← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 157

Sashe 105

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nagode Marka kuma sha Allahu kafin ki tafi zaki ga sauyi. Taron hadin kai zanyi a gidan nan Mairama tana dawowa daga Nijar"

Sai yanzu tayi murmushi "ya dai kamata, ai Radhiya ta fada min dawowar baban nasu da alkawarin zasu zo min."

Hirar zumunci suka yi sosai tana ta bashi shawarwari. Rokonta yayi ta taimaka taje masa bikon Hajjo kafin ya shawo kan Yadikko.

"Wani hanzari ba gudu ba Malamijo" Nene Marka tace kafin ta tashi "ka kira Salame kayi mata jan ido irin na uba mahaifi wanda ya isa da gidansa . Ita ce fa babba a gidan nan"

"Ina jin fa kanta ya kwance wannan. Jiya ta bani mamaki wai sai gata. Nayi zaton dubiya tazo yarinyar nan sai cewa tayi wai tayi magana da wani Malami suna tantamar ingancin auren Mairama da Zayyan. Wai yace mata shekara hudun farko da basa tare matsayin saki daya ne, ta biyi kuma saki biyu ta uku saki uku. A takaice dai wai na rabasu a barshi ya nemi wata itama ta sami daidai ita. Ni dai kaina daurewa yayi sosai nace Salame ko ta fara hauka ne"

Nene Marka bata taba niyar fallasa maganar son da Salame take yiwa Zayyan ba amma jin wannan magana ranta in yayi dubu to ya baci. Da za ta ga Salame yanzu wallahi sai ta mareta. Nan take ta warwarewa Malamijo wannan batu da kuma kakkarfan zargin da take na cewa ita ta makanta kanwarta Mairama tsahon shekaru goma saboda ta auri Alh Indararo.

A kidime ya tashi zaune sosai "Kin gane min 'yar jakar uba"

"Shiyasa nace ka hade min kan yaran nan"

Kan Emzee wata irin sarawa yayi da jin wannan mummunan labari. Kawunsa Ayuba ne yazo da abokansa malamai shine ya turo shi yi musu iso wurin Malamijo kafin ya gama yiwa tagwayen kannensa addu'a.

Kai tsaye Emzee ya shiga dakin cikin bacin ran da bai taba yin makamancinsa ba. Jijiyoyin kansa sun tashi idanu sunyi ja.

"Nene" yace da wani irin yanayi mai ciwo.

Hankalinta da na Malamijo a tashe ta dafa shi "Zayyan don Allah ka bar maganar nan inda ka ji ta. Zancen makarantar kuma zargi ne kawai"

"Tunda kika fadawa Malamijo nasan ya wuce zargi." Yace a fusace.

"Kwantar da hankalinka Zayyanu. Ni dai na haifi Salame ina mai tabbatar maka babu wani iskancin da zata zo dashi da ban ga wanda ya fishi ba. Zan bi diddgin maganar da kaina. Kai dai ka rufa min asiri kada yayarka taji zancen nan mu duka mu shiga uku. Ka fita hakuri da nutsuwa ka bari muyi komai cikin lumana" Malamijo ya sami kansa da lallaba Emzee.

Ficewa kawai yayi daga dakin a hanya yaci karo da Halifa. Wani mummunan kallo ya maka masa Nene tana biye dashi tace da Halifan allurar soja ce ta motsa saboda Malamijo yayi masa fada. Da yake ba bakon zafi bane sai ya yarda harda tausayawa Emzee din.

Dakin da suka kwana ya shiga ya rinka naushin bango ko zai ragewa kansa fushi. Da ya bar maganar a cikinsa gara ace bai ji ba. Kai dama ace Radhiya ce taji ta gwadawa Salame me ake nufi da uwa. Wai saboda wani can Alh Indararo shine ta makanta musu uwa. Kuma karin abin haushi wai Daada dinsu take so.

