← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 173

Sashe 26

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“A'a Wallahi mugun abin ki ya biki, ke daman Allah be raba bakin ki da tsaɓo ba, bari ma na bar miki gidan daman wani haki ne na siya nace bari na sam miki”

Ta faɗa tana fiddo wani baƙin abu a ƴar ƙaramar roba.

“Kin ganshi ɗan matse ne mai kyau Wallahi, sai kin ban labari, nasan ai kayan amarcin ki sun ƙare yanzu ai”

“Wallahi sun ƙare, duk na kyautar da su ni ba son irin abubuwan nan nake ba, nafi son masu zaƙi ko kuma ƴan fruits haka, kin san suma suna gyara jiki”

“Amman gaskiya kiyi amfani da wannan dan Wallahi yana da kyau sosai”

“To na gode zan gwada”

Bata daɗe ba ta tashi ta fita, har gurin gate Kalsoom ta rakata, sannan ta dawo gida.

Tun kamin Asmee ta isa gida ta buga Rashida tana labarta mata cewar saƙonta ya samu isa yadda ake so. Daga ɗayan ɓangare Rashida tayi murmushi tayi mata godiya sannan suka yi sallama.

Tana aje wayar ta tsire baki. Mutumen dake zaune saman wata huge chair ya kalle a ƙasaice yace

“Wacece?”

“Matar ka ce”

Yayi saurin ɗagowa

“Miya kai ta gidan ki? Bayan baki nan?”

“Ai abokiyar zama na nan, gurinta taje”

Ɗan murmushi yayi

“Mata Allah be raba ku da kicihiba”

Dariya tayi ta ɗauki documents ɗin da suke saman teburinsa, ta nufi ƙofa.

“Ki kai min waɗancan documents ɗin a guesthouse”

Ya faɗa yana kallon mazaunanta dake cikin suit.

“Gaskiya yau ba zan samu shiga ba da wuri zan koma gida”

Daf da zata fice ta amsa masa, sannan ta fice.

___________________________________________

Assalamu alaikum Habibaties💖. To all those that are asking about Amira and Uzair labarinsu zai zo nan gaba, so please wait patiently. And masu cewa kaza ya kamata ayi ba kaza ba, blah blah blah, yen yen yen, this and that, na gode duka amman please ku bar tafiyar nan ta tafi a yadda na tsara ta. Ba ku san dalilin da yasa Yasmeen ta fito a Barrister ba, ba ku san miyasa asiri ya koma kam Amira ba instead of Uzair, so please judge less.

Na gode Sosai Jazakallahu Khairan 🌺

I Love You All Fisabilliah 😘
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa20.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                            Website
www.khadeejacandy.com.ng

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 20*

Ba'ayi wasu events ba, bayan salalle da wanki a Amarya, sai Walima da akayi ranar Jumma'ah. Bikin yayi mutane sosai musamman ta ɓangaren Anty, kasancewar Anty Amarya yanzu ne ta fara aurarwa. Har Ƴaƴan Hajiya Barau da suke nesa sai da suka zo.
Kaɗan daga cikin ƙawayen Namra ne suka samu halartar walimar, kasancewar bata yi gayyatar mutane ba, wasu ma ta hanyar Maryam suka ji.
A babban masallacin Jumma'ah akayi ɗauren aurenta, manyan mutane da dama sun tafi ta dalilin Abbah.

Yadda Asim.yake far'ah da nuna jindaɗinsa kamar ya zuba ruwa ƙasa ya sha. Takeaway na Manyan mutane Abbah yasa aka shirya masa ya rabawa abokansa. Asim kan shimkafa da miya yasa aka shirya masa a gidan wani abokinsa, sai ya tare da Abokansa a can bayana ɗaurin auren sukayi liyafar cin abinci.

Namra na zaune ɗakinta tare da wasu cousins ɗinta, Maryam ta shigo da guɗa.

“Ayyyyyyy Yau an ɗaura auren Namra da Asim”

Wani irin faɗuwa gaban Namra yayi, a maimakon tayi murna sai kawai idonta ya cika da ƙwallah. A take ta soma ganin kamar mafarki take. Farinciki da baƙinciki sai suka taru suka mata tsaye a guri ɗaya.

