← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 173

Sashe 155

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana bashi amsa ya gyara tsayuwar littafan da ke hannunta ta nufi hanyar falo.
Tana shiga Maryam da Wasu old friends ɗinta suka jo kanta suna mata murna da zolaya. A abubuwa biyu ta samu kanta, farincikin da akasinsa, ba data dalilin yin duka biyu ɗin, dan har ga Allah bata shirya aure a yanzu ba, sai dai babu yadda ta iya tun da Abbah ya nuna yana son ta yi, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta tuna halin da Lamido yake ciki sai ta ji Abdool ya fita a ranta. Cikin ƙarfin hali take musu dariya tana nuna musu farincikinta sannan ta wuce ɗakinta. Littafanta ta jefar saman gado ta shiga banɗaki ta yi alwala, ko da ta fito wayarta na ringing, wasu kawayenta ne na makaranta hakan yasa bata ɗauka ba, tasan ba zai wuce su taya ta murna ba, ko kuma su faɗa mata yadda zancen engaged ɗin ta ya cika social media. Har ta saka Hijab ɗinta sai wayar ta sake ringing wannan karon Abdool ne, tana son magana da shi sosai hakan yasa tayi picking tana aika masa sallama.

Ya amsa mata yana ƙarantar saƙon dake cikin muryarta na ranshin daɗin rai.

“Tell me i'm wrong, amman kamin ki yanke hukunci ya kamata kisan duk abunda aka yi Mai Martaba ne yayi ba ni ba”

A tunaninsa ko akan kayan ta ya tura ne wani abun be mata daɗi ba, sai kawai yaji ta ɗauko masa wata magana ta daban.

“Miyasa kasa aka ɗauko Lamido daga Kaduna ka kawo shi Katsina? Mi kace masa?”

Yannu ya kai yana shafa dogon hancinsa, tare da maimaita sunan Lamido a zuciyarsa.

“Be faɗa miki abunda Yarima Abdallah yayi masa ba? Be faɗa miki gaskiyar abunda ya faru ba?”

“Be faɗa min ba, amman ga dukan alamu abunda ka yi masa babba ne, domin har hawaye na gani a idonshi”

Ƙafarsa ya ɗora ɗaya saman ɗaya yana imaging fuskar Namra a wannan lokacin duk da kuwa bata kusa da shi.

“You're crying...”

Sai kawai ta katse kiran ta share hawayen idonta ta miƙe tsaye ta kabbatar sallah. Har ga Allah tana jin son Abdool a zuciyarta sai dai bata fatar ta yi amfani da wannan damar ta cutar da Lamido, dan tana jin rashin kyautawa a abunda ta yi masa, sai dai bata da zaɓi bayan na Allah daman can shi ta miƙawa lamurarranta, har gobe roƙon Allah take idan har babu alheri a aurenta da Abdool Allah ya musanya mata.

Haka ta kwashe kwana biyu, babu wata magana mai daɗi dake shiga tsakaninta da Abdool, saboda tana ganin kamar yana amfani da saurautarsa da kuma kuɗinsa ne wajen nuna mata ƙarfin iko ya ita da Lamido, ga kuma farin jikin daya samu a tsakanin iyayenta wanda hakan ya hanata ko da wasa ta cewa Anty wani abu ya shiga tsakaninta da Abdool ba.

Har yanzu Lamido ne yake kaita makaranta, bata tambaye shi yadda yayi da Abbah ba, shi kuma be ce mata komai ba. Sai dai ta kan tsargu da abu ɗaya a yanzu, ya kan tsura mata ido ta madubi mota ko kuma idan tana waje kamar madubinshi.
Ita kuma a yanzu bata magana da shi saboda ya ƙi ya faɗa mata.

ABDOOL POV.

