← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 173

Sashe 46

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da Abbah yake maganar bata ce uffan ba har sai da ya kai aya. Sannan ta sauke ajiyar zuciya tace.

“Zan musu magana, ai dukan su suna da manema, daga Hindatu har Maryam ɗin”

“Ƙara ayi musu magana su fitar da wanda suke so, da ba zan sake zaɓawa kowa miji ba”

“To, Alhaji nacw har yanzu baka je ganin Mijin Namra ba, ya kamata ko a waya ne ka kira shi ku gaisa”

“Ko Namra ce bata da lafiya ba zan kira ba, balle mijinta, ki daina kawo min wani bato daya shafi Namra, baki san irin baƙin cikinta daya ke cikin zuciyata ba”

“Toh ni idan ka min izini ina son na koma naje na ganshi”

“Ba zaki koma ba, idan be gode da ganin da kika masa ba, ya bar shi, ba familyn ta ya aura ba ita ya aura, kuma na sallama masa ita har abada, babu hannuna babu ƙafata a lamarin Namra, ta zaɓi wanda take so sai taje ta zauna da shi”

Ko kaɗan kalaman Abbah basu yi ma Anty Amarya daɗi ba, nan take ta canja fuska, ɓacin rai dake zuciyarta ya bayyana.

“Haba dai, wannan wane irin magana ne? Shikenan bata da damar ta zaɓi mijin da take so? Wannan sam ba adalci ba ne, baka ƙaunar yarinyar nan kamar ba kai ka haife ta, ɗan abu ƙanƙane sai ka ɗauki karan tsana ka ɗora mata”

Ta ƙarasa maganar da kuka.

“Ke kin fi kowa sanin na yadda na nunawa Namra so, ai ke ya kamata kiyi tunani kiga rashin dacewar abunda Namra tayi min, ko da ace ba ni na haife ta, ya kamata ace tayi min biyayya tun da nina raine ta har ta kai inda take yanzu, be kamata ta zaɓi wani ta bar ni”

Kukan Anty Amarya ta cigaba da rera masa. Shi kuma ya ɗauki jaridarsa ya buɗe yana karatu, ba dan kuma yana son karatun ba, sai dan yayi avoiding kukan na Anty Amarya, tana da matsayi a zuciyarsa, ba kasafai yake son kukanta an itace mafi soyuwa a zuciyarsa, duba da yadda take masa biyayya da kuma yadda take da ƙuruciya, sama da Hajiya Barau data kwana biyu.
Idan kuma ya biye mata yasan halinta yanzu ne zata birkice masa, har ya rasa gane kanta.

Data gaji da kukan ne, ta share hawayenta, ta tashi ta bar masa ɗakin.
Tana shigowa part ɗinta duka ƴaƴanta suka lura da yanayinta, ba ma kamar Maryam data fi damuwa da ita sosai.

“Anty Lafiya?”

“Lafiya ƙalau, kawai ina tunanin Namra ne, ban san halin da take ciki ba babu waya hannunta, kuma Abban ku yaƙi ya bar ni naje na duba su”

“Inshallah tana cikin ƙoshin lafiya Anty, kwana ki ma sai da ta turo da text wai ki taimaka mata da kuɗi, ni kuma na goge text ɗin dan nasan Asim ne zai sata”

“Amman miyasa baki faɗa min ba? Baki san halin da take ciki ba, ƙaddara ce ta riga ta faɗa mata babu yadda za muyi”

“Nayi tunanin ko shine yasa ta”

“Nawa tace a bata?”

“Bata faɗa ba”

“Gobe kije ki tura mata 300.000k sai ki kira wayar Asim ki faɗa mata, kuma kice ta siye waya tasa layin ta, kwana kin nan mafarkin ta nake ta yi, ban san halin da ƴata take ciki ba”

“Inshallah zan tura mata”

“Abbah ku ba ban saƙo gare ku, amman sai gobe zan faɗa muku”

Tana kai wa nan ta tashi ta nufi ɗakinta, tana share hawayen da suka zubo mata.

RASHIDA POV.

Tana gama aikin office ɗin ta dawo gida, tasan abunda ta shirya ma kanta shiyasa ta dawo da ƙarfe shida tsaɓanin tara na dare data saba dawowa.
Ɗakinsa ta shiga tana masa bincike ko zata ga takardun results ɗin ko kuma jinin daya ɗiba tun da yace mata be kai, amman bata ga komai ba. Har ta gaji ta dawo dakinta .

Duk da tasan yau ba a ɗakinta Doc take ba, hakan be hanata chaɓa ado ba, dan ta ɗauki hankalinsa. Daman ya saba duk wacce yake ba girkinta ba yakan shiga yayi mata sai da safe, sannan ya wuce ɗakin da zai kwana.
Tun kamin ya shigo ɗakin, ta haɗa masa tea da lemun tsami dan tasan yana son haka, ta kuma saka masa zuma a maimakon sugar, sai ta ɗauko maganin dake jakarta ta buɗe ta kaɗa masa cikin tea ɗin har kusan guda biyar.
Tana mayarda jakar ta aje yana turo ƙofar ɗakin ya shigo, gabanta ya faɗi, abun ka da wanda bata saba ba, sai dai ta wayance taje ta rumgume shi.

To her surprise sai ya sauke hannayensa daga saman wuyanta, yana ɗan murmushi. Bata damu da abunda yake mata ba, dan a tunaninta fushin ɗazun ne na dress ɗin ta tayi. Cup ɗin tea biyu ne sai ta ɗauki ɗayan ta miƙa masa.

