← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 157

Sashe 138

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abincin namu bai kai na 'Yan Abuja dadi bane naga kina ta yafita kamar bakya so?"

Kafin ta kai karshen maganarta Rahima ta zunduma wata katuwar loma wadda ta kasa hadiyewa saboda bata kaunar karkashi ko kadan. Da gudu taje bakin rariya ta zubar ta dawo tana jiran Salame ta soma fada sai taji tayi mata magana babu wannan fadan.

"Ba kya cin tuwo ne?"

"Miyar...miyar ce dama...dama karkashi ne....bana sha"

"Yo maimakon ki fada nayi miki hadin mai da yaji sai ki cuci kanki? In kin fada min ai ba dukanki zanyi ba" tace da ita amma idan kaji yadda muryarta ke fita sai ka dan tsorata. Takaicin yadda yarinyar ke zabura duk motsinta ne yake damunta. Kwanon ta dauka ta mikawa sauran yaranta da gudu suka far masa dama sun cinye nasu ita kuma taje kitchen ta dibar mata wani cikin sauran da zasuyi dumame dashi da safe. Mai kwantirola ta yaryada mata da gishiri ta dauko yaji da rabin maggi a dakinta ta saka sannan ta bata. Ko kadan wannan hadi bai yiwa Rahima dadi ba saboda man danye ne sai karni ke tashi amma kyautatawar da mahaifiyarta ta gwada mata karon farko tun wayonta yasata yin kwalla ta janyo farantin ta cinye shi duka. 

Basu wani jima da gamawa ba Alh Indararo ya dawo gida Salame ta kai masa nasa abincin. Kayan jikinta tun na jiya ne babu zancen wanka a ajandarta duk kuwa da cewa da murhu tayi girki ga kauri ga datti. Tunda ta shiga banda harara da habaici babu abinda yake mata ya gama cin abincin yace ta fita kada ta sake zuwa turakarsa da sunan kwana sai idan da kansa ya nemeta. Abu na biyu kuma ya bata lokaci kankani ta san yadda zata yi su daidaita da Mairama a basu ko da mutum biyu ne cikin yaran shi ma a rage masa nauyi.

Kallon raini ta bishi dashi "wannan shi ake kira karfin hali barawo da sallama."

Hannu ya kawo da sauri zai sauke mata ta fita ba shiri yana ta fada kuma wai kashin tsiya gareta kada ya kuma ganin kafarta a dakin. Dama waye ya aiketa bayan jiya ya mata dukan nan jiki yayi tsami. Dakinta ta koma aka yiwa yara shimfida Khadi tana gado tace da Rahima.

"Kwaba lallen kizo ki yayyaba min dashi zan kwana saboda ya kamu sosai"

"Kada ya cabe ko ba mai ado kike so ba?"

"Ado kai 'yan nan. Kada ki damu zan iya kwana dashi."

Duk yadda idonta yake damunta bata nuna ba ta kwaba lallen nan ta zauna. Wayarta ta soka a gaban dankwalinta bayan ta kunna torchlight saboda rashin wuta sannan ta kamo kafar. Dandakuwa sunan wani abu. Ga datti da wani maiko maiko ga yalwataccen  kaushi yabi ko ina a cikin kafar babu inda babu. Kamar ta ce mata ko zata wanke kafar amma babu fuska sai uwar hamma da Salamen take yi. Ba yadda ta iya haka tasa kasan zaninta ta goge kafar sosai sannan ta baje basira ta soma zane. Goma ta wuce ta gama Salame tace mata ta kwanta a daya gefen ya zamana Khadi na tsakiyarsu. Da kyar ta iya bacci saboda rashin sakewa da sabo. Asubar fari kuwa ta mike ciwon ido yayi sallama ya kara nauyi tana ruwa. Alwala ta dauro ta zo ta tashi Salame ta kwashe mata lallen ta goge hannuwan da kafafu sannan itama tayi alwalar. Tun a lokacin tana iya ganin yadda lallen nata ya fito radau yayi kyau musamman hannuwanta. A sannu sannu gurbin da ta danne Rahima a zuciyarta ya fara neman nuna kansa ga duniya. Sai take jin wani takaici da haushin kanta na kin sakarwa yarinyarta tun farko.

