← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 173

Sashe 113

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Be ji zai iya kwana a yau ba,ba tare da yaje gurin Namra ba, daman yasan duk daɗin bakin da yake yi ma Ummi ba wani barinsa zata yi ya daɗe ba, kuma idan har ta bar shi Mai Martaba ba zai bar shi ba, and what's on his mind nowa ya ji labarin yarinyar duk da bashi da tabbacin ko zata yarda ta saurareshi ma.

Miƙewa yayi tsaye yana duba shaddar da ke jikinsa.

“I really need to do this, ko zan samu peace of mind”

Closet ɗinsa ya buɗe ya fiɗo wata kafirar shadda golden color, ya buɗe ɗayar wardrobe ya ɗauko hular ƙobe ya aje saman shaddar, sannan ya shiga Bathroom ya watsa ruwa.
Bayan ya tsane jikinsa da tawul ya shafa mai, sannan ya saka body spray, ya saka short da white singlet, sannan ya shafa wani turare, ya ɗauki shaddar ya saka.
Wani mai ya ɗauka ya shafa ma fuskarsa, sannan ɗora da turare. Ya ɗan soma jin babu daɗi lokacin daya tuna gidansu Lamido zai je, yasan he has zero reasons to hate Lamido, but he still hate him.

“Maybe he's bad person”

Ya faɗa yana murza wani turaren a wuyansa, kamin ya ɗauki hular ya saka a kansa. Agogon hannunsa ya kalla, yaga tara da kwata, hakan yasa shi ɗan hanzarin ɗaukar wayarsa ya fice.
Sadauki na ganinsa ya tashi, sai Abdool ya ɗaga masa hannu.

“Ni kaɗai zan je”

“Allah ya tsare ya kiyaye hanya, Allah ya kare ka daga dukan ni abun ƙi, Allah yaja kwanan ka”

Abdool be kula shi ba, balle ya amsa addu'ar da yake masa, sai da ya kawo gurin motocin da suke harabar gidan sannan ya ƙwalama Sadauki kira, sai ga shi ya fito da sauri.

“Key wacan motar na ke so”

Ya nuna masa wata baƙar mota mai baƙin gilashi, wanda ke aje can gefe. Da Sauri Sadauki ya koma ciki ya ɗauko masa key ɗin motar ya miƙa masa, sai da ya sake duba agogon hannunsa sannan ya nufi motar ya shiga, gabansa sai faɗuwa yake.

Sai da ya hau titi, sannan ya ciro wayarsa ya dannawa Ummi kira. Sai da yayi mata one missed call sannan a na biyu ta ɗauka.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikissalam. Ummi ki min addu'ah zanje wani guri neman abu a yanzu, kuma babu tabbas zan yi nasara, idan kuma har na ƙyale abun hankali ba zai kwanta ba”

“Abdool mi zaka aikata? Thought baka aiki yanzu ka ce sun baka hutu?”

“Eh ba aikin office ba ne, wannan aikin nawa ne na sa kai”

“Abdallah karka aikata abunda zai sa rayuwarka cikin haɗari, ka dawo gida gobe”

“O my god”

Ya dafa kansa.

“Allah Ummi ba wani abun ba ne, kawai i need your prayers”

“Ka dawo gida gobe na faɗa maka, kasan dai kullum rayuwarka tana cikin haɗari ko? Karka kuskura ka wuce gobe, umarni na ke baka”

Ta kashe wayarta cike da fushi, dan ta san idan ba haka ta masa ba, ba zai ji ba, gashi duk ya tsorata ta, da wannan maganar na shi daman ita ba son take yana tafiya nesa da ita ba.
Iskar bakinsa ya busar yana cigaba da tuƙinsa a hankali.