Yadda ƴan'uwan nata suka riƙa zolayarta yasa ta fito da kukan nata a fili, su kuma suka cigaba da zolayarta. Daker wata Gwaggonta ta lallaɓata ta tashi, tayi wanka lalle ta shirya cikin jar atamfa, mai makeup ta zo ta gyara mata fuskarta.
Sai suka fito da ita harabar gidan inda ake ta kiɗin ƙwarya.
Tsaye tayi a tsakiyar filin riƙe da hannun wata jikar Hajiya, ƴan'uwan Abbah da Hajiya Barau suka riƙa mata ruwan kuɗi suna cashewa, ƴan'uwan Anty Amarya ma sun watsa mata kuɗi sosai. Bata daɗe sosai ba a filin aka dawo da ita dan ta canja wasu kayan, saboda tafiyar da zasu yi, dan tuni motocin da za su ɗauki Amarya zuwa katsina suka iso.

Lokacin da Gwaggwaninta suka fara mata huɗuba akan zamatakewar aure da haƙuri, sai ta riƙa kuka kamar ranta zai fita. Tana faɗuwa tana tashi a aka riƙota aka shiga part ɗin Abbah da ita.

Duk fita suka yi suka barta daga ita sai Abbah, sai Maryam dake riƙe da gefenta itama tana hawayen rabuwa da ƴar'uwarta.

“Maryam tashi ki bamu guri”

Ya faɗa lokacin daya sauke idonsa kar kam Namra dake aikin kuka. Tashi Maryam tayi ta fita. Sai Abbah ya tattara duk kan natsuwarsa ya maida kan Namra.

“Haƙiƙa Khadija ke ƴata ce, kuma ina farinciki da Allah ya gwada min yau na aurar da ke, farinciki ko wane uba ne ya aurarda ƴarsa da ransa kuma ga wanda take so.
Khadija yau igiyar aure ta shiga tsakanin ki da wanda kike so, ina jan kunnenki akan haƙuri zaman aure, duk abunda yayi miki na daɗi ko akasin hakan kiyi haƙuri ki zauna da shi a haka, kar wani tsaɓani ya shiga tsakanin ki da mijinki ki kin tunawa cewa kina da uba! Na ɗaira miki aure da wanda kike so a yau, kuma na sallama masa ke har abada!

Karki kuskura wanke ƙafarki ki zo gidan nan da sunan yaji ko saki. Nayi miki iya abunda ya kamata uba yayi ma ƴarsa na abunda al'ada ta tanada, sai dai kiyi haƙuri ba zan miki gara ba, ba kuma zan ɗora masa kuɗi ba, ke dai yake so kuma ga ki nan na bashi, Allah yayi miki albarka ya baku zama lafiya”

Tun da Abbah yake maganar kan Namra na ƙasa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, duk yadda taso ta tausa muryarta tayi ma Abbah magana sai ta kasa saboda kuka.
Har Abbah ya gaji da sauraren kukanta, ya kira Maryam ta fita da ita. Ko da aka koma da ita part ɗin Anty Amarya numfashinta har rawa yake. Nan ma barinta akayi daga ita sai Anty Amarya. Amman Anty Amarya ta kasa mata magana saboda kukan da take na rabuwa da ƴarta.

Har lokacin da aka bata ya ci ya cinye, Anty Amarya bata iya cewa Namra komai ba, daga ita har Namra suke. Sai da su Mama Zainab da Hajiya Barau suka shigo zasu fita da Namra sannan Anty Amarya ta iya furta

“Na yafe miki Namra Allah yayi miki albarka”

Juyowa Namra tayi ta rumgume Anty Amarya iya ƙarfinta. Har Hajiya Barau da Mama Zainab sai da idonsu ya cika da ƙwallah. Daker suka ɓanɓareta daga jikin Anty Amarya saboda yadda ta rumgumeta.
Yadda Namra take kuka yasa duk wanda yake falon sai da yayi hawaye. Ƙanen Asim da wasu ƴan'uwansa suna tsaye gefe suna kallo.
Muta ɗaya suka shiga da Maryam da Mama Zainab da Hajiya Barau. Ɗayar motar kuma ƴan'uwan Asim suka shiga daman ciki suka zo. Biyun wasu ƴan'uwan Abbah suka shiga, sai ta su Maryam da Aisha da Hindatu da wasu Cousins ɗin su. Ƙarfe uku da ƴan mintuna suka kama hanyar Katsina.

