← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 173

Sashe 166

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wanda be yi mamaki furucin Abbah ga Namra ba, sai dai hakan ya karantar da kowa cewar gaskiya ce Abbah yake son ya buɗe. Namra kamar daman jiran Umarni kawai take sai ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita duk da bata san hanyar da zata sadata da banɗaki ba ko kuma wani gurin makamancin wannan. Hanyar da Ummi ta biyo da ita ta bi tana tafiya har ta fito part ɗin ba, sai barorin dake tsaye habarar gidan suna shanya tufafi suka rugo da gudu suka zube ƙasanta suna kwasar gaisuwa.

“Allah ya taimaki gimbiya ko da wani abun da kike buƙata ne”

Ɗaya ɗaga cikinsu ta faɗa.

“Banɗaki za a kai ni alwala zanyi”

Ta faɗa tana share hawayen da bata san sun zubo mata ba sai a wannan lokacin.

“Yana ta nan Gimbiya”

Sai suka shiga baga tana biye har suka shiga part Hajiya Shafa, a nan wasu Barorin ne suka zube suna ɗubar gaisuwa, Namra zata buɗe baki ta yi magana sai wata daga cikin barorin ta rigata.

“Allah ya taimaki Gimbiya Farida, Gimbiya Namra zata shiga banɗaki ne”

Gimbiya Farida ta miƙe tana aje wayar dake hannunta ta riƙa Namra.

“Muje ta nan”

Tare suka shiga wani ƙaton ɗaki Mai cike da kayan more rayuwa sannan ta kaita bakin ƙofar Bathroom ɗin ta buɗe mata.

“Bilmillah Amaryar mu”

Ta faɗa fuskarta da murmushi Namra tayi bismillah ta shiga, sai da ta fara tsarki sannan ta yi alwala ta fito, a bakin gadon ta samu Farida zaune tana kallon ƙofar ɗakin kamar mai nazari.
Zuwa tayi ta riƙa Namra suka fita tare, ita ta rakata har part ɗin Mai Martaba sannan ta juya ta koma, sai waiwayen Namra take.

Hasbunallahu wani'imal wakil Namra ta karanta sannan ta saka ƙafarta ta shiga falon.
Duk kallon sai ya koma kanta, ita kuma dubanta yana gurin Malamin faɗa dakw riƙe da ƙur'anen fuskarsa da ruwa da alama shi ma alwalar yayi, ƙarasawa tayi ta karɓi alƙur'ane ta riƙe tana kallon Asim ido cikin ido, kamin ta kawarda fuskarta ta kalli Malamin dake karanto mata yadda zata faɗa. Ƙur'ane ta ɗaga sama ta soma ƙaranto rantsuwar kamar yadda Malamin ya faɗa mata, sai da ta rantse sau uku sannan ana ƙarshen tace.

“Ya Allah ka nuna mai gaskiya tsakanin ni da shi”

“Allahu akbar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Shine abunda kowa ya faɗa yana girgiza kai, Asim kan idonsa tsaya dake laƙe suka ƙara fitowa gumi ya soma keto masa ta ko ina.

“Amman Namra baki tsoron Allah da gaske baki so? Yanzu sai da kika rantse? Ni ban sake ki Amman tun da kika rantse amana zata kama ki”

Abunda Asim ya faɗa kenan muryarsa na rawa kamar wanda ya ruɗe. Sai Yayan Mahaifinsa ya soma masa faɗa tana Allah wadan da halinsa. Sai kawai ya soma rantse-rantse.

“Wallahi Baba ban sake ta, idan kuma har na sake ta kada Allah ya tayar da ni a nan gurin lafiya”

Kowa sai mamaki ya kamshi tsakanin ita da shi waye mai gaskiya, ita tayi rantsuwa da Alƙur'ane akan hakan shine gaskiyarta, shi kuma yace idan ƙaryar yake kada Allah ya tayarda shi lafiya, sai dai kowa yasan dole akwai wani abu ya faru da ɗayansu wanda baya kan gaskiya.

