← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 173

Sashe 151

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɓangaren Mardiya ma ƴan kashe wutar gobara ne suke ta kai da koma amman wutar da ƙi mutuwa, babu abunda yaba jama'ah tsoro kamar yadda wutar take ta sama kamar abar da ake sawa fetur, ba ɗakinsu wutar da tashi ba, amman bata rage komai da yake ɗakinsu Mardiya ba, har da kayan baƙi ƴan zuwa biki sai da wutar da cinye, sannan ka bi sauran ɗakunan gidan duk ta cinye.

Mardiya na maƙota aka faɗa mata, daman tun da aka fara bikin maƙota take kwana ita da ƙawayenta, ko da ta zo wutar ta ci har ta cinye babu abunda ya rage a cikin gidan, a take ta saka kuka ganin komai ya ƙone babu abunda take ji kamar kayan mutane da suka ƙone, babu daɗi ace kaje biki wani abu ya faru. Bata ƙara firgicewa ba har sai da wani abokin Asim ya zoɓya labarta mata halin da suke cikin ma ƙonewar da wacan gidan yayi wanda za a kaita.

Hannu ta ɗora saman kai ta fashe da kuka tana kiran ta shiga uku.

“Allah yasa ba wutar da nake mafarki bace take bi na ba, na shiga na lalace”

Kuka ta riƙa yi kamar mahaukaci sai da ka riƙeta ana bata haƙuri.

RASHIDA POV.

Bayan ta gama sallah azahar ta tashi tayi nafila sannan ta ɗauki carbi tana lazimi, haka take kullum cikin ibada take fatanta kawai Allah ya yafe mata kamar yadda mijinta da Kalsoom suka yafe mata, a iya yanzu ta yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko mata kuma ta aminta babu mai iya yaye mata ita sai Allah, tabbas tasan Allah yana son ta tun da har ya ganar da ita tun gabanin ya karɓi rayuwarta.

Ta miƙa lamurranta ga Allah, kwata-kwata ta cire rayuwar daga yin aure dan tasan ba zata samu mijin da zai aureta ba, da ma kuma ta samu bata tunanin zata iya zama aure da namijin wanin Hilal. Daman ta daɗe da aje aikinta, duk wani abunda da take da buƙata Mahaifinta yana yi ma, abokanta kuma suna kawo mata ziyara a gidan, waɗanda suka wayanci miye hiv wasu kuma tuni sun ƙaurace mata gudun kar suma su ɗauka.

Ta ɗauki darasi a rayuwarta sosai, tun daga cin amanar aure da tayi, da kuma neman taimakon wanin Allah wato bokaye da ƴan duba, a iya kallon rayuwar Kalsoom da tayi ta fahimci darasin da yake tattare da itazm, tabbas wanda duk ya miƙa lamurransa ga Allah, lallai Allah yayi alƙawarin jiɓantar al'amarinsa, babu irin shige-shige da bata yi ba wajen ganin da raba Kalsoom da Hilal ko ta raba ta da lafiyarta amman addu'o'in da take suka mata kariya da katangar tsari daga duk wani sherinta. Hakan yasa itama ta tattara lamurranta ta miƙa wajen Ubangiji, ta samu natsuwa da kwanciyar hankali sosai, duk da tasan ciwon dake jikinta ba zai taɓa rabuwa da ita ba, amman tana Allah ya sanyaya mata zuciyarta har ta samu ƙarfin halin sakewa tana fita cikin mutane.

Bayan ta gama istigifari ta ɗauke carpet ɗin ta naɗe ta maida mazauninta, sannan ta nufi kitchen dan ɗora abunda zata ci. Vegetables soup ta girka da white rice daman likita yana yawan faɗa mata ta riƙa cin su. Falo ta fito ta zauna tana cin abincinta hankali kwance tana kallon tv, wayarta ce ta yi ringing sai ta miƙe tsaye ta ɗauko, murmushi ta yi ganin number Hilal a zatonsa zai sadata da su Ulfah su gaisa ne sai kawai ya miƙawa Izzah ta yi masa albishir ɗin Anty su ta haihu.