Tun da ya karanci halin da Namra ta sashi, sai ya ke ganin kamar Lamido ne yake masa zagon ƙasa, daman shi zuciyarsa bata natsu da zaman lamido a gidan ba, a duk lokacin da ya tuna sai yaji kamar zuciyarsa zata rabe biyu, musamman da yasan shi yake kaita makaranta ya ɗauko ta, tabbas yayi sake da yaba har tsawon wata takwas tana keɓancewa da Lamido, aiko dole ta so shi fiye da shi.

Kamar an masa allurar ƙarfi haka ya zabura ya miƙe tsaye be damu da saka hula ba duk da shaddace a jikinsa ya fito ya nufo part ɗin Ummi.

Be same ta a falon ba, sai Amal ya samu tana ta faman solved Maths.

“Dude Ina Ummi?”

“Tana Garden lalle ake musu, Dude na taso mu yi wannan assignment ɗin?”

“No bari sai na dawo fita zan yi”

Ya juya ya fice. A garden ya sameta zaune saman carpet ta jera ƙafafunta ana zizira mata lalle irin wannan na zamani.

Tsaye yiyi ya jingina da icen guava yana wasa da keys ɗin hannunsa.

“Ummi na canja shawara, zanje na ga Mai Martaba”

“Shawarar me?”

“Nan da One Months nake son a yi auren nan?”

Da mamaki Ummi ta kalleshi.

“saboda me?”

“Kawai ni nafi son haka ne”

“To su ƙanenka da aka saka date ɗin aurenku a tare fa?”

“Su a barsu sai lokacin ni kan gaskiya i can't wait, zan samu Mai Martaba mu yi magana”

“Amman zai zama kun yi magana biyu Abdallah, da ka yi haƙuri har lokacin nan da wata biyar a ba wani abu ba ne”

“Haƙuri ba zan iya ba Ummi, kawai ki min addu'a”

“Toh Allah yasa alheri, amman nasan Mai Martaba ba zai amince ba”

“Zai amince ki daina ƙwanƙwanton mahaifina akai na”

Hannu ta ɗaga masa.

“Tafi kai da kan ka zaka dawo ka ba ni labari”

Murmushi yayi ya juya ya bar Garden ɗin tana ta saƙe-saƙe a ranshi har ya isa faɗar Mai Martaba.
Be same shi a gida ba, saboda wani taro da taje, haka ya zauna a gidan har aka yi sallah magariba, bayan ya fito daga masallaci ne Mar Martaba ya dawo, dan shima sai da ya tsaya a can suka yi sallah sannan ya kamo hanyar gida.

Mai Martaba na gaba Yarima Abdool na biye faɗawa sai zuba masa kirari suke har aka shiga fada. Kai tsaye Mai Martaba ya wuce turakarsa Abdool ya rufa masa baya yana masa bangajiya. A saman fafaffaɗa kuma ƙasaitacciyar kujera Mai Martaba ya zauna ya cire rawaninsa ya miƙawa Abdool. Bayan ya aje rawanin ya dawo kusa da ƙafafun Mai Martaba ya zauna yana mai natsar da kai kasa kamar yana gaban sukurinsa, ya kan yi hakan a duk lokacin da da yake neman wata alfarma a gurin mai Martaba saboda kawai Mai Martaba yaji tausayinsa ya amince.

“Buɗe baki ka yi magana, Babana ni mahaifinka ne idan ban maka uzuri ba waye zai maka?”

“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya, daman magana ce na zo da ita akan auren mu, sai dai ban san ta fuskar da zaka kalli abun ba”

Mai Martaba ya jingina da kujera yana cigaba da kallon ɗansa. Abdool ya cigaba ba tare da ya ɗago ya kalli Mai Martaba ba.

“Idan har ka amince min, ina son ka roƙa mahaifin Namra akan ya rage lokacin da ya saka na aurenmu saboda yayi tsawo...”

