talata shabiyu ga watan november 2015 aka kammala bincike akan Lt Zayyan Muhammad Tureta. Babu wanda bai nuna gajiyawa ba sai shi kadai. Da sun bukaci a wayi gari a haka da matukar wahala su ga gazawarsa. Ko da ba a filin training bane, Zayyan ya horo matukar horuwa da hakuri da juriya a zaman gidan yari. Wani Lt. Gen mai mukami daidai da Cheif of army staff ne ya fara tasowa zuwa gaban kujerar da Zayyan yake zaune sai ya mike shima. Hannu ya mika masa yana murmushi da alama shine yake shugabantar committee din.

"Welcome home Lieutenant"

Zayyan ya karbi hannun ya rike kafin kuma ya gyara tsayuwarsa. Sauran mutum hudun da akayi tare dasu kowa yazo ya bashi hannu suka gama sannan shugabansu a zaman da ya fisu nuna shekaru ya murmusa.
Chapter 84 · 0% Book details