← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 173

Sashe 57

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa yana jan kunnenta har sai da tayi ƴar ƙara

“Ouuchhh nima tace na kai mata hancin ka”

Taja masa hanci ta tashi da sauri daga gurin. Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, yana kallon kunkurunta.

“Kalsoom zo nan”

“No no no”

“Please?”

“No no”

Ta nufi ɗakinta da sauri, sai ya bita yana dariya.

******
Washe gari da wuri Kalsoom ta tashi kamar yada ta saba, sai da ta ciro musu uniform ta ɗora musu saman kujera sannan ta nufi kitchen ta haɗa musu breakfast, har ta gama haɗa breakfast ɗin tunanin Rashida take, tana ganin kamar Hilal be kyauta ba idan be barta taje ta ganta ba.

Sai da ta zuba musu abincin a kula sannan ta shiga ɗakinsu ta tashe su, Ulfah ta fara tayarwa t miƙar da ita tsaye tana girgizata, sannan ta shiga tashin Ezzah

“Ezzah tashi ku yi shirin makaranta na gama muku abinci”

“Ki ƙyale ni ni ba zan je ba!”

Ta faɗa a tsawace tana jan bargota ta ƙara rufa, Kalsoom bata sake taɓa ta sai kawai ta shiga da Ulfah ta haɗa mata ruwan wanka ta fito ta nufi ɗakin Doc.
   Zaune ta tararda shi yana karanta saƙon da Rashida ta aiko masa. Daga bakin ƙofa Kalsoom ta tsaya tace

“Doc Ezzah tana ta fushi har yanzu”

Ya ɗago ya kalleta

“Kamar ya me tace?”

“Wai ba zata je makaranta ba”

“What! Ba zata je makaranta ba as how? I hate nonsense”

Ya aje wayar dake hannunsa ya nufi ɗakin nasu, Kalsoom na biye da su a baya, sai dai bata ƙarasa shiga ɗakin ba, ta tsaya daga bakin ƙofa.

Yana shiga ya shiga tashinta, tana jin muryarsa sai ta buɗe bargo ta buɗe ido, fuska a takure tana kallonsa.

“Tashi ki yi shirin makaranta, kika ce ba zaki makaranta ba?”

“Zan je ni bana son tana tashi na ne”

“Saboda?”

“Ni bana son ta Ammyn ta faɗa min itace ta koreta baka son Ammyn Anty kake so kuma ba zaka sake kai mu inda take ba sai dai mu zauna da Anty kuma ba zata sake zuwa nan gidan ba, ni bana son ta Daddy i hate her”

Buge mata baki Hilal yayi, ya katsa nata tsawa.

“Kar na sake jin bakin ki ya furta irin wannan kalamin, tashi kije ki shirya zuwa makaranta ko na zane ki yanzu nan”

Da sauri ta tashi ta shige bathroom tana kuka. Kalsoom dake tsaye jikin ƙofa tayi saurin barin gurin, ta nufi ɗakinta.
A gaban madubi ta tsaya tana hawaye, zuciyarta sai bugawa take,motsin shigowar Doc ne yasa ta saurin juyo ta kalleshi

“Doc ka rabu da Rashida ne?”

Ya saka hannyensa aljihu yana ɗaga mata kai alamar eh.

“Me yasa?”

“Hakan shi yafi dacewa”

“Dan Allah ka dawo da ita ƴaranta suna da buƙatar ta”

Ta faɗa da muryar kuka hawaye na mata zuba. Matsowa yayi kusa da ita ya ɗafa kafaɗunta yana magana a hankali.

“Basa buƙatar ta matuƙar suna tare da ke, i trust you zaki basu tarbiyan daya kamata, kuma zaki kula min da su, ba zan taɓa maida Rashida ba ko da hakan yana nufin ƙarshen rayuwar ƴarana ne”

“Me ta aikata maka ne?”

Ya rumgume ta ƙam-ƙam a ƙirjinsa yana shirin mantar da ita zancen da suke. Sai gurin Takwas saura ya bar ɗakin. Ko da ya fito duk suna falo suna jirana, Ezzah idonta yayi ja sosai daga ganin alamu kuka tayi sosai, amman sai yayi kamar be kula ba har ya kai su makarantar be yi Ezzah magana ba balle ya rarrasheta.

Daga makarantar ya wuce asibiti dan jin kiran da Rashida take masa, sam be ji wani abu a ransa ba, na tsoro ko kuma na tunanin irin abunda ƴan'uwanta zasu masa.
  Mahaifiyarta ya tarar a ɗakin dare da Babanta sun sata gaba, ita kuma sai rusar kuka take. Daddyn ta na ganin Hilal yayi kansa kamar zai dake shi.

“Me ka zo yi cikin asibitin nan me ya kawo ka? Marar mutunci marar tarbiya, wanda be san hallaci ba, sai yanzu data gama zazzage maka mahaifarta dan ka auro wata zaka sake ta? Daman can ne bana son auren ku da ita dan ban yarda da tarbiyarka ba”

“To ai yanzu sai aka aura mata wanda ka yarda da tarbiyarsa, idan ta cika idda zata iya auren wanda kake so”

Momy ce tayi saurin riƙe hannun mijinta ganin yadda ya ware zai zabgawa Hilal mari.

“Karka so ma faɗa min maganar banza, ko ba daɗe ko ba jima sai Allah ya jarrabe ka da son Rashida kuma wallahi ba zan bari ta koma maka ba, tun da ka ci amanar ta”

“Nima ba zan koma ba Daddy nice na nemi ya sake ni, kuma yanzu nice na kira shi akwai abunda zan faɗa masa, dan Allah ka bar ni nayi magana da shi”

Rashida ta faɗa cikin kuka. Wata muguwar harara Mahaifinta ya watsa mata kamin ya fice shi da Momy da idonta ke cike da hawaye.

