← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 173

Sashe 115

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“ I deserve happiness, Allah ka duba lamari na, Allah ka sassauata min wannan rayuwa, ka rufa min asiri, Allah ka juyo da hankalin mijina a gare ni, Allah na tuba ka yafe min”

Ta shafa addu'ar fuskarta shakaf da hawaye, tana jin tsantsar nadamar zinar data aikata da aure, tun da itace silar shigarta duk wannan halin da take ciki, ta rasa kowa nata saboda ciwon dake jikinta, idan ta tuna yadda Mahaifinta ya matsu ta bar gidan sai ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu.

KALSOOM POV.

“Anty Kalsoom, Daddy yana kiran ki, yana falon baƙi tare da Hilal da Abban Hilal”

Da sauri Kalsoom ta ɗago ta kalli Saleena dake tsaye riƙe da gambun ƙofarta tanaata magana. Gabanta ya faɗi sosai, a take ta aje jaridar dake hannunta ta ɗauki Hijabinta ta saka, ta ƙaraso kusa da ƙanwarta Saleena.

“Me kika ji suna tattaunawa?”

“Ban ji komai ba, amman dai har Momi tana can, kuma duka fuskokinsu ɗauke da farinciki”

Ajiƴar zuciya ta sauke sannan ta ratsa ta gefen Saleena ta nufi hanyar da zata sadata da falon Dady, zuciyarta cike da fargaba.
Cikin natsuwa ta shiga falon, bakinta ƙumshe da sallama, sai da ta fara gaishe da Abban su Hilal sannan ta zauna kusa da Momi kanta ƙasa.

“To ga mijin ki nan shi ba zaki gaishe shi ba?”

Cewar Dadyn Hilal yana murmushi, sai duk suka sa dariya har Hilal ɗin da zuciyarsa ke cike da farinciki. Dady ya kiran sunan Kalsoom a natse, ta yadda zata maida hankali ga abunda zai faɗa mata.

“Kalsoom. Hilal ya mayarda sauran igiyoyin aurensa da ke tsakaninku, kuma yace yana da buƙatar ki koma ɗakin ki”

Samun kanta ta yi da kasa furta ko da kalma ɗaya, wani abu ta ji yana ratsa zuciyarta shi ba farinciki ba, ba kuma ɗan 'uwansa ba, wato baƙinciki. Su kuma duk natsu suna son su ji abunda zata ce, ganin hakan yasa Abban Hilal magana.

“Ai ba zata iya cewa komai ba, kasan ita mace ce, kuma ko ba komai suna son junansu. Kawai shiga tsakani ne irin na mata, kai kuma ka biye musu ka zama macen”

Dadyn Kalsoom ya ƙyalƙyale da dariya.

“Matan ne ai sai a hankali, ni na so ta zauna har sai yayi auren ne, tukuna ta koma, zamanta a can a yanzu zai ƙara saka tsanarta a zuciyar Hajiya ne kawai”

“A a ƙara ta koma ɗakinta, aure kuma ban hana yayi ba, kin dai shirya zama da kishiya ko?”

Ya ƙarasa yana kallon Kalsoom wacce ta noƙe kai tana mai jin kunya.

“Tashi ki ɗauko kayan ki muje”

Sai a lokacin Momi ta saka baki

“Tun yanzu ai da an bari har gobe sai ƙanwarta da Ƙawarta ta raka ta”

“A'a nima ai na isa na rakata, tashi ki ɗauko kayan ki”

Kasa tashi Kalsoom ta yi har sai da Momi ta zo ta riƙa ta suka bar falon tare. Daddy Hilal ya kalli Daddyn Kalsoom yana faɗin

“Wato abun ne da ɗaure kai, kasan kuma zuciya wani lokacin bata da ƙashi, ni kai na abun ya ɗan ɗaure min kai da farko, amman ganin soyayyar dake tsakanin dole a ɗaga musu ƙafa, kuma koma minene shi uban ɗa be yarda ba, kai miye na ka a ciki har ka raba musu aure ƙaramar ƙwaƙwalce kawai ta mata”

Murmushi Dadyn Kalsoom ya yi ya girgiza kai

“Allah dai ya kyauta ya bayyana gaskiya”

Dukasu suka amsa da Amin har Hilal dake ƙoƙarin miƙewa tsaye.

