← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 173

Sashe 68

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban mirror ya same ta chaɓa ado tana kallon kan ta. Dik wata gajiya da fushi dake tare da shu sai ya kushe, saboda yana son ado, mutum ne mai son ganin mace ta yi kwallaiya a ko yaushe. Murmushi ya ƙarasa kusa da ita yana ƙyaƙƙyawar fuskarta ta madubi.

Ita ma murmushin take tana lumshe ido tana buɗewa, irin na ɗaukar hankalin nan. Sun samu minti biyar a haka suna kallon junansu kamin ya risina ya rumgume ta.

“Who brought this Cute Babe here?”

Lumshe ido ta yi tana sauraren yadda yake shinshinar wuyanta.
Saukowa yayi ya duƙa gabanta ya kama duka hannayenta yayi mata kiss.

“Sweetheart, I'm sorry we lost our baby...!”

Farincikin da ke fuskarta ya gushe, idonta ya cika da ƙwalla, har sun fara zuba a fuskarta.

“How...?”

“I have no idea kawai result ɗin ya nuna ciki be taɓa zama a mahaifarki ba”

“Amman ina jin alamu na ma su ciki, kuma kai ma ka tabbatar min da ciki ne”

“Yes sai kuma yanzu ya zo akasin tunanin mu, ko kin sha wani abun ne?”

Kai ta girgiza masa tana kuka. Sai ya jata zuwa ƙirjinsa ya rumgume ta.

“Shiiiiii Allah zai ba mu wani”

Ƙamƙame shi tayi sosai tana kuka. Har ƙasan ranta take jin zafin zubewar cikin, ta yi buri akan cikin nan har mafarki take, kuma ita bata san ta sha komai na zubar da cikin ba taya za a ce ya zube?

Daker ya lallaɓa tayi shiru, amman duk kwaliyar da tayi ta dale ta ɓata mata fuska kamar yarinya ta yi kuka.

“Ya Salam, yanzu dik kin ɓata kwaliyar nan”

Bata ce masa komai ba, ta tashi ta hau saman bed ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Damuwar da take ciki yasa be yi mata maganar komai ba, sai kawai ya tashi ya koma ɗakinsa yayi wanka ya shirya cikin kayan bachi, sannan ya dawo falon ya kashe kayan kallo, ya tura yaransa ɗakinsu. Sannan ya ɗibi abincin mutu biyu a plate ya shiga da shi ɗakinta.

Dik yadda ya lallaɓata ta ci abincin ƙin ci ta yi, daya matsa mata ma, sai akwai ta fara masa kuka, a dole ya ƙyale ta ya aje abincin jefe dan shi ma baya jin zai iya cin abinci bayan matarsa tana cikin damuwa.
   Haka ta kwana cikin damuwa tana ganin kamar dai wasa Doc yake mata, cikinta na nan tun da ita dai bata ji wani alamu na zubewar ciki ba, sai dai kuma jinin dake mata zuba ya tabbatar mata haka. Sai da ta yaƙi zuciyarta sosai, sannan ta iya godiya ga mahalaccinta, ta fawwala masa komai dan tasan shine mai yi, shi ne kuma ya bata yanzu ya karɓe dan haka sai ta gode masa.

Cikin kwana biyu ta manta abun a ranta, ta cigaba da walwalarta tana sakewa kamar yadda take a da. Ta cigaba da bawa mijinta kula sai dai har gobe matsala ɗaya take fuskanta ta ɓangaren Ezzah dan yanzu abun nata sai ƙara ta'azzara yake tana ƙara tirjewa.
   Yau ma abunda ta saba mata a kullum shi tayi, ta ci abinci dik ta ɓata falon kuma haka zata tashi ta barshi haka sai dai Kalsoom ta gyara.

Da kallo Kalsoom ta bita har ta zauna saman wata kujera ta zauna ta buɗe school bag ɗinta tana fiddo littafai.

