← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 173

Sashe 118

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samun kansa yayi da damuwar abunda be kamata ace ya dame shi ba, ya sara sukuninsa tun hawayen da ya gani suna zuba a idon Namra.

“Na ɓata komai? Na ƙara ruguza mata rayuwa? Mi take nufin da hakan?”

Magana yake yi da kansa yana kallon tv, babu abunda kunnuwansa suke da buƙata a yanzu kamar jin labarin Namra.

“Allah kai ka san ina son yarinyar nan, kuma Allah kai ka saka min son ta, ya Rabb help me, wallahi daga gani sai ta yi taurin kai”

Ya shafa fuskarsa yana busar da iskar bakinsa. Can kuma ya kai dubansa ga wayar dake gefensa ya ɗauka ya danna number Ummi. Bugu ɗaya Amal ta ɗauka.

“Dude zaka cigaba da ba ni labarin matar ka ko?”

Murmushi yayi marar sauti kamar tana gabansa.

“Ina Ummi?”

“Tana falo, ni ina game da wayarta”

“Tau ki ce mata na isa lafiya ƙalau kin ji”

Be jira abunda zata ce ba ya kashe wayar, yana sauke ajiyar zuciya. Sam be jin yau zan iya haƙura be ji labarin Namra ba, dare kawai yake jira yayi masa ya koma unguwar, sai dai me idan tace ba zata faɗa ba fa?

“Tau ya zan yi? Ni Wallahi tsoro ma yarinyar nan take ba ni”

Ya sake magana a fili kamar mai magana da wani. miƙewa yayi tsaye ya nufi bedroom ɗinsa yana ware hannayensa.

“Ina ta ƙoƙarin zama mahaukaci akan wannan yarinyar, Allah ka da ka jarrabe ni ta wannan hanyar”

RASHIDA POV.

Da taimakon Teema suka kwashe duk wani abu na amfaninta suka mayar a gidan da Mahaifinta ya bata. Ɗan madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyar, da kuma madaidacin tsakar gida.
Gidan yayi datti sosai duk da kasancewar ba a taɓa zama a cikinsa, sai dai daɗewa da aka yi ba a buɗe shi ba yasa ya koma kamar anyi yaƙi a cikinsa. Tare da teema suka jera komai, sam bata yarda ta nunawa Teema damuwarta akan komawarta gidan ba, hasali ma tana yawan maimaita ita hakan ya fi mata daɗi kuma ita ce ta nemi Dady ta bata gidan alhalin ba haka ba ne, duk yadda hawaye suka yi ƙoƙarin zubar mata sai ta yi kamar abu ya faɗa mata a ido.

Sai dai abunda Teema ta saka samun natsuwa da shi, ganin babu ɗan'uwanta ko ɗaya daya zo rakata a gidan, ko kuma su tausasata akan karta bar wacan gidan ta dawo nan ita kaɗai. Bata nuna mata komai ba har suka gama tsara komai suka share iya inda za su iya, sauran ta ce almajiri zai gyara mata, daf da za su fita Momi ta iso gidan da kukanta kamar wance aka cirewa rai. Duk dauriyar da Rashida ta ke sai da ta fasa na ta kukan, sai ita da Momi aka rasa mai bawa wani haƙuri.

“Ni Wallahi sam ban ga amfanin wannan kukan ba, miye na barin gida Rashida in ban da abun ki? Ai ƙara ki zauna cikin danginki, ko danuwa ai kya rage”

Rashida ta share hawayenta, tana jan majina.

“Ni na zaɓi zama a nan, na fi son na zauna ni kaɗai”

Momi kan bata iya cewa komai ba, sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.

