← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 157

Sashe 61

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motsi kadan Radhiya sai ta kalli wayarta babu kiran Awwab. Yadda baiyi bacci ba jiya yau ma hankalinsa gabadaya ya tashi ne saboda rigimar dake neman kunno kai a gidansu. Mami da Daddy sunje har gidan Alh Baba akan ya duba lamarin wanda zuwan nasu ya sake harzuka shi. Mummy da ta sami labari ko kallon arziki ta kasa yiwa yayarta. Ga Ghazalatu ta kwana kuka kuma tsabar wulakanci ko aurenta ba'ayi ba ace suna rokon a auro harda wata. Domin su tsayar da abin haka suka yanke shawarar bari a fara bikin da Ghazalatu. Idan yaso bayan ko da rabin shekara ne Daddy zai sake yiwa su Alh Baba maganar. Kwanaki biyu suka yi ana wannan tashin tashina. 

A Kano kuma Mama ta bude wuta wurin gyara 'yar uwarta Ummi da 'yarta Radhiya. Salon ta kai Mairama da aka gama gyara kan akayi steaming sai ta sake komawa yarinya kyaunta ya kuma bayyana. Radhiya ganin Umminta a steamer harda kuka wai ita ya kamata a yiwa wannan gyaran amma saboda Innawuro bata sonta gashi yanzu tana ji tana gani babu damar shiga. Mai salon taji sai mita take tana fulatanci tana hausa ana ta kiran Innuwuro tace mata tazo ta shiga.

"Soya min fatar kai zaki yi ko"

Matar tayi dariya "gyara dai kanwata"

Bisa tsautsayi ta tuge dankwalin Radhiya wai zata yi mata gyara kyauta sai abin arziki ya bayyana kowa ya gani. Allah Yasa kan ya hade yayi baki sidik gashi ya soma tofowa. Amma duk da haka ranta ya baci ta tashi ta hade fuska tana kallon matan da ake yiwa gyara.

"Yasin mace tayi dariya in rangada mata balotelli ta tafi dashi gida"

Kana ganinta kasan ko bata aikata ba to dai zasu ji ba dadi. Mai salon ta koma bata hakuri sannan tace tazo tayi mata gyaran farcen hannu da kafa da steaming din fuska. Shikenan ta manta da fushin ta shiga jerin gyara tana ta firirita yau gata a salon. Kafin su bar wurin tasa mata da yawa dariya. 

Washegari ana gobe zasu tafi mai kunshi tazo ta rangada musu baki da ja. Ummi dai safa ta saka a kafarta tana jin wani iri. Rabonta da ado haka tun Zayyan bai tafi Liberia ba. Yanzu kam wa zata yiwa. Nene kuwa sai zuga Mama take yi wai a gyare mata 'yarta ta samo miji dan ubansu.

Radhiya da Emzee suka taru suka rafka mata uwar harara sai da Mama ta hade kawunansu ta gwara.

"Nenenmu kuke harara"

"Mama wai miji fa take cewa, Ummi ke da aure sai a aljanna ke da babanmu" Emzee yace da dukkan seriousness.

"Maza iyayen kishi" Mama tace tana tuna lokutan da Ibrahim yake yi mata kunkuni akan me yasa ta tafi tabar babansa.

Ranar wuni suka yi ana ta gyare gyare saboda tafiyar su Mama da ta matso kusa sosai. Ibrahim zai koma gidan kakaninsa ya jira dawowarsu. Da safe ta kaisu tasha. Nene tayi ta yi musu addu'a ita da iyalinta tana fatan Allah Yasa a dace mijinta ya sami lafiya ya dawo da kafafunsa. Kamar kar su rabu ita da Ummi. Emzee ma dai dokin budewar idanun Ummi yasa zai bisu Sumaila. Ba don haka ba jira zaiyi sai sun tashi nan da kwana biyu sannan ya koma.

