← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 173

Sashe 61

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan ta biyu asibiti suka sallame ta bayan anyin mata wankin ciki, sai dai duk tsawon kwana biyun da tayi Hilal be liƙe inda take ba, duk kuwa da kasancewar a gurin yake aiki.
Kuma duk tsoron kwanakin be kawo yaransa ba, sai dai ma'aikaitam gurin sun yi ta zuwa ganinta, sanin cewa ita uwargidan Doc ce.
Ranar data dawo gida ta ci kuka kamar ta mutu, babu irin rarrashin da ƴan'uwanta ba su mata ba amman sam ta ƙi ji sai da tayi kukanta har ta gaji sannan ta saurarawa kanta.
Daren ranar da aka sallame ta ne Asmee ta zo gidan, ita tayi ta bata haƙuri tana ƙara mata ƙarfin guiwa akan inda zata kai ta Hilal ya mayarda ita, sun kitse magana akan zasu tafi tare gobe idan Rashida zata fita. Sun daɗe suna tattauna lamarin kasancewar su biyu ne kawai a ɗakin, tun Rashida na kuka har ta daina.

Tun dawowarta gida bata sa komai a cikinta ba, bata komai sai tunanin Hilal da kuma makomarta, gani take idan har da gaske tana da hiv ya makomar iyayenta zai kasance tun da dole ne tayi mu'amala da mutane. Wayarta ta janyo ta kira wata ƙawarta wace ta kasance likita ce. Bugu biyu ta ɗauka, bayan sun gaisa, Rashida take ce mata

“Dr Fatima, ina son na tambaye ki ne akan hiv, wata sis nace take rubuce-rubuce shine take tambaya ni kuma na ce bari na tambaye ki tun da ni ba sashena ba ne”

Dariya Dr Fatima tayi ta ce

“Amman gaskiya bayanin yana da ɗan tsowo, why not na yi miki ta whatsapp kina online yanzu haka”

“Yauwa to haka ma yafi, bari na hau”

“Daman na san ba zaki kira ni haka nan kawai ba”

Rashida tayi dariya bata daɗin rai ba, ta kashe wayar. A take ta kunna datar ta sa hau online. A contacts list ɗinta ta shiga ta nemi Dr Fatima tayi mata sallama. Sai da ta ɗauki ƴan mintuna sannan ta amsa sallamar sai ta koro mata da bayani.

“CUTAR KANJAMAU/TSIDA (HIV-AIDS)

HIV (human immune virus) ita kwayar cuta ce da take haifar da AIDS (Acquired immunodeficiency syndrome) ma`ana karyewar garkuwar jiki wadda aka fi sani da tsida ko kanjamau. Ita wannan cuta, cuta ce da take karya garkuwar jiki (immune system) wanda ke bada daman wanda, ke dauke da ita ya kamu da wasu cu tuttuka sakamakon karyewar garkuwan jiki. rashin kiyayewa ko kula da wannan cuta kan sa mutum ya halaka a takaitaccen lokaci kamar daga shekara 9 zuwa 11 ya danganta wani yanayi.

HANYOYIN DA AKE KAMUWA DA CUTAR KANJAMAWA/TSIDA

Ana kamuwa da ita wannan cuta ta hanyar shigar kwayan cuta HIV (human immunodeficiency virus) chikin jini. San nan hanyoyin da kwayar cutar ke shiga jiki na dewa, kan iya shiga ta hanyar haduwar jinin me dauke da cutar ga mara dauke da cutar kamar ta hanyar cizon sauro, maniyi, ruwan farji (vaginal fluid) mafi yawan cin masu dauke da wanan cuta na kamuwane ta hanyar saduwa (sex) da me dauke da cutar. Ana kuma iya kamuwa ta hanyar yin anfani da allurar da me dauke da ita yayi mfani dashi. San nan jarirai na iya kamuwa da ita kwayar cutar daga uwa ta hanyar shayar wa, da lokacin da suke a ciki (pregnancy).