Sai da aka ɗauki tsawon ɗakika talatin da huɗu wata kalma bata fito daga bakin Mai Martaba, sannan ya nunfasa kana ya ce

“Ni kaina na yi tunanin hakan, saboda maganganun da suke ta zuwa suna dawowa, ba a son magana ta yi yawa akan aure, kuma idan har aka ja abu nesa wannan kan iya haifarda da wata matsala wace ba a tsammanin zata zo, sai dai ganin lokacin auren yayi dai-dai da lokacin auren ƴan'uwaka yasa ban ce komai a kai ba”

Abdool ya jidaɗin wannan maganar, daman yana neman da inda zai fake yayi hujja da shi akan maganar auren. Sai gashi Mai Martaba ya taɓo masa inda yake masa ƙai-ƙaiyi.

“Nima hakan na gani, kada sheɗan ya shiga ciki, ko kuma baki yayi mana yawa”

“Gaskiya ne, amman kai zuwa yaushe kake ganin ya dace a saka auren?”

“Allah ya taimake ka ina son ace nan da wata ɗaya”

Mai Martaba yayi masa wani kallo.

“Nan da Wata ɗaya sai kace wanda zai auri ƴar tsana? Wata ɗaya yayi mana kaɗan da shirya lamarin auren ka”

“Allah ya taimake ka duk yadda ka yanke dai'dai ne, amman be yi kaɗan ba, indai matsalar lefe ne ciki sati ɗaya za a iya haɗawa, kuma na san bama buƙatar komai daga gareta”

Ɗan Murmushin gefen baki Mai Martaba yayi, lallai ya tabbatar da ɗansa ya matsu, hakan ma yasa shi gane Abdool yama neman girma a yanzu, bayan kuma a da neman masa ake yana gudu.

“Za mu yi tunani akai, kar ya zama mun matsa musu, zan yi shawara da Umminka, nan kuma cikin gida zamu shawara”

Mai Martaba na gama faɗar hakan ya miƙe tsaye...

__________________________________

I think we should create a team for LAMIDO ko 🤔 i pity him bawan Allah 😢
[7/24, 9:38 PM] Khadeeja Candy♥: *89*

Yau day ta leƙa whatsapp domin ta kwana biyu bata hau ba, daman bata hawa sai idan tana da time saboda karatun da ta sawa gaba.

“Abbah na kiran ki”

Aysha ta faɗa tana tsare jikin ƙofar ɗakin Namra.

“Okay ga ni zuwa”

Ta kashe data ta sauka saman gado. Ko da t fito Zinatu na zaune falo ita da Anty Amarya suna cin ɗatun zogale (kwaɗo). Wara ido tayi ta sha mur

“Lallai Anty shi ne cika zauna da ƴarki kika ci ɗatu ni aka ƙyale ni”

“To idan ban ci da ƴata ba da wa zan ci? Kaji min yarinya”

Anty Amarya ta faɗa fuskarta da annuri tana murmushi. Zinatu tasa dariya.

“Na gan ki online fa kuma na miki magana kika share ni”

“Allah ban duba ba, hankalina yana can ina duba chat ɗin grp”

“Gashi ai sai ki zo ki ci”

“Abbah ya kira ni, aje min na dawo”

Ya aje wayarta saman kujera ta nufi part ɗin Abbah. Zaune ta same shi sanye da jallabiya, idonsa sanye da farin gilashi hannunsa da jaridar daily trust. Ƙasa ta zauna bayan ya amsa mata sallamar da tayi idonta kan Arewa24 da suke maimaita shirin Daɗin kowa.

Remote Abbah ya ɗauka ya kashe tv, ya aje jaridar da ke hannunshi sannan ya fuskanci Namra ya ce.

“Magana na ke son mu yi a tsakanin ni da ke, kuma bana son ki takura kan ki, na fi son ki faɗi ra'ayinki”

Ta ɗan kalleshi kaɗan.

“Abbah maganar me ce?”

“Akan date ɗin da aka saka ne na aurenki, Mai Martaba ya kira ni yace a rage musu ranar da aka saka ta yi musu tsawo, amman yace baya son a cilasta miki yafi son sai anji ta bakinki”
Chapter 155 · 0% Book details