← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 173

Sashe 95

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Momy ta tsaya tunanin ta inda zata soma, dan tana jin faɗin kalamar kai tsaye.

“Safiya tace min ta ga ƙawarki Asma'u a... Hiv unit....”

Yadda kasan cida haka gaban Rashida ya riƙa faɗuwa, zuciyarta na zillo kamar ta fito, a take yawun bakinta ya tsarƙe ta har sai da ta soma tari. Tasan Momy ba Asmee take nufi ba, idan kuma har da gaske Asmee take nufi to Safiya ce ta faɗa, kuma taya Safiya zata ga Asmee ita ce ta gani.

“Safiya ce ta faɗa?”

Momy ta ɗaga mata kai tana hawaye.

“Ni ta ce ta gani ko?”

Nan ma kai Momy ta ɗaga mata.

“I tell not once not twice several times, naje nemanta ne a asibitin amman ta ƙi ta yarda gani take kamar ni ce naje a karan kai na...”

Maganar take tana nuna da gaske take, amman bata son kallon Momy. Kai Momy ta girgiza na tausayin ƴarta da kuma ganin wautarta akan abunda take ta ƙoƙarin ɓoyewa.

“What about the results?”

Da sauri ta kalli Momy, tana mamakin kalamanta. Kenan bincike suka mata lokacin da bata nan! Ita da tayi ma results ɗin mugun ɓoyo taya aka yi suka gani?
   Durƙushewa tayi a gurin ta fashe da kuka mai ƙarfin gaske. Momy bata san lokacin data ƙarasa gaban ƴarta ta rumgume suka soma kukan tare.

“Taya haka ya faru Rashida ta ya? Miyasa kika yi ƙoƙarin ɓoyewa?”

Cikin kuka Momy take tambayarta, tana jinjigata. Da sauri Rashida ta zame jikinta daga na Momy ta tashi da sauri ta shige ɗakinta ta kulle da maƙulli. Jinginawa tayi jikin ƙofar tana kuka, irin kuka mai sa kaji kamar ka cire ranka ka huta.

Momy ma kuka take sosai, dan yanzu ne ta ƙara tabbatar da zancen Safiya. Daman tun Safe Safiya ta shiga ɗakin Rashida tana mata bincike har Momy ta same ta a ciki, anan takr faɗawa Momy haɗuwarsu da Rashida a  asibiti. Da kuma maganin da abokan aikinta suke bawa ƙawarta Asmee, a wacan Asibitin ta su.

Babu irin bugun ƙofar da Momy bata yi ba, amman Rashida ta ƙi ta buɗe, kuma ta ƙi tayi magana, sai kuka take. Waya Momy ta ɗauka ta kira Dady ta faɗa masa, cikin ƴan'mintuna sai gashi ya dawo gida hankali a tashe, ɗan har gumi ke keto masa ta ko'ina.

Kai tsaye ɗakin Momy ya nufo, sai ya same ta itama tana kuka.

“Ya aka yi haka ta faru? Amman an tabbatar?”

Kallonsa Momy tayi idonta na zubar da ƙwalla.

“Safiya ce ta faɗa, nima ban yarda ba har dai yanzu dana nuna mata na ga takardun, bayan kuma ban gansu ba nace ne kawai dan na gano gaskiyarta, kuma the way she act ya nuna tana da shi”

Jiki a sanyaye Dady ya zauna idonsa sun rine sun yi wani ja sosai, irin na ɓacin rai da damuwa sun sauka ga mutum.  Can kuma ya sauke ajiyar zuciya yana ta nazarin inda Rashida zata samo hiv da tsakar rana.

“Amman ƙara dai a bincika, ba lallai ba ne tana ɗauke da ciwon to ina ma zata kwaso wannan ciwon?”

“Hilal mana, ai shi kaɗai ne mutunen da take taraiya da shi”

Cewar Momy tana kuka, zuciyarta na ayyana mata shi ɗin ne tun da shine kaɗai mijin Rashida. Da sauri Dady ya kalleta

“Wallahi idan kuwa shi ne ya saka mata shi, sai na ɗaure shi gidan yari har ƙarshen rayuwarsa, marar mutumci marar taddako wanda be san halin girma ba, Allah ya usar mana, wallahi ya cuce mu, shiyasa ya sako ta. Ina Rashida take ne?”

“Tsna ɗakinta, ta ƙi ts buɗe tun ɗazu sai kuka take, ta ƙi tayi magana ma”

Tashi yayi yana cire ƴar saman suit ɗinsa, yana sassauta necktie ɗinsa, ya nufi ɗakinta jikinsa har rawa yake kamar mazari.

Sai da ya soma kiran sunanta, jin bata amsa ba yasa ya soma ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

“Rashida ni ne buɗe mana... Ba wani abun za mu miki ba kawai magana za mu yi, kuma ba zamu faɗawa kowa ba”

Tana jinsa amman ta kasa amsa masa dan bata da abinda zata faɗa masa, tasani matuƙar suka gano gaskiyar dalilin cutar nata ba zasu zauna da ita ba, who else kuma zai zauna da ita bayan iyayenta, lallai ko a haka rayuwa ta tsaya mata ta san ta kai karshenta.

Babu irin maganar da Dady be mata na rarrashi da tausasa zuciya ba, amman ta ƙi ta amsa masa balle ma har ta buɗe ƙofar.
Dawowa yayi ɗakin Momy ya tsaya daga jikin ƙofa fuskarsa da damuwa ya ce

“Ko dai za mu kira shi ne mu tambaye shi?”

