← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 157

Sashe 107

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalmar da har yau take yi mata wuyar maida masa a kunnensa kenan. Nauyi take ji sosai sai dai ta kare da me too. Tun yana korafi har ya hakura.

"Chèri ka turo min hotonka amma yanzu zaka dauka please kafin mu tashi"

"Ba yadda na iya dake" yace sannan ya katse kiran. Shi ba ma'abocin daukar kansa a hoto bane sai dole yanzu ma abokin aikinsa ya bawa ya dauke shi ya tura mata. Bayan kamar minti biyar ta turo masa wani. Daukar kanta tayi tayi kyau sosai dimple dinnan ya fito ta hada da nasa a photo college wani frame mai kyau. Akan hotonsa ta rubuta Alheran Schatzi a nata kuma Awwab Chèri. Sun tafi zasuyi boarding ta sake kiransa.

"Ka saka shi wallpaper dinka. Idan ka dawo zan duba. Yanzu zamu shiga kayi mana addu'a. Yaya Arifah tana gaisheka"

"Whoa, ki dan tsaya mana in amsa kowanne kafi ki cigaba"

"To ai yanzu zamu tashi"

"Allah Ya tsare Yasa kiyi ki gama a sa'a kuma Ya sa mana albarka a ciki. Ki gaishe da Arifah"

"Amin" tayi ta cewa har aka bada umarnin a kashe waya tana masa hira sannan ta kashe.

Arifah ta kalleta tana murmushi "ba fa zaki rigani aure ba duk wannan lovey dovey din naku sai na riga"

"Nima zan fi so babban yayan nawa kada yazo bikina yana gwauro"

Dariya suka yi tare kafin su dora hirar Yousuf da Awwab. Magana dai tsakaninsa da Arifah ta kankama don yace ta fada a gida zai zo wurinta amma da maganar aure so gara a sani tun wuri. Tante ma sai da ta kira Radhiya ta dan yi mata tambayoyi game da Arifan sun gamsu ana jiran komawarsa Nigeria su karasa daidaitawa.

Jirgi na sauka da suka fito motoci biyu na jiransu daga gidan gwamnatin Kwara. Gwamnan mutumin Baban Arifah ne kuma ya fada masa dalilin zuwan nasu. A cikin gidansa aka tanadar musu masauki. Bayan sunyi wanka sunci abinci aka kaisu suka gaishe shi sannan suka kama hanyar Moro inda Radhiya zata yi hira da Maman Dolapo matar da ta fara yi mata wanka ranar da aka haifeta.

[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Ummi da Emzee suna magana akan tafiyar Radhiya Daada ya shigo falon yake fada musu wayar da yayi da Alh Salisu yanzu. Kamar wasa ya ce Halifa ya bashi labarin program din nata shi kuma cikin hira ya fadawa matarsa. Shine take cewa abin zaifi kyau idan suka sami wanda zaiyi directing daukar komai. A yadda tace masa ya kamata aikin yayi kyau a haka ne zai burge masu kallo kuma a sami damar isar da sakon yadda ya dace. 

"Yanzu yaya kake ganin zamuyi gashi tace suna hanyar garinsu Maman Dolapo" Ummi tace bayan ta nuna gamsuwarta akan shawarar da matar Alh Salisu ta bayar.

"Kya tambayi kaza hanyar rafi Fillo. Ni ba don ma kada nayi karya ba da nace muku meye hadin director da daukar video. Naga su Directors ma'aikatan office ne"

Emzee da ya kwana biyu baya fara'a sai gashi yana dariya "Daada kamar masu harkar film din Hausa yake nufi"

"Ina na sansu, ni dai so nake aikin nata yayi fice yadda take so ace 'yar Zayyan ce nima ina so ince nine baban Alheran. Tunda an bata kudin aikin su ma zasu so ganin abu mai kyau. Zan kirata yanzu su koma kai kuma na baka daga yau zuwa gobe ka nemo min wanda zai yi mana directing din"

"Yes Sir" Emzee ya tashi ya kame tare da sarawa mahaifinsa ya fita. Gidan Mama yaje wurin Ibrahim ashe Ibrahim din fushi yake yi dashi bai ma sani ba.

