← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 173

Sashe 76

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasss ya watsa wanke mata fuska da mari, ya hau shurinta sai kaurar fuskarta yake yana faɗin.

“Duk iskancin ki ya tsaya a kan ki, karki kuskura saka uwata a cikin sheɗancin ki, dan ba warin ki ba ce”

Kuka take yi sosai tana rufe idonta da ta ke jin kamar ƙasa ta watsar mata a cikin. Be kula irin aika-aikar da yayi ba yasa ƙafa ya fice.
Haka ya wuni a ɗakin tana aikin kuka kamar ta cire idonta, sai da aka kira salla azahar sannan ta samu kukan ya tsaraita mata har ta unƙura ta tashi.

Wanka tayi tare da alwala sannan ta saka wasu tufafin tayi salla. Sai ta ɗauko qur'ane tana karatu.
Guraren uku da kwata wayarta tayi ringing ita har ta manta da sha'anin wayar sai yanzu. Bata kula wayar ba sai data ta kai ƙarshen suratul Yasin, sannan ta rufe qur'anen ta yi addu'ah daga bisani ta maida alƙur'anen mazauninsa, sannan ta nufi wayar ta duba.

Number Anty Yasmin ce. Ta yi mamakin ganin kiran Yasmin har four miss calls, ta manta when ma Yasmin ta kirata tun suna shiri. Bata da kuɗin da zasu isheta magana amman tasan ba zata rasa na flashing ba.
Kamin ta kira sai ga Yasmin ta ƙara kira. Namra tayi saurin picking ta kara a kunne.

“Assalamu alaikum Anty”

“Na'am My Sis ykk”

“Lafiya ƙalau, ya Gwaggo”

“Tana can gida, ni na zo katsina seminar ne, tun shekaran jiya yau zan koma, kuma bana son na wuce ban gan ki ba”

Gaban Namra ya faɗi bata ƙaunar wani yace zai kawo mata ziyara a yanzu, sai dai bata jin zata iya hana Yasmin zuwa gidanta tun da har ta nuna son zuwa.

“Ayyah Anty Yasmin yanzu za ki zo?”

“Eh anjima kaɗan zamu koma”

“Okay ki ce a kawo ki Nasarawa, idan an kawo ki sai ki shiga ta cikin unguwar zaki ga gidan daya ƙone sai ki shigo nan”

“Okay gani nan zuwa yanzu”

Ta kashe wayar. Namra ta juya tana kallon ɗakinta, to be frank bata son kowa ya san halin da take ciki, sai dai babu yadda ta iya.
Kimtsa ɗakin ta shiga yi dan yau duk batayi shara ba tun da wuni tayi kukan dukan da Asim yayi mata.
Wajen gidan ma ta gyara bakin inda zata iya dan baɗin gidan ba mutum ɗaya ne zai iya share shi duka ba, yaro ta aika da kuɗi aka siyo ma Yasmin gala da ruwan sanye ta aje mata. Sannan ya canja tufafin jikinta ta saka masu ɗan kyau ta zauna zaman jiran isowar Yasmin.

Tana jin an turo ƙofar gate ɗin gidan gabanta ya yi mugun faɗuwa. Cikin ƙarfin hali ta taso ta doso gate ɗin gun da Yasmin take tana doka sallama da kallon gidan tana mamaki.
Rumgume ta Namra ta yi tana nuna murnar ganinta. Ita ma baki har kunne, ta ke ɗokin ganinta.

“Namra ke ce? Duk kin canja”

“Ni ce Anty”

“Duk kin canja kin, kin yi baƙi Namra kin lalace”

“Bana jindaɗi ne kwana biyu, mu shiga ciki”

Cike da ƙyaƙyami Yasmin ta zauna dan ita duk gidan be mata ba, mamaki ma take yadda Namra take zaune gidan.
Namra ta dire mata gala da ta siyo mata ta aje mata tare da ruwan sanyi

“Ban yi girki ba yau shine na siyo miki gala”

“My Sis meya samu fuskarki?”