Ita wanan kwayan cuta HIV (human immunodeficiency virus) bata rayuwa da keu a wajen jiki saboda haka akan iya kamuwa da ita ta hanyar sunbata (kissing) kokuma yin anfani da wani abu wanda me dauke da cutar ke anfani da shi kamar kofin shan ruwa, abun yanke farce, ma gogin baka (brush).
Idan yazama cutar ta kai marhala na karshe ma`ana AIDS (acquired immunodeficiency syndrome) ba`a kamuwa da ita ta hanyar sunbata (kissing), cin abici tare da me dauke da ita, amfani da kayayyakin ko abubuwa da me dauke da ita ke anfani da su kamar kayan sawa, wayan salula, agogo, wanka a swimming pool, zama a kujera, cizon sauro, ma taci (comb), tawul, da kuma tafiya, hada hanu, zama,da yin aiki tare da me dauke da cutar”

Tun da Dr Fatima ta fara bayaninta Rashida take karanta abunda take aiko mata, sai da ta kai nan sannan Rashida ta aika mata da wata tambayar.

“Amman Dr ya alamomin cutar yake?”

Ta samu minti biyar zuwa shida kamin tayi ma Rashida reply

“Alamomin ita wan nan cuta ta banbanta daga mutun zuwa mutum. Mutane biyu kan iya kamuwa a lokaci guda amma ba lallai sun nuna alamomin iri day aba. Anan zamu raba alamomin kamar kasha uku muyi bayani akai.

 (acute illness)
 (asymptomatic period)
 (advanced infection)

Acute illness

(acute illness) ma`ana alamomin farko na kamuwa da ita wannan cuta. Kashi tamanin cikin dari 80% dake dauke da cutar na farawa da jin kamar alamomin mura (flu-like) dake kai tsawon sati biyu zuwa hudu rukunin farko. Abubuwan dake faruwa a wannan rukuni sune:

 Kuraje kana na a jiki (body rash)
 Zazzabi (fever)
 Boshewar makokoro (sore throat)
 Jin gajiya (fatique)
 Kumburi a (lymph nodes)
 Fashewar baki da alaura (mouth and genital ulcers)
 Chiwon nama (muscles pain)
 Ciwon gabobi (join pain)
 Amai da hamami (nausea and vomiting)
 Zufa cikin dare (night sweat)

Wa yan nan alamomin na faruwa mutum ya gaggauta zuwa kuji don gane yana dauke da ita bai dauke da ita.

Asymptomatic period

(asymptomatic period) ma`ana lokachin bacewar alamomi. A wannan lokaci cutar bata nuna ko wace alama na rashin lafiya ko ciwo na wasu watanni ko shekara. Amma akwai kwayar cutar a jikin mutum. A wannan lokacin kwayar cutar na dada yaduwa (replicating) da kuma kashe garkuwar jiki (immune system). Sannan a wann lokaci kwayar cutar tafi karfi da kuma yadu ta hayoyin da mukayi bayani a yadda ake kamuwa da cutar.

Advanced infection

(Advanced infection) a wannan lokachi kwayar cutar ta riga tayi damejin garkuwar jiki (immune system) yana daukan lokachi amma idan ya kai wannan lokachi to cutar ta kan zama AIDS (acquired immunodeficiency syndrome) mutum kan kamu da wasu cututtuka sakamakon damejin garkuwar jiki (immune system damage) zaizama garkuwar jiki bai iya yaki da kwayar cuta. Alamomin wannan bangare sune:

 Hamami
 Amai
 Gudawa
 Ma tsanachin gajiya
 Raguwar nauyi /rama
 Tari da numfashi sama sama
 Zazzabi me tsanani akai akai (recurring fever)
 Kwararraji masu ruwa a baki ko hanchi ko a fata da kuma alaura,
 bushewar makokoro
 kunburin lymph node na gabobi mara warkewa.
 Kidimewa, tabuwar kwakwalwa daga nan kuma watakil sai mutuwa”

Hankalin Rashida ya tashi sosai wasu daga cikin abubuwan da Likitar ta faɗa duk tana jinsu, amman tayi tunanin ko cikine a lokacin. Ji take kamar ace ba da gaske bane

“Amman Dr Bayan wannan babu wata alama da mutum zai iya gano tabbacin yana ɗauke da cutar?”

