← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 157

Sashe 32

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwalla taji a idonta da ta kalli Hadir ta ga ya gyada kai "ni ku tashi mu tafi kuna neman saka mutane kuka."

Ibrahim ke tura kujerar babansa bayan ta yiwa likitan godiya suka kama hanyar wurin ajiye motoci. Gasu dai suna tafiya miji na zaune amma dole su baka sha'awa yadda duk suka yi kyau ga kuma alamu sun nuna iyali ne da ke matukar kaunar juna.

"Mama ki koya min tuki don Allah"

"Da wannan rawar kan"

"Baba ai bani da rawar kai ko?" Ya dukar da kansa yana tambayar Hadir shi kuwa ya gyada kai yana supporting dansa.

"Kuma sunana zaka fara fada idan ka warke ko"

Hararar da Zainab tayi masa ce ta saka shi wata dariyar shakiyanci "baka isa ba yaro"

Dariya suka rinka yiwa juna kowa ba cewa dashi za'a fara ba kace uwa da danta bane.

Tana tuki Ibrahim ke nuna mata hanya don bata waye da garin Kano ba wayar autansu Hadir ta shigo yace yana tare da baki a kofar gidansu. Ya sanar dashi suna hanya sun kusa karasowa. Da ya fadawa Zainab tace su waye.

"Bari na kira na tambayeshi"

"A'a barshi kawai"

Bus ta gani a kofar gidanta da mutane a ciki. Mami tun da Zainab ta karyo kwana ta ganeta. Jikinta na rawa tana sauri ta bude kofar motar ta fito. Major ma haka ya fito yana hango Hadir a daga bayan motar.

Hannunta taji yana rawa da ta tabbatar da su waye a kofar gidan. Ta juya a hankali za ta cewa Hadir ya gane su sai ta ga yana hawaye. Bata iya gyara packing ba ta kashe motar ta fito da sauri ko takalmanta bata saka ba.

Hannu ta dora akan bakinta ta toshe kukan da yake barazanar yin sautin da kila sai makota sun leko ta suka tako gaban juna sunyi sharkaf da hawaye.

"Mami?"

"Antin su Zahra"

A wajen nan suka rungume juna suna kuka, kuka na gaske. Major ya karasa ya budewa Hadir kofar bayan fuskarsa cike da annuri.

"Lieutenant fito mu gaisa"

Hadir ko motsi baiyi ba sai rufe ido da yayi hawaye mai dumi na sauko masa. Da yana da lafiya wallahi zai sarawa Major Mustapha ne domin soja ne a gaban ubangidansa.

Ibrahim ya fuskaci bai san yaya baban nasa yake ba ya cire kai ya kira mamansa.

"Mama zo mu fito da Baba daga motar"

A kidime Major yace "me ya same shi?"

Zainab ta dawo tana kuka tana dariya tace Ibrahim ya bude gate su shiga ciki. Kallonsa su Mami suke yi ya budw gate din ta shigar da motar sannan duka suka shigo. 

Wheelchair Major ya ga Ibrahim ya dauko a boot yaji zuciyarsa ta karye Zainab tazo zata taimaka su dora shi yace bari yasa hannu. Hadir ba kiba gareshi ba shiyasa ma suke jin saukin daga shi din.

Sai da ya zauna Major ya dube shi da tausayawa "kai kuma taka lalurar kenan Hadir?"

"Baba baya magana"

Zainab ta share hawaye ta bude musu kofar gidan. Mami da Major mamaki ya kara kama su da jin wai baya magana kuma.

Sai da suka zazzauna yaran suka sake gaishe su Zainab ta rike baki "yanzu Zahra da Fauziyya ne haka? Ikon Allah, Inna Awwab din Mairama. Ita kuma wannan 'yan matan kamar a tafi a barmin ita wace"

"Zayyanatu sunana" ta amsa da kanta.

