Sashe 92
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka Mamamijo yasa bare da ya soma dubawa a gigice ya fahimci manya manyan bijiman sa aka kwashe "da su taba shanun nan ba gara su lasheni ba ita da yaranta"
Talle dai lallashi yake yi Malamijo ya kama hanyar gida fakam fakam yana zubar da hawaye kamar yaro. Daga tarewarta sunci kaji yafi hamsin. Sau biyu ana daukar tumaki duk yayi shiru don tace masa magana na fita ko ita bata cinyeshi ba yaranta zasu ci. Dakinta yaranta ne a ciki ita kuma ta tare a dakinsa sauran matan basu da girki. Sai dai kowacce ta dora abinda ya samu suna kallo ana wadaka da nama kullum. Babur ya tare ya hau don yayi saurin zuwa gida.
Yana zuwa gidan bata dakinsa ya tafi nata. A can yaji tana waya tana kyakyata dariya "Talle baka da kyau. Kasan shawararka ta maita tayi sosai. Tsohon banza yana son ransa da na kada idanu sai kaga yana tsuma. A sayar da shanun nan ko dubu hamsin hamsin ne tunda kace manya ne kowa ya dau rabonsa"
Wani gululun bakinciki ne ya turnuke shi yadda Hajiyayye tayi masa wasa da hankali. Yanzu yana fito da maganar nan magauta sai su sami abin dariya. Ta ina zai samu ya gasa musu gyada a hannu kafin ya damkawa hukuma? Shawara daya ce tazo masa ga bacin rai ya dauki waya ya kira Mairama.
A lokacin tana ta koyawa Zayyan yadda ake tura sako a waya yana ta mamakin fasaha da kimiyar nasara sai ga wayar Malamijo. A ladabce ta amsa ga tsoron ko lafiya saboda shi dai baya kira sai dai a kira shi. Ko gaisuwarta bai amsa ba ya soma bambami.
"Yanzu Mairama kin kyauta min kenan? Yarinyar nan 'Yar soja ance tazo hutu amma ni ban ganta ba har yau. Naka naka ne Mairama a rinka zumunci."
"Malamijo kayi hakuri dama satin nan zasu zo da Karami sai wani dalili ya gifta amma suna tafe wallahi"
"To ni dai idan da hali su taho gobe ko jibi. Idan ma kudin mai ne babu zan biya. Ina ta shelar akwai jikata a Faransa abokai sunki yarda. Shi kuwa Zayyanu kice ya taho da kayan sojojinsa idan da bindiga ma ya dauko ko ta katako ce."
Jikinta ne ya bata ba lafiya "Malamijo me ya faru ne?"
Kamar ya fada mata amma zuciyarsa na zargin tana cikin masu murna. Duk wanda yaji me ya same shi cewa zaiyi Allah Ya kara. Radhiya kuwa yasan ko zata yi dariya sai ta rama masa su Hajiyayye bazasu tafi haka nan ba. Zayyanu karami kuma ai soja ne dole ya tsaya masa ko baya so tunda hukuma dai anyita ne domin kare al'umma eheee.
Tana ajiye wayar ta kalli Zayyan da 'yar damuwa a fuskarta "ina jin fa an tabo min uba, akwai abinda ke damun Malamijo"
Dagowa yayi daga kan cinyarta da yayi matashi "tun baki tabbatar ba kin soma hade rai"
"Sai naji duk na matsu nima na ganni a Sumailan. Idan wasu ne suka taba shi ba yarda zanyi ba, ina son tsohona"
"Mairama wai ni wa Alheran ta gado ne? Tawa ce ta fito fili amma kema fa ba jin magana kike ba"
Dariya tayi sosai kafin suka yanke shawarar tafiya Sumaila jibi su ajiye yaran su wuce Sakkwato. Daga can kuma suyi Nijar in sun dawo su tsaya a rugar Barkindo kafin su dawo Abuja.
