← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 173

Sashe 91

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da yayi ma Rafiq Alurra bachi sannan ya rufe ɗakin. Ya koma office ya cigaba da aikinsa, bayan ya gama, ya sake leƙa ɗakin yaga har yanzu bachi yake. Sai kawai ya nufi gurin motarsa dan yana buƙatar taje gida yayi wanka.
Yana hanyarsa ta tafiya Hajiya ta kira shi wai zata shigo da dare akwai magana mai muhimmanci da take son suyi, shi dai da to kawai amsa mata ba dan ransa yana cikin daɗi ba, ya faka a rabar gidan ya fito jiki ba ƙwari ya shiga ciki.
Tun a falo gabansa ya soma faɗuwa jin sautin kukan Kalsoom, da sauri ya karasa ɗakinta, sai dai kamin ya shiga ya ji ba acan kukan yake fitowa ba, a ɗakin su Ezzah ne. Ƙarasa yayi ɗakin ya tsaya daga jikin ƙofa yana kallonta. Juyowa tayi ta kalleshi da idonta da suka yi ja saboda kuka.

“Haƙiƙa ina son ka Hilal, dukan abunda ya dangance ka ina sonsa ko da kuwa abun nan mai cutar da ni ne, miyasa zuciyarka ta yarda na aikata bayan ban aikata ba? Ka raba ni da ƴaƴanka Hilal bayan yanzu sun zamo jinin jikina, ban aikata abinda kake zargina da shi ba Hilal Wallahi ban aikata ba”

Ya rumgume hannayensa yana mai jingina da jikin ƙofar.

“To waya aikata?”

“Ban sani ba, amman na rantse maka da Allah ban aikata ba, idan har na aikata Allah ya isar masa ya saka masa, kuma ya bayyana gaskiya”

Jikinsa yayi sanyi sosai, yasan ba zata yi ma kanta wannan mugun furucin ba. Kasa cewa kamai yayi sai kawai ya juya ya nufi ɗakinsa. Saman gado ya zauna, ya dafe kansa dake masa wani zafi.

Jin yayi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ɗagowa da zai ya ga hannunta rike da ƙur'ane da dukan alamu rantse masa zata yi. Da sauri ya tashi ya ƙarasa inda take.

“No need Please ki aje ƙur'anen nan Kalsoom”

“Rantse maka zan yi Hilal ko zaka yarda da ni”

“Na yarda da ke aje please”

Bata son musa masa, sai kawai ta aje ƙur'ane saman durowarsa tana kuka. Rumgume ta yayi tsantsan a ƙirjinsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.

*NAMRA POV.*

Tun lokacin da Asim ya bata 500 yace tayi cefane bata dake saka shi a idonta ba, kullum idan ta kira zai ce mata aiki ne ya sashi gaba, yau kusan kwana uku kenan.
Ita kam abun duk yabi ya dame ta, musmman yanzu da take ɗan samun sakewa da shi sai kuma aiki ya ɗauke masa hankali.
Sai dai kwana biyu bata jindaɗin jikinta, yawun bakinta ya kan canja ɗanɗano, ga kasala da take fama da shi, sai yawan amai akai akai, ga ciwon kai.

Sai dai bata kawo ma kanta komai ba, sai hawan jini, duk da bata san alamominsa ba, amman tana jin kamar wannan ba zai rasa nasaba da hawan jinin ba, a iya saninta ta saka roba balle tace ko ciki ne, dan tana jin irin alamomin da ake faɗi na masu ciki. Tun jiya ta ci alwashin zuwa asibiti dan bincika matsalarta gudun kar ciwo yayi mata zurfi a rasa gane kansa, amman Allah be yi ba sai yau. Dan haka da wuri ta shirya ta nemi ƴar fulani data raka ta suje tare, dan bata son xuwa ita kaɗai musamman inda bata saba zuwa ba.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *59*

*RASHIDA POV.*

Ganin Safiya ta fita yasa ta juyo bata tsayawa karɓar maganinba, ta fito gabanta dai faɗuwa yake, saƙe-saƙe take na abinda zata cewa Safiya yau kan ta san kashinta ya bushe, bata da wata mafita sai ta Allah.
Kalle-kalle ta fara lokacin data fito harabar gurin ko zata Safiya amman bata ganta ba, da sauri ta nufi harabar asibitin gurin da tadan tayi parking motarta.
Zagawa tayi ta ɗayan ɓangaren ta buɗe motar sai taga Safiya tsaye tana kallonta, idonta cike da hawaye. Yanzu kan babu kayan ɗazu a jikinta, daman suna saka su ne idan zasu shiga ciki.
Dakewa ta yi tana ƙoƙarin ɓoye tsoro da fargabar dake ranta ta kalli Safiya tana murmushin ƙarfin hali

“Ke baki wuce ba, tun ɗazu nake neman ki fa”

“Ke na zo nema daga asibitin ku nake aka ce kun zo nan ku yi wani aiki”

“Ni...?”

Ta nuna kanta cike da mamakin yadda ƴar'uwarta take ƙoƙarin canja abunda yake a zahiri.

“Amman bayan kin gan ni kin cigaba da tafiya ciki...!”

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke a hankali yadda Safiya ba zata ji ba, sannan ta kalleta da fargaba ta ce

“Safiya kar dai kina zargina da wani abu ne? Don't you trust your sister?”

“I trust you but... Me kike nema gare ni?”