Sai da suka tashi Mama ta koma gida tare da Ibrahim mai nuna hanya. Suna isa Aisha 'yar wajen Alh Musa ta kirata. Sun gaisa da ita da kanwarta tace mata ga Mamansu su gaisa. Matar mai mutumci suka gaisa da tambayar juna iyali.

"Antin yara na bugo ne nayi miki godiya irin dawainiyar da kika sha da yaran nan. Na dawo gidansu biki ya matso babu abinda baki saya kin ajiye ba. Don Allah ina rokon mu cigaba da zumunci."

"In sha Allahu. Nagode"

"Ina fata kuma zaki zo bikin 'ya'yan naki"

"Ahhh banyi alkawari ba."

Nunawa tayi bata ji dadi ba har tana tambayarta ko don sun rabu da Alh Musa ne. Mama tayi dariya tace mata tafiya ce a gabanta zata kai mijinta asibiti. Maman su Aisha ta tausaya mata ta kuma jinjina mata wannan sadaukarwa da ta hanata zama gidan mutum kamar Alh Musa mai kudi da halin dattako. Bata yi kasa a gwiwa ba bayan ya dawo daga wurin aiki ta fada masa. Abin yafi taba shi duk da yasan ta koma gidan tsohon mijinta amma sai da yaji wani iri. Soyayyarta da tausayinta duka a hade. Nasa salon kaunar shine ya tura mata miliyan biyu da rabi a matsayin gudunmawa. Mama tayi kuka a ranar yadda Allah ke budawa bawanSa a lokacin da bai taba tsammani ba. Aurenta da Alh Musa ta yarda silar arzikinta ne da nemawa Hadir waraka.

A Sumaila kuma su Ummi sun isa gida ya fara cika da 'yan biki. Yawanci 'yan uwansu ne na bangaren Malamijo. Washegari kuma sai ga dangin iyayen amaren mata su ma sun fara zuwa. Innawuro da matan su Baffa Gide duka sun iso. Ranar ne za'ayi Kamu amare kowacce dangin uwa na kokarin rufa mata asiri. Shi dai Malamijo tunda ya bada abinda zai iya ya janye hannuwansa. Duk wannan abu da akeyi Salame bata samu zuwa ba saboda bata ma da kayan sawa ta shiga taro ga yunwa kamar taci babu ita da 'ya'yanta. 

Ranar da yamma Nene ta rufa mayafi ta tafi gidan Salamen. A gaban murhu ta sameta tana ta uban kauri. Tsaki ta samu zata yi musu danmalele ita da yaranta suci. Girman kai ya hana ta kwantar da kanta gaban mahaifinta komai lalacewarsa ta nemi taimako. Taji labarin Mairama tana gidan amma bata gabanta tunda tasan ba ido gareta ba bata da abinda zata tsinanawa kanta ma. Kauyen da akace ta koma na dangin babarta ta tabbatar kila wahala kawai take sha daga ita har yaran. 'Yan lokutan da suke zuwa Sumaila lokacin tana shanawa a jikin Indararo bata ma zuwa gidan don kada a fara yi mata bani bani. Sai gashi a kasa da shekara guda duniya tayi mata juyin waina...sama ya koma kasa.

Idanu jazur ta dago tana fyace majina da gefen mataccen zaninta sannan ta kakalo murmushin dole.

"Nene kece a gidan namu yau?"

Rai a bace Nene Marka tace "nice Salame, cewa nayi bari nazo na gaishe da hamshakiya matar Alhaji tunda kinfi karfin kowa."

Kamar wata gaula tana fama da cikin da yake neman rinjayarta tace "to ni me nayi"

"Ban sani ba Salame. Mahaifinki ya kwanta ciwo yaci ya cinye har ya warke babu ke babu inuwarki balle asa rai da mijinki ma zai je. An kai lefen kanenki baki je ba yanzu don tsabar bakin hali ana biki a matsayinki na babbar 'ya a gidan kin gagara zuwa kuna gari daya. Anya Salame kin dauko hanya mai bullewa kuwa?"

