← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 157

Sashe 113

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maimakon ya amsa sai cewa yayi "Rinka juya shi hagu da dama zaifi saurin sakewa"

A hankali ta dago kai su ka hada ido. Wata irin faduwar gaba taji tamkar yau ta fara ganin Ibrahim din ba shiri ta kawar da kanta. Bai sake mata magana ba sai da ya rage tafiyar tasu saura kadan.

"Zayyanatu"

Babu inda bai amsa kiran nan ba a jikinta sai bakinta da ta kasa motsawa.

"Nasan kinji abinda naji yanzu kafin ki koma kallon titi haka ne?" Baiyi tsammanin jin amsarta ba ya cigaba da kallon gabansa "my feelings are true idan na sami karbuwa ina fatan kare rayuwata Zayyana Mustapha tana tale min baki idan tana jin shagwaba. Abu daya ne bana so....dena yi min magana da kike yi"

Cusa kanta tayi kawai a tsakanin cinyoyinta gabanta na tsananta bugu ba ita ta sake dagowa ba har aka bude gate din gidan suka shiga. 

A raunane Ibrahim ya dakatar da ita da zata fita "please Zayyana kice wani abu". Saboda yadda yake jinta a ransa idan taki amincewa bai san ina zai saka kansa ba.

A guje ta fice batare da tayi magana ba. Tana shiga gidan tayi sama da gudu dakin Radhiya ta kankameta tana murna. Lokacin ko awa daya basuyi da isowa ba Rahima tana wanka.

"Kalau kike kuwa?"

Dariya tayi "Ras ras Adda" yau anya ma zata iya bacci kuwa take kissimawa a ranta. Gani take kamar ba gaske ba. Wai sai da yayi maganar take ji a ranta tamkar ta shekara da soyayyarsa sai yanzu ta farga. Wayarta ce tayi kara ta kasa dauka da ta ga shine sai rawa da jikinta yake yi ta saka a silent ta fice daga dakin zuwa wurin Ummi. A can tayi zamanta daga baya suka sauka kasa tare Ummi na son dora girki kafin Daada ya dawo tunda bata da mai aiki yanzu dai suke neman ko da mai shara ce ita zata cigaba da girkinta.

Ibrahim suka tarar a falon ya kunna tv amma hankalinsa baya wurin. Kamar ta koma Ummi ta gama amsa gaisuwarta ta turata kitchen ta samo masa abin sha. Tana tafiya Radhiya da Rahima suka sauko daidai fitowarta daga kitchen Radhiya tana dariyar shakiyanci ta mika mata wayarta.

"Gashi nan kin barta a daki wani Khaleel yana ta kira"

Da sauri ta karbe tayi sama sauran kadan ta fadi Ummi ta bita da kallon tuhuma. Ibrahim ne ya hade rai ya cika yayi fam wato tana da wani Khaleel shine taki amsa masa dazu. Ummi ce tace ya hau sama dakinta su gaisa da Innuwuro don tace ita da saukowa sai da safe saboda ba ta kaunar hawa bene. 

Saman ya hau ya sami Zayyana a falo tana ta kai kawo da waya a hannu. Karbe wayar yayi ran nan a bace ya ga akwai lock ya mika mata.

"Bude min"

Budewar tayi ya sake karba da sauri ya nemo sunan Khaleel din ya kira a fusace yana jira a dauka ya fara fada sai wayarsa ta soma ringing. Guntun tsaki yayi saboda Khaleel din yaki dauka ga wayarsa ta dame shi da ruri. 

"Ana yi maka waya" Zayyana tace tana kallonsa a kunyace 

"Babu ruwanki....shi Khaleel din baya daukar waya ne?"

"Nima ban sani ba"

Kira yayi na uku can ba'a dauka ba tasa wayar kuma anki hakura. Yana zaro ta daga aljihu Zayyana ta karbe da sauri ta daga tasa a kunne idanunta a kansa.

"Ya Khaleel ya akayi ne?"

Kallonta yayi ya ciro wayarta dake kunnensa ya tabbatar muryarta ce a ciki yaji. Wani kayataccen murmushi ya saki idonsa yana yawo tsakanin wayar da fuskarta.

"Ni Ibrahim Khaleel din?" 

"Bani wayata ni" ta shagwabe masa.

Biye mata yayi batare da ya sani ba shima tasa fuskar yanayin yadda tayi...tale bakin nan da baya so.

"Kin tayar min da hankali Zayyana. Its not fair sauran kadan zuciyata ta tsaya"

Dariya take a hankali tana sadda kai shi kuwa tamkar ya hadiyeta ya fada tsundum baya fatan fitowa. Wayar ya mika mata da yaji kamar ana hawowa saman ya motsa bakinsa kadan "nagode"

Dakin Ummin da yake a bude ya tafi wurin Innawuro ita koma ta koma kasa inda Radhiya ta hadata da Rahima. Kafin dare su biyun sun dinke tamkar sun jima da sanin juna.

Sai wurin tara Zayyan ya dawo. Sallamarsa kawai Radhiya taji ta tashi a guje kamar yarinya taje ta rungume shi suka sa dariya. Rahima ya kalla da ta gaishe shi a ladabce tare da Zayyana.

Ya saki fuska "Rahima ko? Yaya mutanen gida?"

"Lafiya kalau, mun sameku lafiya?"

"Alhamdulillah" ya amsa mata sannan ya bi bayan Ummi ya hau sama. 

***********

A kwanakin da suka gabata Innawuro ta dage wurin wanke jikarta da ruwan lalle mai kyau wanda babu wani hadi cikinsa sai zallan garin da take jikawa ta hada mata da ruwan turare wanda matar Baffa Gide ta hada mata da wasu itatuwa. Ranar da zata nuna mata yadda zata yi sai ga Radhiya ta fito daga toilet a guje fuska sharbe da hawaye tana cewa ita bazata yi wanka dashi ba.

