← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 173

Sashe 162

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruwan tsanyi ta dire masa tana dariya tare da kai hannu ta karɓi iv ɗin.

“Lallai mutumen da gaske kake, budurwa ce ko bazawara”

“Budurwa ce yarinya ce ba zaki sha wahala gurin kishi da ita ba”

“Ai ni na yafe kishi da kowa, sai dai ina fatar tasan halin da kake ciki”

“Ta sani kan, sai dai bayan ke da ita da kuma Asmee babu wanda ya san da wannan maganar”

“To ita mai cutar ce kenan”

“Ai kema kin sani baƙya buƙatar na faɗa miki”

“Amman Asmee ta ji?”

“Ta ji mana, to me zata yi?”

“Ba komai kawai ina tuna lokacin da take cewa ba zaka taɓa aure ba ne”

“Ni kaina ina tuna wancan lokacin da ina son aure amman sai na kasa yi sanadin hakan muka faɗa hallaka ni da ke, sai dai kin san komai lokaci ne da shi, ko magani kika yi kika ga ya kama to daman can Allah ya rubuta zai kama ɗin”

“Na yarda da hakan ai ni sai dai na faɗawa wani, kuma ina fatar idan ka yi wannan auren zaka ɗaga min ƙafa, saboda mutane suna ta zargin muna tare ne, kuma zaka iya tonawa kanka asiri indan kana cigaba da ziyarta na, saboda kai ma za a iya gano kana ɗauke da cutar, abu na uku kuma kasan ance idan mace da namiji suka kasance su biyu sheiɗan ne na ukunsu, dan haka bana son wata alaƙa ta saɓon Allah ta sake shiga tsakanina da kowa”

“Nima bana nufin wani abun makamancin wannan saboda i realized that duk abunda ka yi wa ɗan wani sai an yi ma naka, tun bamu je ko ina ba a scul wani malami yayi raped ƴata, ban taɓa faɗa miki ba ne saboda ba labari ne mai daɗi ba, amman a lokacin na samu kai na a wani irin kalar mutum, abun da ciwo sosai Rashida, sai na dinga jin kamar na kama duka familynshi nayi musu yankan rago, but a dole na rufe magana domin idan na buɗe yanzu ne zata shiga duniya kowa yasan abunda ya samu ƴata bayan kuma nine sila saboda ban tsare kaina ba, kuma zan jawa ƴata abun faɗi ne kawai”

Ya share guntun ƙwalla da suka zubo masa.

“Ki dubi Family Hilal ki gani da yake ya tsare kansa, sai Allah ya tsallakar da shi, duk da kina a cikin gidanshi Allah ya tsare ƴaƴansa da matarsa da shi kansa mu kaɗai muka kwashi abun, dubi rayuwar gidansa ki gani gwanin sha'awa, ni ko rayuwa baƙinciki ne da kuka, saboda halin da muke ciki, ko wannan ciwon da ke jikinmu tawace gashi kullum muna cikin kafakafa kar ƴaranmu su ɗauka, muka tsoron mu kai su wani gurin riƙo asirinmu ya tonu”

Rashida ta girgiza kai cike da tausayawa.

“Ba ku kyautawa rayuwar ƴaƴanku ba, ku ɗauke su ku kaisu gurin ƙaƙaninsu mana, ko karka yi sake yaranka suma su kwasa su girma suna nadamar da kasancewar ƴaƴanka, karka ɓata rayuwar ƴaran ka tun suna da ƙurciya, ka taimaki future ɗin su, kai taka ta ƙare su kuma ka yi tattalinsu...”