Cikin shesshekar kuka Rashida ta kalli Hilla ta soma magana dashi tana jin zuciyarta kamar zara narke.

“Hilal ka san ina son ka, shiyasa ka yi min haka ko? Duk irin zamantakewar da muka yi da kai haka zaka saka min? Taya kake tunanin zan rayu babu kai”

“Ta yadda kike rayu da wani na a lokacin da nake tare da ke, haka zaki rayu da wani a lokacin da ba ni, ƙaryar so kike min Rashida tun da har kika iya aikata zina da wani namiji bayan ni ban rage ki da komai ba”

“Ni ba dutse bace Hilal, dole akwai lokacin da zan buƙace wani a kusa da ni, a lokacin bana gida, idan nayi kwalliya sai dai mutanen office su yaba min, su za su gani ba kai ba, kuma dole ce tasa na fara aikatawa kamin abun ya zame min jiki”

“Faɗa min dawa kike tarayya?”

“Ba zan faɗa maka ba, amman ina son ka san da wani abu ɗaya, har a bada ba zan daina son ka ba, kuma ina roƙon alfarmar karka faɗawa kowa sirrina”

“Ba zan faɗawa kowa ba, kuma ba saboda ke ba, sai dan saboda Ƴaƴana”

“Ba zaka sake jindaɗin rayuwar aure ba Hilal, iya rayuwar da muka yi itace ta jindaɗin aure, wallahi Kalsoom ba zata mallake min ƴaƴa ba, idan har ban zauna da kai ba babu wata mace da zata zauna da kai a duniya da sunan rayuwar aure, baka isa ka raba ni da ƴaƴana ba, wata mace kuma bata isa ta maye gurbina ba”

Matsowa yayi kusa da ita cikin zafin rai zai mata magana. Sai ga Asmee ta shigo ɗakin. Sai kawai ya juya ya fice ba tare daya faɗa mata abunda yayi niya ba.
Da sauri Asmee ta ƙaraso kusa da ita ta dafa ta.

“Ke lafiya Hilal yake kuwa? Wai jiya bayan na bar nan asibitin na ji mummunan labari da gaske ne kuwa?”

Kwantowa tayi kikin Asmee tana kuka

“Da gaske ne Asmee ya sake ni”

“Me kika masa?”

“Ban masa komai ba haka kawai ya sake ni”

“Hmmm sherin kishiya ne, ai kinsan yadda mijinki yake son ki ba zai sake ki haka nan kawai ba, wani asiri ne aka masa”

“Ba zai mai da ni ba, shikenan ƙarshen aurena da shi”

“Wallahi ƙarya ne, ƙarya ne wallahi Allah ya sa kiji sauƙi da wuri, kin ga malamin nan da na kai ki gurinsa? Wallahi ki koma yayi miki aiki a gigice Hilal zai maida ke”

“Zan koma yayi min aiki, amman bana Hilal ya mayarda ni ba, sai dai na wani abun daban, na riga na yafe Hilal har a bada”

“Kar kice haka Allah dai ya baki lafiya”

Ƙara fashewa tayi da kuka ta ƙamƙame Asmee tana jin wani irin zugi da zuciyarta ke mata.

AMIRA POV.

Daga ita sai tawul ta fito daga banɗaki, ta zo ta zauna gaban mirrow tana taje kanta. Sai da ta gama ta shafa mai tayi kwalliya sannan ta kalli Guy son dake kwance saman gado yana kallonta tace

“Amman kasan matar nan ta raina mana hankali? Sai da tasa muka bincika ko waye likitan sannan zata ce mana wani ta fasa”

“Manta da ita kawai, akwai wani aiki da zamu je yi Abuja jibi, akwai wanda ya kira ni kuma na san zamu samu kuɗi da yawa”

Ta baro inda take zaune, ta nufo inda yake tana wara ido

“Da gaske?”

“Na taɓa miki ƙarya?”

“No I'm just asking, you know how a like Abuja”

“Yeah shiyasa zan je da ke ai”

Rumgume shi tayi cike da jindaɗi, shi kuma ya shiga shafa jikinta.

NAMRA POV.

Cikin wani irin kuka ta isa gida. Yau duk wani tsoro da take na gidan be ziyarce ba, dan baƙinciki dake tare da ita tafi tsoro, yadda ta ga dare haka taga dare, sai ta tashi tayi sallah, tayi addu'ah samun mafita da sauƙi a zuciyarta. Tana gurin bata tashi ba har aka kira sallah asuba, kasa cin komai tayi da safe, ji take kamar ta kashe kanta ta huta, kalaman Asim sun tsaya mata a rai, sai yanzu ta fara gasgata kalaman Anty Amarya, ayau Asim ya nuna mata ko waye shi, ya buɗe mata sirrin dake ransa, sannan ya zarge ta da abunda wani be taɓa mata ba.
A tau ta tabbatar da tayi zaɓen tumun dare, sai a yanzu tana ganin laifin zuciyarta.

“Miyasa kika bar ni na kamu da son wanda ba dan Allah yake so na ba? Dan me baki bar ni na so waninsa ba? Duka yaushe muka yi aure da shi amman yau ya sauya min ya nuna min abunda ban taɓa mafarki ba? Yanzu ya zanyi da rai na? Na bar karatuna saboda shi na zo garin da ban san kowa ba saboda shi amman duk ban masa ba?”
Chapter 57 · 0% Book details