YASMEEN POV.

A gajiye ta aje hakar hannunta ta karɓi Babynta daga hannun mai mata reno tana murmushi.

“Sorry Dear i'm back”

Uzair ya aika mata wani kallo mai cike da jin haushi.

“Ni fa wannan aikin na ki ya ishe ni, ace har kana jego ma sai kaje, yau kwana biyu da suna har kin fara fita”

Kallonsa ta yi fuskarta da annuri.

“Am sorry dear, daga yau ba zan sake fita ba sai next week”

Wani tsakin haushi yayi

“Ai kaji fa fitan ya fara kenan, ai ba aure lawyer ba, zamanta a gida ma aiki ne”

Dariya tayi tana gyara sunan da take ba ƴarta, tare da kallon Adnan dake wata tafiya a wahalce.

“Kai me ya same ka?”

Bude baki yayi zai yi magana sai Uzair ya karɓe.

“Da...”

“Ina jin Basir ne yake damunsa, ko kuma ya zauna wani abu ne, ɗazu ma na duba gurin ya masa ja sosai, i will take him to hospital”

Yana gama faɗar hakan ya miƙe tsaye ya riƙa hannu Adnan da sauri suka fice, ita kuma bata wani ɗauke abun serious ba, ta maida hankalinta gurin Mai mata reno.

“Me aka girka?”

“Wake aka yi, shi yace na girka ta daya ga Namra na ta kuka”

“Ayyah Namra na, i'm sorry ba zan sake fita ba dake ba, i love you”

Ta aikawa babyn kiss tana murmushi. Sannan ta tashi ta nufi ɗakinta tana cire ɗankwalin kanta, ɗayan hannunta kuma na ɗauke da new babynta Namra.

ASIM POV.

Be farka ba, sai bakwai da rabi, yana yin sallah asuba ya sake komawa baci,ba shi ya tashi ba sai sha ɗaya na safe, wayarsa dake kusa da shi ya ɗauka ya lalubo number Mardiya dan yau a bachinsa na safe ita yayi mafarki, be wani daɗe sosai yana waya da ita ba, ya miƙe ya shiga wanka.
Sha biyu saura ya shirya ya fita, kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya zuwa, tun kamin ya taso ya tanadi ƙarya da zai mata akan Namra, sai ya tarar bata gidan, mai gadi ya labarta masa tun jiya da dare ta bar gidan wai taje birnin kebi.

Ko kaɗan Asim be jidaɗin hakan da Hajiya tayi masa ba, sai ya zuciyarsa ta soma nuna masa ko dai Hajiya ta yi fushi da shi ne, shiyasa har taje Kebi bata faɗa masa ba, duk da ta faɗa masa zata bashi hutu saboda baƙi zata yi ai bata ce masa zata bar garin ba. Har ya ciro wayarsa ya kirata sai kuma wata zuciyarta ta hanasa, a ganinsa yanzu ba zata sauraresa ba tun da tana cikin fushi ƙara ya bari har sai an kwana biyu sannan ya kira ta, idan bata dawo ba.

Ƴar ƙara wayarsa ta yi, yana duba ya ga alert daga diamond bank saƙon miliyan biyar ya shiga asusun ajiyarsa.

“Wow”

Ya faɗa yana karanta sunan wanda ya aiko masa da kuɗin.

“Yayi Kyau Alhajina”

Ya faɗa cike da tsananin farinciki, kaminɓya ɗora da saƙon daya biyo baya.

“Na aiƙo maka da kuɗi, kazo gobe sokoto ina son ganinka, kuma ka zama mai riƙe sirri”

“Zan zo gobe tun da safe inshallah”

Haka ya mayar masa da amsa, sannan ya rumgume wayar a ƙirjinsa yana dariya har ta fitar hankali. Komawa yayi motarsa ya shiga, yana cigaba da dariya har da jijjiga jiki.