Zuwansa headquarter dazu an kare komai amma duba da cewa dole ya bukaci lokaci da iyalinsa shiyasa aka bashi zuwa farkon sabuwar shekara wanda daya ga wata ake son yin taron karrama shi. Idan an gama zaiyi wata uku yana daukar training da courses domin ayi updating dinsa tunda Nigeriar da ya dawo ba ita ya bari ba a 1994.
Akan wannan shawarar suka tsaya bayan magariba lokacin su Radhiya sun dawo ya shiga wurin Baba Hadir. Nan ya sami Awwab zaune a kasa a gabansa yana rokon shi dai yana dawowa don Allah ayi aurensu da Radhiya kafin ta koma. Ya kara da cewa ya bada cigiya jiya a cikin estate din block C akwai gida.
A dan littafinsa Baba Hadir ya rubuta masa cewa zai yi magana da ita da kuma su Daddy.
"Ni dai Baba da ka kyaleta wallahi tsoronta nake kada a maimaita irin na da. Kawai ka yanke hukunci shikenan"
"Kada ka bada maza mana Awwab ya haka kake tsoron matarka" cewar Zayyan yana dariya.
Awwab sai ya tashi ya fice yana mai jin kunya. Hadir ne ya rinka masa bayani a rubuce na abinda ya taba faruwa da kuma bukatar yaron har yanzu.
Sai da Zayyan ya gama karantawa tsaf sai ya bata rai "nifa na baro A B C D din a Liberia kayi min bayani kawai."
"Zayyan" Hadir yace yana dariya.
"Kaga yara dai naku ne bani da ta cewa akan komai nasu nima dan gayya ne. Fatana Allah Yasa wannan karon babu wata matsala da za'a samu daga Katsinan"
"Baka ji haushi ba?" Baba Hadir ya rubuta masa.
"Ko kadan dan uwa. Major Mustapha da iyalinsa sunfi karfin haka a wurinmu kaima ka sani. Ya kula min da iyali sannan ya kula min da kai. Me zan nema kuma? Maganar yara wannan mukaddari ne idan akwai rabo sai kaga anyi"
"Zayyan" Baba Hadir ya kira sunanshi kawai don jindadin halin abokin nasa.
Dan daure fuska Zayyan yayi "kada ka karar min da suna. Rinka hadawa da wata kalmar don naji dadi"
"Zayyan...fitina" yace yana dariya.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Kinci albarkacin 'yarki bazan biye miki ba" Maman Danmama tace tana sakin labulen.
Bata bar wurin ba Halifa yayi sallama. Muryarsa kamar a kan Salame akayi recording tuni ta gano ko waye tace ya shigo. Sai da ta fita ta harari Maman Danmama irin abin nan na danta yazo sannan tace ya shigo ciki. Kannen nasa ma an sabar musu idan sun ganshi sun ga kudi ko abincin kirki shiyasa suna ganinsa suka fara murna zasu rungume shi ya dakatar dasu. Kazamai ne na ajin karshe shi kuma tsaftarsa har taso tayi yawa. Zama ma kasawa yayi dakin wari da zarnin fitsari kawai yake yi. Rahima da kanta ke duke tana sharar kwalla ta dan dago da murmushi don tasan sunan ko da suke dadewa basu hadu ba.
"Yaya Halifa barka da zuwa"
Wata muguwar tsawa Salame ta daka mata "tashi dan ubanki kwadayayiya. Wuce ki tafi gidanku ai kin dubani mun gaisa ko."
Zabura tayi ta mike a gigice saboda yadda ta razana da tsawar tayi hanyar kofa Halifa ya fincikota saboda gefen fuskarta kawai ya gani ya gane kanwarsa ce.
"Rahima" ya furta a hankali yana kallon jajayen idanunta. Yarinyar da kadan ta fi rabinsa. 'Yar karama ce wahalar rayuwa ta tsotseta.