Sunyi sallah Rahima ta gaisheta ta amsa tare da cewa ta bude idon da ta rufe mana. Ai kuwa tana ganin yadda ya kuma hadewa gabanta ya fadi. Hakuri ne tun jiya ta kasa bawa Rahima sai yanzu take sake ganin rashin hankalinta. Ruwan kunu taje ta dora da ya tafasa ta debi wani a bokiti tazo ta gasa mata wurin. Babu wani sauki da taji amma abubuwan kyautatawar da Ummanta ke yi mata kadai sun isheta farinciki. 

Kafin ta dawo daga dama kunun Rahima ta soma janyo kayayyakin da suke soke a lungu da sakon dakin babu wadatar isa ga zarni da wari duk ya hada. Gari guda ta hada wanki sannan ta soma shara Salame ta shigo. Tunda take dan cikinta bai taba yi mata shara ba. Na gabanta banda cin tsiya da fitsara basu san komai ba. Halifa namiji ne, macen da zata yi kuma ta dauki karan tsana ta dora mata. Bata ce mata komai ba Rahima ta aikatu sai wuraren shabiyu ta gama gyara dakin. Wankin kuwa Salame tace zata yi da kanta.

"Lokaci na kurewa shirya ki tafi gidan Malamijo zan taho anjima ki bar min wankin"

Wanka taje yi bandakin babu kanta sai kawai ta shafa ruwa a fuska da kafa ta fito sauran ta wanke musu bandakin. Da sauri ta shirya suka yi sallama ta fito. Sai yanzu ta saki ajiyar zuciya ta sami nutsuwa saboda duk a tsorace take.

Da zuwanta gidan tayi sa'ar samun bandakin da babu kowa ta nemi ruwan zafi tayi wanka. Ido suntum ta shiga daki wurin Ummi hankalinta ya sake tashi. Abinci ta sa ta ci suka tafi asibiti a cikin garin. Sai bayan azahar suka dawo anyi mata allurai tasha magani ta kwanta bacci.

Biki yayi biki gida ya cika da dangi abin farinciki harda wasu cikin mutanen Sakkwato banda na rugar Barkindo zuga guda. Anci an sha babu kwandalar Mairama ko ta mijinta. Malamijo ne yayi kusan komai sai kuma kannen Mairama su ma wasu katan din lemo, akwai wadda tayi zobo da ginger aka kulla a leda, cincin da meatpie kowa dai ya nuna da gaske sun gaji da zaman doya da manja zumuncin suke muradi ayi.

Amarya Radhiya sanye take da leshi mai dan karen kyau ja da adon duwatsu anyi mata dinkin buba ta daura zamin a kai. Kafarta babu lalle sai yatsu kawai haka ma hannu amma tasha ado ba kadan ba. Sarkar beads aka yi mata shirin ya kayatar matuka tana tsakiyar fili ita da Mama da 'yan uwa ana kidan kwarya. Rawa take tana juyi karaf idanunta suka gano mata shigowar Gwaggonta Salame tana tafiya tana dafa bango saboda takalminta. To da yake Allah baiyi ta mutum mai riko ba indai anyi abu ya wuce to fa ya wuce kenan a wurinta sai dai dan abinda ba'a rasa ba. Shiyasa take kaifi daya babu munafurci ayi komai a wuce wurin. Tana takun rawar a girgiza 'yan mata da masu kidan suke yi taje ta riko kafadun Salame ta kawota tsakiyar fili. Ba laifi tayi kyau atampa ce a jikinta ta sako wani takalmi da bai tsufa ba tun na lefe saboda bata sakawa sosai yayi mata tudu. Yau kuwa dole a dama da ita kowa yasan cewa bata karewa Salame ba.