Da kunya taje gidan nan bayan kowa ya santa a lokacin da take tsaka da jindadi dama kiris 'yan bakinciki suke jira ayi mata dariya. Jiya Ta Madina tazo har gidan itama ta kare mata tanadi wai kanwarta ta haihu bata je ba. Yaran da suka gama rainata suke murna da talaucinta.

"Kin dai ga yanayin da nake ciki dama shi kuke buri shiyasa babu wanda ya damu dani"

"Kaniyarki, idan zakiyi fitsararki kada kiyi min bazan miki da dadi ba. Idan ban ganki a wurin bikin nan gobe ba wallahi sai na saba miki. Mutuniyar banza wadda bata sawa zuciyarta komai ba sai kyashi da hassada. Malamijo ya cuceku wallahi"

Bayan fitarta Salame kuka ta saka. Tana ji tana gani ta zama bolar gida kuma miji yaki ya saketa ko tasan matsayinta. Tana cikin wannan halin ne kamar daga sama Halifa yazo. Matashin saurayi dan gatan Alh Salisu. Yaron babu abinda ya nema ya rasa a wurin mahaifinsa sai dai abu guda. Da matukar wahala babansa yake bashi kudi idan zai zo Sumaila. Da can yana bashi sai ya zamana Salame tana karanta masa bukatunta idan zai sake zuwa. A hankali Alh Salisu ya fahimci cewa kudaden da yake bawa dan nasa aikinta ne ko kunya babu. A yadda yayi matukar tsanar halinta tuni ya dakile hakan. Taje can ta karata idan Halifa ya soma sana'a yayi mata da nasa gumin.

Tsabar murna ji tayi kamar an ga watan sallah. Ta rasa inda zata saka kanta don dadi harda yada habaici wa Maman Danmama danta yazo. Shi dai kunyar irin wannan abubuwan nata yake yi to amma uwa uwace. Bai wani dade ba da zai tafi ya bata dubu biyar cikin abinda ya rage masa. Salame duniya tayi dadi ta rasa ina zata kai farinciki. Dreba ne ya kawo shi kuma yana jiransa ya tafi dashi. Dan cikinta a wannan hadaddiyar mota harda dreba. Kai inama dai ta kwantar da hankali a gidan Alh Salisu.

Washegari bayan sunci fara da mai harda hadin salak da kifi sukunbiya ta shirya 'ya'yanta kowa cikin kayan sallarsa na bara kafin Alh Indararo ya banzatar dasu. Itama wani leshi ta saka cikin irin alkhairin da ta samu albarkacin aikin malamin tsibbunta wanda ya fita yayi yanzu. Mayafin ma irin mai bakin leshi da ta dade da dena sakawa ta dauko don na yayin duk sun mutu babu na mora.

Tana tsakiyar yaranta dayake tafiyar kafa ce zata kaita gidan tana murmushin jindadi. Yau 'yan bakinciki sai dai su mutu. Tana nan kuma har yanzu tana damawa don tasan da wuya a sami mai dressing irin nata.

Ta kusa gidan bai fi taku kadan ya rage ba ta ji dirin motoci a bayanta sun taho a guje. Kana ganinsu kasan tafiya ce ta jerentawa wato convey. Motoci ne da suka amsa sunansu mota masu masifar kyau da daukar ido duka a maimakon nambar mota an rubuta G. AGALI wato Ghousman Agali kakan Zayyan Muhammad Tureta na wurin uwa.

Guda takwas ne sai kuma helux guda biyu da aka ciko su shakare da buhun hunan kayan abinci da lemuka na kwali da na roba. Mota cikon ta tara da ta fita daban da sauran duk da cewa itama tana da kyau sosai Awwab ne a ciki. Shine yayi musu rakiya zuwa garin Sumaila domin cika umarnin mahaifinsa da hada masoyiyarsa da dangin mahaifinta. Daga ita har Ummin an kasa samunsu a waya bare a sanar dasu zuwan bakin.
Chapter 61 · 0% Book details