“Akwai inda na so ki raka ni, but seems you don't trust me ba sai na je da ke ba”

Bata tsaya jiran abunda Safiya zata sake cewa ba, ta buɗe motar tana mai nuna tsananin ɓacin ranta ita ala dole abunda Safiya ta gani ba shi bane, gaskiya take son canjawa ƙiri-ƙiri.
Da kallo Safiya ta bita har ta tuƙa motarta ya bar harabar asibitin, kallo na mamaki abinda Yayarta take son canjawa, da kuma tunanin abunda ya kawo ta asibiti a hiv unit. Tana ɗa buƙatar bincike dan gano gaskiyar lamarin, dole ne ta bincike ƴar'uwarta, wata ƙila ma tana da masaniya akan Asmee tana da shi.

‘What if ita ma tana da shi fa?’

A zuci tayi furucin tana tafiya, da sauri ta girgiza kai.

“No no A'uzubillahi min shaidanin rajin”

Ƙoƙarin kawar da abin take, dan tana ganin kamar hakan ba zai faru ba, idan kuma har ya faru to sai idan Mijinta ne ya laƙa mata shi, dan bata san yayarta da ɗabi'ar banza ba, sai dai kuma abinda ya tsaya mata a rai tunanin abinda zata faɗi a gida, idan ta faɗi ta tonawa ƴar'uwarta asiri idan kuma ta rufa na su asirin ya tonu.

Tun a cikin mota Rashida ta fara kuka, ganin take kamar asirinta ya tonu, tun da Safiya ta ganta, har kuma ta soma zarginta, idan kuma har ta faɗa a gidan to tasan kowa zai gujeta ne, sunanta zai ɓace haka zai dagula lamarin komawarta gidan Hilal, sannan kowa zai dan dalilin fitar ta gidan, za'asan alaƙar dake tsakaninta da mijin Asmee taren su da Asmee zai lalace, duniya zata san ko wacece ita...!

“Anya zan iya bari wannan abun ya faru? Ya zan yi na hana Safiya faɗa? I can't let her do this, zata saka rayuwata a matsala data tsaka ni a matsala ƙara komai zai faru ya faru”

A fili ta yi furucin, bayan ta faka motarta a harabar gidan, ta ɗan ɗauki lokaci kamin ta buɗe ta fito tana farucin

“Idan Asirina ya tonu ai zaman gidan nan ma sai ya gagare ni, duniya ba zata kawo ƙarshe yanzu ba, i can't let it happen”

Jakarta ta ɗauka ta rufe motar already ta cire hijabin tun a hanya. Sannan ta nufi ciki tana ra saƙe-saƙe a ranta, da tunanin mafita.
Bata bari kowa yaga dawowar ta a gidan ba, saboda bata son a takura da magana ko wani abun na daban, nata ya isheta, har aka yi salla magariba bata leƙa falo ba, sai ana daf da salla i'sha, shima kuma dan taji muryar Safiya ne, sai ta fita ta zauna falo tana ganin kamar idan tana gurin Safiya ba zata iya faɗar komai ba.
Kallonta kawai Safiya take tana saƙe-saƙen faɗar ko a'a, ita kuma taɓa mata kallo ɗaya ta ɗauke kanta tayi kamar bata san da ita ba a zaman falon. Da zaman ya isheta ne yasa ta tashi ta nufi kitchen ta ɗubi abinci ta zo falo ta zauna tana ci ba dan taɓa son cin ba sai dai ta nunawa Safiya kamar babu komai a ranta.
Ita dai Safiya bata ce mata komai ba, bata kuma nuna mata ba sai kallon mbc 2 take, sai dai a ranta ta ƙudiri aniyar sai ta binciki ɗakin Rashida gobe da safe tun da tana rigan kowa fita a gidan saboda aikinta.

Sai da ta gama ci tsab sannan ta tashi ta maida plate ɗin ta sha ruwa, ta wuce ɗakinta, babu komai a zuciyarta sai tashin hankali. Saman gado ta zauna tana mamakin yadda duniyarta ta canja mata lokaci ɗaya, lallai duniya idan ta so ka, kai wawa ne, idan kuma ta ƙi ka, ka shiga uku, kai ne ya kamata ka ƙi ta a lokacin da take so ka, take zaurencen ka, ka so ta a lokacin da take ƙin ka, tana nuna maka kai ba kowa bane, ta haka zaka gama rayuwarka ba tare da ta yaudare ka ba.
Hawaye take, irin hawayen da baƙin cikinsu kan hana kuka fita, makomarta kawai take tunani ta san ko yau ba, wata rana zata samu kanta a irin wannan rayuwar da take gudun shiga, dan tasan asirita ba zai cigaba da rufuwa ba har abada.

“Na yi dama wallahi, duk wannan Alh Bashir ɗin ne yaja min, laifin Asmee ne ita taje ta ɗibo a wani gurin ta saka mana, wallahi duk na shiga matsala ita sai ta shiga, sai na sata a matsala”

Kaɗan-kaɗan take rera kukanta dan bata bukatar kowa ya ji, yau ma ya zame mata kamar ranar da Hilal ya sake ta, har garin Allah ya waye babu abunda take tunanin sai rayuwar da ta yi a baya, yadda take farkawa a gidan, ta wuni da Hilal sahibin ruhinta, yau kuma duka babu wannan, wacan rayuwar ta zamar mata kamar mafarki.
Chapter 91 · 0% Book details