← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 173

Sashe 58

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita ƙaɗai take magana da kanta, tana wani irin kuka mai taba zuciya. Bata ji a yau zata iya kwana a katsina, dan a yau bata buƙatar kowa a kusa da ita sai yan'uwanta, da mahaifiyarta, tasan ko hira kawai tayi da su zai rage mata damuwa, sama da zaman kaɗaici da take yanzu.
Tashi tayi ta matsa kusa da inda ta aje ƴan komatsanta.
Jakarta ta buɗe taga kuɗin da yayi mata saura, sai ta shiga BQ ɗin ta ɗauko Sarƙa da wayarta ta saka a jakarta ta sauya hijabinta ta jawo BQ ɗin ta fito tana kuka.

Sai da ta tari Napep ta shiga sannan wani tunanin ya zo mata. Idan ta koma gida da wane ido zata kalli Anty Amarya? Me zata cewa Abbah? Masu jiran su yi musu dariya tasan zasu yi. Har ya kai ta tasha bata samawa kanta wata mafita ba, sai dai hakan be hana ta shiga motar sokoto ba, tun da bata da wani gurin zuwa sai can.

ABDOOL POV.

Yana zaune ƙasan Carpet yana cin abinci, Ummi dake zaune saman kujera ta tsare sa da ido tana kallon ɗan nata cike da tausayawa.
Sai da ya gama cin abincin sannan ya kalleta yana murmushi.

“Ummi wannan kallo ai sai ki tsorata ni, gani zanje Abuja gobe ai sai kisa nayi tunanin ko mutuwa zan yi”

Ɗan murmushi tayi ta kawar da kai.

“Kawai ina tausayin ka ne, jiya da zafin jiki ka kwana saboda tunanin nan yarinyar how i wish ina da wani abu da zan yi akai”

“Karki damu, ni ai haka jiki na yake, mutane suna cewa ba komai bane dan kaji mutum da zafin jiki”

“Ba irin naka zafin ba, wacan ɗan ɗumi ake nufi kuma shi ma a mace ne ba namiji ba”

Dariya yayi ya tashi tare da plate ɗin

“Ummi kenan, ni fa bana da wata damuwa yanzu sai ta Mai Martaba”

“Zan yi magana da shi ai na faɗa maka, kawai kai dai ka samu natsuwa kuma ka kwantar da hankalin ka”

“I will try inshallah”

“Ni Allah yasa ma Abujar nan da zaka je ka haɗu da wata wanda zaka so fiye da wannan ma”

“Ai gurin aiki zamuje ba gurin hutawa ba, idan kuma kina son na ɗauko miki soja shikenan, sai na auro soja”

Wani tsaki taja ta ɗauke kai ta mayar gurin tv. Shi kuma yayi dariya ya shige kitchen.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*

*© Khadeeja Candy*

*PAGE - 42*

NOT EDITED ⚠

Da yamma lis Namra ta sauka babbar tashar sokoto, sai da kowa ya gama fita motar kasancewar ita ce a can baya sannan ta fito jiki a sanyaye, tana kalle-kalle kamar mai tunanin inda zata je.

A hankali ta cira ƙafarta da tayi mata nauyi saboda zaman mota ta fara takawa, ta doshi ƙofar fita tashar gabanta sai faɗuwa yake kamar zai fito, wani abu ta ji ya zo ya tsaya mata a zuciya, yana ƙoƙarin danne mata numfashi.

Ta daɗe a tsaye bakin ti-ti sannan ta tari Napep ta shiga, sai da ya fara tafiya da ita suka yi nisa sannan ta ɗan karkato ya tambayeta inda za a kai ta ganin bata ce masa komai ba tun da ta shiga Napep ɗin.

“Hajiya ina za mu?”

Shiru tayi kamar mai tunani, ta ɗauki tsowon lokaci bata amsa shi ba, har sai da ya ƙara tambayarta.

