← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 173

Sashe 171

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kusan hoto kala biyar ana masa amman result ɗaya yake badawa, jijiyoyinsa na ƙafa sun murɗe, akan maganin likitoci suka ɗorashi wai ko za a dace amman shiru babu wani labari, tun da aka kawo shi asibin sau biyu kawai abokansa suka riƙa zuwa suna dubasa, ko su ba dukansu ba, masu ɗan sauran imani domin basa kula mutun idan baya da lafiya ganin suke bashi wani amfani, Ubangidansa be taɓa zuwa duba shi ba sai dai ya turo masa da kuɗi kusan miliyan ɗaya ya siye magani, ganin babu wani canjin a ciwon nasa yasa suka nemi ya fita waje ko Allah zai sa a dace. India ya fara zuwa watansa ɗaya a can shi da Amaryarsa amman babu wani canji, bayan sun dawo naija ne ya sake biyan wasu kuɗin aka fitar da shi ingila nan ma labarin babu wani banbancin, can kan satinsa biyu kawai yayi ya dawo saboda kuɗinsa sun fara ƙasa komai na tsada ne a can. Wata asibitin ya canja da suka dawo nigeria, haka yayi ta kashe kuɗi amman babu wani sauƙi balle ma canji wani lokacin idan abun ya taso masa sai yaji kamar a cire masa ƙafafunsa gaba ɗaya ya huta. Lokacin da Amaryarsa ta fara lura da abubuwa sun yi ƙasa sai ta koma gidansu aka bar Mardiya da jinya.

   A familynsu babu wani mai arziki sosai da zai iya ɗaukar ɗawainiyar Asim, wani lokacin ma zuwa su ganshi yana musu wahala musamman yanzu da suka ji shine dalilin mutuwar mahaifiyarsa sai kowa ya daina tausayinsa, suna cewa shi ya jawa kansa, mai gidansa ma tun yana ƙoƙarin aiko masa kuɗi yace ya siye magani har ya daina ganin ɓba sauƙi zai ji ba, kuma bashi da wani a amfani a gareshi yanzu, daman idan suna sonka to kana amfanarsu ne. Wasa wasa ciwon nan ya jawa Asim hasara da yawa duk abunda da ya tara sai da ya ƙare be ji sauƙi ba, hakan yasa suka tattara suka koma gida.

Daga nan ya fara saida filayensa guda biyu da kuma gidansa guda ɗaya da suka rage masa a rayuwa, ranar da aka kawo masa kuɗin jikinsa ya tsananta sosai har ya bawa  Mardiya tsoro sosai.

“Asim ko asibiti zamu koma ne?”

Kai ya girgiza mata hawaye na masa zirya, ga wani wahalallen numfashi da yake.

“Ni kaɗai nasan irin azabar da nake ji Mardiya, ina zanje da waɗannan kayan?”

Kuka kawai take tana riƙe da hannunsa da yayi mugun zafi, sai shi ma ya kalleta cikin hawaye.

“Na yi hasara na tsaɓi Allah, yanzu gashi zan koma gareshi ina ƙazami, bana da ɗa Mardiya balle na samu mai min addu'ah kaico na!”

Ya damƙe hannunta ƙawai zuciyarsa na wani irin fisgarsa har jikinsa sai ya girgiza.

“Makomata tana jirana Mardiya, kwanciyar ƙabari Mardiya, idan Allah ya tambaye miyasa na aikata luwadi me zan ce masa? Nice silar mutuwar Mama, nine na keta haddin Allah, Mardiya na cutar da Namra, na yi isgili, na tara kuɗin da Allah zai tambaye ta ya na samu naira taya na kasheta, na tara kuɗin da basu tare min hisabi ko azabar ƙabari ba, Allah ya ce kar a kusanci mace ta dubura ni na yi, ina zan je da waɗannan kayan Mardiya zafi nake ji zafi zafi...”

Ya fara tari muryarsa na sarƙewa, a take baƙin idonsa ya ɓata sai farin akwai akw gani, halshensa ya karye, tana son ƙara wata magana amman ya ƙasa sai hawaye ke masa zuba, yana wani irin banƙara yana numfashi daker, zafin fitar rai ya tattara a jikinsa sai karkawar yake yana kallon sama.
    Tashi tayi a gudu ta fita daga ɗakin ta shiga maƙota domin kiran jama'ah a kama mata ta kaishi Asibiti, tana ganin alamun ya fara fita hayyacinsa.

Kusan mutun shida suka shigo mata huɗu maza biyu domin taimaka mata, sai dai yanayin yadda suka tararda shi yasa jikinsu mutuwa, idonsa a kafe kansa ya malguɗe halshensa ya fito.
Dattijiwar cikinsu ce ta duba da kyau tana girgiza kai ta ce.

