← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 157

Sashe 132

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A kaina saboda ba kya kaunar ganin murmushi a saman fuskata kika yi shirka Adda? Shin Adda kina tunanin zaki iya rayuwar da nayi ne har kika zabi neman yadda zaki mayar da rayuwata taki? Kin taba tsawaita tunani kice Mairama shekararta ashirin da hudu da aure amma har yau bata taba zaman shekara uku tare da mijinta ba har girma ya soma zuwa garesu. Ban san kiyayyar da kike yi min ta kai haka ba amma ina rokonki da ta tsaya a kaina ni kadai kada ki kuma bari ta shafi 'ya'ya. Daga yau kuma nayi miki alkawarin idan har ba bisa lalura ba ko ke kika nema da kanki bazaki kara ganin fuskar Mairama ba bare ta sanya miki bacin rai." Tafiya ta soma yi cikin wani irin kunci mara misaltuwa su Malamijo suka bi bayanta tunda babu wani amfanin jan magana kuma.

Bacin rai sosai Mairama take ji a wannan lokacin. Ita kam bata taba nufin kowa da sharri ba amma ga wadda tafi so duk duniya tun kafin tasan kanta tana neman ganin bayanta. Wanda zai makantaka ko na kwana guda ne ai babban makiyi ne bare wannan shekaru haka cikin kwanciyar hankali. 

Da sauri Salame cikin rashin sanin madafa ta bi bayansu ta sha gaban Mairama. Kuka ta ga kanwarta tana yi sosai fuskarta tayi ja. 

"Me kuma ya rage, raina kike nema?" Mairama tace da kaushin murya. Da sauri Salame ta girgiza kai "to bani hanya in wuce don ni da kike gani na haufu cikin uwa da uba bana amai na lashe. Tunda nace kin dena ganin fuskar da kika tsana to kin daina da gaske ba wasa ba" tace tana rabewa ta gefenta ta fita daga gidan.

A kafa su ka tafi gida babu mai cewa wani uffan kowa da nasa tunani. Sun kusa kofar gidansu Malamijo ya yanke jiki ya fadi tunani yayi masa yawa saboda ko ba'a fada ba ya sani cewa shine musabbabin lalacewar duk wani bara gurbi ciki 'ya'yansa kamar yadda yasan cewa duk wanda ya shiryu a cikinsu daga Allah ne da taimakon Yadikko matar da bata haifi ko tsinke ba amma taci kashi da fitsarin kusan duka 'ya'yansa.

Allah Yasa Baffan Rahima yana biye dasu saboda son ya ga halin da 'yarsa take ciki ya tafi da ita gida. Hankalinsu duk ya tashi musamman Mairama da take yiwa yau din kallon bakar rana ya ciccibe shi ya saba a kafada ya karasa dashi gidan. A kidime Mairama ta kira Radhiya ta turo musu Lucas tace ai sun kusa gida an duba su.

Da sauri sauri suke shirin saka shi a mota ya farfado yace babu inda zashi.

Hajjo tun tana lallaba shi har ta koma fada "so kake ka cuceni kawai. Cikin shekarar nan na dana zaman iddah yanzu kuma takaba kake son kakaba min don mugunta daga dawowata"

Duk da yana jin jiki bai hana shi galla mata harara ba "ina jin har kin gama lissafin tumunin takaba to ta Allah ba taki ba. Ina nan garau ba mutuwa zanyi ba. Ke in bakiyi wasa ba fa Hajjo sai na kaiki zan taho daga baya"

Cinya ta buga tana dariyar jindadin ya tashi amma duk da haka bata barshi haka ba "ashe da rabon ayi suna da kai"

Sam ya manta a waje suke ya kalleta a tsorace yana hadiyar yawu da kyar "wace take da ciki kuma ni Ali wai ku baku da tausayi ne bazaku barni na huta ba"

Radhiya, Rahima da Mama basu san lokacin da suka sa dariya ba Ummi ta tallewa Radhiya da Rahima keya tana murmushi suka shige cikin gidan. Manyan daki suka shiga suna cigaba da tattaunawa Mama da Ummi kuma su ka tafi dakin da aka basu. Radhiya ma da Rahima daki daya suka shiga nan Rahima tana hawaye ta soma cewa Addarta tayi hakuri da abinda Ummansu tayi mata. Daure fuska Radhiya tayi tana harararta da wasa

 "Rahima bana son kina sake tada wannan maganar. Nasan ko ma meye su Ummi sun gama daidaitawa a junansu babu ruwanki"

Wani kukan ne ya taho mata ga idonta daya yana zugi kamar zai fado "Adda ni shikenan Umma bata sona, me nayi mata ta tsaneni?"

Tausayi da kaunar kanwarta ya sake kamata ta zauna a kusa da ita ta rungumeta haushin Salame yana kara kamata. Allah Yasa kada Rahima taji sauran maganar game da Gwaggo Salame don tasan it will break her heart fiye da yanzu. A tausashe tace "Ummi tana sonki kinji kuma bazata sake bari ta dakeki ba"

"Mu ga bayanki" Rahiman tace a kokarinta na nemo nutsuwa ta yafawa kanta a dole. Radhiya kwanciya tayi Rahima ta dage rigarta wurin yayi wani iri da yanzu ita za'a sake saukewa wannan bulala bayan wadda ta sauka a fuskarta. Maganin da aka basu tace za ta shafa mata Radhiyan tace ta bari suyi wanka sai su shafa.

