← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 157

Sashe 35

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A yi haka kuwa?" Baffa Gide yace yana kallon Ardo "a son ranmu dai suyi zamansu da yaran a tare damu har Allah Yasa duka suyi aure."

"Abinda baffanta Gide ya fada gaskiya ne. Ita ga matsalar idanu ga marayunta gara suna tare damu. Lokaci lokaci idan kun bukaci su zo su kwanan muku biyu sai a turo su"

Ransa dama ya bashi da wahala kai tsaye su bari ya daukesu. Sai dai kam yaci alwashin bazai yarda alkawarin da ya daukarwa kansa na cigaba da kula da bayan Zayyan ya tashi ba.

Sauran labarin da ya kasa bayyanawa jiya na ainihin yadda Zayyan ya rasu ya fada musu. Baffa Habubakari sai da yayi kuka don tausayi.

Cikin damuwa da fami ga gyambon zuciyarsa yace "Bazan taba iya kallon idanun matarsa in bata wannan mummunan labari ba. Tana da hakuri amma ina ganin sai ta tsaneni da iyalina. Yau da nake raye ku ke ganina Allah ne Yayi da sauran kwana na amma Zayyan shine sila." 

Ya nuna Hadir "wannan bawan Allah da lafiya kalau yake wallahi kunji na rantse zaiyi komai don ganin 'ya'yan Zayyan sun koma karkashin kulawarsa. Sai dai shima lalura ta same shi ne da ya cigaba da kokarin kare rayuwata kamar yadda dan uwansa ya fara. Ku taimaka ku barni na kyautatawa bayan Zayyan sannan kuma na saukewa Hadir nauyin da nasan da yana da lafiya bazai taba bari na dauka ba"

Jikkunansu sunyi sanyi da maganganun Major. Ardo ya kira Innawuro yace "kece uwar Mairama kakar 'ya'yanta me zaki ce game da batun da bawan Allahn nan yazo dashi?"

Nazari Innawuro ta soma don abun da yake nema ba karami bane. Mairaman da mahaifinta ya gagara rikewa, dan uwan tsohon mijinta ya tozarta ta yaya zasuyi saurin amincewa bare. Idan a gaba gori ya taso ko wani abu makamancinsa fa. Bafillatani duk talaucinsa akwai pride. Basa son zubar da mutumcinsu gaban kowa saboda babu azo aji dadin takasu.

"To na amince amma Zayyanu kadai zaku dauka. Dalili kuwa kun dai ga irin halin 'Yar Soja wallahi zama da ita akwai dadi akwai wuya. Mairama kuwa bana son nisa da 'yata ko kadan."

Hadir ya kafe Major da ido har ya fahimci so yake ya cigaba da rokonsu. Ai kuwa bai fasa ba yana ta kawo hujjoji.

"Kayi hakuri amma indai ka ga 'Yar soja ta bar garin nan to aure ne ya dauketa" Innawuro tace don ta kawo karshen muhawarar.

"Na ji na amince" Major ya amsa batare da dogon nazari ba.

Baffa Gide ya kalle shi da mamaki "kada kace min aurenta zakayi."

Mafita daya ya hango ya kuwa yi amfani da ita "a'a , akwai babban dana Awwab shine nake son aurawa. Dreban jirgin sama ne yana bakin aiki shiyasa bamu zo tare ba."

"Lallai da gaske kake, amma bana so ka cuci yaronka da auren dole don a baka yarinya. Kasan yanayin zamani"

"Na sani amma ina da yakinin bazai bani kunya ba. Don Allah ku amince. Yanzu ku bari mu tafi dasu har Sakkwato saboda wancan wan Zayyan din. Sai kuma danginsu na uwa dake Nijar su ma ina so na hadasu kafin nan da lokacin bikin"

Tsakaninsu da Allah basu da niyar hana shi yaran ko kadan sai dai magana ta gaskiya sunyi masa haka ne domin kada nan gaba a raina musu. Da mutumcinsu da rufin asirinsu ya nemi daukar yaran ba wai talauci ko maula ya kaisu ba. Sun kara jinjinawa Marigayi  Zayyan domin wannan abu halinsa na kwarai ne ya kawo haka. Idan akwai wani abu na bajinta a rayuwar Mairama da Malamijo ya taba yi bai wuce aura mata dan kwarai irin albarka Zayyan Muhammad Tureta ba.