"Cikani" tace wasu hawayen masu zafi na sauko mata ta kwace hannunta ta fita. Ta sani Ummansu bata kaunarta amma yadda take nuna bambanci kirikiri yana kona mata rai. Mahaifinta talaka ne futuk amma yana kaunarta tamkar rai. Amaryarsa da ta fara son azabtar da ita dashi da babarsa suka tashi tsaye akan ko ta rungumeta kamar 'ya ko ta koma inda ta fito. Kudin sana'arta da Salame take sakawa ido har nawa ne? Zuwan karshe gabadaya ta tattara mata kudin ta bayar. Wannan karon kuma a kofar gida taji wani makocinsu yana yiwa babanta tijara akan ya ranta masa kudin da ya biya mata WAEC da zata rubuta a farkon sabuwar shekara bai biya ba. Tilas da fito da kudin ta bashi ya bawa mutumin ba don yaso ba. Abin ko kwana uku ba'ayi ba kuma babu wanda ta yiwa lalle bayan nan bare ta sami na zuwa dubiyar. Yanzu abin takaici zani daga akwati Salame ta dauko za ta shimfidawa Halifa saboda babansa yana da kudi.
Ta soma tafiya kenan Halifa ya risketa ashe ya biyota "Rahima tsaya mana"
Cak ta tsaya amma bata ce masa komai ba. Hannunta ya kama ya dora mata bandir din naira dari bibbiyu sababbi "kiyi hakuri da halin Umma. Ki rike wannan zan zo gidan naku muyi magana kinji ko"
"Nagode" sai dai kudin mika masa tayi yaki karba sai kawai ta ajiye akan wani bulo da yake gefen hanyar irin wanda ake zama a kai tayi gaba abinta tana goge hawaye.
Ko kadan Halifa baiji dadi ba. Sai ya tuna da Radhiya tace shine babba ya kamata ya hade kan kannensa. Idan suka tafi a haka tabbas Salame zata ginasu da kiyayyar juna ne. Kana ganin Rahima kasan tana bukatar taimako amma zuciya irin tata ta sanya bazata kwantar da kai tana roko ba bare aji dadin goranta mata. Idan ruwa kadai babanta zai iya bata tasha in sha Allahu zata yi hakuri dashi bazata gaza ba.
Da yake ana ji dashi ko fadan bin Rahima da yayi bata masa ba sai kudurin ko nawa ya bata sai tasa ta kawo mata.
"Zauna mana mu gaisa ka tsaya"
"Sauri nake yi Umma. Dama munzo da baki ne gidan Malamijo shine nace ko zaki zo ku gaisa"
Fuskarta ta nuna bata ji dadi ba "can kuma ka fara zuwa?"
"Ko shiga banyi ba na taho nan"
"Su waye bakin?"
"Su Gwaggo Mairama ne..."
So tayi ta kwada masa mari sai dai kuma kada ta toshewa kanta kofar ihsani dan abinda zai bata ya fasa.
"Mairaman zanje in gaisar saboda ka raina uwarka? Me ya kaika wurinta har kake cewa tare kuka zo?"
Shi fa irin wadannan abubuwan ke kara nesanta shi da ita.
"Umma tare muka zo daga Abuja kuma ba ita kadai bace"
Tabe baki tayi "wato ka fara shege mata kawai saboda ance tana wani karatun banza a Kano kuma suna zuwa Abuja ko. To bari kaji in fada maka duka kwarewa ne a maula ita da 'ya'yan suke zubar da mutumcinsu a gaban masu kudi. Ni nafi tunanin aikatau take yi"
"Umma ni zan tafi idan bazaki je ba. Na rasa me tayi miki ba kya gajiya da aibata ta. Ga wannan" ya mika mata kudi a cikin envelop da ya riko dominta.
"To muje bari na dauko mayafi" tace a sanyaye bata kaunar batawa yaron nan rai. Iyaka idan taje ta yanka mata kashedi ta dena bibiyar danta ba tare suka haifeshi ba.