“Daga neman sa'ah sai kuma abu ya zama ɗan zane, ban san salon da ya kai ni faɗa mata ba, Allah ka taimake ni”

Unguwar bata da kyau sosai, amman haka ya riƙa kunno kai cikinta yana kallon ƙananan gidajen da suke unguwar har ya isa bakin ƙofar gidan. Wani tunanin ne ya zo masa, sai kawai ya ƙara gaban da gida sannan ya faka motar, ya buɗe ya fito.

Ya samu minti salati tsaye a gurin sannan ya kira wani almajiri da ke bara ya nuna masa gidan su Lamido.

“Je can gidan ka ce ana sallama da baƙuwa”

Sai da almajirin ya kama hanya, sai kuma Abdool ya kira shi ya dawo.

“Ba haka zaka ce ba, ka ce Abdallahi daga Katsina ya na sallama da Namra, Namra ko? Yes Namra zaka ce”

“To”

Almajirin ya nufi gidan da sauri. Faɗuwan gabansa ya ƙaru lokacin daya fara tunanin irin amsar da almajirin zai dawo masa da ita.

NAMRA POV.

Ba laifi yau ta dan sake bisa da jiya, ko dan yau sun ɗan tausasa ta ne kuma ta wuni a tsakar gidan ansha fira da ita. Sai dai bata janye maganar tafiyarta ba, ta yarda ta bari har sai nan gaba, idan ta ƙara jin sauƙi abubuwa sun ɗan dai-dai.

Yau ba iya Maltina da madara kawai Lamido ya bada aka siyo mata ba, har da gasasshen nama, sai dai bata ci ba kasancewar komai bata jindaɗinsa a yanzu.
Sai da aka yi sallama magariba sannan ya bada aka siyo mata tea, yadda yake damuwa ta ci abinci shi kansa be damu da ya ci abincin ba, sam mantawa yake da nasa ciwon wata ƙila ko dan be jimu sosai ba, yake dauriya irin ta maza, ko kuma dan hankalinsa ya ɗauko gurin Namra ne. Shi kansa yana mamakin yadda yake damuwa da Namra, sai dai yana fi karkata hakan da tausayinta da yake, su kansu su Neina suna kula da halin kuwalar da Lamido yake bawa Namra, duk da sun san halinsa na karancin amman wannan kamar yana ƙoƙarin wuce guri, dan ko magana ake Namra ta saka baki zasu ga ya tattara hankalinta ya miƙa mata ya natsu sosai yana saurarenta.

Yau Neina taja Namra da fira sosai musamman bayan Sallah isha'in nan, abinci na fula take labarta masa da kuma al'adansu na fulani, a nan take taɓo labarin Baban su Lamido da kuma ƙuruciyar Lamido, dariya sosai Namra take idan ana faɗin labarin halin ƙiriniyar da Lamido ya yi. Shi kam iya karsa murmushi idan Neina ta faɗi wani abun.

“Salamu alaikum, wai Abdullahi daga Katsina ya ce yana kiran Namra”

Dam dam dam, gabanta ya tsinke ya faɗi, duk wani farinciki da yake zuciyarta sai ya ta neme shi ta rasa, a take murmushin fuskarta ya disashe. Da sauri ta kalli almajirin dake tsaye can jikin ƙofar gidan yana jiran amsa.
Bata san ko waye ba, amman jikinta ya bata wani yanayi na daban, ga shi kuma anxe daga Katsina, kuma an faɗi sunanta, lallai ko wanene ya santa. Sai dai ya akayi ya san inda take zaune? Miyasa be zo da rana ba sai da dare? Shin waye Abdallah ma? Ko dai Asim ne ya canja suna? Amman taya Asim zai san inda take?

“Ko mijin ki ne?”

Tambayar da Lamido yayi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Kai ta girgiza.

“A'a ba haka ne sunansa ba”

“Ɗan'uwan ki ne?”