"Ka huce daga kumburin da ka ke yi ne kazo nema na?"

Shiru Emzee yayi kafin ya dan shafa keyarsa "kayi hakuri mana Ibrahim. Tun a Kano nace maka babu komai"

"Ai shikenan fita zanyi ni ka gaida gida Mama na ciki. Idan kuma kwana zaka yi sai na dawo" sa kai Ibrahim yayi zai fita fuskarsa a daure.

Ba haka Emzee yaso ba. Tun daga Sumaila yake cikin kuncin maganar da yaji daga bakin Nene Marka shine har suka gama kwanakinsu a Kano baya sakin fuska. Sai da ta kai Ibrahim ya fara zargin ko Kanon ne baya son zuwa a dole ya shiga kirkirar murmushi. Dayake da wuya ransa ya baci shiyasa wannan karon ya kasa mallakar kansa. Makantar shekara goma da Umminsa tayi bazai taba mantawa ba.

"Surbajo tsaya don Allah" ya kamo Ibrahim kagin ya fita daga dakin.

Shi kuma ya sake hade rai "gidan nawa kakannin ne baka son zuwa shine...."

"Haba kai kuwa wallahi ba haka bane" Emzee yace hankali a tashe baya son ya batawa dan uwansa.

"To yane?" 

Hannunsa yaja ya zaunar dashi a gefensa "Zauna mana".

Da gaske Ibrahim baiji dadi ba shiyasa ma ya wayance ya baro gidan bayan an gama murnar tashin nasu. Shine abokin Emzee na farko wanda har yau bashi da kamarsa. Abokan sirrin juna ne wadanda suke kokarin koyi da iyayensu. Duba da wannan da kuma gudun wancan zargi da ya darsu a zuciyar Ibrahim din ya sa Emzee fada masa abinda yaji.

Baki Ibrahim ya rike yana mamakin wannan labari "tab, inama dai Radhiya ce taji wallahi da anyita ta kare. Yanzu kai bazan so ka soma fadawa su Ummi ba rigima ce kawai za'ayi gashi Nene tace bata tabbatar ba"

"Amma da gaske fa wai Daada take so yana auren kanwarta." Tsaki yayi ransa yana kara baci "seriously man abin nan ya dameni fa"

"Ai dole amma zancen gaskiya shawarar da zan baka kada ka bari yayi affecting alakarka da Halifa. Ni sai yanzu na gane yadda ka rinka shareshi kafin mu bar Sumaila"

"Kuma kasan Allah bana jin dadin yadda nake masa. Kawai ji nake idan ina kula shi naci amanar su Ummi"

"Tunda Malamijo yace zaiyi bincike ka bari yayi. Shine fa babansu nasan ko don abinda ya faru da majalisar dinkin duniya ta mayu bazai bari irin haka na faruwa a gidansa ba"

Dariya sosai Emzee ya rinka yi suka mayar da hirar kan shirun da gidan yake yi saboda rashin Radhiya. Kofar dakin suka ji an kwankwasa sai muryar Zayyana tana tambayar ko Emzee ne a ciki. Tare suka fito da Ibrahim suka zauna tana tsaye da Daada karami a hannu Emzee ya karbe shi.

"Zan wuce dakin Mama naji kamar muryarka Ya Emzee. Yaushe kazo?"

"Ban dade ba ko Mama bata san ina gidan ba. Ya su Mami...zan ma dai shigo ai"

Shi kadai take kallo ta dauke ido daga saitin Ibrahim tace "DK na kawowa Mama ya tashi daga bacci bari na mika shi na koma girki nake yi"

"DK kuma?"

Ibrahim yayi saurin cafewa "ta dage a rinka kiransa DK wai Daada Karami saboda a bambanta shi da Daada. Sai nake ga hakan yafi ko?"

