← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 173

Sashe 1

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zago-asa01.html

BISMILAHI RAHAMANIN RAHIM

*GABATARWA*
Wani ɓangare na labarin nan ya faru ɗa gaske, sai dai an ƙara da wasu abubuwan dan ilmantarwa da nishaɗi. Labarin na iyalai uku three family.

NAMRA FAMILY.
DR. HILAL FAMILY.
KALSOOM FAMILY.

Sunan Novel ɗin *ZAGON ƘASA*
Green snake under green grass, people with two colors. A tension, Schemed Novel of slut.
Witness to regret.
Witness to love.
Witness to tears.
Witness to drunken.
Witness to revenge

*MEANING OF THE NAMES*
NAMRA - Delicious water
UZAIR - Name of a prophet
HILAL - Crescent
KALSOOM - Name of Prophet Muhammad (pbuh) daughter
EZZAH - A person who give the honor, respect
RASHIDA - Intelligent sober
IFHAN - Respectful, nice, precious
RAFEEK - Friend
YASMEEN - Flower
ABDULLAHI - Servant of Allah
ASIM - Person who keep away from sins.

*SADAUKARWA*
Na sadaukarda wannan littafin ga (Daughter) RASHIDA ABDULLAHI KARDAM kin cancanci fiye da haka a gareni

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandycom.ng for your updated.

FIRST FAMILY...

*1.......* Ƙarfe biyar da minti arba'in da takwas na yamma, ta faka Motarta a parking space, ajiyar zuciya ta sauke ya fi sau uku, sannan ta kalli takardun da ke gefenta kamar mai tunani, daga bisani ta kai hannu ta ɗauka, ta buɗe motar ta fito.
Jiki a sanyaye ta nufi harabar gidan, gurin da Mahaifinta yake zaune yana shan iska, daman a al'adarsa ya kan zauna a habarar gidan da yamma, wani sa'in ya kan duba jaridu wani lokacin kuma ya leƙa yanar gizo, dan sanin me duniya take ciki.
Da kamar fargaba Namra ta doshi gurin da yake, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama.

talkamin ƙafarta ta fara cirewa tun kamin ta ƙasara kusa da carpet ɗin da aka saba shimfaɗa masa, sallama ce ta fito bakinta kanta na ƙasa kamar mai jin nauyin kallonsa.

“Assalamu Alaikum”

Bai amsa sallamar ba, sai dai ko kaɗan hakan bai bata mamaki ba, daman bata tsammaci zai amsa mata ba, sai kawai ta ɗora da gaisuwa.

“Abban sannu da hutawa ya aikin?”

Ya yi jinkirin amsa mata na daƙiƙon da zai kai ashiri zuwa ashirin da biyar, sannan ya amsa mata can ƙasan maƙoshinsa

“Al-hamdulillah”

Bata yarda wata kalmar ta ƙara fito daga bakinta ba, sai kawai ta tashi jiki ba ƙwari ta saka takalminta, ta nufi hanyar da zata sadata da part ɗin Mahaifiyarta.
Sai da ta share hawayen da suka zubo mata kamin ta kai hannu ta murɗa ƙofar falon ta shiga. Babu kowa a parlor sai air conditioner dake ta aikinsa, Kai tsaye ɗakinta ta wuce zuciyarta cike da rauni.
Saman gadonta ta zauna ta lumshe ido tana sauraren bugun zuciyarta, kalaman da Mahaifinta ya yi mata ɗazu da safe suƙa riƙa dawo mata, irin yadda ya riƙa aibanta ta, yasa ta ta yi saurin dafe kanta, sai kuma ta fashe da kuka tana murza zoben dake hannunta.

Haka ta zauna a ɗakin bata fito ba har sai da aka yi sallah Magariba, bayan ta yi sallar ta fito ta nufo parlor fuskarta babu yabo babu fallasa.
Duk ƙannenta suna zaune parlor suna kallon Dadin kowa, babu wanda ya lura da fitowarta sai Mahaifiyarta. can nesa da Mahaifiyarta ta zauna tana gaisheta.