Innawuro da kanta ta fada musu su hada kaya zasu tafi tare suyi musu kwanaki don kowa ya sani hirar jiya da wadda aka sake dorawa yau tayi kadan ta cike gurbin shekarun da suka yi basa tare.

Radhiya sai murna nan da nan ta shiga jibgar kaya. Zainab ta ja ta gefe tace mata ta debi kamar biyar biyar nata da na Mairama.

"Ni fa na zaci kuna sonmu ne sosai baza ku so muyi kwana kadan ba mu dawo"

Tunda suka farka suke cin dariyar Radhiya ashe abin bai kare ba. 

"Mu kuwa muke son ku Radhiya, ko nima 'Yar sojan zan fara fada ne"z

Turo baki tayi "to meyasa kika ce na debi kayan 'yan kadan?"

"Kinga muna zuwa zan sa a kaiku wurin tela ayi muku dinkuna masu kyau. Ko da wadannan kayan zaki je bikin Zahra da Fauziyya da za'ayi karshen wata mai zuwa?"

Dariya Radhiya tayi kumatunta na dama ya lotsa. 

"To gidan wa zamu fara zuwa?"

"Gidana mana"

Mami da take tahowa daga bayansu ta rike baki "sannu maman yara, ashe wayo kike shirin yi min. To ban yarda ba Katsina zamu wuce"

Zainab ta mairaice "habaaa Mami, mu da zamu zo biki muyi kwanaki. Ki bari a ya da zango a Kano don Allah"

Mairama suka tambaya ina take son fara zuwa tayi murmushi "duk inda mota ta fara tsayawa zan sauka ne."

Ta kashe bakin nasu ta barsu da muhawararsu. Wayar Mami aka kira tana dubawa ta ga Awwab ne. Dariya tayi don jiya yayi ta kira bata sani ba. Tana dagawa a kunnen Mairama ta manna wayar.

Ko gaisuwa baiyi ba ya fara mita "Kai Mami tun jiya nake kira ki bani Ummi mu gaisa kinki dauka."

"To Allah Ya huci zuciyarka dan Ummi"

"La ila ha illallahu Ummi kece?" yace yana mai farincikin sake jin muryarta.

"Nice Awwab, yaya aiki?" 

"Lafiya kalau, kinga sun taho sun barni ko"

"Kayi hakuri, kana dawowa zaka ganmu in sha Allah"

"Ummi ina Alheran?" 

"Tana can wurinsu Zahra tana damunsu da surutu"

Dariya yayi yana imagining yaya ta koma yanzu "ta dena fada ko?"

"Awwab kenan baka manta halin nata ba ashe. Sai kazo zaka ganewa kanka."

"To Ummi don Allah kice Mami ta turo min numbar da zan rinka samunki. Ki gaishe min da Alheran"

Mami ta bawa wayar ya shiga tambayarta wai yaya girman Alheran yake yanzu don tsaraba yake son yi musu ita da Umminsa, Anti Zainab da Ibrahim.

"Kai kana fa da wani kanin Zayyan sunansa. Dama mun rabu Ummin taka ta kusa haihuwa"

Mamaki da jindadi suka baibaye shi nan yayi musu sallama zai fita. Suma aka gama shiri suka rankaya sai Katsinan Dikko.

**********

Mairama ta rasa wa zata goyi baya tsakanin Mami da Zainab. Gobe su Zainab zasu koma Kano bayan sun zo sunyi kwanaki uku a Katsina. Gidan kullum cikin hayaniya yake sun taru sun gama gyara shi an saka komai a muhallinsa. 