“Clapperto....road, gurin....gawon nama”

“Dari biyu zaki biya Hajiya”

“Ok..ay.. Allah Kai... Mu lafiya”

“Amin”

Ya kai hannu ya kunna waƙar Umar M Shariff ta duniya makaranta. Sauraren waƙar take tana hawaye, hankalinta da tunaninta gaba ɗaya ya tattara ya koma gidan su da take tunkara yanzu. Abunda zata faɗa musu take ta saƙawa amman har ta saka samun mafita.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta furta a hankali lokacin da Mai Napep ɗin ya kunna kai cikin unguwar. Jin tayi kamar tace ya juya da ita, sai dai idan ya juya da ita ɗin ina zata ce ya kai ta?

“Ya isa...”

Ya faɗa a lokacin daya kawo bakin ƙofar gidan su. Sai da ta share hawayen idonta sannan ta ciro kuɗinsa ta miƙa amsa, sannan ta fita jikinta har rawa yake irin na tsoro da rashin gaskiya yana tare da ita.

Sai da Mai Napep ɗin ya wuce, sannan ta doshi ƙofar gidansu, cikin wani irin mugun faɗuwar gaba. Har ta kai hannu zata tura ƙofar gate ɗin sai kuma ta tsaya tana jan numfashi.
Tafi kowa sanin waye mahaifinta, ta kuma san halinsa ba zata manta furucin da yayi mata ba, bata san iya furucin da zai ƙara mata ba.
Babu wacce ta faɗo mata a rai, sai Gwaggo Kulu, ƙanwar Abbah, mahaifiyar Anty Yasmin.
Tasan ƙanwar Abbah ce amman Abbah yana jin maganar ta sosai kuma tasan yadda Gwaggo Kulu take son ta cikin ƴaƴan Abbah.

Juyawa tayi da saurin ta nufi farƙon unguwar dan ta can ne zata fi saurin samun abun hawa. Sai da ta kusa ƙarasawa babban ti-ti sai ta ga Motar Maryam ta kunno kai cikin unguwar. Da sauri Namra ta kawar da fuskarta dan kar Maryam ta ganta, ashe tayi a banza dan baya-baya Maryam tayi da mota ta fara leƙen fuskarta, hakan be gamsarda ita ba har sai da ta faka motar gefe ta fito ta fara bin Namra da ƙafa tana kiran sunan ta.

“Anty Namra ke ce?”

Juyowa Namra tayi ta kalleta idonta da hawaye ta ɗaga mata kai.

Wani irin tsalle Maryam ta daka ta rumgumeta tana ihu.

“Wallahi ban ɗauka ke bace nayi zaton wata ce mai kama da ke, Anty Namra ina za ki?”

“Gidan Gwaggo Kulu zan je”

Ta faɗa cikin kuka tana rumgume da ƙafaɗar Maryam. Maryam ta ɗago ta kalleta

“Miyasa ba gida kika zo ba?”

“Amman nasan Abbah ba zai bari na zauna ba, korata zai yi”

Maryam ta dafa kafaɗunta.

“Fushi kika yi?”

Tayi shiru bata amsa ta ba, hakan ya tabbatar ma Maryam amsar tambayar.

“Wani abun Asim yayi miki ne? Karki ɓoye komai Anty Namra ki faɗi abunda yayi miki, dan ba zai yiyu ya taɓa mana ƴar'uwa ba mu ƙyale shi”

“Be min komai ba, ni dai kawai na gaji da zaman can ne”

“To ki zo muje gida”

“A'a ni ba zan je ba, Abbah zai kore ni kuma Anty ba zata ji daɗi ba”

“To ya zaki yi? Kina da inda ya fi miki gidan uban ki ne? Ko yanka namanki zai yi yayi gunduwa-gunduwa da shi dole ne ki shiga tun da baki da inda ya fi miki nan”

“Ni dai ba zan je ba, gidan Gwaggo Kulu zan je”

“To muje na kai ki”