KALSOOM POV.

Yanayin yadda Doc. Hilal ya shiga yau, ya bata tsoro, sai dai bata damu sosai ba, dan tasan haka rayuwa take yau daɗi gobe ba daɗi. Ballantana ma yau ba ɗakinta bane wata ƙila ma uwargidan tasa ce ta ɓata masa rai.

Sai dai hakan be sa tayi ƙasa a gwuiwa ba, wajen zuwa tayi masa kyakkyawar tarba. Sai ta aje Rafiq a falo ta tashi ta nufi ɗakinsa, tana faɗaɗa murmushinta.
Kwance ta kararda shi saman gado ya lumshe ido yana, hannunsa ɗaya dafe da kansa.

Kusa da shi ta zauna, ta kai hannunta ta shafi gefen fuskarsa.

“Ya Omri lafiya kake kuwa?”

Shiru be amsa ta kamar ba zai yi murmushi ba, can kuma ya buɗe ido ya kalleta, sam baya jindaɗin ransa, amman a haka yayi ƙarfin hali ya ƙirƙiro murmushi ya kai hannu ya shafa bayanta.

“Matar Doc. Yau jina nake sai a hankali Wallahi?”

Duk sai taji babu daɗi, daman tasan ba banza tun da taga ya shigo babu ko sallama, kuma be kulata ba ya shigo ɗakinsa.

“Wani abun ne yake maka ciwo?”

“No”

Ya sake lumshe ido.

“Kawai bana jindaɗin rai nane, shiyasa na baro office ɗin”

“Ko wani ne ya ɓata maka rai?”

Idonshi a lumshe ya girgiza mata kai.

“No haka kawai Wallahi”

“Toh Allah ya sauwaƙe ammn idan irin hakan ya same ka, ka riƙa karanta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zaka ji sassauci”

Tashi yayi zaune, ya sakar mata ido kamar yau ya fara ganinta, sai kuma yaja ta jikinsa ya rumgume gam-gam, yana maida numfashi.

________________________________________

Yan Katsina ga Amanar Namra nan mun kawo muku 😢

Anya Hilal lafiya yake kuwa?🤔

#Comment
#Share
#Blogger
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa21.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                             Website
         www.khadeejacandy.com.ng

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 21*

Ana kiran Sallah magariba suka isa Katsina. Kai tsaye suka wuce unguwar Nasarawa. Sun yi mamakin ganin gidan da aka sauke su da sunan gidan da Namra zata zauna.
Ba dan komai ba sai dan sanin Asim ɗin ba shida halin da zai iya kama hayar irin wannan gidan balle kuma har ya siye. Daman tun lokacin da aka zo jere an labartawa Hajiya Barau irin tsarin gidan. Gida ne plate mai kyau da shike-shike, ga farin fentin daya ƙawata gidan. A can ciki an ware dinning area da kitchen a gefe sai two bedrooms da babban falo, ga manyan kujerun da Abbah yasa aka zuba mata kamar ƴar wani shugaban ƙasa, duk bedrooms ɗin an saka mata furniture masu kyau da tsada.
  A ƙaramin ɗaki ta tare ita da ƙannenta, su Hajiya kuma suka fito falo sukayi sallah, bayan sun gama direba ya kawo musu takeaway data aika a siyo musu, sai da suka ci abinci suka ƙoshi sannan Hajiya Barau ta shiga ɗakin da Namra take tana mata sallama, wai zata je gidan wata ƴar'uwarta ita da sauran waɗanda suka zo tare, su Maryam kuma sai idan Ango ya shigo sannan za su je.
Chapter 26 · 0% Book details