← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 173

Sashe 99

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karon Momy ce take magana tana wani ɗagowa kamar ta kama Hilal ta dake shi.

“Kuna magana ne a jahilce baku san gaskiyar lamari ba, ya kamata a kira Rashida ayi komai gani ga ta sai a fitar da wanda be da gaskiya”

Dady ya kalli Momy.

“Jeki ki kirata. Wallahi na rantse maka Hilal sai duk abunda na tara ya ƙare amman tun da kayi ma ƴata haka sai na wulaƙanta ka”

Ya ƙarasa yana kallon Hilal, jijiyar kansa har wani tashi take irin na ɓacin rai ɗin nan ya kai maƙura.
Momy ta tashi a hasale ta nufi sashenta. Kai tsaye ɗakin Rashida ta nufa sai da ta soma da buga mata ƙofa amman ta ƙi ta Buɗe har yanzu, sai kawai Momy ta zauna a gurin ta soma mata kuka.

RASHIDA POV

Babu yadda Momy batayi amman Rashida ta ƙi ta buɗe ƙofar har duka ƙanenta suka dawo daga makaranta.
Sai da aka yu salla la'asar sannan ta buɗe shima dan Momy ta zo ta zauna a gurin tana kuka ne. Da sauri Momy ta shiga cikin ɗakin cike da tausayin ƴarta.
Bata yarda ta zauna kusa da ita ba, sai dai space ɗin dake tsakaninsu ba wani mai tsawo bane sosai.

“Hilal ne ko? Shine ya saka min wannan cutar shiyasa ya zaɓi rabuwa da ke”

“Miye amfanin sanin wanda ya sa min wannan cutar, bayan cutar ta riga da ta kamani, babu amfanin ayi ta jayayar abu har a tona asirinsa, duk abunda ya faru da ni, Dady ne ya ja min”

Momy ta kalleta

“Ga Hilal can mum kira a falon Dady ki amman ya ce ba zai yi magana ba sai kina nan”

Gabanta yayi dakan huɗu-huɗu har bata san lokacin data kalli Momy baki sake ba.

“Miyasa kuka kira shi? Me zai muku?”

“Shine silar wannan ciwon na ki Rashida dole na zauna da ke, dan me zai sake ki”

Fashewa tayi da sabon kuka.

“Ni bana son ganinsa dan Allah yayi tafiyarsa”

“Ba zai je ko'ina ba har sai an tabbatar da wannan maganar yau”

Momy ta riƙa hannunta suka fito tare. Ba dan Rashida ɗin ta so ba, sai jan Momy dake janye da hannunta har suka isa falon. A jikin ƙofar Rashida ta tsaya ta risina kanta na ƙasa dan bata son kallon Hilal.
Shi kuma ya tsare ta da ido tausayinta duk ya kama shi.

“Dawo nan ki zauna, babu abunda ya isa yayi miki”

Cewar Dady yana nuna mata kusa da shi. Tasowa tayi ta dawo nan tana shirin zama kukan da take ɓoyewa ya fito fili.

“Yi shiru yanzu ba lokacin kuka ba ne, faɗi maganar ki”

Kasa magana Rashida tayi har sai da Hilal ɗin da kansa ya soma bada labarin abunda ya faru from a to z. Sun gamsu sun kuma samu tabbaci ganin yadda Rashida take ta kuka ta kasa ta kare kanta.

Dady ne ya miƙe tsaye ya soma safa da marwa. Ajiyar xuciya kawai yake saukewa yana maimaita

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Momy kan saka kanta yai cikin hijabi tana kuka. Rashida ma kukan take kamar ta mutu. Dady ya kalli Hilal cikin idonsa na marasa kunyar iyaye ya ce

“Zaka iya tafiya”

“Na gode”

Hilal ya furta sannan ya miƙe tsaye ya fice, jiki a sanyaye.

“Kin cuci kan ki Rashida kin kuma watsar da tarbiyar dana baki yanzu ai kin ci ribar zina sai kije ki auri wanda kuke aikata saɓon tare, uban waye ne ma wannan mutumen?”