“Idan shine taya zai amsa cewar shi ne? Zai yi ƙoƙarin kare kansa ne, kuma kasan babu wanda Rashida take mu'amala da shi sai Hilal dan shin mijinta kuma ni ƴata ba ƴar iska ba ce, ta bakinta ya kamata aji komai”

“Ta ƙi tayi magana, ɗakin ma ta ƙi ta buɗe”

“Zata yi magana, dole zata buɗe kabarta hankalinta ya kwanta kawai, ka koma gurin aikin ka”

“Ba zan iya wani aiki ba ko naje, jikina ya riga da ya mutu, Wallahi Hilal ya cuce mu, amman miyasa Rashida ta yi ƙoƙarin ɓoye irin wannan babban al'amari?”

“Allah kaɗai ya sani, amman rufawa irin wannan mutumen asiri ai ba abun yi ba ne, wallahi sai na sashi yayi nadama sai ya ƙwammace kiɗa da karatu”

A bakin ƙofar Dady ya zauna irin zaman nan na baka san ka yi ba, hankalinsa baya jikinsa, natsuwarta ta gudu ta barsa.

*NAMRA POV.*

Maganganun Asim sun tsaya mata a zuciya, duk bayan dogon numfashinta sai kalmar rabuwa da yayi mata ya maimata kanta a kunnenta. Da zancen ta kwana a ranta, tana mamakin Asim, yadda yayi tsaye yana faɗa mata magangu kamar wani ɗan shaye-shaye. Bw ɗauke a matarsa ta sunna ba be riƙe ta da muhimmaci ba, shiyasa har ya zaɓi aikin da yake sama da ita, yanzu kuma yake neman rayuwa da ita saboda tana da ciki.  Sai yanzu take nadamar rashin bin Anty, dan tasan babu makawa Asim rabuwa zai yi da ita, matuƙar bata zubar da cikin ba, dan ta ga gaskiyar maganarsa a idonsa, sai dai ita kuma bata jin zata iya zubar da cikin ko da kuwa shege ne balle na Sunna.

Sai dai idan Asim ya sake ta ina zata je? Ta koma gida da ciki  ta faɗawa Abbah Asim ya sake ta? Ta bi sawon Anty bayan ta nemi taje gidan ta ƙi yarda sai yanzu da Asim ya sake ta kuma take ɗauke da cikinsa.?
  Tashi ta yi zaune, sai ta nemi kuka da take ta rasa, washe ƙaramin abun ake yi ma kuka, tashin hankalin dake tare da ita baya barin hawayenta zuba.

“Kaico na ni Namra, Ina zan sa kai na sanyi? Ina zan sa rayuwar na samu sassauci? Haƙiƙa wanda duk ya so abinda iyaye suka ƙi yayi hasara, da nasan haka aurena da Asim zai kasance da ban aure shi ba, Allah ka yi min gata Allah”

Hannayenta ta ɗaga sama, tana roƙon Ubanjiginta, zuciyarta cike da yaƙinin lallai Allah zai ƙarɓa mata.

“Ya Allah ka tsare min mutunci na, ka tsare min lafiyata,
Allah ka yi min gata ka tsare min imani na da hankalina,
Allah ka yi min sutura ka kwantar min da hankali
Allah ka kyautata min rayuwa ta, Allah idan aure da Asim Alheri ne Allah ka tabbatar da shi, idan rabuwa da shi ne samuwar jindaɗina Allah ka zaɓa min abunda yafi zama Alheri a gare ni,
Allah ka shirya tsakani na da iyaye na, Allag ka gafarta min kurakurai na
Allah ka tabbarda duga duga-dugaina akan addinin ka”

Bayan ta shafa ta koma ta kwanta, ta kai hannu ta shafa cikinta, tana mai jin tsantsan ƙaunar abinda yake kwance a mararta.

*ABDOOL POV.*

Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana jirginsa max air ya sauka a tashar sauka da kuma tashin jirage da ke katsina.
   Be sanar da Ummi zuwansa ba, dan haka be tsamaci ta tarbe shi ba, ko ta aiko da motar da zata ɗauke shi. Sai dai hakan be a aiko masa da motar da zata ɗauki daga headquarter ba dan sun san da zuwansa. 

A yadda suka tarbi shi ya burge kowa a gurin, mota uku suka faka. Already sun buɗe motar suna hangosa tafe sai suka duk suka fito wajen motar suka tsaya, a jikin kayan gida yake amman hakan be hana dukansu su tsara masa ba, babu wanda yayi motsi a cikin su har sai da ya shiga motar sannan suka rufe masa suka shiga.

“Gurin Mai Martaba zamu je”

Yanda yayi maganar ba ka ce shi ne ba, dan hankalinsa gaba ɗaya yana kan wayarsa sai faman duba shafukan yana gizo yake dan sanin abinda ƙasa take ciki.
   Har aka isa Ahmad Mai-doki road, Abdool be ɗago ya kalli mai driving ɗinsa ba, balle ti-ti. Yana jin motar ta tsaya ya buɗe ya fito ƙamshin gidan ne yasa shi murmushi, dan ƙanshim gidansu daban yake, ko'ina ya ke zai iya gane ƙanshin gidan Mai-martaba.
Chapter 95 · 0% Book details