← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 173

Sashe 156

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abbah ban da wani zaɓi sai naka, abunda duk zai fito daga bakinka shi xai fito baki na, kai da Mai Martaba duka iyayene a gurina, duk yadda kuka yanke yayi, idan ma a yanzu kuke son a ɗaura auren babu matsala ni dai a guna, sai idan gurin Abdool”

Abbah ya jidaɗin maganarta sosai, daman haka yake son ta kasance gareshi mai biyar dukan umarninsa da yarda da abunda ya zaɓa mata, babu ruwanshi da duba zamani ya canja a ƙyale yara su yi ra'ayin kansu, yafi son duk yadda ya zaɓa maka kawai ka bi.

“Na jidaɗi da wannan kalami na ki Namra, kuma tun da har kin amince zan faɗawa Mai Martaba kuma na san shi ma zai jidaɗin wannan maganar, daman shi yana son a saka me nan da wata ɗaya”

Dam! Gaban Namra ya yanke ya faɗi sai ɗai bata nuna komai a fuskartaba.

“Babu matsala a gurina Abbah, amman ya maganar Lamido?”

Abbah ya sauke ajiyar zuciya.

“Yadda kike so Namra ba zai yiyu ba, ba zan ɗauki mutun haka kawai na bashi MD, mutanen duniya a yanzu ba abun yarda ba ne, abunda Uxair yayi min kawai ya isa ya lurar da ni duniya, zan iya bashi aiki dai a ƙarƙashina, kuma daman ina da niyar gyara musu gidansu kuma na ƙullawa mahaifiyarsu jari, ko da be yi komai ba zan iya masa haka balle kuma ya taimake ki sun riƙa ki tsakani da Allah, na san yana son ki Namra kuma kema kin san da haka, sai dai hakan ba zai sa na ɗauke shi haka kawai na bashi mb ba”

“Amman Abbah idan ya fara aikin nan ka aminta da shi zaka iya bashi md, wallahi mutumen kirki ne”

Abbah yayi murmushi.

“Har yanzu akwai ƙurciya cikinki, ai ba a gane mutum mai amana a fuska sai a aiki, sai dai na yarda da abu ɗaya, duk yadda duniya ta lalace za a samu na ƙwarai, zan jarrabashi na gani”

“Na gode Abbah”

“Allah ya miki albarka”

“Amin Thank you”

Haka ta tashi jiki babu gwari ta fice. Tun daga lokacin aka fara shirye-shirye, a dukan ɓangarorin guda biyu. Kullum sai Abdool ya kirata safe, rana da dare domin jin muryarta da kuma son sanin ko akwai abunda take shiryawa, sai dai duk lokacin da ya tambaye cewa take bata shirin komai.

Hakan yasa ya baro Abuja a daren ranar ya sauka sokoto, dan kwata-kwata ya rasa gane kan matarshi (His wife to be). Haƙuri yayi har sai da yayi sallah isha'i sannan ya doshi gidansu Namra. Wannan zuwan na musamman ne baya son kowa yasan da zuwanshi sai ita, a harabar gidan ya faka motarshi ya kira a waya yace mata yana gefen gate. Bata yarda ba har sai da ta saka Hijab ɗinta ta leƙo ta hango mota a gurin sannan ta yarda da gaske yake.
Ƙarasa ta yi kusa da motar ta buga ƙofar motar sai ya fito ya buɗe mata motar ta shiga sannan ya koma mazaunin direba ya zauna. Wasa take da ƴatsun hannunta ta kasa buɗe baki ta gaisheshi ma balle ta yi masa wata maganar, ta dai yi shiru tana shaƙar turarensa da ke kaiwa hancinta ziyara. Wani dogon numfashi yaja ya sauke kana ya kalleta ya ce.

“Na miki zuwan bazata, saboda na lura kamar baki cikin yanayin da ya kama ki kasance, idan har bakya ra'ayin aurena Namra, wallahi ba zan cilasta miki ba, duk yadda nake son ki zan iya bawa zuciyata haƙuri matuƙar ke hakan shine farincikinki, ba jindaɗina ba ne muyi aure kuma mu koma muna zaman da be kamata ba ni da ke, ba zan aureki dan wani abu ya shiga tsakanin mu har na sake ki ba, burina idan mun yi aure ni da ke mutuwace kawai zata raba, ba zan aureki dan wani abu na ki ba sai dan so da tausayi waɗanda abubuwa ne guda biyu da ba zasu taɓa saka ka ganin laifin mutum ba, shiyasa bana ganin laifin abunda kike min, sai dai ina kallon hakan da rashin so, ina ganin kamar na cilasta miki ne akan abunda baki da niya...”

Ɗagowa ta yi ta kalleshi idonta tab da hawaye, cikin rawar muryar ta fara magana.

“Tun bayan abunda Asim yayi min, ban taɓa tunanin zan so wani ɗa namiji ba, haka na saka a zuciyata kuma haka na ayyana. Amman daga lokacin da na saka ka a idona gidansu Lamido, sai wani irin kwarjini da ƙimarka suka kama ni, sai kuma gashi ka zama sanadiyar haɗa ni da iyayena, wannan ne yasa son ka ya ɗasu a zuciyata, ko da ban aureka ba, zan son ka Abdallah, irin son nan da ƴan matan hausawa suke yi ma mazan hausa novels da larabawa, kasan irin wannan son yafi ko wanne haɗari da saka rayuwa cikin ƙunci da nadama, da kuma ganin munin kowa, sai gashi Allah ya ƙaddara zan zama matarka, amman son da na ke maka doesn't give you the chance to hurt innocent people”

Sanyayiyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta irin kallon nan mai cike da shauƙin so da ƙauna.

“Wana cutar?”