A dakin da su Ummi suke kuwa suna shiga ta haye gado ta kwanta tare da juyawa kofa baya. Kuka take yi sosai jikinta har wata irin karkarwa yake yi. Abin na Adda Salame har ya kai haka ashe. Ita kuwa banda auren Zayyan me kuma tayi ta konawa 'yar uwarta rai haka. Mama jikinta duk yayi sanyi a hankali ta zagaya gabanta ta zauna daga gefe.

"Mairama" tace cikin sigar rarrashi.

Sake juya mata baya tayi muryarta har tana sarkewa tace "ki barni inyi kuka Zainab, ashe a duniya akwai wanda zai tsaneni har ta kai ga yi min asiri na makance. Ina nan ina yiwa kaina kallon wadda bata shiga gonar kowa ba ashe na kure yayata kiyayar tayi tsamari" dago rinannun idanunta tayi suka hada ido tace "Allah kadai Yasan mutum nawa ne suka tsaneni"

Hawaye Mama ta soma yi itama "mijinki yana sonki Mairama. Ni da Mami muna kaunarki kamar ciki daya muka fito kuma ga Malamijo da sauran mutanen gidan nan, banda su Radhiya rabin rai" ta dage mata gira.

Murmushi Ummi tayi kamaninta da Radhiyan suka fito sosai "nagode Zainab Allah Ya kara mana zumunci. Inama Mami tana nan da nasan bazata gudu ta barni yadda kika yi ba dazu kawai ina cikin fada na juya neman support na ga wayam"

Mama sai da tayi dariya sannan ta kira mata Mami. Tana dauka bayan sun gaisa take basu labarin yadda suka yi da Alh Baba wurin shiryasu ita da kannenta.

"Nan ma fa fama muke ina jin shirin ne za'ayi idan an gama hawa saman" cewar Mama.

Ummi cikin kuka take yi musu bayanin abubuwan da suka faru. Su duka ukun kuka suke yi musamman Mami da tayi nisa tana jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta wanke Salame irin wankin babban bargon nan. Zumuncin da yake tsakanin su uku abin burgewa ne da sha'awa domin kowacce da zuciya daya take son sauran.

Bayan sun gama Mama tace "to saura Oga tun dazu wayarki ke haske nasan shine"

Murmushi na musamman Ummi tayi ta mika hannu ta dauko wayar wanda yayi daidai da sake kiranta da Zayyan yayi. Tana dauka ko sallama bata yi masa ba ya kira sunanta a kagauce saboda yadda hankalinsa ya tashi. Jin muryarsa kadai ya sake tado mata abinda Salame tayi sai kawai ta fashe masa da kuka. Yi take yana sauraronta yayin da Mama ta dauke DK tayi waje don ta basu wuri. Sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta. Hakuri ya bata tare da kalmomi na kwantar da hankali sannan ya nemi jin ba'asi.

"Ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allahu jirgin safe zan biyo"

"Sojana" yaji ta yi masa kiran da dole ya amsa.

"Mairama Fillon Zayyan me kuma akayi?" 

Kukan yaji ta cigaba da yi "Don Allah ka fada min ni muguwa ce ko naso kaina ne da yawa da na aureka har ya janyo min kiyayyar Adda Salame?" Ta fada da wata irin murya abin tausayi.

Kwafa yayi kawai yana jin kamar ya baro garin Sakkwato a lokacin saboda yazo ya nunawa Salame kurenta.

"Ki bari inzo goben sai na baki amsar da ta dace. A haka babu abinda zaki fahimta"

"To don Allah ka taho da wuri sosai, yau ina jin ko bacci bazan iya ba" 

"Saboda kewata ko saboda Salame ikon Allah?"

Dariya ya bata "bani da sauran abinda zance mata na bar maka komai Daadan Alheran" ta kare cike da kunya.

"Ki cire komai da kowa a ranki ki barni ni kadai yau dinnan bana son tunani ya dameki. Ina nan tare dake babu wanda zai taba min ke batare da na nuna masa mijinki yana sonki ba"

Sannu a hankali ya mayar da akalar hirar ta soyayya inda yayi nasarar rabata da duk wata damuwa.

**********

Hawaye kafewa yayi a idanun Salame tun bayan fitarsu Mairama ta koma ciki tana tafe kamar kwai ya fashe mata a ciki ta shige dakinta. Mayafi ta dauko ta fito Alh Indararo yayi wuf ya fito daga falonsa.

"Ina zaki je?"

Bata da wani kuzari bare tayi masa rashin kunya "ka yiwa Allah ka barni inje gidan Ta Madina"

Baki ya rike saboda tsabar mamaki kamar wata mace "Ta Madina dai mahaifiyarki?"

Kai ta gyada masa kai kace kadangaruwa ce.

"To sai kin dawo yau nasan zata ce tayi gamo. Idan kin fita ki turo min 'ya'yana. Kuma Yasin kika kuskura isha ta riskeki a waje ko a ina ne har can zani na sabunta miki kamanni muguwa mai muguwar zuciya"

Bata iya tankawa ba ta fita tayi sa'a kuwa jikin gidansu yaran suka shiga. Gida tace su koma sannan ta wuce gidan babarta a kafa tafiyar minti sha bakwai ta kaita. Da sallama ta shiga jama'ar gidan su ka rinka kallonta kamar an ga wata sabuwar halitta. Babu wanda ta kula ta kunna kai dakin Ta Madina ta sameta zaune akan tabarma tana gurza goro. Da mamaki ta dago tana kallonta kafin ta soma magana.

"Iko sai Lillahi...Salame ke nake gani ko kuma gizo kike min. Tohhh ni dai ban kwana dake a raina ba bare ace saka ki nake a zuci har kika fara min gizo"
Chapter 132 · 0% Book details