Mami tana murmushi tace "Daddy yaso yiwa Zayyan takwara sai tazo a namiji"

"Allah sarki Mairamu da Zayyan ban san yaya suke ba"

Hadir sai runtse idanu yayi Mami da Major na kallonsa da ita. Mami ta daure tace "ashe baki san Allah Ya karbi ran Zayyan tun a Liberia wurin ceton rayukan mazajenmu ba"

A gigice tace "ME??? Baban Radhiya ya rasu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Kuka suke yi sosai mazan na hawaye harda Major duk dakiya irin tasa. Zainab ta tsahirta tace su Zahra da taga suna tayasu kukan su shiga dakinta bari ta aika a siyo abinci don bata yi girki ba.

"Turasu kitchen kawai su dafo mana"

"Ayi haka ko ware gajiya basuyi ba. Naga alamun daga nesa kuke"

"Babu komai ku shige kitchen ku duka kowa tasa hannu"

"Ibrahim jeka sai ka nuna musu. Su dafa mana abin da suke so, ko motsi bana son yi daga wurin nan"

Sun san dai wai wayo ake son yi musu. Suna yin hanyar kitchen din Ibrahim ya dawo da baya ya labe sai ga Zayyana ita ma ta dawo kusa dashi tana kara kunnenta a jikin kofa.

"Meye haka" ya dan sha kunu.

A shagwabe tace "Your mummy and daddy are making mine to cry" 

Wane kallon sama da kasa yayi mata "sannu baturiya ai ni ya kamata nace haka"

Kunnuwansu Zahra ta rike su biyun Fauziyya kuma tace "ku rufe mana baki dalla can muji me ake cewa sosai"

Duka su hudun suka sami wurin tsayawa suna jiyo labaran ban tausayi daga iyayensu. Yadda su Mami ke kuka a falon haka suma suke yi.

Sun tausayawa juna sosai kowa da irin tasa kaddarar. Damuwarsu sai kuma ta karkata kan Mairama da Radhiya.

Sun share kusan awa suna jajantawa juna sannan Mami ta dan bude murya "yaya ne shiru babu ku babu abinci"

Zahra ce ta fara fitowa taje ta fada jikinta tana kuka.

"Kuji min yaran nan, labe kuka yi kenan?"

Zayyana ta gyada kai tana sababbin hawaye. Zainab tayi dariya "to yau kunji rayuwar iyayenku ko"

Ibrahim ba kunya ya koma gefen Zainab kamar zai shige mata ciki yana kara son mahaifiyarsa.

"Anya wannan zaiyi soja kuwa?" Inji Major

"A'a wallahi ni malamin makaranta zan zama." yace da dukkan gaskiyarsa.

Suna ta dariya Zainab ta dauko kudi ta bashi "kayi sauri ka siyo mana abinci tunda labe ya hana ku girki"

Kwanan Radhiya biyu da yiwa gidan Ardo yaji tunda aka yi mata aski. Yaran dangi sa'aninta duk Emzee ya fesa musu sai ta wuni suna zuwa gidan tsokanarta. Na yau yafi bata haushi harda cire mata dankwali gashi Zakari dan gidan Baffa Habubakari da take hasashen yana son ta yana gidan.   'Yar yayarsa ce ta cire mata kullin maganin da take yi a kanta yanzu kunya ta isheta. Zakari sai ya rufe yarinyar da fada ya fita.

Zaune take a daki tana kwafa don idan ta kamata sai jikinta ya fada mata, dazu ma albarkacin kawunta taci kada abin kunyar yayi yawa. Muryar Baffa Gide taji yana fada yana sanar da matarsa ya rasa taurin kan da yake damun Mairama. Maza sun fi biyar masu neman aurenta amma kowa yazo sai tace wai ita makauniya ce. Yayi iya kokarinsa ya samu makaho dan wani attajiri a cikin Giade mai mata biyu shine yaje ya sanar da ita ta watsa masa kasa a ido.

"Na fuskanci yarinyar nan dama can fakewa take da makanta amma bata son yin aure"

"To banda abinka Malam ku kyaleta mana."