“Mashallah me aka samu?”

“An samu Baby boy, Momi Mai kyau sosai”

Wannan karon Ulfah ce take magana.

“Allah ya raya ashe kun samu ƙane ko? Ina dady ku?”

“Yana can gurin Anty be san mun kira ba, Momi Boy ɗin kato ne sosai kuma fari”

Ezzah ta faɗa with so much joy and excitement. Idon Rashida ya cika da ƙwalla dan har gobe har jibi tana son mijinta sai dai tasan yayi mata nisa.

“Zan zo gobe na ga Baby kun ji”

“Toh Momi”

Suka kashe wayar, ita kuma ta share hawayen idonta tana tuna lokacin da ta haifi Rafiq yadda Hilal ya dinga ɗauki kamar zai haɗeta ita da yaron.

‘Allah sarki duniya’

Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuma sai ta amsa salamar da Alhaji Bashir yake yayinda yake turo ƙofar falon ya shigo.
[7/21, 10:29 AM] Khadeeja Candy♥: *86*

“Miya kawo ka gidana?”

Murmushi yayi ya zauna saman kujera yana kallonta fuskarsa da annuri.

“Haba Hajiya ai ko baki san inda na fito ba kya saurara min ko?”

“Na fi ƙaunar ganin baƙin maciji da kai, bana son abunda zai sake kusantar da ni a gareka Alhaji bashir dan Allah dan Annabi ka tashi ka fitar min daga gida”

“Ban zo gidanki da wata manufa ba Rashida sai ta alheri”

“Babu alheri a tare da kai, dan Allah ka tashi ka bar min gidana”

“Miyasa kike alaƙanta rayuwar da kika shiga da laifina? Bayan kuma idan baki amince ba ba zan iya miki da ƙarfi ba?”

“Nasan nayi kuskure ai a lokacin shiyasa yanzu na tuba na koma gurin Ubangijina, kuma Alhamdulillah rayuwata da dai-daita”

“Nama ai tuban na yi shiyasa nake son dai-daita rayuwa da taki, har ga Allah Rashida ina son ki ba wai so na zina kawai ba, so na haƙiƙa kawai saboda babu yadda zan yi ne, ni da ke kukan mu munyi kuskuren faɗawa a halaka, ke saboda baki da lokacin da zaki tsaya ki bawa mijinki kulawa shi ma kuma ya baki, ni kuma na kasa ƙara aure duk da ina ganin sha'awar wasu matan saboda sherin da matata ta yi min, yanzu kuma Alhamdullillah na gane kuskurena kuma am ready to marry you idan kin aminta, saboda kin rufa min asiri a lokacin da ya kamata ki tona min, kin rufe bakin ki kin haƙura kin bar ni akan aikina, bayan kuma kina da damar da zaki tona min asiri, ki faɗawa duniya abunda muka aikata”

“Ban shirya aure yanzu ba Alhaji Bashir idan ma shi ya kawo ka ka tashi ka bar min gidana”

“Kin fi son ki yi ta zama a haka? Indai akan Asmee ne karki damu bata isa ta hanani ƙara aure ba yanzu”

“Baka tsoron ace ka auri mai cutar ƙanjamau?”

“Daga lokacin da kace zaka damu da matsalar mutane zaka saka kan ka ne kawai cikin matsala, ni da ke da Asmee duka muna ɗauke da abu ɗaya, miye amfanin ke na ƙyale ki akan gudun abunda duniya zata ce min? Zan yi ritaya gudun kyamar da za a nuna min gurin aiki, amman karki manta ina da hannu jari kuma ina da kasuwancin da zai iya riƙe jikokina ma ba ƴayana da matana kawai ba, ki yi tunani Rashida karki yaudari kanki akan abunda zuciyarki take muradi”

Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya fice. Da kallo ta bishi tana sauke ajiyar zuciya, sam bata shirya irin wannan rayuwar ba, aure yanzu? Ita da yanzun tana jin ta samu sukuni a rayuwarta, taya zata yi aure ta sake jefa rayuwarta cikin wani halin kuma? Ita kan bata shirya kishi da Asmee ba.