Tabe baki tayi ta wani juya idanu irin na 'yan mata masu tasawa suna jin kansu ta murguda baki "uhumm Ya Emzee sai ka shigo kaji akwai story" wucewa tayi ta kai DK wurin Mama tazo ta sake cewa Emzee sai ya shigo sannan ta fita.

Rufe kofarta yayi daidai da dariyar Emzee harda rike ciki. Ibrahim ya bata rai kuwa "me kake yiwa dariya?"

"Babu komai wani labari na tuna" yana kokarin danne dariyarsa saboda yadda damuwa ta mamaye fuskar Ibrahim sosai.

Kamar mai shirin kuka yace "Kaga ka dena dariyar nan muyi magana sosai. Ka lura da abinda Zayyana tayi min ko? I can't remember the last time da tayi min magana ko ta amsa min." 

Wata muguwar dariyar Emzee ya kuma yi sai da Mama ta fito. Gaisuwar ma da kyar yake mata yana kallon Ibrahim dariya na cinsa.

"Sojoji fa baku da kirki idan kunso mugunta. Yanzu wannan dariyar ta mene?" Mama ta tambayeshi don tasan ba abu bane da ya saba.

"Mama ki sa mana albarka kawai"

Kai ta girgiza ta koma ciki kawai. Ibrahim kuwa tashi yayi zai bar wurin Emzee ya riko shi.

"Dawo mana muyi magana dan uwa"

"Kana wannan dariyar kamar sabon kamu"

"Ba dole inyi ba ina kallon fadan masoya"

Duka hannu bibbiyu Ibrahim yake kai masa "ni da Zayyana? Amma ka cuceni ma. Kai baka ga yadda take murguda min baki bane?"

"Ibrahim wai kana nufin baka san kana son Zayyana ba?" Ita ce tambayar da Emzee yayi masa da ta shige shi ba zato ba tsammani. 

"Matsalarka kenan ko yaya ka sami chance sai zancen soyayya. To ni dai kada kaje kayi min sharri bance ba"

"Naga ka damu ne saboda ta dena kula ka. Kana magana kamar kayi kuka duk dan tale bakin nan kaima sai da kayi min yanzu"

Ya fuskanci kamar tsokanarsa Emzee yake yi kawai ya tashi "meye laifina don na damu? Kanwata ce fa. Ko gaba kake so muyi bayan kasan matsayin masu gaba a addini"

Haba Emzee ya rike shima yana tashi "da gaskiyarka kuma fa. Bari naje dai naji nasan story din nata baya wuce tayi sabon saurayi. Zanyi mata fada kuma akan wannan halin da ta tsiri yi maka"

Duka zancen dena shigar Ibrahim yayi daga lokacin da Emzee yace labarin saurayi zata bashi. Ransa har ya soma baci.

"Yanzu hirar samari kake yi da karamar yarinya Emzee, gaskiya bai dace ba. Muje idan kai bazaka iya yi mata nasiha ta dena kula samari ba ni zan iya."

"Ta dena kula kowa sai kai ba" Emzee yace a hankali yadda bazai ji ba.

Bangaren Mami suka je. Jawad yana ta wasansa a falo shi kadai sai motsin Zayyana a kitchen. Saboda tana tsammanin shigowarsu tunda ta dawo daga kai DK bata cire hijabin jikinta ba dan madaidaici iya kugu saboda saukin aiki da kare jikinta. Wannan tarbiyar Mami ce kaf dinsu har Radhiya ta koya musu zama da mayafi ko hijabi a kusa saboda samarin dake gidajen uku. Idan daya muharraminki ne to fa sauran biyun ba haka bane. Yana daga cikin kuskurenmu a fake da 'yan uwantakar da aure zai iya shiga tsakani 'yan mata suyi ta saka kaya su matse jiki iyaye na kiran wanta ne ko kanwarsa. Bayan zamanin yanzu ko muharraman ba kowace shiga ce ake iya bayyana a gabansu da ita ba saboda yadda shaidan yayi tasiri a kwakwalenmu.
Chapter 107 · 0% Book details