“Ezzah miyasa baki jin magana ne? Kullum idan kin ci abinci sai kin watsar kuma ki bar ni da gyara, da nace ki gyara sai ki buɗe baki ki fara yi min kuka? Wannan wane irin rayuwa ne?”

Gunguni ta fasa mata irin maganar nan ta can cikin maƙoshi ta wanda yara ke yi idan suna takarar rashin kunya. Hakan ya harzuƙa Kalsoom ta har ta ƙarasa inda take ta dangwale ta.

“Me kike faɗa? Ke marar kunya ko? Ina miki magana kina min gunguni”

Ɗan wannan abun da Kalsoom tace mata sai kawai ta ɓare baki ta fara kuka tana, ta tashi da gudu ta bar falon.
  A harabar gidan ta je ta zauna tana kuka kamar wacce aka cirewa rai.

Haka ta zauna a gurin har mahaifinta ya dawo ta sanar da shi dukan da Kalsoom ta yi mata. Sam be jidaɗi ba dan babu abunda ya tsana kamar duka, komai zai iya ɗauka amman ban da a dakar masa yara, dan shi be sa musu hannu ba ba zai yarda wata ta sa musu ba, Rashida ma data haifesu baya bari ta dakesu.

“Ba ki mata komai ba zata dake ki? Kalsoom ba zata dake ki haka kawai ba”

“Wallahi ban mata komai ba, kawai tace na share falon nace ta bari na gama homework shine kawai ta mare ni”

“To ya isa yi haƙuri zan mata magana”

“Daddy yaushe Ammyn zata dawo?”

“Ba zata dawo ba”

“Miyasa?”

“Tace ta zaɓi haka”

Ya riƙa hannunta suka shiga ciki. Suna shiga falon ta fisge hannunta ta nufi ɗakinsu da gudu.
   Kallo ɗaya Kalsoom tayi mata ta ɗauke ido tana masa sannu da zuwa.

“Yauwa me Ezzah tayi miki kika mareta”

Ya faɗa yana mai zama a kusa da ita.

“Mari? Ita tace maka na mareta haka tace maka?”

“Baki mare ta ba?”

“Haba Doc mi zai sa na ɗaga hannu na mareta sai kace wari na? Ni dai nasan na zungureta”

“Amman Kalsoom be kamata ace kin dake ta ba, Ezzah yarinya ce dik abunda take yi ƙurciyace, sannan rashin mahaifiyarta yana damunta dole sai kin yi haƙuri da ita, bata da uwa a yanzu sai ke”

“Amman idan ta ɗauke ni uwa mi zaisa ta min rashin kunya? Did i treated her badly ne? Miye bana mata tun mahaifiyarta na nan, sai yanzu dan daga bata nan zata fara min rashin kunya? I'm tired Hilal I'm tired ba rainon ƴaƴanka na zo yi ba, nima aure na zo, idan rainon ƴaƴanka kake so ayi maka kaje ka nemo mai raino, amman ni ba zan iya, ba kuma zan yi ba, ko da zai zamo silar mutuwar aurena ne!”

Kallonta kawai yake irin yadda take zuba masa ruwan masifa har hantanta tashi suke, gaba ɗaya ta fita hayyacinta saboda abunda be kai ya kawo ba.
But all what he thought tana cikin damuwar zubewar cikinta ne, he feel her pain, hakan yasa ya ɗaga mata ƙafa be biye mata ba, sai kaiwai ya tashi ya barta falon.

Fashewa ta yi da kuka ta cire ɗankwalinta ta jefar tana kuka.

“What is wrong with me? Miye same ni? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta tashi da gudu ta shige ɗakinta tana cigaba da kuka, zuciyarta cike da tsanar Hilal bayan be mata komai ba.

NAMRA POV.