Innawuro ta rasa yadda zata yi da ita saboda kukan gaske take sai ta Ummi ta shiga tsakani. Tana faman hawaye da jan hanci daure da tawul tace "Ummi so take kawai jikina yayi faci faci da jan lalle a ce min dodo ranar bikin. Kinga fa haka ta taba yi min aski yanzu kuma ruwan lalle...ja take so na koma?"

Zayyan yana jiyo su don ranar asabar ce babu inda yaje hankalinsa yayi dakin kunyar Innawuro ta hana shi shiga amma da tuni ya fito da 'yarsa. Ummi tun tana fada sai ta koma lallabata karshe dai ita tayi wanka da ruwan tace ta jira ta gani ko nata jikin zaiyi ja. Ai kuwa ta jira sai gashi Umminta ta fito jikinta yana wani irin santsi ga kamshi mai dadi.

Washegari da kanta tace Innawuro ta hada mata tace taki suka gama dramarsu sannan aka fara gyaran jikin jika. Rigima ta biyu tana wannan baccin nata kamar wadda aka saukewa buhun siminti Innawuro ta daura mata lalle dungulmi har kusan rabin kafa. Kafa daya akayi ta farka a gigice zata cire Innawuro tasa Zayyana da Rahima suka danneta. Babu abinda Radhiya bata ce zata yi musu ba idan ta tashi ko a jikinsu sai da aka gama Innawuro tayi mata jan ido sosai.

"Wallahi idan kika cire sai na saba miki. Wannan lallen dumama miki jiki zaiyi ana miki gata kina shirme"

Hawaye ne ya digo mata "to sai ki min tsohuwa ta fada kwata ina laifin ma kice a siyo salatif ayi na gayu"

Dun jgure mata kai Innawuro tayi "nasan damuwar taki bata wuce kada azo na biki wannan bai fita ba ko. To kisha kuruminki kina da akalla kwana ashirin dole zai fita kuma bayi miki zanyi a hannu ba"

Baki ta zumburo "kuma safa zan rinka sakawa kullum"

"Da kuwa kin burgeni domin so nake ki rabu da taka wannan tayil din naku duk ba gata bane a jikin mace sanyi na ratsa ta"

Ta dai kwana da lalle amma da safe Rahima da Zayyana sai da tasa suka gudu daga gidan suka koma gidan Mami don cewa tayi balotelli zata yi musu. Tun suna dariya sai gata da almakashi tuni Zayyana ta tsure saboda ta tuna da.

Akan lallen Awwab kansa yasha mita kamar shi ya kulla mata sai hakuri yake bata. Shima suna ta nasu shirin da Yousuf saboda ba wasu abokan kirki garesu ba. Awwab idan ka cire mazajen kannensa da Yousuf din a yanzu da suka yi muguwar shakuwa bashi da abokai a Nigeria sai na wurin aiki. Shiyasa kayan da zai yi amfani dasu na daurin aure iyayensa ya barwa ragama. Baba Hadir kaninsa ya turawa kudi da wasu kayan Awwab din domin ayi masa daidai jikinsa.

A bangaren mata kuwa Mama tuni ta warke don bata zama. Duk abinda za'ayi ita ce gaba Mami da Ummi 'yan kallo. Siyayya suke yi sosai zuwan Mama Kano sau biyu. Zayyan dai ya saki bakin aljihu ne hankali kwance wannan arziki da Allah Yayi masa na ganin auren 'yarsa ba karamin abu bane. Duk wani abu da ake bukata na auren 'yar gata ya yiwa Alheran. Ana haka sai ga dankareren gado da setin kujeru 'yan Italy masu dan karen kyau da tsada Alh Mousa mahaifin Yousuf wato mijin Tante Nasara ya aiko dasu banda kudi masu yawa da ya tura ta account dinta yace kada ta tambayi Zayyan komai idan tana bukatar kari ta neme shi. 
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Sake kiranta akayi taji cikinta yayi wata irin murdawa. Ina ita ina yin magana kuma wai a gaban wadannan mutane harda shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisu. Kan Awwab taji a daidai kunnenta saboda kamshin turarensa ta gane shine cikin rada yace.

"Get up baby" taji tsigar jikinta ta tashi.

A sanyaye ta mike ya rike hannunta suna tafiya cikin burgewa ana daukarsu hotuna sai da ya kaita bakin steps din da zata hau ya tsaya yace mata "go on zan jira ki". 

Har ta haye yana jin taushi da dumin hannunta a cikin tafin hannunsa. Tsayuwa ta gyara ta kalli iyayenta taji wani kwarin gwiwa ta soma magana a nutse. Ta yabawa sojoji akan rayuwar da ba kowa yake da zuciyar yinta ba ta kara da rokon a dube su domin sun cancanci kulawar al'ummar da suke yiwa bauta.

"Soja shi kadai ne yake mayar da kowane dan kasarsa dan uwansa a lokacin tashin hankali. Kowa zaiyi kokarin ceton nasa amma soja zai tsaya ya kai ceto ga wanda kila har ya gama taimakon ko kwakkwaran kallo bazai sami damar yi masa ba bare ace akwai wata alaka. Soja babu ruwansa da bambancin al'ada ko addini. Yare daya yake fahimta shine SAVE, HELP AND PROTECT  EVERYONE." Daada ta kalla tace "Ina rokon afuwar babban bakonmu domin zan saci kalmominsa long live Nigeria, God bless my country"

Haka aka rinka tafawa Radhiya sai da tazo step din karshe Awwab ya mika mata hannu ta rike ya kaita har gaban seat dinta sannan ya koma ya zauna. 
Chapter 113 · 0% Book details