“Sai haƙuri Mardiya mijinki na amsa kiran mahallincinsa”

Da gudu Mardiya taje tana girgiza gawarsa tana kuka.

“Asim Asim”

Dattijuwar tasa hannu ta shafe masa idonsa tana hawaye kamar yadda kowa ke yi. Kamar wacce ta haukace haka Mardiya ta koma tana tsalle tana direwa tana kirama kanta hallaka, da shiga uku.

“Wayyo Allah na shiga uku Asim ya tafi ya bar ni, na bani na lalace wayyo ni Allah na kaicona ni Mardiya”

Sai da jama'a suka riƙata aka fitar da ita waje. Ba'a masa jana'iza ba sai da ƙanen mahaifinsa dake sokoto suka iso, misalin huɗu da rabi na yammancin ranar talata aka sanya Asim a cikin ƙabarinsa bayan an masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada, a saman ƙabarinsa suka tsaya suna masa addu'ar samun sauƙin karɓa tambayar mala'iku kamar yadda Annbi ya koyar. Rayuwa kenan Allah kasa muyi ƙyaƙƙyawan ƙarshen, dukan mai rai dole ya bar duniya😭

NAMRA POV.

Tun da suka je abuja kullun sai ta yi waya da Anty Amarya da Abbah saboda kewarsu, da gangan Abdool ya hanata zuwa ɗauren auren Yasmin duk da taso zuwa, wai baya son yawan nan zata wahalar masa da baby, haka ta saka shi a gaba ta yi masa kuka amman ya ƙi ya barta taje.
Bata zuwa sokoto sai idan zasu yi jarabawa, shi ma dan babu yadda zai yi ne kawai, aiko tana ƙarewa be sake barin ta leƙo sokoto ba.

Katsinar ma tun aurensu Meesha da Haleema da Fauziya, shi ma dan Ummi ta matsa ne da yaso ba zata zo ba sai ranar da za'ayi ɗaurin aure su zo tare, Ummi ta tirsashi ya kawo ta wai zai koya mata ƙin shiga mutane bayan kuma yasan familynsu suna da yawan hidima.

A falo suke zaune, Namra na saman kujera yayinda shi yake zaune a ƙasa ta ɗora masa ƙafafunta saman kai suna kallon wani series drama ya ɗauki hankalin Abdool sosai, saboda criminal case ne ake. Sai dai duk yadda yake son maida hankali gimbiyar ta hana shi, sai wasa take da kunnensa tana sa kunnensa a babban yatsan ƙafarta ta matse sai ya ture mata ƙafa ta maida ya sake turewa ta maida, can kuma ta saka ƙafarta ta dinga zungurar masa kai, duk abunda tayi masa ƙyaleta yake saboda kawai yana son drama da ake.

“Omri yunwa na ke ji, ka ji? Yunwa na ke ji sosai”

Ya kama ƙafafunta gaba ɗaya ya riƙe yana cigaba da kallon tv.
Be bi ta kanta ba sai da ya gama kallon da yake sannan ya tashi ya zuba mata abincin da ke kan dinning a plate ya kawo mata ya koma ya ɗauko mata lemu da cup ya aje a saman tebur ɗin da take gabanta, shi ya riƙa feeding ɗinta har ta ƙoshi sannan ya miƙe tsaye ya kwashe kayan ya kai kitchen sannan ya dawo ya miƙa mata hannu ta riƙa hannunsa ta miƙe tsaye.

“Ɗazu Anty ta faɗa min wai Maryam bata da lafiya”

“Allah ya bata lafiya, babu inda zaki je”

Ta taɓe fuska kamar ta fasa kuka.

“Wallahi ni na gaji da zaman nan, kullum guri ɗaya”

“Ke kin fi son kullum kiyi ta yawo baki Katsina baki sokoto, haba Abnam ki riƙa tausayin abun da yake cikinki mana, kuma nima ki riƙa tausayina kin san ba son nake kina nisa da ni ba”

“Malam ba wani tausayinku, shikenan sai na kashe kai na ku na raya ku? Haka fa ka hanani zuwa gaisuwar Hajiya Sadiya ƙiri-ƙiri, kuma yanzu Maryam bata da lafiya ace ba zan je ba”

“Bari na kira Maryam ɗin naji yadda jikinta yake, kin san ai rashin lafiyarta ba zai wucw a ce ciki ne ba”

“Ni bance ka kirata ba”

Ta faɗa kamar tayi fushi ɗin nan. Zagayowa yayi ta bayanta ya ɗora hannunsa saman ƙaton cikinta.

“Idan kin haihu sai kije ki gansu ai, Abnam miyasa baki tausayin kan ki ne wai? Yanzu baki ganin ko guntun tafiya kika yi yadda ƙafarki yake kumbura balle kuma babba ace daga nan har sokoto haba Hajiya, a riƙa tausayawa kai mana”
Chapter 171 · 0% Book details