← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 173

Sashe 125

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kin biyani Mardiya, zan baki mamaki, kuma auren mu nan kusa nake sonsa ba sai nesa ba, dan haka daga yanzu ki shirya a ko yaushe zan iya zuwa gaishe da iyayenki, sannan na turo magabatana”

Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta 5ana dariya, sai tayi cikin gidansu da gudu kamar wata mai kunyar gaske.
Ya daɗe tsaye a gurin yana kallon ƙofar gidansu, sannan ya zaro wayarsa dake ringing ya kara a kunne.

“Na'am Hajiya kin dawo ne?”

Ban ji ma tace masa ba, sai kawai naga ya gyaɗa kai yana faɗin.

“Okay kina ina yanzu?”

Can kuma sai naga fuskarsa ta canja.

“Eh nasan gurin. Okay gani nan zuwa”

Ya sauke wayar kamar mai tunani. Can kuma ya ɗaga kafaɗunsa. Ya buɗe motarsa ya shiga.

Yana cikin driving ya kira ƙanen mahaifinsa dan jin yadda aka yi maganar gida.

“Eh yana da kyau sosai? Bedroom nawa ne a gidan? To ko dai mu bari sai an samu wani? Okay ba matsala”

Ya kashe wayar, sannan ya ƙara gudun motarsa, cikin ƴan mintuna ya isa unguwarsu Nably, a kusa da gidansu ya faka ya sake kiran Hajiya.

“Gani na ƙaraso unguwar, amman ban ganr gidan ba”

Daga ɗayan ɓangaren ta amsa masa.

“Baka ga wani green gate ba?”

“Na gani, Mai farin fenti”

“Eh to ka shigo ciki amman ka tsaya daga gate zan fito na kawo maka”

“Okay”

Ya tashi motarsa ya nufi gate ɗin gidan. Be ƙara gasgatarwa ba har sai da ya shiga harabar gidan, kusa da gate ya faka, yana ƙara kallon harabar gidan.

“Akwai bura'uba...”

Ya faɗa yana kallon Hajiya Sadiya wacce ta fito riƙe da ƙatuwar leda, sai faman sauri take kamar wacce ta yi sata.

“Ka saka min a wannan account ɗin”

Ya miƙa masa farar takarda tare da ledar dake hannunta. Cikin ladabi ya karɓa ya na faɗin

“Hajiya wannan ma gidanki ne?”

“Eh jeka dan Allah da sauri, bana son a tararda kai”

“Okay”

Ya koma cikin motar yana ta kallon gidan. He just can't believe gidan Hajiya ne, mi hakan yake nufi ita mahaifiyar Nably ce ko yar'uwarta.? Har ya bar gidan be samu amsar tambayarsa ba.

YASMEE POV.

Tana jin tsayawar motarsa ta tashi da sauri ta nufi kitchen, cox she dunno what to do, kuma tana jin kamar bata son ganinsa, duk da tana ƙoƙarin yaƙar zuciyarta dan sanin gaskiyar lamari. Hannayenta biyu tasa ta dafe fuskarta tana busar da iskar bakinta.

‘Ni fa lauya ce, ni nake fawa wasu magana, ni na saba bincike, dan me yau kuma zan rikice, i need to do this ko dan na cire kaina daga zargi’

A zuciyarta take wannan maganar, a fili kuma murmushi ne shimfiɗe a fuskarta ta juyo tana amsa kiran da yake mata.

“Yau wace rana baki je office ba ne?”

Yayi mata kiss.

“No naje yau cases biyu ne kawai da ni, ina gamawa na dawo, ya aikin naka?”

