← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 157

Sashe 133

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga bakin kofar Salame ta zube saboda ganin uwa mai dadi ta shiga kuka tun daga kasan zuciyarta. Ta Madina kamar mai kallon film haka ta kare mata kallo ta gama kukan bata ce komai ba. Sai da ta fuskanci kamar tayi shiru ta tabe baki tace "alhaki kwikuyo ya biyoki kenan. Ina kyautata zaton wannan hawayen na Rahima ne ko hakkinta. Ko ma wanne ne a dakin nan nace miki da sannu zaki ganewa idanunki illar abinda kike matar Alhaji"

Da kyar ta iya cewa "Ta Madina baki kika yi min gashi ya kamani"

"Karya kike" ta nunata da yatsa a harzuke "ke idan nayi miki baki buzunki ma bazai ganu ba in fada miki."

Kai ta sunkuyar tana ji Ta Madina ta cigaba da fada "wai ni Salame zaki nunawa kina auren maikudi ban isa dake ba. Nan inda kike zaune lokacin kika tsaya kina fada min maganganu saboda Rahima tazo ta roki in baki hakuri ki yafe mata ko ma menene tayi ki dena dukanta. Saboda kinci maiko kin tada kai kika kada baki kika ce mata idan ta kuma zuwa wurina baki yafe mata nononki da tasha ba. Ni...ni Salame kika yiwa wannan rashin arziki"

Ta sani ita din mai laifi ce sosai a wurin mahaifiyarta. Idan bata ga ba daidai ba a dalilin kowa dole ne ta gani a dalilin Ta Madina. Muryarta ta ji tana ta koro bayani kamar yau akayi.

"Yarinyar nan tayi kuka kamar me tun daga ranar idan tazo daga waje take kwada sallama na fita mu gaisa. Yau shekara biyu rabona da ita saboda kaninki Sa'adu rannan yayi fushi ya daukota a ka ya dire min ita yace idan kin isa kizo gabansa ki tabata. Da yake ta gaji halin kwarai wurin babanta a guje ta fita tana tuna kalmar rashin yafiya da kika jefa mata...shikenan ta dena zuwa"

Ajiyar zuciya ta saki ta gurfanar da kai "Ta Madina ki yafe min amma yau abinda ke damuna yafi karfin Rahima"

"Wa kuma kika tabo kuma?"

Cikin kuka ta zayyane mata komai batare da ta boye wani abu ba. Bacin rai sosai take gani akan fuskar Ta Madina kafin ta nuna mata kofa "ga hanya nan idan kika sake shigo min gida nima ban yaf...."

A guje Salame ta tashi "kada ki karasa zan tafi"

"Baki ga komai ba ma indai bazaki dena wannan shashancin ba. Duk kinbi kin tsangwani kanki kin lalace kamar alayyahu yaji rana" Ta Madina ta daga murya yadda zata ji. Sai da ta tabbatar ta tafi kuma hankalinta ya tashi kawai sai ta kira wata jikarta 'yar kanin Salamen ta saka ta kiran Halifa a waya. Cewa tayi ya gaggauta zuwa Sumaila indau yana Kano yace to. Rahima ya kira tana dauka ta fashe masa da kuka sai ya kara jin hankalinsa ya tashi. Gashi ta kasa cewa komai. A ranar ya dauko hanya kai tsaye gidan Ta Madina yaje. Matsa mata yayi da tambaya ta kasa cewa komai kawai ya wuce gidan Alh Indararo gashi dare yayi. Alhajin da bai san ina Salame ta makale ba ya fyede masa biri har bindi....bai karasa bindin ba dai tunda kuwa iyaka abinda ya fada masa bayan dukan Rahima da 'yae uwarta wadda ya gano Radhiya ce daga kwatancen da yayi masa sai kuma baton makanta Mairama. Bai kai ga fada masa soyayyarta ga Zayyan ba Maman Danmama tayi saurin dakatar dashi. Halifa idanunsa kamar garwashi sai jijiyoyin kansa da suka tashi kamar zasu fasa fatar su fito. 