“Ga tea”

Hannu ya kai ya karɓa ya furta

“Thank you, good night”

Har ya juya, sai kuma ya juyo ya kalleta kamar zai ce wani abu, sai kawai ya sakar mata murmushin irin na fatar faki, ya juya ya fice.

Ɗakin Kalsoom ya nufa, ko da ya shiga ciki be ganta ba, ya duba bathroom bata ciki, sai kawai ya nufi ɗakin su Ezzah dan yasan ba wuce tana can ba.
A tsakiyar gado ya tsame ta tana ta tofawa yaransa addu'o'i, su kuma sai bachi suke tayi abun su. A bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta yana murmushi, har ta gama ta taso ta nufo shi.

Hannu ya kai ya laƙƙamo kunkurunta, jikinta ya haɗe da nashi, ita kuma sai haɗiyar yawu take tana kallon kofin dake hannunsa, ƙamshin tea ɗin yana kai ma hancinta ziyara.
Kaɗan ya kurɓa ya kai mata kofin a baki, ɗan tsami tsamin data ji yasa ta jidaɗin tea, ta riƙe kofin da hannu biyu har sai da ta shanye tea ɗin gaba ɗaya.

Tana shanye tea ɗin ta saki kofin tayi masa kwance a jikin, wani irin bachi mai bala'in nauyi yayi gaba da ita.

“Hey...”

Ya faɗa yana girgizata, amman ina, tayi nisa har ƙoƙarin zubewa take a ƙasa, hannayensa yasa ya ɗauke ta cak, ya nufi ɗakinta da ita. Saman gado ya kwanatar da ita ya kwanta gefenta yana shafa fuskarta, zuciyarsa cike da mamakin abunda yake cikin tea ɗin.
Ya kusan minti talatin a gurin kwance, sai yaƙi yake da bachin dake son sace shi, yana unƙurin tashi yaji an turo ƙofar ɗakin, ƙin motsawa yayi sai ya lumshe ido kamar yayi bachi, sai ga Rashida ta ƙaraso har gurin tana leƙen fuskarsa, har da sa hannunta tana masa yawo da shi dan ta inda gasken yayi bachin.

Da sauri ta juya ta fita ta nufi ɗakinsa, keys ɗin motarsa ta ɗauka, ta fito waje ta buɗe motar tana masa bincike, seat ɗinsa na gaba ta buɗe ta fara bincikar takardun da suke gurin. Jikinta ne ya bata ana kallonta, da sauri ta fito daga motar, sai taga Doc tsaye ya rumgume hannayensa yana kallonta.

Kasa motsawa tayi, numfashita mai sai da yayi nisan zango sannan ya dawo, jin tayi kamar ƙasa ta buɗe ta shige ciki, a take mararta ta cika da fitsari.

___________________________________________

One free Page remained 🙌

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY 😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                            Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 35. Last Free Page*

NOT EDITED ⚠️

Bata taɓa sanin gume na da zafi ba, sai a wannan lokacin, wani irin nauyi ta ji kanta yayi kamar an ɗauki duniyar nan an ɗora mata, yau ganin Hilal take ya cika ko ina na duniyar idanunta.
Yau kam ba ranar kuka ba ce, tashin hankalin daya same ta ya fi ƙarfin kuka, hakan yasa hawaye ba kusanci idonta ba, ashe abu mai sauƙi ake ma kuka, ta kasa yarda yau ita ce Hilal ya kama dumu-dumu ba.

“Kin san kina da HIV kike ƙoƙarin ɓoyewa Rashida? Do you know what lokacin dana ɗibi jinin ki result ɗin ba ɓata yayi ba, nace miki haka ne saboda ban yarda da abunda idona ya gani ba, na dawo na ɗibi jininki da na yarana da na Kalsoom nawa dan na gwada, so that na tabbatar idan da gaske kina ɗauke da cutar ne, amman ke kin san kina ɗauke da cutar kika bar ni ina kusantar ki?

Da ba dan wanann cikin ba, da sai mu ɗauki dogon lokaci a tare da dake baki faɗa ba right? What if all of us mun kamu da cutar nan?”

Ƙiri-ƙiri tayi masa da ido, cikin ƙarfin hali ta cira ƙafarta da tayi mata mugun nauyi ta tako ta ƙaraso kusa da shi.

“Kana tabbacin ni ce kaɗai nake ɗauke da cutar? Kasan ta ina cutar ta shige ni? Miyasa idon ka zai rufe har haka?”

“Ke da kan ki kike zargin kan ki, dan me zakiyi ma Doc Sabo transfer 100,000k? Dan me zaki ce idan ya kawo jinin kamin ya auna ya kira ki? You late Rashida ko da kika kira shi na riga na kai jinin amman yaƙi ya faɗa miki saboda ya san ni kamin ya sanni kuma ya san aikinsa, daman nasan ziyarar da kika kawo min ɗazu a office bata banza bace cox na lura dake kwata-kwata hankalinki baya jikin,

Bincike da kika min da tambayoyin da kika min ya tabbatar da akwai wani abu, and now what kin sa abu a tea ki bani nasha so that kiyi iya binciken ki ko? To bari na faɗa miki if something happens to my wife hmmm you're in trouble”

Sai a yanzu hawaye suka samu damar cika idonta har suka silalo zuwa kumatunta.
Chapter 46 · 0% Book details