"Wallahi sai dai ki mutu amma yafi karfinki" 

"Kai da wa?" Yaji Ibrahim yace daga bayansa. Kasa amsawa yayi sai kwanciya da yayi yana ta juya zancen. Abin ya dame shi matuka ya dena walwala ya matsawa Ibrahim suka tafi Kano gidan kakaninsa. Halifa da Hibbah su ma zasu tafi amma kememe Emzee yaki yarda su hada tafiyar saboda baya ko son ganin Halifa. Washegarin tafiyar tasu yaje yace da Malamijo ya basu kudin mota. Dubu goma ya bashi duk da yasan kudin yayi yawa amma gara ya tafi ko hankalinsa ya kwanta. Kullum da zulumin kada Radhiya ta gane yake kwana. Ta shiga damuwa sosai akan yadda kanin nata ya koma sai matsawa Malamijo take yi akan ya tambaye shi ko ta sanar da iyayensu.

**********

Kwanan su Zayyan uku a Sakkwato sai birnin Agadez a kasar Nijar. Da kwatance suka isa unguwar inda gidan Alh Ghoumar da Alh Sidi suke makotaka da juna. Mammee suna Niamey da mijinta tunda dan siyasa ne. Kowa yayi mamakin zuwan Mairama ita kadai tace banda yaran ta tahi lokacin da ta kira kwaya domin a kwatanta musu hanya. Tante Nasara sai da ta kira Radhiya da Emzee taji muryoyinsu ta tabbatar kowa lafiya kafin isowarsu gidan.

Murnarsu kuwa bayan sun ga Zayyan bazata misaltu ba. Masu kuka na yi masu suma suna yi. Dangin Innar Zayyan sun sake nuna bajintarsu da kwarewa wurin rikon zumunci da murnar dawowarshi. Mammee tayi kuka tayi fadan me yasa basu sanar da ita ba sai da suka iso gashi kowa ya rigata ganinsa. Kwanansu biyar 'yan uwa suna faman kokarin kyautata masa da nuna masa cewa shi din dan dangi ne. Tamkar kada ya baro kasar sai dai dole ya koma saboda litinin zaiyi reporting a headquarter ana nemansa.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: ***********

Tsattsaye suke maza da mata a kofar dakin a aibitin likitoci suna ciki suna aikin kokarin ceto rayuwar yarinyar da ke ciki.

Daga can gefe Hussaina ce take kuka wiwi jikinta duk jini tana sambatun kada autarta ta mutu. Duk cikin yaranta kowa ya shaidi yadda take masifar son auta Hany. Yarinya ce kyakkyawa mai mugun shiga rai. Bata da hayaniya ga kokari a makaranta. Hussaina duk inda ake hirar yara tamkar sauran shidan babu su zancen bai wuce Hany tayi kaza ko Hany tace kaza.

"Kiyi shiru mana Hussaina mu samu su fito aji halin da take ciki" Ummansu tayi mata tsawa.

Alh Baba da akayi komai a kan idonsa ya biyo su asibitin shima hakuri yake bawa Hussainar hankalinsa a mugun tashe. Saboda soyayya yarinya ta sanya reza ta tsinke jijiyoyin hannunta wai gara ta mutu da a rabata da wanda take so. Wannan wane irin zamani ne rikirkitacce haka.

Lokaci ya shude kafin likitan ya fito yace anyi nasarar tsayar da jinin amma fa wanda ta zubar da yawa ana bukatar a kara mata ko leda daya ne zuwa biyu. Hannu na rawa Hussaina ta kira Nura. Blood group dinsa daya da Hany tace maza maza yazo a debi jininsa.

"Kawai ki nemi wani" taji ya bata amsa ga alama ma cikin maye yake don a datse maganar ke fita.