“Alhamdullah, ina da labari mai dadi, Abbah (Baban Namra) ya buɗa mana wani sabon kamfani a Abuja, kuma nasan niɓe zan kula da shi”

“Wow amman Abbah ya kyauta mana, Allah yasa hannu a ciki, ko shi yasa aka aiko maka da wasiƙa? Ɗazun an kawo wasiƙa a aje maka”

“Waya kawo”

“Wallahi ban sanshi ba, tana nan ɗakinka na aje maka”

Freezer ya buɗe ya ɗauki gorar ruwa ya nufi ƙofar fita yana tambayar abunda aka dafa. Da kallo Yasmin ta bishi bayan ta bashi amsa idonta cike da ƙwalla.

“Allah ka sani ina son mijina, Allah karka tabbatar da zargina akan sa”

Ta share hawayen da suka zubo mata. Tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo riƙe da wasiƙar hankalinsa tashe.

“Kin karanta wasiƙar nan Yasmin?”

“A'ah miya faru?”

Ba komai, ya juya ya fita da sauri. Sai da ta tabbatar ya shige ɗakinsa sannan ta rufa masa baya. A bathroom ɗin falo ta tsaya ta sakama ƙafafunta ruwa gudun kar yaji sawun takun ƙafarta. A bakin ƙofar ɗakinta ta kara kunnenta, sai dai bata ji alamar motsinsa a cikin ɗakin ba. A hankali ta tura ƙofar ɗakin daman be mata rufin ƙwarai ba, nan ma babu alamunsa har toilet ɗinsa taje ya leƙa bata ga kowa ba. Mamaki ne ya kamata ina yaje,da sauri ta juyo ta fito. Har zata shiga ɗakinta, sai kuma ta nufi gurin engine ɗin wankinta. Daga inda take tsaye ta hangosa yana waya, daga gani ba wayar aiziki bace yake, dan yadda yake jinjiga jikinsa yake safa da marya na ya nuna haka. Yana gama wayar ya juyo yana faɗin.

“Namra bata zame min matsala ba ke zaki zame min, babu wanda ya isa ya datsa min rayuwar jindaɗi wallahi”

Karaf idonsa cikin na Yasmin, dake tsaye gafen ƙofa.

THE GAME IS ABOUT TO START...😿
_____________________________________

I feel much better Alhamdulillah. Na gode sosai da addu'ah da kulawa, Allah ya bar zumunci. Jazakallahu khairan all 😘
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *74*

Ko parking ɗin kirkir bata yi ba a gidansu Teema ta fita Motarta, zuciyarta na bugun bugawa, taron mutanen da tara a gidan ya ƙara tabbatar mata da maganar Asmee da kuma Momi.

Teema na hangota ta tashi daga cikin mutanen da take ta nufi wani ɗakin wanda babu kowa a cikinsa.
Kai tsaye Rashida ta bita daman ta ga shigowarta, wasu daga cikin ƙawayen Teema har sun fara magana, dan wasun su sun san mijin Rashida ne zata aura, wasu kuma a yanzu suke samun labari, ganin yadda ta shigo cikin gidan a birkice.
Da wani irin ƙarfi Rashida ta banki ƙofar ɗakin da Teema take ta shiga hasale.

“Marar mutumci wacce bata gaji arziki ba, ni zaki yiwa ha'inci? Ki zagaya ta bayan idona ki ci dunduniyata”

Hannayenta biyu Teema ta kama ta riƙe tana hawaye.

“Dan Allah ki saurare ni, karki yanke min hukumci ba tare da kin saurare izuri na ba...”

Rashida ta fisge hannunsa tana mata wani kallo na uku saura kwata, kamin ta katsa mata tsawa kamar wata ƴarta.

“Babu wani daɗin baki da zaka min, macuciya wai tsabar rashin kunya ni zaki ciwa amana..”

“Ban ci amanarki ba Rashida ko kowa ya zarge ni ke be kamata ki mun haka ba, ni kaina ban san da wannan haɗin ba, dan be taɓa zuwa fira gurina ba sai da zai kawo min iv, su Hajiya ne suka haɗa komai”

Ta ƙarasa da kuka tana wani ƙara narkewa kamar gaske. Rashida ta watsa mata wani kallo.