Shiru ta yi tana tunanin irin amsar da zata bashi, idan har ta ce ɗan'uwanta ne zata sanu damar fita ta ga ko waye ne, to idan kuma ya kasance Asim ne ya canja suna fa?
Idan ma shi ɗin ne ai babu yadda zai yi da ni, dan yanzu babu aurensa a kai na, idan kuma har aurensa ya zo maidawa to yayi satti, dan na cika idda tun da na yi ɓari!

“Eh ɗan uwana ne”

Sai a sannan hankalinsu ya ɗan kwanta, Neiɓa ta ce da almajirin.

“Je ka ce tana zuwa”

Sai da almajirin ya juya sannan ta kalli Namra ta ce.

“Ɗauki fitila ki je”

Miƙewa tayi tsaye sai Lamido ya ce.

“Ya aka yi ya san gidan nan?”

“Ni na kwatanta masa, a waya”

Kai tsaye ta bashi amsar ta nufi fitilar ta ɗauka ta nufi ƙofar fita gabanta sai faɗuwa yake. Sam Lamido be so ta fita ba, haka kawai ya samu kansa da rashin jindaɗin kiran da aka mata duk da be san me kiran ba. Neina kuma ta kawo wani zargi a ranta, dan tana ganin kamar Namra ta ɓoye musu wani abu ne.

Zuciyarta cike da tsoro ta fita daga gidan, da tunani biyu, Asim ne ko kuma wani nasa yake mata sallamar. Bata ga kowa a ƙofar gidan ba, hakan yasa ta ɗan ɗaga fitilar tana yade, hangota da ya yi yasa ya tako ya ƙaraso kusa da ita.

“Assalamu alaikum”

Ya furta nata cikin murya mai taushi, da sanyaya zuciyar mai sauraro.

“Amin wa'alaikassalam”

Ta amsa masa ba tare data wayence shi ba. Ya ɗan yi gyaran murya.

“Na san baki gane ni ba”

Ya fido wayarsa ya kunna fitar wayar ya haska fuskarsa. Wannan karon ba faɗuwar gaba kawai Namra ta ji ba, har da tsoro, ja tayi da baya yana nuna shi da yatsa, sai maganar ta naƙale ta ki fitowa.

“Nasan zaki yi mamakin gani na, amman ina son ki ba ni aron lokacin ki kuma ki saurari abunda zan faɗa miki”

“Ba kai ba ne ɗan sarki daya kaɗe Lamido?”

“Ni ne, kuma na san ba a nan kika san ni ba, a Katsina ko?”

Kai ta ɗaga masa duk da bata da tabbacin zai ga hakan kasancewar akwai duhu a gurin.

“Miyasa kake bibiyata?”

“Ba saboda ke na zo garin Kaduna ba, ke ma kuma ina da tabbacin ba dan ni kika zo ba, amman zuciyata ta kasa natsuwa da hakan, direba ne ya kaɗe yaron gidan sai kuma na gan ki a gidan shine abun yake bani mamaki, bayan nasan a Katsina na san ki”

“Ba wasu kalamai na ce ka min ba, amman bari na gargaɗe ka, karka sake zuwa ƙofar gidan nan da sunan gurina ka zo”

Ɗan murmushin takaici da mamaki yayi.

“Babu mace da ta taɓa ɗaga hannu ta mare ni sai ke, babu mace da nake gani na bibiya sai ke, babu mace da ta taɓa faɗa min irin wannan maganar sai ke. Zan bar ƙofar gidan nan amman ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah kina da aure? Kuma ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah waye Mahaifinki, kuma miye alaƙarki da mutanen gidan nan?”

Wani haushi ne ya cika mata zuciya, har take jin kamar ba zata iya amsa masa tambayoyinsa ba, amman Allah daya haɗa ta da shi ne take jin ba zata ɗaga daga gurin ba har sai ta ba amsa.

“Ba na da aure, kuma babu wata alaƙa tsakani na da mutanen gidan nan, sunan Mahaifina Manjo Usman Zamau”
Chapter 113 · 0% Book details