← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 173

Sashe 127

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan kana da buƙatae wani abu ka riƙa min magana, dan yanzu nauyinka ya dawo kai na, shiyasa na tura maka wannan kuɗin dan ka samu na ƴi ma kan ka hidima, amman fa a riƙe sirri, kuma ni ina da kishi gaskiya ɓana son ka yi mu'amala da wani idan har ba ni na haɗa ku ba”

“Zaka same kamar yadda ka tsammace ni inshallah”

Daga haka Alhaji Nasir ya miƙe tsaye.

“Ni zanje Abuja ajima kaɗan, yanzu zan leƙa gida ne”

“Ba matsala Alhaji Allah ya kiyaye hanya”

Sai da ya fita da kusan mintuna latatin sannan Asim ya fito daga gidan ya nufo gida. Ko da ya shiga Mama har ta soya nasa dankali da ƙwai ymta haɗa masa tea mai kyau dan tasan shine favorite ɗinsa, shi kam ko kallon su be yi ba, dan yanzu ya wuce gurin kwaɗayin irin waɗannan, beside yama riga da ya ƙarya gurin Alhaji Nasir.

“Nayi tunanin zaka dawo jiya muka ta jira baka dawo ba, na kira wayarka kashe”

“Eh masallaci na kwana, bayan gama sallah isha'i daman na kan yi haka ko a gida yanzu saboda ina nafila dare”

Yayi mata ƙaryar ne saboda bashi da hujjar cewa ya kwana a wani guri bayan kuma ga gidansu. Ita kam daɗi ya mamaye ta.

“Ai haka na da kyau, ƙara a riƙa godiyar Ubangiji, sai kaga yana ƙara maka, kuma ya kamata ka samu lokaci muje gurin Malam na Allah ya baka ƙaiƙayi koma kan masheƙiya saboda maƙiya”

Miƙewa yayi tsaye.

“Kai Mama ni duk bana da lokacin wannan, yanzu dai ga kuɗi nan ki rabawa maƙota, idan na samu gidan sai a faɗa min”

“Toh ya yi Allah ya tsare min kai, amman har zaka koma yanzu? Jiya jiya fa ka zo garin nan ”

“Wallahi aikwai aiki a can, kuma ki ciri kuɗi ki buɗe account a bank zan turo miki kuɗi ki bawa su Baba sani, kuma ki faɗa musu anytime zasu iya jin kirana akan maganar auren nan”

Yadda yake mata magana kamar yana bada umarni ne. Wani jin kansa yake yanzu kamar minister. Ta so ya tsaya su yi fira amman bata samu dama ba dan ya nuna yafi son tafiya kamar wanda ake tsakala. Har bakin mota ta rako shi tana faɗar masa

“Yanzu sai iyayen Namra sun samu labari ka yi kuɗi, amman basu san ka sake ta ba, tun da bata zo gida ba”

“Dole ne ai su samu labari, ni nafi son haka ma”

Ya buɗe motarsa ya shiga. Tana ɗaga masa hannu har ya kama hanya.

Be tashi da wuri ba, dan ko da ya baro sokoto shabiyu har da kusan rabi. Ko da iya isa Katsina yamma ta yi sosai, sai dai Nably ta yi masa kira ya fi biyar dan jin lafiyarsa, Mardiya ma ta kira ta faɗa masa tana son ganinsa.
  Yana isa katsina ya kira wayar Hajiya ya fara gaisheta, still ta faɗa masa tana birnin keebi, dan ya so ya fara zuwa ya gaishe da uwar ɗakin tasa ko zai goge laifinsa. Gidansu ya sauka yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan ya wucce gurin ƙanen dad ɗinsa wanda ya manta rabonsa da yaje can sun suna aikin ƙira kamin su haɗu da Hajiya Sadiya.