Cije lebensa na kasa yayi har yana jin dandanon gishiri yana magana da kyar yace "yanzu kowa ya sani?"

"Ina maganar kowa Halifa, wannan zance fa yarinyar Mairaman ce ta kira waya wani yake fada mata muna ji mu kuma. Da su Malamijo suka zo kowa yaji mana."

Hawaye Halifa ya soma abin tausayi "Rahima ma ta sani?"

"Eh tohhh...lokacin da muke zancen dai bata gidan sun tafi asibiti amma ban sani ba wala Allah ko a can gidan an fada mata." Alh Indararo yace bayan guntun tunani.

Jiki a sanyaye kamar wanda yasha duka ya kira Mairama. Tana ganin kiran hankalinta ya tashi. Kuka Halifa ya saka mata muryarsa tana rawa yake mata magana.

"Ummi ki yafe mata ba don ita ba don Allah..."

"Halifa kana ina?"

"Gidanta"

"Waye ya fada maka?" Tace tana taya shi kukan.

"Yanzu zan zo gidan Malamijo amma don Allah don sonki da Annabi Ummi kada ki bari Rahima taji don bansan yadda zata dauki abin ba"

Kwantar da murya tayi tace ya taho tana jiransa. Babu wanda ya san ya shigo ta kaishi dakin Malamijo inda ya sha kukansa kamar ba gobe Malamijo yana ta bashi baki.

Ranar babu wanda yayi baccin kirki cikin manyan ba don komai ba kuwa sai tausayin Halifa da yadda ya dami kansa. Radhiya sai da ta ga Rahima ta kwanta ta soma nata kukan itama. Tana tausayin 'ya'yan Gwaggon tasu sannan a gefe daya ta tsaneta saboda wahalar da ta sanya Umminta fuskanta. Awwab ba karamar damuwa ya shiga ba da yayi ta kiranta babu amsa ashe ta yar da wayar a dakin Salame. Itama bata tuna ba sai daga baya sai dai bata son yaji muryarta a yadda take gashi kowa da tasa damuwar shiyasa ta kasa aron waya.

Cikin bargon kuma Rahima ce ta boye kanta tayi kuka har sai da taji kanta yana neman rabewa biyu don ciwo. Bata san me Ummanta tayi ba amma yanzu ace mahaifiyar mutum tayi masa tsanar da sai wasu ne suke tare masa? Wace irin kiyayya take gwada mata da har ta kasa ko da sau daya yi mata kallo irin wanda take yiwa sauran 'ya'yanta? Da wannan tulin tambayoyin bacci a kwasheta. Gashi ta kira Emzee yafi sau ashirin sai dai wayar ta tsinke don kanta batare da ya dauka ba.

*********

A bangaren Emzee wutar kiyayyar Rahima ke cin ransa kamar gobara yayin da ya kasa gane a wane matsayi ya barta a cikin zuciyarsa. Kunci da bacin ran da ya shiga a wannan dare bazai misaltu ba. Da abin ya ishe shi Daada ya kira ya rasa yadda zaiyi ya fada masa halin da zuciyarsa take ciki. Ya dai yi masa kuka abinda ya daurewa Zayyan kai sosai. Kallon jarumi mai dakakkiyar zuciya yake yiwa dan nasa ashe akwai abinda zai kawo hawaye a idon mazaje. 

"Ba kace dama an baka leave har zuwa bikin Alheran ba?" Ya tambaye shi bayan ya samu yayi shiru.