Tun da Namra ta soma rantsuwar Abdool ya rumtse idonsa yana saurarenta muryarta, zuciyarsa kuma cike da tsanar Asim. Maganar da Malam ya fara ne yasa shi buɗe ido.

“Tun da har Namra ta rantse akan ka saketa, ya tabbata aurenta da Yarima Abdallah yana nan, idan kuma har akan ƙarya ta rantse to Allah zai nuna mata isha dan Allah ba abun wasa ba ne, daman ana samun irin wannan matsalar idan har miji yayi jayayyar shi akan sashi rantsuwa ne, idan kuma mata tayi musun haka akan sata ra rantse ne, duk wanda yake akan gaskiya Allah ya sani kuma zai masa hukunci. Saboda haka akwai aure tsakanin Yarima Abdallah da kuma Gimbiya Namra, idan kuma har yana da ja akan hakan zai iya zuwa kotu saboda tabbatar da gaskiyarsa”

Allahu akbar suka faɗa. Asim kuma ya girgiza kai yana kallon Namra hawaye na bin idonsa ya ce.

“Da gaske ba zaki dawo gareni ba kenan! Ko da ke kika rantse, shikenan na rasa ki har a bada”

Cikin wani irin zafi rai Abdallah ya miƙe tsaye sai Mai Martaba ya ɗaga masa hannu alamar kar yace komai ko ya aiwatar da wani abu.
Mai Martaba yayi gyaran murya yana kallon Asim.

“Yaron ka gamsu da wannan hukuncin da akan yanke?”

Ya gyaɗa kai hawaye na masa zuba.

“Na gamsu ranka ya daɗe, tabbas na yi kuskure”

Ya maida dubansa gurin Namra da itama hawayen ta ke.

“Ina son ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah, zubar da cikin nan kika yi ko kuma ɓarewa yayi?”

“Babu dalilin da zai sa na zubar da ciki Asim, da ace zan zubar da na yarda na zaɓi zama da kai na zubar da cikin kamar yadda ka buƙata, cikin ya zube ne ta dalilin matsalar da nake da ita a mahaifata na rashin tsayawar ciki”

Murmushi yayi tana tuna lokacin da ya cilasta mata zaɓen cikin ko kuma aurenta, lokacin da yake iƙirarin be shirya haihuwa ba, yanzu kuma yana kan nema Allah be bashi ba, a tunaninsa idan har Namra ta rantse to za'ace ta koma ɗakinta ne, yana tunanin kamar yayi mata wayo yadda rantsuwar ba zata kama shi ba.

“Na gode Mai Martaba da ka saurareni Allah ƙara maka lafiya”

Ya faɗa kamar ba shi ba, gaba ɗaya jikinsa yayi la'asar ya saduda da lamarin dan yasan ya rasa Namra har a bada, bayan kuma yanzu ne yake jin mashin son ta na sukar zuciyarsa, yasan nan Mai Martaba yayi masa da sauƙi ne idan aka je kotu shi za a saka ya rantse, duk da yasan Abdool ba zai ƙyale shi ba.

“Baba ku tashi muje”

Ya faɗa yana fashewa da kuka. Sai duk suka miƙe tsaye jikinsu na rawa suka yi ma Mai Martaba sallama suka bi bayan Asim da ya rigasu fara tafiya. Kamar jira ake ya kai bakin ƙofar fita falon sai gashi yayi waɓi mugun faɗuwa kamar wanda aka kwashewa ƙafafu, Subhannallahi ƴan uwansa suka riƙa faɗa suka ƙarasa da sauri suka mashi suka tayar tsaye, amman sai ya kasa tsaye ƙafafunsa suka murɗe kamar an shanyesu, a nan kowa ya ƙara girmama Allah a take ishara ta bayyana iƙirarin da yayi na cewar idan ƙarya yake kada Allah ya fitar da shi lafiya ya kama shi, da ace ma shine yayi rantsuwa kamar yadda Namra ta yi da take zai faɗi ya mutu saboda bashi da gaskiya, da kama-kama suka fitar da shi.