Ta tambaya ganin fuskar duk ya kumbura. Namra tayi shiru bata ce mata komai ba.

“Haka kike wannan rayuwa Namra? Dube ki dubi gidan da kika zaune, yaushe kuka yi gobara?”

“Tun Asim na asibiti an kwana biyu, abubuwan ne suka sauya amman yanzu ai ya samu aiki komai zai walwale”

“To Allah yasa”

Sama sama suka yi fira, bata wani daɗe ba tayi ma Namra sallama ta ciro 20k ta bata. Har bakin gate Namra ta rakata, sai da ta shiga motar da ta kawo suka kama hanya sannan Namra ta koma cikin gida.

ASIM POV.

Cike da ɓacin rai ya fito gida, ya doshi gurin sana'arsa. Ko da ya isa ya tararda abokan aikinsa har sun buɗe shagon suna fitar da kayan aikin.
Haka ya samu guri gefe ya zauna sai fuci yake kamar sune suka masa wani abu. Har suka gama fitar da kayan aikin suka rura wuta suka zauna suka fara zuga. Yana can gefe yana tunanin rayuwarsa yadda zai yi ya rama abinda Namra da iyayenta suka masa.

Wayarsa ya ciro ya dannan number Hajiyar nan dan yayi saving ɗinta tun jiya. Ringing tayi sai da tana daf da katsewa sannan ta yi picking.

“Hajiya Ina wuni”

“Lafiya ƙalau who's this?”

“Asim ne Hajiya, wanda kika ba number ki jiya, kika ce za a miki gyaran gate”

“Oh that Handsome Guy ko? ”

Yayi dariya cike da jindaɗin lafazinya

“Hajiya, ɗan talakan nan dai”

“Ai ajinka ya wuce talaka, kawai dai ka riƙe sana'ar da bata dace da kai ba ne”

“Hajiya abin ne sai a hankali kin san nigeria tayi zafi”

“Ta yi zafi ga wanda be san kanta ba, amman wannan sana'ar ai bata dace da kai ba sam. Anyway yaushe zaka zo ka duba min gate ɗin ne?”

“Wai da yanzu zan ɗauko abokanin aikina sai mu zo mu gani”

“Eh amman kai ya kamata ka fara zuwa ka ga yadda aikin yake, sai ka ce su zo daga ba ya, ko kuma ka koma ka ɗauko su”

“To aikin yana da yawa ne”

“Ba wani yawa gefe ne kawai ya ɗan ɓalle”

“Okay to bari na zo yanzu na duba yadda aikin yake”

“Sai ka iso, number ka ne wannan?”

“Eh Number na ne Hajiya”

“Okay”

Ta kashe wayar. Shi kuma sai faman murmushi yake

“She's so friendly, bata wulaƙanta mutane duk da tana da arziki, ta hutawa kan ta”

Ya faɗa a fili sannan ya tashi yana kaɗe rigar ya nufi gurin aikin nasa, sai da ya sanar musu da aikin ya faɗa zai je ya duba ne sai ya dawo sannan ya tari ɗan a chaɓa ya hau.

Kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya nufa, be sha wahalar ganewa ba, saboda ta karanta address ɗin na ta tun farko.
House number 7 ya shiga, kai tsaye ya shiga gidan kamar wani wanda ta saba zuwa, sai wara ido yake yana ƙara kallon gida da kyau da kyau. Mai gadin ne ya tare shi yana tambayar inda zaije.
Kamin yayi ma mai gadin magana ya ciro wayarsa ya kira number ta.

“Hajiya ga ni na iso, mai gadin ki na ƙoƙarin hana ni shiga”

Sai kawai ya miƙa masa wayar. Mai gadin na karɓar wayar ya kara a kunne sai kawai ya ce

“To Hajiya”

Ya miƙawa Asim wayarsa, yana nuna masa inda zai shiga. Ka ɗa kai kawai yayi ya doshi gurin daya nuna masa yana tsaki, dan ya tsani mai gadi ya wulaƙantasa, shiyasa baya son zuwa gidan da za a tambayeshi inda zai je.