"Eh Daada"

"Gobe da sassafe ka sameni a Kano Janguza barrack wurin Captain Onomza zamu je Sumaila tare. Akwai jirgi karfe bakwai da rabi shi zan biyo in sha Allah"

Suna gama wayar ya kira Captain Onomza ya sanar dashi yana bukatar mota guda ta sojoji. Allah Yasa da uniform dinsa a mota sai dai tunda ba da dreban zai tafi ba zai dauki jakar ne kawai. Akwai mutum uku da suke tare a daya motar masu bashi kariya duka dasu zai tafi Kano. Ziyarar tasa ba official visit bane amma ya kamata a tauna tsakuwa domin aya taji tsoro. Yau daya banda Mairama, Alheran da Zayyanunsa da yayi ta aikin rarrashi daga nan Allah kadai Yasan mutum nawa Salame ta sa zubar da hawaye. Ita mace ce mai rauni bazai dauki hukunci irin wanda aka yiwa Maikudi ba akanta amma tabbas zai nuna mata ta taba masa mutane mafiya suyowa a ransa.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: **********

Daddy ya fito daga daki ya tarar da Awwab yasa Mami a gaba kamar zaiyi kuka. Yana ganin mahaifinsa ya tashi da sauri "yauwa Daddy ka ga Mami ko"

Girgiza kai tayi da guntun murmushi ta kalli maigidanta da yake yi mata kallon tuhuma tace "yana da hannu, waya da kuma kudin kiran waya amma haka kawai yazo ya tsattsareni da tambayoyi, to nima ban sani ba"

Idanun Daddy suka koma kan Awwab jikinsa a sanyaye ga damuwa karara yace masa "wa kake so ta kira maka?"

Mami ta riga shi cewa "zuwa yayi fa zaiyi min wayo...wai nayi waya da su Ummi nace eh, shine ya koma tambayar wai in sake kira inji kowa da kowa lafiya yake. Idan matarsa yake nema baya samu ya kira Ummin tashi da kansa mana"

Murmushi Daddy yayi "kinci sa'a babansu Sakkwato yaje da da kaina zan kira ince a kaiwa 'yata mijinta yana nemanta"

Kai Awwab ya sunkuyar yana jin kunyar mahaifin nasa. Da ya ga abin bazai kare ba Mami tana tsokanarsa ya tashi ya gudu amma zuciyarsa babu dadi ko kadan. A tunaninsa ko bata da chaji za ta ari waya ta kira shi musamman tunda tafiya su ka yi tasan cewa zai damu da jin lafiyarta. Tamkar an tsikare shi ya sake janyo wayarsa ya kira Zayyana shiru bata shiga sai ya nemi Zahra yace ta bata tace masa tayi bacci. Kai ya dan sosa ya kashe tare da kiran Emzee.

Rai a jagule ya dauka duk da ganin nambar Awwab din amma baya cikin nutsuwa. Daga muryarsa kadai Awwab ya gane akwai abinda yake damunsa. Emzee da yake very jovial amma yanzu da kyar yake amsa masa. Tambayarsa nambar Rahima yayi tunda yasan duk rintsi suna tare da Alheran.

"Bani da ita" yace a takaice yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa. Tun dazu ya goge numbar abin bakinciki da takaici shine lokacin da ya bude zaiyi deleting a take kwakwalwarsa ta haddaceta.

Abin ya bawa Awwab mamaki yace "ka ji me nace kuwa? Numbar Rahima fa...Alheran nake nema tun suna hanya ban sake jinta ba"

"Hamma bani da ita kuma ba kanwata bace idan kana so zan turo maka ta wasu a gidan ko ka kira ta Mama"

Sai lokacin ya tuna da Mama aka tafi da tuni ya kira ta. Yanayin kanin nasa ne ya dame shi a tausashe yace "Emzee are you okay?"

Zafi kirjinsa yake masa yana kara jin haushin wannan soyayya da yake yiwa Rahima. Dumin hawaye yaji a karo na barkatai yau yana zubar da hawaye.

"No"

"Want to talk about it?" Awwab yace a hankali saboda ya kwantar masa da hankali.

Muryarsa gabadaya tayi breaking kana ji kasan kuka ne ake dannewa "Not yet Hamma kawai ka tayani da addu'a" 
Chapter 133 · 0% Book details