"Sai ta rayu babu aure? Yaran nan suna nasu auren fa zata soma jin shiru da kadaici. Ni gata nake son yi mata amma taki gani. Fitowa nayi na barta tana ta kuka"

Hijabinta ta figo bayan ta gama jin bayanin Baffa Gide tace zata tafi gida.

"Dena hararata ba kinji nace na barta tana kuka ba ni ban taba miki uwa ba"

Iyalle matarsa ta soma dariya don fuskar Radhiya a hade take.

" 'Yar soja a gaida gida"

Tana zuwa gidan ko dakin Innawuro bata je ba ta tafi wurin Umminta. Hotuna ne a hannunta tana shafawa tana kuka. Babu mai sanin yanayin da zuciyarta take ciki sai wadda ta tsinci kanta a irin yanayin. Zayyan ya tafi ya barta kuma babu wani kwakkwaran bayani da zata kama taji salama a ranta game da mutuwarsa. Ko ranar da ya rasu bata sani ba sai kiyasin lokaci da aka bata. Saurin daga pillow tayi zata boye su da taji motsin mutum.

Radhiya ta rigata ta hanyar karba tana kallon iyayenta a ranar bikinsu.

"Ummi"

Share hawayen take da sauri kafin ta fara tsareta da tambayoyi.

"Meye, ba yaji kika yi mana ba mai kwal kwabo"

Radhiya tayi dariya duk da ta tsani askin. Tana son farantawa mahaifiyarta.

"Kaina yanzu fa yafi dadin wanka. Insa sabulu harda soso in dirje shi. Idan na shirya na mulke abina da man kwakwar da Yadikko ta bani wancan zuwan da mukayi Sumaila"

"Da kike ishi mutane da kuka harda yaji"

"Ba'a kyauta min bane...da kinga kan nan bazaki so ace nawa bane"

A hankali sai ga Mairama tana dariyar shiriritar Radhiya.

**********

Bayan kwana biyu da zuwan su Major Kano suka shirya harda su Zainab sai birnin Shehu. Da yake Zainab 'yar gari ce dadewa bata sa ta manta hanyar gidan ba. Sun so bata saboda gyare gyaren da aka samu kadan. Sojan da ake turowa kudi ya riga ya bar garin ma ta banki yake turawa MaiKudi kudin.

Alhamdulillah gida ya cika da yara ko ta ina. Ibrahim yana tura Hadir gefensa Major ne yana fada masa dawowar Awwab nan da kwana goma.

Matan ne suka fara shiga aka amsa musu. Sun gaisa Mami ta tambayi Jume wata yarinya ta nuna musu dakinta.

"Fada mata abokan aikin marigayi ne da iyalansu suka zo"

Yarinya ta ruga sai gasu sun fito tare Jume tana musu marhabin da lale. Tabarmi uku aka shimfida musu suka zauna aka gaisa.

"Jama'a ina kuka shige duk shekarun nan ba'a jin duriyarku?"

Kunya ta kamasu duk da kowa dai da nasa uzurin. Sun dan yiwa Jume bayanin da zata iya fahimta Major yana dariya yace "ina Alheran ne?"

"Wai, 'Yar soja ai tana rugar Barkindo, da yake dai akwai bikin yayarta 'yar wajen Mubaraka nasan suna tafe in Allah Ya so"

Kallon juna suka shiga yi sai Mami ta gyara tambayar "aka ce mana bayan Mairama tayi aure ita ta dawo nan wurinku"

Itama nema suke su juya mata kai ta kwalawa Matar Badaru kira "kinji wai 'Yar soja suke cigiya ni duk ban fahimci zancen ba, nasan Badaru yana ciki turo min shi ya musu bayani."

Tsayawa tayi suka gaisa sannan taje ta dawo tare da maigidanta. Shima ya gaisa dasu a mutumce Major yayi masa bayanin yadda suka yi da sojan da yake turo musu kudi akan cewa Mairama tana gidan miji, Radhiya kuma tana nan.
Chapter 32 · 0% Book details