“Dadyn ki ya ce zai aiko da furniture da abinci, da kuɗi kuma duk abunda kike so ki riƙa faɗa mana”

Daga haka ta fice hawaye na cigaba da mata zuba. Bayan fitarta da minti goma shabiyar Rashida ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanke fuskarta ta fito suka ɗauki hanyar dutsen Malam.
Rashida ce take driving, Teema kuma na zaune front seat, sai kallon Rashida ta ke yi ƙasa-ƙasa. Ɗan ƙauye ne da yake can waje gari sai dai kuma ba sosai ba. Shi wannan malamin da alama aikinsa ba yayi ko kuma sabon farawa, dan babu ƙowa a ƙofar gidansa. Matan biyu masu far'ah da son mutane, suna shiga suka ɗauko musu tabarma suka shimfiɗa musu da zimmar za su aika a kira Malam wai yana gona.
Sai ga shi ya iso cikin ƙanƙanen lokaci, jikinsa har ɓari yake, bakin nan cike da goro. Bayan ya gaisa da su yayi musu iso zuwa ɗakin da yake aikin nasa.

“Bismillah”

Ya nuna musu gurin zama yana ɗauko farra ƙasarsa dake cikin ɗan ƙaramin windi. Sai da Teema ta fara gabatar masa da Rashida sannan ta fara faɗa masa matsalolinta da kuma abunda ke tafe da ita. Kai ya girgiza ya sake girgizawa sannan ya shiga duba ƙasar, can ya ɗago ya kalli Rashida ya ce.

“Wato ni bana ɓoye komai, magana ta gaskiya ƙasa ta bada bayanin ba zaki taɓa komawa gidan mijin ki ba”

Rashida ta daki ƙirji.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Sai hawaye ya fara bin fuskarta. Teema ta nuna damuwa sosai.

“Malam ko dai ƙasar bata ba da bayani dai-dai ba ne? Dan Allah a sake bincikawa”

“Ai babu wani bincike, ni ba zan cuce ku ba, kun ga idan wani ne sai ya nuna muku kamar aiki zai ci ya riƙa cin kuɗin ku”

Miƙewa Rashida ta yi tsaye tana hawaye

“Teema tashi mu je”

Kamin Teema ta tashi har Rashida ta kai ƙofar gida.

“Zan kira ka Malam”

Teema ta faɗa tana aje mishi kuɗi masu ɗan dama gabansa. A tsakar gidan ma Teema ce ta yi musu sallama da godiya, ko da ta fito waje har Rashida ta yi ma motar key ita kawai take jira.
Wani mahaukacin gudu Rashida ta fara, kamar marar hankali, har sai da Teema ta riƙa ta.

“Idan har kw baki son kan ki ni ai ina son ki, be kamata kina wannan gudun ba, yawancin bokayen nan ƙarya suke faɗa fa, ki bari zamu je wani gurin”

Uffan Rashida bata ce cewa Teema ba har suka isa ƙofar gidansu Teema.

“Idan Hankalin ki ya kwanta ki kira ni zan kai ki wani gurin”

Sai ta buɗe motar ta fita. Rashida ta fi ƙarfin minti goma a gurin tana kukan sannan ta kaɗa motarta ta yi gaba.

ASIM POV.

“Nice House”

Ya faɗa yana ƙarewa gidan kallo, hannu Nably tasa taja hancinsa.

“Gida zaka yaba ba ni ba?”

“Ke ai babu kalmomin da zan iya amfani da su na ya be ki da su, amman gida ko akwai kalmomi da zan yabe shi da shi”

Ɗan murmushi ta yi, tana ƙara kallon harabar gidan.

“Momi na ta so ta gaisa da kai, sai dai tafiyar gaggauwa ta kama ta yau, amman gobe dole ne ka dawo, dan momi ta ga wanda nake yawan bata labari”

Ya kai hannunsa ya riƙo nata.

“Wato gulma na kike?”

“Ba wani gulma, ba kai ba ne ka sace mata zuciyar ƴa ba”

“Ko kuma ƴarta ta sace zuciyar wani ba”

Cikin wasa ta kai masa duka, shi kuma ya goce yana mata wani kallo, tuni idonsa har sun soma canjawa. Yar yar daya fara jin jikinsa na yi ne yasa ya saki hannunta yana faɗin

“Bari ma zo ma tafi na wuni a gidan na ku ai”

“Wato har ka gaji da gani na kenan?”