“Ke kar nake kallon ki, kamar naira a hannun yaro, yadda kika yi boka haka na yi karki nemi raina min hankali, wallahi mafitarki ɗaya ki fasa auren nan ko kuma na ci uwarki”

Teema ta yi wani Shu'umin murmushi tana kawardar hawayen ƙarya dake fuskarta.

“Idan kuma ba ki ci uwata ba, ni sai na ci ubanki, da aka halitto Hilal an ce miki ke kaɗai zaki aure shi ne? Ke in ban da haukarki ma miye na kishi bayan ya sake ki da ya kama ki da wani ƙato ko kin ɗauka ba'asan abunda ya fitar da ke gidan Hilal ba? Kina ganin kamar ba san komai a rayuwarki ba ko? To malamin dana kai ki gunsa, shi ya faɗa min komai a kan ki”

Jikin Rashida yayi sanyi har tana sassauta murƴarta duk da tana cikin zafin rai ne.

“Yayi dai-dai kuma ina fatar ya duba miki ya faɗa miki igiyar aure ba zata taɓa shiga tsakanin ki da Mijina ba, dan Wallahi sai na rusa wannan auren ko ta yaya, dan babu yadda za'ayi yar iska irin ki ta tarbiyantar min da yara, sai na faɗawa Hilal irin matar da zai aura”

“Yar iska kamar uwarsu ko? Ai abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, kuma idan baki rusa auren nan ba, baki haihu ga uwarki da ubanki ba, ai Hilal ba mijin ki bane mijin Kalsoom ne da Angon Teema, ƴar baƙin asiri kinje kin yi ma kiahiya ya dawo kan ki kin kashe ɗan ki da hannunki, Ni ko nafi ƙarfin ki gaba ɗaya ke da danginki, kuma wallahi duk kika kuskura sake saka baki a maganar auren nan sai na faɗawa duniya dalilin mutuwar auren ki, da kuma dalilin mutiwar ɗan ki, ga kuma cutar da take tare da ke, dole har ƴaran ki su gujeki, ko kin ɗauka ba a san dalilin korarki da ubanki yayi ba?”

Gaba ɗaya jikin Rashida ya gama sanyi, zafafan kalaman da Teema tayi masa sun ƙatse mata duk wani hanzari da take da shi, har ta samu kanta da nauyin baki kasa furta mata komai, abun ka da mai sauri karaya nan da nan sai ta fara hawaye.

“Kin fi kowa sanin yadda na ke son mijina Teema, amman kika min zagon ƙasa har kika ja hankalinsa akan ki, waya sani ko asiri kika masa?”

Teema ta yi ƴar dariya.

“Wallahi ban masa magani ba, uwarsa cw da haɗa mu, kuma yaga yana so na, nima ina sonsa shikenan fa, amman ki kwantar da hankalinki zan ƙwatar miki ƴancin ki, kuma zan miki hanyar da zaki dawo gurin mijinki”

“Allah ya isa tsakanina da ke, kin ci amana ta kin min zagon ƙasa Teema wallahi ba zan taɓa yafe miki ba”

Tana kaiwa nan ta juya ta fice fuskarta da hawaye.
Wani banzan tsaki Teema taja.

“Aikin banza ai daman Allah ishenshe ne, kinji na roƙe ki ki yafe min ne, ni wallahi ko ubanki yayi min aurensa zan balle wani mijin ki ex-husband mtssssssss”

Rashida ya fito ɗakin idon kowa yana kanta, wasu na Teema rashin gaskiya wasu kuma suna ganin bata yi laifi ba, daman yanzu ko mijin ƙawarki ne aure shi za'ayi balle ita da har ta fita gidan miji. Bama kamar hawayen da suka gani a fuskarta. Ita kam ba ta nasu take ba, haka ta fito abunda yake ranta ya isheta, damuwarta tayi mata yawa.
Chapter 125 · 0% Book details