"Gaskiya Mami wannan fa amfani da girmanki kike yi kina yi min wayo. Ki bar min 'yan matan nan muje suyi sati. Aure fa zasu yi ina ni ina sake cewa su zo su kwanar min"

"Ai ban hanaki ba, Radhiya ce na hana"

"Ummin Awwab kice wani abu mana"

"Ni ban san yaushe kuka koma haka ba. Ina nan bacci zanyi wadda tayi nasara ta tasheni. Idan zama ne na zauna. Idan kuma Kano ce tayi kira a hada min kaya"

Dariya ta basu daga baya dai an yanke Zainab zata tafi da 'yan mata kuma mazan ma ko don Hadir dole su bita. Mairama ce zata rage tare da Mami.

Taron mata ne a kitchen su Zahra na girki Radhiya na koyo.

"Kunsan nima mai aikacin asibiti zan aura a Bauchi zan zauna. Gara na koya kada aji kunya wata rana"

Emzee da yake shan ruwa sai da ya kware da yaji me take cewa "Adda saurayi gareki bamu sani ba?"

Daure fuska tayi zai bata kunya a gaban mutane "fata nagari lamiri yaro...meye aibu don nayi fatan auren likita?"

Ibrahim ya rinka mata wani kallo kafin yasa dariya "na gama harbo jirgin naki. Wato dai wani ma aikacin asibiti kike so"

"Hhhhhh Adda Kawu Zakari kike so hala? Shi kadai na sani a asibiti"

Yadda tayi da fuska ya karasa fallasata. Suka taru ana tsokanarta, Emzee yace wannan labari duk rugar Barkindo sai ya tona.

Tun tana da bakin ramawa ta gaji ta watsar ta fita ta koma daki. Zayyana ta samu tana busar da gashinta da ta wanke da hand dryer. Sai ta dena fushin hankalinta yayi gaba.

"Shi kuma wannan ya sunansa Zayyana?"

"Hand dryer, kema ki wanke kanki sai na busar miki. Mai kitso zata zo an turota daga gidan Alh Baba"

Tsit Radhiya tayi kamar ruwa ya cinyeta. Zayyana tayi tayi tace bazata wanke ba kanta babu datti.

Da su Fauziyya suka shigo Zayyana ta fada musu. Radhiya ta galla mata harara "kinga ki fita idona, ina ruwanki don naki wankewa ba kaina bane?"

Zayyana ta mike a fusace ta fita "kuma sai na fadaki da Daddy"

"Sannu shasshaka uwar narkewa, shagwabar nan nima na iya. Kuma bazan wanke kan ba"

"Dama masu gashi bakwa son bude kai fa. Shiyasa kullum kina cikin hijabi" inji Fauziyya.

Zayyana kuwa tana kai karar Radhiya wurin Daddy ashe Mairama ta jiyo yana cewa a fada mata yace ta wanke shi zai bada kudin kitson. Idan kuma taki wankewa a gida zai bada kudin salon.

"Daddy fada fa zaka yi mata, kara na kawo"

"Yi hakuri Zayyana ai ko ni bazan taba Alheran ba."

Harda guntun hawayenta tace "kafi sonta akaina"

Ibrahim yana gefensu yace "Daddy ka barni na dan saita yarinyar nan mana."

"Taron dangi zaku yiwa auta. To a kira min Alheran yau sai an wanke kan nan"

Mairama tana ji ta tabo Mami "taimaka ki hana wankin kan nan wallahi idan suka bude mata kai gidan nan yau ba lafiya"

Mami ta tashi da sauri duk da bata san ko meye matsalar ba. Tana zuwa Zayyana ta kai rahoton Daddy. Dama su Zahra sun matsu su ga gashinta saboda na Mairama da suke gani mai tsaho sosai.

Duk sun dauki abin nata wasa suka danneta aka cire dankwalin suna cewa yau sai sun ga gashin da take boyewa.

**********
Chapter 35 · 0% Book details