“Lamido, ya ƙi ya faɗa min abunda ka yi masa amman nasan abunda ka yi masa ba ƙarami ba ne”

“Dukan abunda na yi masa saboda ke ne Namra, saboda ina son ki ne, nasa an kawo min shi daga kaduna zuwa katsina ne saboda na masa magana a akan ki, nace zan biyashi ko nawa ne, ya ƙyale ki saboda bana son mu tarayya ni da shi a lokaci ɗaya mu raba miki hankali, saboda na lura yana son ki, kuma zuciyata tana nuna min zai bibiyeki, amman shi be ƙarbi tayin da na masa ba, har ma yayi min iƙirarin shi ne zai mallake zuciyarki, kuma yayi nasarar aurenki, amman duka be faɗa miki wannan ba sai a yanzu da yaga komai ya kankama kuma ya ɓoye miki saboda yana son shiga tsakanin mu, wannan yasa na roƙi Mai Martaba akan ya nemi a rage tsawon lokacin auren da aka saka, saboda magangu sun yi yawa akan zan auri bazawara, kuma gashi Lamido yana ƙoƙarin yi min zagon ƙasa, ina gudun kar shedan ya shiga ciki ya lalata lamarin aurenmu, saboda duk lokacin da aka shirya abun alheri za'ayi sai ka ga shedan na neman ɓata abun”

“Amman abunda ka masa baka kyauta ba”

Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka. Shi kuma ya kwantar da kansa jikin kujera yana kallonta, dan har cikin jininshi maganarta ta shiga ta zauna, a take kasala ta sauƙo masa.

“Naji Gimbiyata ayi haƙuri a gafarta min”

Yanayin yadda yayi mata maganar yasa ta jin kunya har murmushi ya suɓuce mata bata shirya ba.

“I love you, i can't wait to see us on one bed...”

Ya faɗa muryarsa ƙasa sosai kamar mai raɗa. Buɗe motar ta yi zata fita sai yayi saurin riƙo hannunta, ta zaro ido tana faɗin.

“A'uzubillahi...”

Sai ya saki hannunta da sauri.

“I cross the limit... But sorry wai ba mu gama maganar ba”

“Mun gama mana”

“Dan Allah ki yi magana da kyau Abnam ki daina kashe min jiki”

Ƙyalƙyale ta yi da dariya, saboda har ga Allah ya bata dariya ita bata yi dan ta kashe masa jiki amman shi yana ƙoƙarin juyarda abun. Shima dariya ya samu kansa da yi saboda be taɓa ganin ta yi irin wannan dariyar a gabanshi, ta tafi da imaninshi sosai.

“You're so cute Abnam na fi kowa sa'ar mata”

Ƙoƙarin kawarda maganar ta yi.

“Na san maganar akan events ne, so bazawara zaka aura bana buƙara events bayan walima”

“Amman ni saurayi ne ai, ina buƙatar ayi mana wani ɗan event haka ko da biyu ne ko ɗaya”

“Ni dai idan ta ɓangarena ne bana so”

Ya ɗaga kafaɗunshi.

“As you wish your royal highness”

Dariya ta yi ta rufe masa motarta ta tafi. Shima murmushi yayi yana mai jindaɗi.

Namra ta kusan minti talatin tsaye a jikin windo tana kallon motar Abdool, sai ya kunna motarsa ya bar gidan sannan ta fito ta nufi sashen BQ.

Tun daga nesa ta hango Lamido zaune yana danna wayarsa. Ta ƙarasa kusa da shi tana masa sallama.

“Wa'alaikissalam, Hajiya”

“Na'am hutawa kake yi”

“Ina ɗan duba duniyar facebook ne”

“Hakan na da kyau, amman miyasa bakinka yayi nauyi har ka kasa faɗa min Abdool ya nemi ka siyar masa da soyayyata ne?”

Murmushi yayi ya cire hular taɓani ka ji hadisi da ke kansa ya ce

“Saboda soyayyarki tana da girma a gareni, amman ina fatar ya faɗa miki mahaifinshi ne dalilin talaucewar mu”

“Abunda ke tsakanin Mahaifinka da mahaifinshi be kamata ya shiga tsakanin ku ba, balle kuma ni har na shigo ciki, be nuna min ya san kamin lokacin ba kuma kai ma baka nuna min ka san shi, dan haka babu ruwana da abunda ke tsakaninku”

“Na gode Namra na gode sosai”

Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya shige ɗakinshi. Ita kuma ta juyo ta dawo part ɗin Anty Amarya, a bakin ƙofa ta samu anty amarya a tsaye tana mata wani mugun kallon.

“Me kika je yi can?”

“Magana na yi da shi”

“Wace magana bata da suna ne? Ban miki maganar tun ranar akan ki daina keɓewa da shi ba?”

“Wallahi ba abunda kike tunani ba ne, yana ta ƙoƙarin shiga tsakani da Abdool ne ni kuma ban ga ne ba sai yanzu, shi ne na masa magana”

“ko ma minene karna sake ganin ki part ɗin nan, ai ba zarginki nake ba, kawai ina gudun shaedan ne, kuma tun da yana son ki zai iya aikata miki komai, ki yi taka tsantsan”

Ta gyaɗa kai.

“Ba zan sake ba daga yau”

“Good”

Anty ta bata hanya sannan itama ta shiga.
Ko da Namra ta shiga ɗakinta ta tararda missed calls na Abdool. Dan haka tana cire Hujabinta ta kirashi.

“Hi Babe-Abnam”

“Abdallah”

“Faɗa min wani abu mai daɗi...”

“Ni ko tambayar ka zan yi, miye tsakanin mahaifinka da Mahaifin Lamido”

“Me kuma ya sake ce miki?”

“Yace wai mahaifinka ne silar talaucinsu”
Chapter 156 · 0% Book details