“Kai ni har na isa, kawai dai naga magariba tana gabatowa ne, ai kin ga dole jibi naje na kai ki birthday ɗin friend ɗin ta ki, kuma mu zaga gari”

“Ai gobe ne”

Ya buɗe ido.

“Tab aiko dai gobe tafiya za mu yi da oga na, ban da haka kan wallahi babu abunda zai hana ni kai ki ko ina ne a faɗin duniyar nan”

Ta wara ido.

“Kar ka damu, nima ai ban cika son kaje ba gudun kar wata ƙwace min kai”

Sai da aka soma kiran sallah, sannan ya tashi, ta rakoshi har gurin motarsa, ta buɗe masa, har zai shiga sai kuma a juyo ya kalleta ya ce

“Haka zan je ba good bye?”

Murmushi ta yi ta juya ta juyo, kamar mai nuna masa mazaunanta, daman jikinta babu mayafi, sai kawai ta kai masa kiss a baki.

“Shikenan?”

Ya ɗaga mata kai yana wani shegen murmushi. Sannan ya shiga motarsa tana ɗaga masa hannu har ya bar gidan.

“Wow wayayiyace sosai, i'm so lucky”

Abunda ya furta kenan yana ƙarawa motarsa giya. Be tsaya ko ina ba sai da isa unguwarsu, a lokacin har an sauko daga sallar magariba, sai da ya shiga gida yayi wanka sannan ya fito a masallacin unguwar yaje ya yi alwala ya yi sallah, sannan ya koma cikin gidan ya ɗauki motarsa ya ƙarasa ƙofar gidansu Mardiya.

Ko da ya kirata yace yana kofar gidansu, bata cikin gidan, dan haka sai da ya jirata har na tsawon mintuna talati sannan ya ta iso gurin da saurinta. Ta kanta ta buɗe motar ta shiga tana masa sallama.

“Ya gida ya su Mama?”

“Wallahi lafiya ƙalau, ya naka gidan?”

“Gida na babu daɗi fa”

“Subhannalla miya same ka?”

“Kin san na zama gwauro yanzu, tun da kin kore min Namra”

Mardiya ta riƙe baki kamar gaske.

“Wai da gaske ne da ake cewa Namra ta fita?”

“Ba ki sani ba? Kuma saboda ke ta bar gidan?”

“Saboda ni kuma?”

“Eh dan ta gano ina son ki, shine ta so na sake ta ni kuma na ƙi na sake ta, shine sai ta tafiyarta”

“Kai amman ban jidaɗi ba, kaje ka dawo da ita dan Allah”

“Ni yanzu ba ta ita nake ba ta ki na ke”

“Ni kuma?”

“Eh mana, ni fa tsakani da Allah na ke son ki, kuma auren ki zan yi, shine abunda ya kawo ni yanzu, na baki kwana biyu ki je ki yi shawara”

“Amman Namra ba zata ce komai ba?”

“Ke kike ta kanta, ga wannan ni zan wuce, dan gobe zan yi tafiya yau nake son na fara shiri na”

Ya miƙa mata dubu goma, ƴan ɗari biyar-biyar. Ƙin karɓa ta yi har sai da ya matsa mata sannan ta karɓa tana masa godiya, ta buɗe mota ta fita.

KALSOOM POV.

Be barta ta yi aikin komai ba, shi ya haɗa musu abun kari, kuma ya haɗa musu ruwan wanka. Daman ita ta gaji sosai, tun da ta yi sallah asuba ta koma bachi, shi kuma ganin hakan yasa be tashe ba, ya barta ta yi bachinta, har ta gaji ta tashi dan kanta, sannan ya shigo ɗakin fuskarsa da Annuri.

“Tun ɗazu breakfast yake jiran ki”
Chapter 118 · 0% Book details