KALSOOM POV.

Hilal kamar ya haɗe yaron dan murna, duk wanda ya ga Baby boy ɗin sai yayi mamaki ace da kanta ta haihu musamman da suka ji gida ta haihu, wasu daga cikin abokansa suka riƙa zolayarta wai ai matar doc ce dole ya karɓi haihuwarta. Hajiya ta nuna farincikinta sosai duk bayan kwana biyu sai ta zo gidan duba jikanta, Salman kam kullum tana biye da hanya, sai da aka kwana uku sannan Rashida ta zo ganin Baby shi ma kuma da dare, ta yi siyayya mai yawa ta kawo, sai dai bata yarda ta karɓi yaron ba duk da Kalsoom ta yi kawaicin miƙa mata shi, bata yi minti ashirin a gidan ba ta fito su Ulfah suka rakota har bakin mota ta basu kuɗi da chocolate.

Ranar suna Baby ya ci sunan mahaifin Hilal wato Abubakar aka yi masa laƙani da Rafiq. Fuskarsa sak ta Hilal yaro ya sha stickers har ya gaji, an raba abubuwa da yawa ranar sunan, da yamma aka yi walima ta gani ta faɗa, kuloli da manyan kofuna da agogo sai har ma da handbags masu kyau, wasu kuma su samu shoes.

An kashe kuɗi da yawa gurin walimar nan kai kace ma yanzu ne Hilal yake samun haihuwar fari, yadda ya zuba mata kayan barka ma a abun kallo ne, ga kuma waɗanda ta samu daga ɗai-ɗaikun mutane ƴan uwa da kuma abokan arxiki.

ABDOOL POV.

Tafiya yake shaddar dake jikinsa tana amsa amo saboda maiƙon da ke jikin shaddar da kuma sabuntakarta.

Ko da ya shigo part ɗin Ummi yana waya da Mai Martaba dake faɗa masa yana nemansa, a falon ya zauna sai da suka gama tattaunawa sannan ya kalli Ummi da ke cikin shirin ta na fita ya ce

“Ummi fita zaki yi?”

“Eh Asibiti zan je na duba Hajiya Sadiya kasan ciwon nata ya zama abunda ya zama, kuma kaima ya kamata ace ka duba ta, tuɓ da ta kwanta asibitin nan baka taɓa zuwa duba ta ko sau ɗaya, wai anya ma ka mata gaisuwar yarinyar ta da rasu?”

Ya shafa kansa yana murmushin rashin gaskiya.

“Kin san ko da ta rasu ina Abuja, amman dai na kirata a waya”

“Abdallah baka da kirki sam, kai kullum aiki ƴan uwanka ma baka da lokacin ziyartarsu? Sai yaushe zaka huta ne?”

“Ai yanzu zani iya zuwa na mata gaisuwar daga nan na duba jikin nata”

“Allah ya sauwaƙe maka wannan rayuwa, wai ya maganar yarinyar nan ne?”

“Muna nan muna ta sutsa kai, yanzu haka maganar da Mai Martaba yake min kenan, yace min yayi magana da Abbah”

“Ban gane ba, ita bata son ka ne?”

“To gani dai wani ne yake min zagon ƙasa, ita kuma tana min jan aji, yanzu haka anjima kaɗan gurinta zanje, domin hankali yaƙi kwanciya tun lokacin da yaron nan na zo gidansu, last week ma da naje gidan kamar...”

Sai kuma ya fasa maganar ya miƙe tsaye.

“Muje na dubata Ummi, sai na wuce airport flight zan hau”

“Ka fara bani labari baka ƙarasa ba, zan ƙarasa”
Chapter 151 · 0% Book details