Su kansu sun yi mamakin ganinsa, daman suna jin labarin yayi kuɗi sama-sama a gurin jama'ah, bama abunda yafi basu mamaki kamar yadda kuɗin suka taso masa lokaci ɗaya. Sun yaba da motarsa da kuma shigarsa har suka masa fatan Allah ya tsare, a nan ya ɗauki kuɗi mai yawa ya bashi, abkan da suka yi aiki tare ya raba musu wani abu. Sai da Ƙanen Baban nasa ya rakosa zuwa gurin motar yake labarta masa dalilin zuwan nasa.

“Gida nake so a sama min kamar na miliyan biyar, mai kyau sosai”

Shin kam riƙe baki yayi jin Asim ya ambaci miliyan har biyar, yana mamakin ace yana da wannan kuɗi haka da yawa, a take zuciyarsa ta raya masa ba kuɗin halal ba ne, sai dai babu damar faɗa masa gaskiya dan yana tsoro, daman idan kana da abun hannu ana tsoron faɗa maka gaskiya balle Asim da yasan zai iya yin cikinsa da masifa.
  Da zimnar idan an samu za a kira shi a sanar da shi suka aje, sannan ya yi masa sallama ya kama hanyar gidansu Mardiya.

YASMEEN POV.

Tana shiga ta aje kwalin, ta koma kan Adnan daya sauka ƙasa yana zare zaren shoes ɗinsa, da hannu ɗaya but still hannunsa ɗaya yana gurin sai susa yake. Yana ganin Yasmee yayi saurin dainawa, yana wara idonsa na marasa gaskiya.

Hannu biyu tasa ta ɗauke shi sai ta zauna ta ɗora saman jikinta tana murmushi.

“Aya tell me mi Dadee yake ma ka?”

Rufe ido ya yi yana dariya, ita kuma ta maida kunnenta gurin bakinsa.

“Faɗa min mana ko mu ɓata”

“Ba zaki faɗa ba?”

“Ba zan faɗa ba”

“Wannan abun ƴake sa min a nan”

Ya nuna mata gurin fitsarinsa, sai ta sauke shi ƙasa.

“Nuna min mi yake sa maka”

“Wannan abu yake samin a baya, sai yacw na kwanta, kuma da zafi sosai yace idan na faɗa sai ya yanka ni da wuƙa ƙamar yadda ake yiwa rago”

Ya cire wandonsa ya nuna mata. Wani irin faɗuwa gabanta ya yi, a take ta samu kanta cikin wani irin tashin hankali, wanda bata taɓa sa masa rana ba, a take zuba ta fara karyo mata, numfashinta yayi mata mugun nauyi, sai tayi saurin rumgume Adnan dan kar ya ga hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.

“Your Dadee did a great thing”

Ta soma shafa bayansa cike da tausayinsa kanta da kuma nata, sai dai ko kaɗan bata son ya ga hawayenta. Sai ta sauke shi ta mike tsaye.

“Bari na zuba maka abinci ka ji”

Ta yi saurin juya ta bar ɗakin. Kitchen ta shiga sai ta samu mai aikinta tana yanka salat da tumatur.

“Jeka kawai zan ƙarasa”

“Toh”

Aje ragowar da ke hannunta ta fice. Hannu biyu Yasmin tasa ta riƙe kitchen cabinets sai ta fashe da wani kuka marar sauti. Ƙafafunta kasa ɗaukarta suka yi, sai gata ƙasa jikinta har karkarwa yake.

“Innalillahi wa'inna ilaihi”

Shine  abunda take ta maimaitawa, gudun kar kukan ya ci ƙarfinta. Kulolin ta buɗe ta ɗauki plate ta zuba masa white rice and pepper soup, ya saka nasa spoon, sannan ta ɗauki ruwa ta wanke fuskarta ta fito tare da abincin.

Ɗakinta ta nufa riƙe da abincin, hawaye sun ƙi tsaya mata. Aikin baban giwa ta samu yana yi, dan har ya buɗe kwalin data aje, azatonsa wani abun ci ne a ciki ko chocolate ganin. Ita bata ma bi ta kan kwalin da ya fasa ba, shi kawai take kallo har ta aje abinci, tausayinsa duk ya kama ta, sai ta riƙo hannunsa ta karɓi takardar dake hannunsa ta aje gefe. Taja shi jikinta, ta rumgume.