“Anty barka da dare”

Bata amsa mata ba, sai kallonta take tana karantar irin halin da ƴarta take ciki.

“Tunda kika dawo daga makaranta Namra kina cikin ɗakin, so kike yi damuwa ta yi miki yawa ko? Yau ranar girkina ce amman saboda ke Abbanku bai leƙo nan ba, na shiga sashensa na rasa gane kansa, so kike ki kashe min aure ko Namra? kin fi son ki rayu da son zuciyarki fiye da farincikin iyayenki? bana ƙin zaɓin ki Namra, amman tun da mahaifinki ba ya so barin shi ya fi alheri”

Matsewa ta yi cikin kujerar tana wani irin kuka da ba zata iya fitarwa ba.
Sai yaushe Abbah ta zai fahimci halin da take ciki ne, sai yaushe zai tausayawa rayuwarta? ji take idan har ta yarda ta rabu da Asim zata iya mutuwa, bata jin zata iya rayuwa da wani Namji da ba Asim ba, kuma idan har bata aureshi ba, ta san Allah ba zai yafe mata ba, mutane zasu masa dariya, daman an daɗe ana masa kirarin ita ɗin ba sa'arsa bace, ta san irin son da Asim yake mata, ta ya zata iya sanar da shi ba zata aurensa ba? Yayyu ta Mata da Maza Tara Mahaifinta ya aurar, duk kuma a cikinsu babu wanda ya yi ma zaɓin miji ko matar aure sai ita.

Sallamar Barrister Yasmin da Mijinta ne, ya ankarar da ita ta yi saurin share hawayenta, tana gyara fuskarta dan kar su gane ta yi kuka.
Anty Amarya ce ta amsa musu fuska a sake kamar yadda ta saba tarbonsu.

“Maraba maraba da Lauyoyi, cikin daren nan ake tafe”

Yasmin ta zauna a kujerar da Anty Amarya take zaune, yayin da Uzair ya zauna a kujerar da ke kusa da ƙofa, idonsa na kan Namra wace ta banye ɗaurin ɗankwalinta tana ƙoƙarin magana da matarsa.

“Anty Barrister ina Afnan?”

“Yanzu na biyo uban daren nan na miƙe hanya ki rasa wanda zaki tambaya sai Afnan? amman yarinyar nan akwai ki da rainin hamkali”

Kusa da ita Namra ta dawo ta zauna tana faɗin

“Kaji Anty da wata magana, toh ai ita ce Ƴata dan haka ni ita zan tambaya”

“Idan kina son ganinta kawai ki je gidan Gwaggo ki ganta, amman indai tambaya zaki yi, ki riƙa cewa ya na ke ni da Mijina”

“O'oh masu miji manya, toh ni ban ga mijin na ki ba ai”

“Ni ai na ganki”

Uzair ya amsa daga inda yake zaune yana kallon ƙugunta zuwa saman ƙirjinta.

“Jar uban nan, ka ji min wata magana! saboda ke fa muka biyo ta nan amman zaki wani ce baki ganshi ba”

Duk suka sa dariya Maryam ta ce

“Toh mijin na ki ai tsoron mutane yake shiyasa ya maƙure gurin kamar wani ɗan fashi”

Anty Amarya ta kai mata dudu

“Wai dan kun ga baya magana shiyasa kuka raina shi ko?”

Dariyar suka sake yi, sannan Anty Amarya ta shiga tambayar Barrister ya aiki. Namra kuma ta nufi hanyar kitchen dan ta ɗauko musu ruwa, tun da ta tashi Uzair ya bi bayanta da kallo har ta shige kitchen ɗin.