Manyan motoci ya gani a harabar gurin jere, ciki har da wacce taje da ita gurinsa jiya. Tsayawa yayi ya ƙwanƙwasa ƙofar har sai da aka masa ixinin shiga sannan ya tura ya shiga yana sallama kamar ba shi ba.

Da murmushi a fuskarta ta tarbeshi tana nuna masa kujera.

“Maraba da samari”

“Hajiya ina wuni”

“Wuni ko kwana? Ko ɗazu fa wuni kace min ko matar ka ta caja maka kai ne? Kasan matan yanxu sai a hankali, ko da yake baka yi kama da mai aure ba”

“Bana da mata gaskiya, sai dai zafin ƙasar nan”

Tayi dariya tare da nufar gurin freezer ta ɗauko masa lemu da kofi ta zuba masa.

“Ga lemu ka sha, na san dai ka karya ko a kawo masa breakfast?”

“A'a na gode”

Ya ɗauki lemun ya sha, yana kallon ƙaton tv ta na bango dake can ƙarshen ɗakin.
Kallonsa take sosai tana murmushi, tare da gyara doguwar rigar atmafa dake jikinta.

“Na ce ka duba gate ɗin in ya zo gobe sai ku zo ayi aikin, dan yau zan yi baƙuwa gaskiya”

“Okay to ba matsala, gate ɗin na bakin ƙofa ne?”

“Wh ka tambayi mai gadi zai nuna maka”

Ya aje lemun bayan ya shaye shi kaf sannan ya tashi.

“Yo bari naje na duba gobe kamar gaushe zan zo?”

“Da la'asar idan rana ya yi san yi”

Wani irin rausayarda ido take lokacin da take magana da shi tana wani langaɓarda jiki. Shi kuma yayi murmushi yana sa hannayensa aljihu.

“Tau ina zuwa”

Ta juya ta soma tafiya cikin wani irin karairaiya, ta nufi ɗakin. Bata wani daɗe ba ta fito riƙe da sabbin yan ɗari biyu biyu ta mika masa.

“Ga 10k ka hau a chaɓa, sai na gan ka goben”

Ya faɗa tana murmushi tare da shafo hannunsa a lokacin da zai karɓa ɗin.

“Haba Hajiya ayi haka?”

“Ba komai ai irin ku abun tausayawa ne masara aikin yi”

“Na gode Allah ya saka da alheri ya ƙara aixiki”

Ya fito daga falon baki har kunne. Sai da ya tambaya mai gadin ya gwada masa gurin da gyaran yake sannan ya wuce.

KALSOOM POV.

Yau da wuri ta sallami yara da Hilal kasancewar yau Monday ce ranar aiki. Sannan ta shiga gyara gidan, baya ta share ko ina tayi mopping sannan ymta shiga kitchen ta haɗa kayan wanke-wanke ta somawa wankewa tana sauraren ƙira'ar dake wayarta.

Tsin-tsin'tsin ta riƙa jin kamar ana tsokararta, sai tsikar jikinta ya fara tashi.

“A'uzubillahi minal shaɗanin rajin”

Ta furta tana girgiza kanta da take jin yayi mata nauyi. Tunawa tayi da bata da ɗankwali a kanta, sai ta yi saurin komawa falo ta ɗauki ɗankwalin ta ɗaura, ta koma kitchen ɗin ta cigaba da wanke-wanken. Tana cikin wanke wanke ta ji kamar an kiran sunan, cikin muryar Hilal tsayawa tayi tana saurere ba tare data amsa ba, daman can bata da ɗabi'ar amsa kira idan har sau ɗaya ne, sai kuma ta ƙara jin kiran a karo an biyu, a maimakon ta amsa sai kawai ta aje wanke-wanke da take ta nufo falo dan taga idan har Hilal ɗin ne. Har waje ta fito tana dubawa amman vata ga motar Hilal ba balle alamunsa. Tana juyawa ta koma ta sake jin an kirata in Hilal voice.
Chapter 76 · 0% Book details