“Momee babu komai a ciki”

Cikin kuka ta amsa shi.

“Ba na ka ba ne, na Dadee ka ne”

Kuka take sosai tana ta ƙoƙarin ƙaryata abunda zuciyarta take son yarda da dashi, can kuma ta sake shi ta janyo abinci ta aje masa a gabansa. Ta zauna ta tsare shi da ido hawaye na cigaba da mata zuba.
Kamar kuma an tsikare ta share hawayen idonta, ta miƙe tsaye ta ɗauki wasiƙar da jimmar maidawa cikin kwalin, babu abunda ya bata mamaki kamar ganin da tayi babu komai a kwalin sai wasiƙa, babban kwali kamar wannan a'ce babu komai a ciki sai wasiƙa, to me wasiƙar ta ƙumsa ne haka?
Zaunawa ta yi a kusa da kwalin ta warware wasiƙar, gabanta sai faɗuwa yake ta soma karantawa.

_Zuwa ga Azzalumin mutun, macuci mayaudari, nasan kana nan raye kamar ƴadda nima na ke raye, ko kuma na ce ka so ka halaka ni Allah be baka dama ba, ka yaudare ni Uzair kace Namra zamu ma Asiri ashe ka haɗa kai da ita ne ni kuka yi ma wannan asirin na bar gida, ban taɓa gane haka ba, sai a yanzu da nake da buƙatar da dawo na kasa, Wallahi Wallahi kaje ka karya wannan asirin ko kuma na sa a kashe ka, dan kasan na san ka, kuma na san inda kake, ni ko baka san inda na ke ba a yanzu, kuma ina tabbacin baka san ko wacece ni ba_

Sai number wayarta daga ƙarshe. Abunda ya tsayawa Yasmin a rai, wacece wannan yarinyar? Sannan mi suka ƙulla da Namra? Mi mijinta ya aikata ne?
Ta miƙe tsaye cike da rashin kuzari, abubuwa biyu sun tsaya mata a lokaci ɗaya kuma akan mutun ɗaya. Wani tunanin ne ya zo mata, da sauri ta ɗauke kwalin ta fita da shi ta saka cikin shara, sai ta dawo ɗakin ta ɗauki wasiƙar ta mayar da ita a yadda take, sai ta je cikin littatafanta na aiki ta samu wata silver paper, ta yi wrapping ta naɗe wasiƙar ciki da kyau ta saka salatif, ta kai masa ɗakinsa ta aje masa.
Tana shigowa ɗakinta jiri ya kwasheta, ta faɗi dafe da kai.

ANTY AMARYA POV.

Cikin ƙarfin hali ta unƙura ta nufi part ɗin Abbah, dan yau bata jin daɗin jikinta sosai, wata ƙila fever ɗin ne zai sake dawo mata. Yadda ta tararda Hajiya Barau da Abbah a falon ya ɗan tashi hankalinta, dan a zatonta ya aika kiranta ne dan su tattauna maganar auren da ake na su Hindatu da Maryam. Zaunawa tayi tana kallon yanayin Hajiya Barau da ta riƙe baki tana kallon Abbah, sam bata lura da takardar dake hannun Abbah ba sai da ya mika mata takardar.

“Wai wasiƙa ce daga Faɗar Mai Martaba sarkin Katsina, wai ana bukatar gani na gobe”

“Subhanallahi miya faru?”

Anty Amarya ta tambaya zuciyarta na rawa fat fat fat.

“Wallahi ban sani ba, ni abun ya ban mamaki mi na aikata da Sarki Katsina zai aiko kirana? Ina ma na san shi?”

Hajiya Barau ta mere baki, har da wani ƙis take.

“Allah yasa ba Namra ta yi maka janye janye ba”

Kallo ɗaya Anty Amarya ta yi mata ta ɗauke kai, maganar na sukarka, ta miƙe tsaye ta bar musu falo.
Chapter 127 · 0% Book details