Asim be yarda ta dawo ba, har sai da ya ganta asibitin, aiko ya dinga murna kamar ya ɗauke ta ya haɗiye, Mama ba laifi ta tarbe ta far'ah tana na'am-na'am kamar ba ita ba.
Namra ta jidaɗin haka, sai taga kamar saboda tayi fushi ne Asim ya tsorata yayi canja, duk sai ta ji farinciki ya baibayeta ance so hana ganin laifi, ita dai har gobe zuciyarta na son Asim, duk da da shakkun da take da shi akansa, dan ta ƙudiri aniyar naira biyar nata ba zai sake shiga hannun Asim ba, tun har ta gano nufinsa.

Ya samu sauƙi sosai, dan har likitoci suna maganar sallamarsa ganin yanzu yana taka ƙafar sai dai yayi ɗingishi, Mama ta fi kowa jindaɗin samun sauƙin nasa saboda ta matsu ta koma gida zaman asibitin dik ya isheta.
Ranar da Namra ta kwana biyu da dawo taja ƴar fulani suka je kasuwa ta siye wasu abubuwan na kitchen da na ɗaki, da kuma tufafi da hijabi, da ta dawo da yamma ne ta share ɗakin ta wanke ta zuba center carpet ɗin data siyo da taimakon yarinyar ta kira yayanta namiji ya laƙa mata labulaye sannan ta shiga da katifa, da sauran tarkace. Ta haɗa BQ ɗin ba laifi kasancewar ɗakun biyu ne sai ta mai da ɗayan kamar kitchen ɗinta, ta saka abubuwan zuba ruwa da sauran kayan aikinta ciki.

AMIRA POV.

Washe gari Ummi ta dawo ta ga Amira dan tasha alwashi ba zata bar Abuja ba sai ta yi ma Amira godiyar abunda tayi ma ɗanta.

Amira ta jidaɗin haka, ta san ko ba komai ta samu shiga zuciyar Ummi ganin yadda take tausayinta, har da zubar mata da ƙwalla, gashi jikinta ya nuna ita ɗin wata ce, tun daga kan tufafinta zuwa yadda naman jikinta ya kwanta.
Amira ta kama hannunta ta riƙe sai hawaye take tana son shige mata jiki.

“Na ji daɗi da kika zo, na ji kamar a'ce ke mahaifiyata ce”

“Ni mahaifiyarki ce mana miyasa kike magana haka, Allah ya baki lafiya”

“Amin na gode”

Ta faɗa tana kife saman gado asibitin. Abdool na tsaye hannayensa a aljihu yana kallonsu, shi dik ya gundira Ummi ta bar ɗakin, coz he don't trust Amira, kuma hankalinsa be kwanta da ita ba for no reason.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: 4»»»7»»»»»»»»»»»»»»»

“Wai Daddy yace kin ce ba zaki dawo ba”

“Yaushe yace miki haka?”

“Jiya da ina tambayarsa yaushe zaki dawo, wai yace ke kika ce ba zaki dawo ba”

“Baya son ya faɗa miki ne, saboda yanzu baya so na Kalsoom yake so, idan har kina son na dawo dole ne ki riƙa yin abunda na faɗa miki, idan kina irin haka shine sai za ya tausaya muku yace na dawo”

“Amman ita bata jin daɗin abunda nake mata”

“Ke kina jindaɗin data koreni?”

Ta girgiza kai alamar a'a.

“Idan baki yin abubuwan da nake faɗa miki ke ma wata rana sai tasa Daddy ki ya kore ki, sai ta mallake gidan daga ita sai nata ƴaƴan”

Ezzah ta.yi shiru tana tunani sai kallon ƴan makarantar su take masu kai wa da dawowa.

“Ezzah dik duniyar nan baki da kowa kamar ni, duk wacce zata so ki abaya na take, kuma ƙarya Kalsoom take tace tana son ku, tana nuna muku haka ne dan ta mallaki Daddy, yanzu kina jindaɗi zama da ita? Bata dukan ki? Lokacin da ina nan Daddy ki yana miki faɗa?”

Duk ta girgiza kai.
Chapter 68 · 0% Book details