Ajiyar zuciya ya sauke yafi sau goma sannan ya miƙe tsaye jiki a mace ya fice ba tare da ya ce da ita komai ba.
    Rayuwa kenan sau da yawa Allah yake maka talala kayi ta iskancin da zarar ya tashi kama ka ba zaka ga da kyau ba, kuma matuƙar be yafe maka ba, zaka je lahira ka tararda abunda ka aikata. Duk magane-magane da Asmee ke yi tana ganin kamar ta ci riba wajen hana mijinta aure ashe ba riba bace lokacin auren ne be yi ba sai yanzu, tun da gashi yanzu zai yi auren,garin neman gira an rasa ido ta kwaso musu cuta tana nadamar da babu ranar daina kukanta. Ita kanta Rashida dake yi wa Kalsoom magani a dole ai yanzu ta saka mata ido ta ɗauke ta ƴar'uwa tun da taga addu'ah da tsarin Allah yana tare da wanda duk ya nemi taimakon Allah, tayi iya yinta amman bata raba Kalsoom da gidan mijinta ba saboda Allah ya riga ya rubuta ita ɗin ce dai.
Mata da yawa suna shiga haƙƙin mazajensu wajen ganin sun hanasu aure ko kuma sun mallake miji da kishiya, bayan kuma sun san Allah zai tsayar da su a gabanshi yayi masu shari'ah ranar da baki baya iya magana.

Jiki a mace ta miƙe ta yi nafila wato ƙabli asri sannan ta ɗora da la'asar ɗin, tasbihi da hailala da hamdala ne suka biyo baya tana gode Allah da ya nuna mata kuskurenta tun a nan duniya da ake karɓar tuba, kuma ya bata ikon tuban, kana ya tsare mata yaranta kuma ya basu uwar da zata riƙesu ta tarbiyantar da su, tabbas yanzu ta tabbatar Ubangijinta yafi kowa sonta, shi ta tsaɓawa kuma ya yafe mata har ya musanya mata ta wani ɓangare.
[7/31, 9:26 PM] Khadeeja Candy♥: *93*

Lafewa ta yi a ƙirjinsa tana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa, sai ƙara shigar da kanta take tana shaƙar ƙamshin turarenshi.

Hannu yasa yana shafa bayanta, idanuwansa a lumshe. Wani abu yaji yana sauko masa marar misaltuwa, be taɓa hugging wata mace kamar yadda yayi a yanzu ba, wata mace kuma bata taɓa kwantawa a ƙirjinsa kamar haka ba, ɗayan hannunta dake cikin hannunshi ya soma matsawa a hankali yana lume baki.

Jin shafar da yake mata ne ya sauya salo ne yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, idonsa har yanzu kulle yake, hakan yasa ta ɗaga daga jikinsa gaba ɗaya ta zare hannunta daga nashi.
Sai ya buɗe idonsa yana kallonta, fararen idonsa sun fara rinewa zuwa ja ga wani ruwan hawaye da ya kwanta masa. Hannyensa yasa ya riƙa fuskarta.

“I Love you so much Abnam”

Kallonshi take kamar yadda shi ma yake kallonta, sai hawaye suka zubo mata.

“Ban san mi Asim yake nufi da ni ba, ban san miyasa ya ɓullo ta wannan hanyar ba, na masa iya hallacin da zan iya, saboda shi na rabu da iyayena, na bishi na zauna da shi a inda ban taɓa mafarkin zan zauna ba, lokacin da arziki ya zo masa sai ya guje ni, yace min baya son haihuwa, da cikin ya kure na je garin kaduna ba tare da na san kowa ba, Lamido yayi min masauki a gidansu, a gidan cikina ya zube.

Wallahi tallahi ya sake ni Abdallah, ban san miyasa ya canja min ba, har yana tambayar ɗan sa”

Hawaye na bin fuskarta take maganar zuciyarta cike da rauni. Fuskarta ya saki ya kama hannayenta ya riƙe gam.

“Na yarda da ke Abnam, Asim yana son shiga tsakaninmu ne, saboda yana tunanin zamu fara sabuwar rayuwa mai kyau, karki saka ranki cikin matsala nasara bata zuwa ba tare da wahala ba”

Ƙofar da Hajiya Kilishi ta buga ne yasa shi kallon ƙofar sannan ya kai hannu ya share mata hawayenta. Sannan ya miƙe tsaye ya buɗe ƙofar.

