← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 173

Sashe 33

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Bari kiji na faɗa miki, ko ki nemo dubu ɗari uku da hansi ko kuma a bakin auren ki!”

Bata san lokacin data kwantar da kanta gefe tana masa kallon da ita kanta bata san tana masa ba, ta kasa tantancewa shi ne ko ba shine ba.? Fuuuu ya bar ɗakin kamar walƙiya yana wani irin huci.

________________________________

I need more and more comments. 🙌
Bari na ga suwa suke son nayi long chapter gobe 🤔

BEST REGARDS 💖
Khadeeja Candy 😘🌺
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                            Website
www.khadeejacandy.com.ng

Masu Tambayar Labarin Uzair da Amira zai zo muku a gaba, tare da nasu Zagon ƙasa. Just keep moving komai zai zo daki-daki.

*PAGE - 25*

NOT EDITED ⚠️

KALSOOM POV.
Ta daɗe a gurin tsaye duniyarta na juya mata, kunnuwanta sun kas ɗaukar abunda suka ji Hilal ya faɗa mata, idonuwanta kuma sun kasa yarda da ba mafarki take ba.
Makomar aurenta take tunani, yadda zamanta a gidan zai kasance yake mata yawo a ƙwaƙwalwa, taya zata biya abunda bata ɗauka ba? Akan me zai nuna dubu ɗari uku sun fi aurenta daraja a gareshi? Dan me idonsa zai rufe har yayi mata wannan furucin?

Ta kasa zaɓa tsakanin igiyar aurenta da kuɗin da idan har ta bashi zai iya tabbatar masa da lallai ita ɗin ce ta ɗauka.
Hawayen dake idonta ta share, ta tashi ta ɗauko akwati ta buɗe wardrobe ta ɗauko tufafinta ta saka aciki, ta ɗauki jakarta ta saka wayarta da duk wasu abubuwa da tasan zatayi saurin buƙata, ta zari mayafin ta yafa ta jayo akwati ta fito. A lokacin Hilal yana zaune falon ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya.

“Ina zaki je?”

“Gidan mu, ba kace na kawo kuɗi ba ko kuma a bakin aure na? Ni ba zan iya biyan abunda nasan ban ɗauka ba, amman Allah yana nan baya bachi baya angaje zai bayyana gaskiya, amman ni ba ɓarauniya bace”

Tasowa yayi ya ƙaraso kusa da ita.

“Look Kalsoom ...”

Sai kuma yayi shiru ya kasa magana, ya kuma kasa kallonta. Ganin hakan yasa t share hawayenta ta cigaba da jan akwatin. Sai ya riƙe ya kai hannu ya riƙota, kuma ya kasa mata magana, shi dai ji yake babu daɗi ya rasa abunda ke damunsa, sai yanzu yake jin nadamar furucin da yayi mata, mamakin yake yadda ya alaƙanta sakinta da kuɗin da basu taka kara sun karya ba a gurinsa, bayan kuma baya da tabbacin ita ɗin ce ta ɗauka.

“Ban aureka dan dukiyarka ba, balle har ya kai ni ga yi maka sata, nayi tunanin kasan darajar aure, ashe na yi kuskure, daman an faɗa min baka son haihuwa kana son kayi amfani da wannan damar ne ka wulaƙanta ni ko? Zan bar maka gidan ka sai ka zauna da wanɗanda ba ɓarayi ba!”

Kalamanta sun harzuƙa shi matuƙa, sai kawai y saki hannun nata.

“Kije duk inda zaki je, amman bari na faɗa miki duk wani abu ya samu cikin nan na ki, Wallahi sai kin yabawa aya zaƙinta”

Cikin wani irin ɓacin rai ya nufi ɗakinsa, ita kuma ta bishi da wani kallo na takaici na baƙinciki, kamin ta saka kai ta fice.