Dady ya tambaya a tsawace. A nan Momy ta ɗago kai ta kalleshi cikin ɓacin rai ta ce.

“Duk waya ja mata wannan abun ba kai ba? Tana zamanta lafiya ƙalau da mijinta kace dole sai ta yi aiki, babu irin lallaɓar da yarinyar da mijinta ba su maka ba, amman ka dage akan dole sai tayi aiki, ai ga ribar aikin nan ta kwaso ta kawo maka, shine yanzu zaka taso ka rufe ta masifa ka barta ta ji da abunda yake cikinta ko so kake ta kashe kan ta”

Tashi Rashida tayi ta bar musu falon tana wani irin kuka kamar ta mutu. Momy ma miƙewa tayi tsaye ta fice a hasale tana kuka da bata san ranar tsayawar haweyen ba.

Komawa Dady yayi ya zauna har yanzu xuciyarsa bata gama gamsuwa Rashida ƴarsa tana ɗauke da cutar ba, shi dai ya fi son ayi wani gwajin.
Ajiyar zuciya ya sauke, wani yana tuna wani kalami da wata tayi masa a 1952.

KALSOOM POV

Har yanzu hankalinta ba a kwance yake ba, amman ba kamar da ba, dan yanzu tana da tabbacin Hilal ya yarda da ita, ta kan samu sassaucin hakan idan ta tuna.
Sai dai har yanzu bata cin abincin kirki, sai dai abu mai ruwa ko kuma ruwan kawai.

Tana cikin kitchen ta ji ƙarar tsayawar motarsa, nan da nan ta je aikin da take ta nufi ƙofar falo ta tarboshi.
Yanayinsa ya kararta da ita damuwar mijinta, dan haka bataa buƙatar tambayarsa akwai damuwa ko babu mafi ala kawai ta kwantar masa da hankali sannan ta nemi sanin dalilin damuwar tasa.

Da kanta ta zaunar da mijinta ta ɗauko ruwan sanyi ta siyaya masa a kofi ta kai masa a baki, kaɗan ya sha, ya ɗauke baki, sai ta cire ɗankwalinta ta soma shafe masa gefen fuska.

Hannunta ya riƙe ya jata zuwa ƙirjinsa ya rumgume ta, zuciyarsa cike da tsantsar ƙaunarta.

“Hajiya ta har yanzu bata yarda da ke ba”

Ya faɗa dan ya canja tunaninta izuwa wacan damuwar ta gurin Hajiya.

“Ba lallai ne tayi saurin yarda da ni ba, kuma tana da damar ta zarge ni yadda ranta yake so, zan ɗauki ko wani irin hukumci Hajiya ta yanke matuƙar hakan xai sa ta aminta da ni”

Tana kwance a ƙirjinsa take maganar hawaye na bin fuskarta.

“Hukuncinta ɗaya ne, wai sai na ƙara aure”

Ɗagowa tayi ta kalleshi ta girgiza kai ta fashe da kuka. Ɗan murmushi yayi dan kukanta ya sashi nishaɗi, yana shafa gefen fuskarta ya ce

“Ba zaki yarda mijin ki ya ƙara wata ba ko?”

Kai ta ɗaga masa. Sai ya ce

“To ya zaki yi da Hajiya?”

“Wallahi ban aikata ba Hilal Allah shine shaida na”

“Ai ba nine ban yarda ba, Hajiya ce bata yarda dake ba”

“To a tambaye Rafiq ɗin ai yana magana idan na bashi wani abun zai faɗa”

“Rafiq baya magana yanzu, ya koma wani iri kamar ba shi ba”

Cikin rashin jindaɗi yayi magana, yana ciro wayarsa dake aljihu tana ringing. Saurin picking yayi ganin number Nurse ɗin dake kula da Rafiq.

“Subhanallah okay gani nan zuwa”

Yayi saurin ɗaga Rashida daga jikinsa, ya tashi ya nufi ƙofa hankali tashe. Rashida sai tambayar lafiya take be kula ta ba.