“Hajiya...”

“Na'am, Abdallah ya mai jikin”

“Ta ji sauƙi”

“Ga breakfast nan Hajiya ta aiko su Amal su kawo ance wayarka na kashe”

“Oh Okay bari na kunna”

“Okay ka gaishe da ita”

Ta juya shi kuma ya rufe ƙofar ya dawo yana ciro wayarsa da ke aljihu ya kunna, sai ya kira Ummi.

“Abdallah na kira wayarka kashe”

“Na kasheta ne saboda Doc yace min ana bukatar ta samu bachi, barka da safiya”

“An tashi lafiya ya jikinta? Miya same ta? Meesha tace min kawai sun ga ka fito da ita a sume”

“Ummi labari ne mai tsawo da rikitarwa zan zo anjima”

“Okay ga abinci nan na aiko muku nasan zata buƙaci abincin a yanzu, amman dai ka faɗa min ko minene”

A nan ya soma labarta mata abunda ya faru. Ta kiɗima sosai abun ya zo mata kamar almara, sai dai ta kwantarda hankalinta saboda kar hankalin ɗanta ya tashi.

“Allah zai muku mafita Abdallah”

“Na gode Ummi I love you”

“Allah ya maka albarka”

Yana sauke kiran wayar Mai Martaba ta shigo, cike da ladabi yayi picking.

“Assalamu Alaikum Mai Martaba”

“Wa'alaikassalam, Babana ya mai jiki”

“Alhamdullillah ta ji sauƙi fatar ka tashi lafiya”

“Alhamdullah, Babana bana son ka tashi hankalinka na san kana sonta sosai, sai dai bana son da kake mata ya iya rufe maka ido ka tsallake gaskiya, kai ɗana ne nafi son komai za'ayi ka tsaya kan gaskiyarka”

“Mai Martaba kafi kowa sani na, ba zan taɓa aikata abun assha ba, kuma zan saurareshi matuƙar yana da hujja”

“Allah ya maka albarka”

“Amin Mai Martaba Allah yaja kwananka”

Daga haka ya sauke wayar sai ga kiran sisters ɗinsa ya shigo sai kuma na Maryam, sai dai be ɗaga ba sai kawai ya kashe wayar. Ya miƙe tsaye ya fita. Sojojin da ke gurin da dogarai ya sallama sai dogara ɗaya ya bari, sannan ya dawo ɗakin.

Wannan karon jikin windo ya same ta tsaye fuskarta na kallon ƙasa kasancewar inda suke gidan sama ne. Ƙarasawa yayi ya riƙe kunkurunta ya ɗora kansa saman wuyanta.

“Jiya ya kamata ace na tare, amman hargitsin da ya faru jiya ya hana hakan, dare biyu kenan na amarci ina kwana ba cikin daɗi ba, a wacan daren fargaba da tunanin halin da na bar mahaifina da kuma tunanin makomar aurena, yanzu kuma wannan hargitsin ya taso, Ina roƙon Allah ya tsayar a nan kar wannan abun ya shafi rayuwar auren da zanyi nan gaba”

Ɗayan hannunshi yasa ya zagaye cikinta.

“Wannan rigimar ma na ɗan lokaci ne, kar zuciyarki ta sake irin wacan tunanin, ko kaɗan Abdallah be yi kama da Asim ba, a halitta balle kuma a hali da ɗabiyu da halaiya, Wannan karon da Abdalla aka ɗaura miki aure ba Asim ba, kar ki sake irin wacan mafarkin”

Juyowa tayi ta riƙa fuskarsa tana hawaye.

“Zuciya bata iya tantance gaskiya da ƙarya a yanzu, shi ma haka yayin ya yaudare ni da daɗaɗan kalamai, da su ya siye ni har na rufta a duniyarsa mai cike da duhu da kuma hayaƙi”
Chapter 162 · 0% Book details