Bata gama gyara tsayuwa ba Radhiya ta rinka juyi da ita ana girgiza jiki ana rawa. Salame tayi wuri wuri ta jigata 'yan uwa aka basu fili ba abin ta gudu ba ace bata son zumunci tafi kowa laifi. Wata kanwarsu ce ta leka dakin da Mairama take zaune da Rahima mai bacci tace mata ta leko tasha kallo. Daga bakin kofa ta hango rawar da suke tika harda su Hajjo amma Salame jikinta yafi na kiwa girgiza saboda Radhiya ta matsanta mata. Me Mairama zata yi kuwa banda dariyar yadda suke yi. Daidai lokacin Salame ta dago kai suka hada ido Mairama ta daure fuska kamar ba ita ke dariya ba ta shige dakin.

Kwafa Salame tayi cike da takaici a zuci take ta babatu "jimin rashin mutumci fa, tana kallo 'yarta za ta ballani maimakon ta tsawatar shine ta koma daki, yanzu kayi magana a hadaka da sojoji saboda rashin gata"

Wani kanin Mairama ne mai hoton yazo aka fara sannan fa Salame ta samu damar sabulewa. Malamijo ma yazo ansha hutuna yana rike da 'yan biyunsa. Kyautar saniya da sa ya yiwa Radhiya babbar jika yace amma a barsu a gonarsa ya cigaba da kiwata mata. Abu yayi kyau zukata sun haskaka da farinciki.

Bayan isha ne Salame ta gama shirin tafiya ta shiga neman Rahima. Haka kawai take son su tafi tare jiya taji dadi har ranta ko da bata iya nunawa ba. Tana daki wurin Mairama tana faman lallabata taci abinci. Gobe da sassafe zasu tafi saboda a kaita asibiti. Yanayin idon ya soma bata tsoro. 

Daga jikin kofa Salame ta coge taki yiwa Mama da Ummi magana sai Rahiman ce tace mata "Umma inzo mu tafi ne?"

Keyar Mairama kawai take gani amma jikinta ya bata gara ta hakura kafin wani abu ya biyo baya. Duk da haka ta ga yana da kyau ta tunawa kanwarta wace tayi ciki da goyon Rahima.

"A'a yi zamanki Rahimata, gobe zan shigo da wuri kafin ku wuce mu karasa hirarmu ta dazu. Kayanki kuma zan bayar a kawo miki yanzun nan"

Dariya ce ta ciwo Ummi wai Rahimata...to dama waye yace ba tata bace? Ita kadai ta nesanta kanta da yarinyar kuma zata fi kowa farinciki idan taja ta a jiki ta sami soyayyar uwa kamar kowa. Sake maimaita kalmar tayi sai dariya tana ta kokarin dannewa amma yadda Salamen tayi magana dole mutum ya dara. Mama na ganin haka ta tace Rahima ta kawo ruwa kwarewa tayi. 

Tana fita ta kalli Salame da ke tsaye har yanzu "dan bubbuga mata bayan mana Adda Salame kina tsaye tana tari"

Idanu ta zaro kamar zasu fado tace "wa? Ni....shegiya inji dan daudu. Rufa min asiri ina tabata yanzu zaki ji dirin motocin sojoji ana kiran Salame"

Kan kace kwabo ta fice abinta ko da Rahima ta dawo bata nan. Washegari sammako suka yi saboda yadda Ummi ta matsu suje asibiti kullum idon kara kumburi yake yi. Ta yiwa Malamijo zancen masu zuwa biki yace kada ta damu zai turo wasu Abujan wasu kuma su bisu Sakkwato har zuwa kai amarya Katsina sannan wasu daban suje Nijar. Hakan yayi mata kuwa sosai.
Chapter 138 · 0% Book details