Falon yayi tsit kamar ba kowa sai lamarin Allah suke jinjunawa, bayan kamar mintuna goma Mai Martaba ya ɗaga kai ya kalli kowa da ke cikin falon ya ce.

“Allah kenan ba a masa wasa, wani lokacin ɗan'adam muna da rauni da gazawa, da kuma isgili da gajin haƙuri, bayan ba mu wuce Allah yace mana ku mutu mu faɗi mu mutu ba, ko da beyi wannan isgilin ba dole ne yaga ba dai-dai ba saboda ƙoƙarinsa na raba auren sunna da kuma ƙoƙarinsa na saka auren cikin rikici.

Nasan hakan zai faru, dole ne a cikinsu akwai mai gaskiya, walau ita ko kuma shi yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa na hana Abdallah yi masa komai saboda za ayi duban kamar shi Abdallah baya da gaskiya ne ko kuma an zalumce amman yanzu shi kansa ya san tsakaninsa da Allah ne ba da mu ba, ƙara Allah yayi masa sakamako da ace nan aka cutar da shi, nasan zuciyarka ta kawo Abdallah zaka iya masa komai ido a rufe, sai dai ko da yaushe ina yawan faɗa muku da ku cuci mutum ƙara ka bari shi ya cuce ka, kar ka yarda ka ɗauki haƙƙin wani ko kuma ace haƙƙin wani yana kan ka, Ubangiji yana yafiya, amman baya yafe laifin wani akan wani, kuma duk lokacin da kaci amana ko haƙƙin wani ya hau kanka zaiyi ta cinka ne a dukiyarka ko lafiyarka sannan kuma idan kunje lafiya Allah ya karɓa masa haƙƙinsa.

Ko wace rayuwa tana zuwa da jarabawa, wani lokacin aka gwada mutun dan a auna imaninsa, kuma aga iya tawakkalinsa da haƙurinsa, abunda duk haƙuri be baka ba to rashinsa ba zai baka shi ba, da ace ba ayi haƙuri ba da yanzu ba kawo nan ba, kuma daga ƙarshe ba za a ga abunda ake so ba. Ina addu'ah wannan aure Allah yasa masa albarka kuma ya kawarda duk wata fitina da zata zo nan gaba, Allah ya muku albarka, kuma yau Namra zaki kwana ɗakinki da yardar Allah”

Nasihar Mai Martaba ta ratsa zuciya da jikin duk wanda ke cikin falon, tabbas mai martaba yayi musu nasiha mai haɗe da wa'azi a lokaci ɗaya.

Hajiya Sadiya ce ta riga tashi ta fice daga falon, sannna Ummi ta tashi tare da Namra suka yi ma Mai Martaba sallama, sannan suka fito, jingine da mota suka samu Hajiya Sadiya tana hawaye, har sun buɗe motar sun shiga sai Ummi tace a ɗan jira kamar tasan Mai Martaba zai aiko kiran Namra, sai ga Waziri da kansa ya zo ya faɗa ma Ummi cewar Mai Martaba yana kiran Namra, sai Ummi tace ta buɗe mata motar ta fito ta bi bayan waziri. Falon da suka fito suka koma sai dai wannan karon babu kowa sai Anty Amarya da Abbah, da alama Mai Martaba ya basu dama su tattauna ne, waziri ma yana kawowa bakin ƙofa ya kama gabansa.

Ƙarasa Namra tayi cikin kuka ta faɗa jikin Anty Amarya da ke murmushi ta rumgume ta.

“Mamana kenan kin ga rayuwa, wannan duka sharar fage ne alamu ne na rayuwar jindaɗi da farinciki tana nan tafe, Allah ya miki albarka”
Chapter 166 · 0% Book details