Ɗakinsa ya koma ya zauna, rasa yayi abund ke masa daɗi, dawowar da yayi ɗaukar kuɗi sai ya kasa komawa. Ba shi ya fito ɗakin ba sai da lokacin ɗauko yaransa daga makaranta yayi har ya gota, sannan ya fito daga ɗakin.
Kukan Rafiq yaji da yaji yasa shi ya nufi ɗakin Kalsoom dan shi sam ya manta da Fariq na bachi.

Ɗaukarsa yayi ya ɗora a kafaɗa yana jijjigashi, ya fito ya buɗe motarsa ya saka shi gidan gaban, sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar.
Ko da ya isa ɗaukarsu duk sun ƙosa, ga Rafiq sai kuka yake masa, har suka dawo gida.
Da gudu suka shiga falon, sai suka tsaya a gurin da Kalsoom ta saba nuna musu su aje safunan su suka aje sannan suka nufi ɗakinta suna rigangan.
Ganin bata ɗakin yasa suka fito suka nufo kitchen da gudu, nan ma basu ganta ba, sai suka nufo dinning gurin da Hilal yake tsaye yana haɗawa Rafiq madara.

“Daddy ina Anty?”

Yi yayi kamar be ji su ba, har sai da suka ƙara tambaya sannan ya kalli Ezzah kasancewar ita ce babba.

“Anty ku taje unguwa”

“Yaushe zata dawo?”

Ulfah ta tambaya. Sai da ya sawa Rafiq madara a baki sannan ya amsa musu.

“Ni ma bata faɗa min ba”

“Daddy ta dafa mana abinci?”

“A'a bari Rafiq ya gama zan muku takeaway yanzu”

“Anty tace mu daina cin takeaway sai abincin gida”

Kallonta Ezzah yayi da kyau.

“Amman yau Anty ki bata nan na ce zaku ci takeaway”

“Daddy ka dafa mana Indomie”

Ulfah dake ƙoƙarin cire uniform ɗinta ta turo baki tace

“Ba za mu ci indomie ba ai da safe Indomie muka ci, Daddy ayi mana takeaway”

Ezzah ta nufo a fusace tana faɗin

“Allah kuwa duk Anty ta dawo sai na faɗ mata nace kin ci takeaway”

Ita kuma sai ta taɓa hannayenta alamar ma shiryawa masifar.

“Nima na faɗa mata na ce kin yi faɗa da wata a makaranta, ai ta ce ki daina faɗa a makaranta”

Hannu Ezzah ta kai zata daketa sai Hilal ya katsa mata tsawa.

“Ezzah karki dake ta, zan dafa miki indomie, ke kuma zan miki takeaway is that okay?”

Duk suka haɗa baki gurin amsa masa.

“Yes Daddy”

“Come and take your brother”

Ezzah ce taje ta karɓe shi, sannan ya nufi ɗakinsa kansa na masa wani mugun zafi.

NAMRA POV.

Tare suk kwana a gidan ita da Mardiya. Sai dai ita batayi bachi ba, har safe Asim take tunani da halin da yake ciki.
Tasan ita kaɗaice a duniyar nan zata iya taimakonsa, idan kuma har bata masa ba waye zai masa, tun da mahaifiyarsa bata da hali.

Babu abunda ya fi ɓata mata rai kamar abunda Anty Amarya da Maryam suka mata, kuma bayan su bata tunanin akwai inda zata iya zuwa ta kai kukanta.
Tun da tayi sallah asuba ta shiga kitchen ta haɗ ma Mama abun kari, sannan ta shigo ɗakin da suka kwana da Mardiya ta tasheta.

Tashi tayi zaune tana murtsikar ido.

“Ina kwana har kin tashi?”

“Ba dole na tashi ba, har na haɗa muku abun karyawa,dan Allah shiga ki wanke bakin ki ki karya, idan kin san gidan wat dillaliya ki kai ni ko kuma ki kira min ita ta zo ta siye gadona”

Mardiya ta daki ƙirji

“Gadon ki kuma? Haba Namra karki siyar da gadon ki mana”

“Idan ban siyar da shi ba, kai na kike son na siyar ? Ko sata zan yi? Ba ki ga hali da mijina yake ciki ba”

“Amman ba ku da ƴan'uwan ne da za su iya taimaka muku?”