Bayan sun sha ruwan ne Barrister ta ce

“Anty Mun zo aron Namra ne, Uzair zai yi ɓaƙi daga Abunja,kuma yana son ayi musu wainar kaza kinsan Namra ce ta iya shiyasa muka zo mu faɗa miki”

“Aa ni ba ruwana ga ku ga Namra”

Cewar Anty Amarya tana kallon Namra da ta ɗan ɓata fuska kaɗan, dan sam yanzu bata son zuwa gidan Yasmin, Hakan kuma ya samo asali ne tun lokacin da Uzair ya soma nuna mata maitarsa a fili.

“Kai gaskiya na so nayi tilawar haddata, dan Saturday nan ne walimar mu fa”

Yasmin ta ɗan zungureta

“Ke uwar kuiya, just for one day ne fa zaki mana, ai yau Wednesday, zaki iya yi Friday”

“Haba kije mana idan kin gama musu da wuri ma ai zaki iya dawowa”

Anty Amarya tasa baki. Yasmin ta ce

“Kuma ni kin ga fita zan yi ba gida zan wuni ba, ina da cases har huɗu ƙila sai yamma zan dawo balle ki ce zan dame ki da surutu, Uzair kuma sai biyar yake dawowa, ke kaɗai ma za'a bari a gidan”

Ta amince ba dan ta so ba, sai dan babu yadda zata yi, indan har ta ce ba zata je ba, Yasmin zata zargeta, Anty Amarya kuma zata mata faɗa, sa'arta ɗaya gobe ba su da lacca.
ba su wani daɗe sosai ba, suka yi ma Anty Amarya sallama suka fice. Har gurin Mota Namra ta rakasu, Yasmin na laƙame da kafaɗarta tana mata tambihi game da haƙuri, dan ta fi ƙowa sanin halin da Namra take ciki, kasancewar shaƙuwarsu, Namra bata ɓoye mata ƙomai.

Bayan sun wuce ne ta dawo jiki a sanyaye ta shigo parlor.

“Ni wallahi bana son zuwa gidan Anty Yasmin”

Ta faɗa tana ƙoƙarin zaunawa saman kujera. Maryam ta kalleta ta ce

“Saboda me?”

Kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru ta kalli tv.

“Tashi kije ki ci abinci”

“Bana jin yunwa”

“Ai gaki nan, duk kin bi ki koɗe sai fama kike da rama kamar wata marar lafiya”

“Wallahi Allah bana jin yunwa Anty”

“Ta ya zaki ji yunwa kin ɗauki damuwa kin sawa ranki, Allah ya sauwaƙe miki wannan rayuwa”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, dan ta dan duk yadda zata yi ma mahaifiyarta bayani, ba ganewa zata yi ba.
Annur ne ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa hannunsa riƙe da lemu ya ce

“AntyAmarya wai Abbah ya ce ki zo tare da Anty Namra”

Gabamsu ya faɗi dukansu, bama kamar Namra data ja wani dogon numfashi ta sauke, kamin ta kalli Mahaifiyarta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka tashi suka nufi part ɗinsa, kishingiɗe suka tararda shi, kofin tea na gefensa yana sanye da madubi fuskarsa babu annuri yana duba wasu documents.
Namra ta zauna ƙasa cikin ladabi, Anty Amarya kuma ta zauna saman kujera tana faɗin

“Annur ya ce kana kiran mu!”

Bai ce uffan ba, har sai da ya ƙare duba takardun da yake sannan ya cire gilashin idonsa, ya kalli Namra babu alamun wasa a tare da shi ya ce

“Kin san Alhaji Madu Sanusi?”

“Eh”

Ta amsa ƙasa-ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa, aikan ta san Alhaji Madu akan farin sani, mutumen da kwana biyu, uku yana gidansu, aminin mahaifinta.

“Shekaran jiya ya yi min magana akan ki, saboda yana son ƙara aure dan ki zame masa first lady tunda sauran matansa basa jin turanci, kuma a takarar da yake akwai buƙatar ya auri mace ƴar boko, mun gama magana da shi gobe da dare zai zo ku gaisa”

Tun da ya soma maganar hawaye ke zuba a idonta har ya ƙare, daker ta iya amsawa da

“Allah ya kai mu”
Chapter 1 · 0% Book details