Ko da ta tura mata saƙon ta riga ta sauka online, a lokacin 10:23pm ne. Kasa natsuwa tayi har sai da ta lalobu number Dr Fatima ta sake kiranta.

“Dr kina min bayan sai kika sauka”

“Eh Wallahi mai gida ne ya shigo”

“Dan Allah ki taimaka ki ƙarasa min, gobe zata rubuta abun yanzu haka duk ta dame ni”

“Okay bari ya gama cin abinci zan hau online”

Daga haka ta kashe wayar tana tunanin nata mijin. Whatsapp ta shiga tana duba last seen ɗinsa, ta ga biyar da kwata na yamman nan. Dp shi take kallo wani hoto ne ya ɗora yana sanye da kayan likitoci yana murmushi. Fashewa tayi da kuka ta rumgume wayar a ƙirjinta.
Sai da tayi kukanta ta gaji sannan ta ɗago wayar ta sake kallon hotonsa tayi masa kiss sannan ta shiga chat ɗin su da Dr Fatima, ashe ma tuni ta turo mata da bayanin bata gani ba.

“Ana gano mutum na dauke da wannan cutar ta tsida ta hayar gwajin jini, (serum), miyau, ko fitsari ta hanyar sanya musu wasu sinadarai dake sanya a gano kwayar cutar aciki wato HIV (human immunodeficiency virus) wadda ita take haddasa AIDS (acquired immunodeficiency syndrome) wanda mukayi bayani a sama. Anfi gano mutum na dauke da cutar ta hanyar gwajin jini”

Ta haɗeye yawu ya fi sau biyar sannan ta sake aika mata da wata tambaya, wace ita ce dalilin tambayarta tun farko.

“Dr ya mutum zai kare kansa ko kuma wani nasa daga kamuwa da wannan cutar?”

 “Yin gwaji don sanin akwi ko babu.
 Rage yawan saduwa.
 Anfani da roba (condom) wajen saduwa.
 Kiyaye saduwa da mata/maza daban daban.
 Gwaji da kuma maganche cututtukan saduwa STDs (sexual transmitted disease).
 Kiyaye yin amfani da allurar da wani yayi anfani da ita.
 Tabayar likita dangane shan PrEP (pre-exposure prophylaxis) shima wani hanya ne na kiyaye kamuwa da ita wannan cutar

Rashin kiyaye ita wanan cuta kan sa mutum ya halaka da wuri. Ana kiyaye cutar ta hanyar yin anfani da (antiretroviral drugs) magunguna ne da ake afani dasu wajen magance cututtukan virus, kusan ita wanna cuta bata da maganin warkewa sai kiyaye ta, ta hanyar anfani da magunguna da likitan ya dorashi mutum akai”

“Na gode sosai likita Allah ya saka da alheri”

“Ba a son mai cutar yana kusantar hayaƙi, ko cizon sauro ko wani abu makamancin wannan, saboda abu kaɗan yana iya ƙara cutar, an fi mai cutar ya ci abubuwan gina jiki like vegetables”

“Thank you”

Rashida ta rubuta daga ƙarshe, sannan ta kashe wayarta tana hawaye.

“Dole ne naje nayi gwaji dan na tabbatar, wata ƙila ma na ɗauke da cutar, ai za a iya min sheri tun da ba a son zamana da Hilal”
Chapter 61 · 0% Book details