“Ƴan'uwana sun juya min baya, shi kuma ƴan'uwansa ba wani hali ne dasu sosai ba, nasan ko da za a samu ba zai wuce ayi karo karo ba, kuma kin ji abunda likita yace kar ya wuce kwana biyu ba'ayi masa aikin ba”

Sosai Mardiya ta ɓata rai tana nuna mata rashin jindaɗinta akan siyar da Gadon da Namra zata yi.

“Gaskiya ni ban jidaɗin haka ba”

“Ba komai Allah zai bani wani, tashi ki shirya ai kin san wata mai siye ko?”

“Eh akwai wata a nan unguwar mai siye sosai”

“Dan Allah ki min magana da ita yanzu kar rana yayi, kuma ina son kije ki kai musu abincin su”

“To bari na tashi”

Ƙoƙarin tashi take tana wani kare-karen zane, kar sarƙar dake jikinta ta faɗo. Ita kam Namra bata ma kula ba sai ta tashi ta bar mata ɗakin.

A haɓar zanenta ta ƙulle sarƙar sannan ta shiga banɗakin, ta wanke fuskarta, koda ta fito har Namra ta kawo mata taliya a plate da ruwan sanyi ta aje mata.
Haka ta riƙa aika abincin kamar wata tsohuwar mayunwaciya, nan da nan ta ƙare ada plate ɗin, ta sha ruwa sannan ta fito falon tana faɗin

“Bari naje na kira miki ita”

“Toh dan Allah ki yi sauri”

Namra ta faɗa tana shan tea ɗin dake hannunta, idonta duk sun wani zurun-zurun kamar ita ce marar lafiyar.

Mardiya bata ɗauki dogon lokaci ba ta dawo tare da matar, sai da suka gaisada Namra sannan Namra ta ta shiga da ita cikin ɗakin ta nuna mata gadon. Tana ganinsa tasan sabo ne, amman duk da haka sai da ta gama duba ko ins nasa sannan ta kalli Namra tace

“To nawa aka masa kuɗi?”

“Babu wanda ya taya, ki siya kawai”

“Toh ai ba siyen ba, kin san irin wannan manyan kayan ba ko wace mai keya ke siyen su ba, sai su daɗe baka sai da ba amman ke nawa kika ga zaki iya sai da su?”

“Ni dai miliyan ɗaya har da wani abu Abbah ya siya min su, ke kuma sai ki kwatanta”

“Kai kai aiko an daki hancinsa, dan wannan kayan yanzu wasu ma sun daina yayinsu, ai sun faɗi sosai. Sabin ma ba zasu wuce ɗari bakwai ba”

“Tau ki bayar da haka ɗin”

Tayi ma Namra wani kallo tana taunar goron dake bakinta.

“Ni ko ai ba zan ci riba ba, magana ta gaskiya zamu yi, dan ni bana son nakkasa mutum, ƙara ayi ciniki babu cuta babu cutarwa, indai zaki iya bari ɗari, shima dai ƙoƙartawa zan yi dan ba duk dillaliya ke zuba kuɗi da yawa ta siye kayan data san ko ta sai da ko karta sai da ba”

“Haba baiwar Allah, Wallahi lalura ce tasa zai sai da abu na, ba kiga sabo ba ne”

“Na gani amman ai kin san duk abunda aka riga aka fitar indai kuɗi kake so sai ka faɗi, amman yanzu zan yi miki magana ɗaya idan yayi miki na siye ɗari uku da ashiri”

Kallon gadon Namra tayi ta sake kallonsa ta kalleshi sannan ta kalli Matar tace

“Kawo kuɗin”

“Amman fa sai naga mai gidan ki, dan wani lokacin ana siyen kaya sai kuma miji ya zo yace shi ba za'a siyar da kayan matarsa ba”

“Mijina ba shi da lafiya kuɗin magani nake nema shiyasa zan siyar da wannan gadon, yanzu haka yana asibiti aiki za a masa”
Chapter 33 · 0% Book details