ABDOOL POV.

Sai da dare ya dawo Part ɗin Ummi ɗan ya tabbatar ta dawo a lokacin. Duka falo ya same su zaune suna ta fira. Ummi na ganinsa ta aje lemun fata dake hannunta tana masa kallon mamaki.

“Ni nace fa naga Motar ka Haleema tace min wai ba kai ba ne”

Ya ɗan wara ido yana kallon Haleema, kamin ya zauna a kujarar da Amira take zaune dan three seater ce.

“Ai ba zata faɗa ba, a ɗakin ki na same su suna ta miki taɓe taɓe ita da wannan yarinya”

Ya nuna Amira data tsare shi da ido.

“Wallahi gyara ne Amira take miki, ba wai komai muke miki ba, hba sai ka ce yara”

Ummi bata bi ta kan Haleema ba ta kalli Abdool.

“Ya hanya? Ka ci abinci?”

“Na ci gidan Babana, ku da ban ma tarar da ku ba”

“To ai baka faɗa ka ce za ka zo ba, gashi ma miyar kifi aka yi kuma baka son kifi”

“Ni wallahi wannan zuwan ma be min daɗi ba, ɗan hutu ne na samu ina da zumuɗi zan zo gida shine wai kuma Mai Martaba sai naje zaria ɗaurin aure”

“Ai shine dai-dai kai kenan baka son shiga mutane kamar wani aljani. Me za'a girka maka?”

“Wa zai girka min?”

“Ni”

“Okay to a min wani abu new. Ba wanda aka saba ba”

Tashi Ummi tayi ta nufi ɗakinta tana dariya.

“Kai kam matarka ta shiga uku kullum.ba maimata abinci sai anyi wani abu new”

Shima.dariyar yayi ya tashi ya rufa mata baya yana faɗin

“Lallai kam, idan kam mace bata iya abincin ba zamu samu matsala da ita”

“Ko da kana son ta?”

“Aifa...”

Amira ta bishi da ido, daɗi har cikin rai. Dan tasan indai ɓangaren abincine ba daga baya ba, tun daga kan waɗanda ake yayi har na gargajiya gwargwado ta iya. Ga kuma xama da yayi a kujerar da take zaune abun yayi mata daɗi.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *62*

*1952*

```Cikin rawar jiki ta shigo gidan sai rabon ido take idonta tab da ƙwalla, kana ganinta kasan tana cikin halin damuwa. Bata san inda zata dosa ba tun ba data samu masu gadin suka barta ta shigo cikin gidan, gaba ɗaya a rikice take har bata iya kwantar da hankalinta ta banbanta parts ɗin

“Ke me kike a nan?”

Da sauri ta juyo ta kalle tana ganinsa sak tasan ɗan mai gidan ne, hakan yasa ta risina har ƙasa ta gaisheshi muryarta na rawa. A maimakon ya amsa mata sai kawai ya ƙara haɗe fuska dan ya fahimci irin mutanen ne masu zuwa gurin mahaifinsa a taimaka musu

“Gurin Mai gidan nan na zo, taimako za a min, mahaufiyarmu ce bata da lafiya shine aka rubuto mata magani a asibiti kuma sun ce za a mata aiki, shine aka ce na zo nan za a taimaka mana”

Da kuka ta ƙarasa maganar tana nuna masa takardun asibiti dake hannunta. Karɓar takadardun yayi yana kallon fuskarta da kuma yanayinta, taga komai a rubuce amman saboda mugun nufinsa ya kasa gasgata ta.

“Wata ƙila ma ƙarya kike, haka kuke dan kawai kun ga mahaifina yana taimakawa mutane, kowa sai ya kwaso ƙaryarsa ya kawo ”

“Wallahi ba ƙarya na ke ba, idan baka yarda da ni ba zamu iya zuwa ka duba ta tana nan babbar asibibiti, layin masu ciwon ulcer”
Chapter 99 · 0% Book details