Maryam ta faɗa tana nuna mata motarta. Kamar ba zata shiga ba, sai kuma ta nufi motar ta buɗe ta shiga. Sannan Maryam ta shiga driver seat ta tashi motar, ribas tayi ta juya ta inda ta fito, sai da suka hau babban ti-ti sannan Maryam ta kalleta tana takaicin halinta tace

“Wani lokacin Anty Namra kina ban haushi da mamaki wallahi, kina abu kamar ba kece yayata ba, abunda kike yi ko Aisha da take ƙaramar mu ba zatayi ba. Kin san abunda yake cutar da ke? Tsoro da gudun zuciya, da ganin ke ba zaki iya ba, sune suke cutar da ke.

A duk kuma lokacin da kike ganin ke ba zaki iya ba, to ba zaki taɓa iyawa ba har a bada, lokacin da zaki hankalto kice zaki yi a lokacin ba ki da time, shiyasa yan karon magana suka ce if you say yes to others make sure you didn't say no to yourself, saboda zaki cutar da kan ki ne kawai, ba zaki taɓa burge kowa ba a duniyar duk abunda za kiyi wani sai yace kin masa ba dai-dai, ya kamata ace kin canja haka nan accept responsibility for your life, ya kamata ki san it is you who will get you where you want to go, no one else, duk wanda kika gani yana kusa da ke wallahi da zaki waiwaya wata rana zaki ga duk babu so, sai mai miki so na haƙiƙa, wasu duk dariyar fuska ne bda xaki san abunda yake zuciyarsa da ba zaki sake kallonsa ba.

A maimakon ki ƙara hankali da tunani amman kullum sai wata iri kike zama, kamar wanda ake cirewa ƙwaƙwalwa ana zubarwa, tsoron nan da yake ran ki dan Allah ki cire shi Namra, you have to your fears, kuma ya kamata ace kisan cewa kema kina da right and freedom...”

Tun da Maryam ta soma maganar in banda kuka babu abunda Namra take, ta san gaskiya ƴar'uwarta ke faɗa mata, tabbas akwai tsoro a a tare da ita, tsoron abunda mutane za su ce, tsoron ɓacin rai, tsoron ganin ita ba zata iya ba, da kuma gudun zuciyar wanda duk take tare shi. A rayuwar Namra bata iya so ba, irin son nan take yi na sadaukar da komai nata saboda wanda take so ko kuma ta yarda da shi. Indai Namra ta aminta da kai to kai je ka kwanta kawai kayi kwana, ita zata maka komai idonta ya kan makance ga duk wanda take so, bata ji bata gani.

“Mtsssssss”

Maryam taja tsaki.

“Aikin kenan sai kuka, da anyi miki abu kuka dai kuka, da kuka zai miki magani ai da tuni yayi miki, haka kika zo kika sakarwa yarinyar Amira jiki ta yi ta cin amanarki, Allah kaɗai yasan dalilin guduwarta daga gida, amman kullum uwarta ke take cewa ke ce sanadi”

Unguwar Bafarawa estates Maryam ta kai Namra, gidan Gwaggo Kulu.
A bakin gate ɗin gidan tayi farkin ta kalli Namra

“Yanzu idan kin shiga sai kice mata me?”

“Zan ce nan na fara sauka ne”

“Toh nidai ba zan shiga ciki ba, kuma idan na koma gida zan faɗawa Anty duk yadda muka yi da ita zan dawo na faɗa miki”

“Amman dan Allah karki faɗawa Abbah”

“Tau ina gaida Gwaggo”

Namra ta fita motar cikin yanayin damuwa ta shiga gidan Gwaggo. Sai da ta shige sannan Maryam ta juya da motarta tana mamakin lamarin Namra.

Cikin sanyin jiki Namra ta shiga harabar gida,har ta ƙasa falon tana jin tsoro kamar wanda za'ayi ma wani abu.

“Assalamu alaikum”
Chapter 58 · 0% Book details