"Nura ni kake fadawa haka? Kanwarka fa nace"

"Tare fa aka gwadamu kuma kema irin naki ne ki bata mana" ya kashe wayarsa ya fada gado rigijib. Kwance a kasa Ghazalatu ce rike da cikinta bayan yayi mata mugun duka. Da rarrafe ta soma tafiya domin ta bar dakin sai ta gano ashe jini ne yake naso a duk inda ta bi ga azababben ciwon ciki ya murdeta. Lallabawa tayi zuwa dakinta ta kira Mummy Gambo ta fashe mata da kuka.

"Sai da nace bazan dawo ba Mummy gashi nan zai kasheni"

Hannu ta kai ta tabo Daddy Haroun ta saka wayar a speaker hankalinta a tashe saboda yadda take jin muryar Ghazalatun.

"Me ya sameki?"

"Mummy dukana yayi ga jini yana bin kafata kuma cikina...cikina..."

Kashe wayar tayi da sauri ta kira Hussaina wadda take kwance ana diban nata jinin. A zatonta Nura ne shiyasa ta matsawa Ummansu ta bata wayar sai dai tana karawa a kunne ta jiyo masifar Gambo hatta Umman tana ji.

"Hussaina ki rubuta ki ajiye sai nasa an daure Nura in ga uban me kuke takama dashi. Yarinyata ba jaka bace da zai rinka dora mata hannu duk lokacin da ta raya masa. Dama kuma na fadawa Alh Baba idan ya kuma dukanta ya daki aurensa"

Muryarta ta zama weak sosai tace "Gambo muna asibiti da Hany ki bari..."

"Bazan bar komai ba. Ki tura a dauko min yarinya a kaita asibiti tace jini yana bin kafarta"

Yunkurin tashi tayi Umma tace ta kwanta ta fita ta sanar da Alh Baba wanda ya hana a fadawa mijin Hussaina da Baban biyu komai sai yadda ta kaya. Dan tsohon sai ya kara shiga firgici ba yadda ya iya haka ya kira Baban Biyu ya sanar dashi. Yana gida a zatonsa Umma tana gidan Alh Baban ne ashe kuma suna asibiti. Kanin su Mami ya nema Allah Yasa ya dawo gida dayake bashi da nisa daga gidan iyayen nasa yazo suka fara tafiya gidan Nura. Bugun duniya Kawu Mas'ud yayi a dan karamin gate din gidan ba'a bude ba. Ya shiga kiran Ghazalatu tana can bata san inda kanta yake ba sai da Baban Biyu yace ya zai kira wasu cikin 'yan uwa su taru a balle kofar sai ga Nura cikin maye ya bude gate din.

"Wane dan...."

Naushi yaji ya sauka a bakinsa da hanci zaiyi magana hasken fitilu ya nuna masa fuskar kakansa da kuma kanin babarsa wanda ya sauke masa naushin kafin ya bangaje shi ya shiga ciki. Kofa biyu ya bude yana leke ya sami dakin da Ghazalatu take kwance a kasa. Da sauri ya ciccibota don ma wahala ta sake zugeta bata da nauyi ya fito ya sakata a bayan mota. Nura yana tsaye ya yi ribas suka bar wurin bai iya motsi ba. 

Asibitin da aka kwantar da Hany suka kaita tunda nan Alh Baba yace su samesu. Ana zuwa Ghazalatu tayi bari na 'yan biyu. Umma kuka ta zauna tana yi sosai kamar yadda Hussaina duniya tayi mata zafi.

"Kinji dadi Hussaina, ga ribar shiga tsakanin Gambo da Hassana kin gani zahiri ko. Itama Gambon da shegiyar kafiya da kin jin magana zata zo ta ga nata sakamakon na dora son zuciya akan komai."

"Umma kada kice haka" Hussaina tace a raunane.

"Matsa min ni na wuce"

Umma ta fita tana share hawaye. A wajen inda motar Kawu Mas'ud take ta sami Alh Baba da Baban Biyu. Ranta yana kuna yau ta manta da surukuta da girman Alh Baba ta soma magana.
Chapter 105 · 0% Book details