Yana yi ma motar ki kiran Nably ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗauka yana dariya.

“Hello my second wife”

“Au ba ma nice ta farko ba kenan?”

“Yes karki sa ma ranki zaki zauna ke kaɗai a gidan Asim”

“Ashe kai ba Saurayi ba ne?”

“Saurayi ne kuwa sabo hul, amman bayan ke wata zan ƙara, ko kuma ma akai ku ku biyu a tare”

“Kai da bakinka kake faɗin haka, lallai na yi fushi, na bar mata”

Da sauri ya haɗe hannayensa kamar tana gabansa.

“Sorry my nurul khalbi, wasa nake miki just to get your angry, yanzu dai ya hanya?”

“Au kasan da tafiya na, amman baka kira ka tambaye ni ba”

“i'm sorry dear i'm just kind of busy, In fatar kin sauka Lafiya”

“Na sauka ƙalau idona sai ƙaiƙayin ganinka suke yi ”

“Gani na kan hanya nan da mintuna talati”

“I can't wai to see you”

“The same here”

Yana aje wayar ya ƙara ma motarsa jiya ya nufi wani boutique, dan siyen kaya mai kyau da tsana wanda zai sa yaje gurin gimbiya Nabila.

ABDOOL POV.

Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi jirginsa ya sauka Katsina, yana sauka ya kira Ummi ya faɗa mata ya sauka, amman ta ƙi ɗaukar wayarsa, har sai da ya aika mata da saƙo, Sannan ta aiko masa da direba.
Daga filin jirgi zuwa gida tafiyar minti goma sha biyar ce, amman sai yaga ta yi masa tsayi kamar na awa ɗaya saboda zumuɗin da yake na bawa Ummi labarin dake cikin ransa.
Suna shiga harabar gidan farincikin fuskarsa ya ɗaɗa ƙaruwa, ko fakin ɗin kirki direban be yi Abdool ya buɗe ya fito, sai duk sojojin da suke gidan suka maƙe guri ɗaya suna sara masa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi Babbar ƙofar gidan.

Amira da Haleema na tsaye dinning suna jera abinci Abdool ya shigo da sallama.
Da gudu Amal taje ta rumgume shi.

“Dude i miss you”

“I miss you more”

Kaɗan kaɗan Amira take satar kallonsa tana murmushi, Haleema ma kallonta take tana murmushi dan tasan abunda yake zuciyarta. Fitowar Ummi ne ya ɗago da duka hankalinsu har Amira ta samu damar kallon Abdool da kyau tana auna irin missing ɗinsa da ta yi.

“Ka kuru da baka dawo yau ba ko”

Dariya yayi yana wasa da hannun Amal.

“Ummi ina da labari mai daɗi da zan ba ki, duk da kin katse min uzuri na”

Zaunawa tayi saman kujera tana murmushi.
Sai shi ma ya zauna yana tambayar Amal abunda ya hana ta zuwa makaranta. Lemu Amira ta ɗauko ta kawo masa a gabansa ta dire masa, tana masa sannu da zuwa.

“Yauwa Thank you so much”

Ta jidaɗin kalma nan da yayi mata, bama kamar murmushin da ta gani shimfiɗe a fuskarsa. Cikin natsuwa ta tashi ta nufi dinning dan zuba masa abinci.

Kallon Ummi yayi fuskarsa ɗauke da abunda ke zuciyarsa.

“Ummi kin yi suruka, matar da na taɓa baki labari ina so na samo ta, finally mafarki na zai zama gaskiya...”

Tartsatsa... Suka ji ƙarar fashewar plate mai ɗauke da abinci, wanda Amira ta sake saboda maganarsa da ta soki gadon bayanta, da sauri ta ɗuka tana kwashewa, kamar wacce ta ruɗe, a take hawaye ya fara bin fuskarta, sai dai su basu gani ba kasancewar ta basu bayana ne.

“Ba ki ji ciwo ba?”
Chapter 115 · 0% Book details