← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 173

Sashe 60

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wallahi ba haka Allah yayi ka ba, ko minene dai daga baya ne ya same ka, ai da can ba haka kake ba, ko dai dan na haihu ne na daina burge ka?”

“A'a karki sawa ran ki wani abu, wallahi bana neman mata a waje, babu ruwana da mata, kawai dai sauyin yanayi ne”

Ya sa hannayensa aljihu ya nufi ƙofar fita. Da kallon ta kaici ta bishi, har ta fice, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta nufi ɗakinta dan dauke faralin da yake kanta na sallah magariba.

A masallacin unguwar ya yi,alwalah yayi sallah magariba, shi kaɗai yayi abarsa dan su tuni suka sauke jan'i. Bayan ya fito ne ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira number Hajiya Barau dan tsegunta mata labarin Namra, duk da yana tunanin ta san da zuwan na ta.

Two missing calls yayi mata, bata ɗauka ba, har ya mai da wayar aljihu sai gata ta kira, cikin sauri ya ɗaga kiran nata yana takowa zuwa gida.

“Hajiya ina wuni?”

“Lafiya ƙalau Uzairu ka kira ni ina sallah, ya gida ya mijina da Yasmin?”

“Suna nan ƙalau, yanzu ma Yasmin take faɗa min wai Namra ta zo, tana gida da yake ita gida ta wuni daga gurin aikin ta wuce gida”

“Namra kuma? Amman bata sauka nan?”

“Au daman bata sauka nan ba? Ai na ɗauka ta kwana biyu da zuwa ma”

“A'a Wallahi ni ban ji labari ga kowa ba, amman ita taga Namra ɗin da idonta?”

“Haka tace min, yanzu haka tana gidan Gwaggo”

“To ko fushi take da Alhaji ?shiyasa bata sauka nan ba?”

“Idan ma fushi take da Abbah ai ke ba zatayi da ke ba, kuma ga Anty”

“A'a mu a su wa? Kishiryar uwa mai ƙaurin suna? Ta dai san ba zuwan lafiya bane shiyasa ba zata sauka nan ba, dan tasan halin Alhaji shiyasa aka ce in  za a yi tukka a yi mata hanci don kada ta warware, irin wannan ranar ake gudu, daman ni nasan abin da ya ci doma ba ya barin awai, yadda yarinyar nan ta ci amanarka ai dole alhakin ka ya fita”

Uzair yayi wani shegen murmushi

“Ashe baki san ta zo ba, amman ina jin Anty ba zata rasa sani ba”

“Ina jin ta sani sai ta ɓoye, waya sani ma ko ita tace mata ta sauka gidan Hajiya Kulu tun da tasan tana son Namra, ba zata bari Alhaji ya wulaƙanta ba, ji fa ko gobarar nan da tayi har yau bata taɓa maganar ba, in ban da ƴan'uwana da suka ce suka faɗa min da ban ji ba, ai ni naji daɗin da Alhaji ya juya mata ƴarta baya, dan duk abunda take da sanin uwar nan take  yinsa, ita ke goya mata baya, ko auren nan naku da anyi da sai uwar nan ta kashe shi dan bata son ka”

“Allah ya kyauta, ai ga ta nan ta dawo mata sai tayi yadda take so da ita, Yasmin tace min duk ta rame ta yi baƙi”

“Lallai kam, kowa ya keta riga tasa, ya san inda zare ya ke”

“Kaɗan suka fara gani”

Ya faɗa sannan yayi sallama da ita ya kashe wayar. Hajiya Barau ya aje wayar ta cire Hijabin dake jikinta ta tashi ta nufi part ɗin Abbah.

MARYAM POV.

Da takaicin Namra ta koma gida, sai dai bata labarta ma Anty Amarya komai ba, dan bata san ta yadda zata ce mata ba, sai bayan magariba, sannan ta labarta mata abunda ake ciki.

Duk rikicewa Anty Amarya tayi murna da farinciki suka zo mata a lokaci ɗaya, murnar ƴarta ta zo da kuma baƙinciki bata sauka a gidan ba, ita kan ta tasan sai anyi yaƙi da Abbah kamin ya barta ta zauna gidan.

“Amman Maryam ita kaɗai kika ganta?”

“Eh ita kaɗai, Anty duk ta lalace ta rame Allah kaɗai yasan abunda yayi mata tun da har kika ga ta baro shi ta zo nan, bayan kuma ta san halin Abbah”

Sai duk Anty Amarya ta ji babu daɗi, a take ta ji tana buƙatar ganin ƴarta.

“Zan faɗa ma Abbanku ta zo ganin gida ne, ai dole ya barta ta zauna”

Maryam zata yi magana sai ga wayarta tayi ringing, Sweet PaPa ta gani hakan ya tabbatar mata da number Abbah ce, da sallama ta ɗauki wayar dan tasan Abbah ya tsani ya kira mutum ace masa hello.

“Maryam”

“Naam Abbah”

“Ki ce Mamanki ta zo yanzu”

“To”

Ta kashe wayar gabanta na faɗuwa, duk da bata san anyi komai ba, amman ta ji kamar ba lafiya ba, ta kalli Anty Amarya dake cikin yanayin damuwa tace

“Wai Abbah ki zo”

Shiru Anty Amarya ta ɗan yi sannan ta tashi cikin rashin ƙarfin jiki ta nufi part ɗin Abbah ba. Zuciyarta da biyu, ta faɗawa Abbah Namra zata zo ganik gida, kuma ta ji kiran da yake mata. Sai dai duk hanzarinta ya katse lokacin da Abbah ya gargaɗe ta akan kar ta bar Namra ta shigo masa gidan.

“Ki faɗawa ƴar ki karta kuskura zuwa min gida, ta tsaya can inda ta sauka”

“Ƴata ce kai ba da kai ba? Ko shegiya na haifa ne?”

“Nine ubanta, amman na riga na yafe ta, kuma tun ranar da zata je gidan mijinta na faɗa mata karta kuskura dosomin gida da sunan yaji ko saki”

“Ai ganin gida zata zo”

“Ba ganin gida ta zo ba, na dai faɗa miki karta doso min gida”

“Ƴata tana da buƙata na, kuma dole ta zo nan gidan nan tun da ina ciki, ko wane munafukin ne ya zo ya faɗa maka sai na ci masa mutunci”

Abbah yayi banza da ita yana kallon agogon hannunsa.

“Yanzu zamu je karɓo kuɗin kwangila, karki kuskura ki bari ta shigo min gida indai ba mugun wulaƙanci kike so na mata ba”

“Idan bata shigo ba, ni zan koma gidan mu na zauna da ita, dan ba galihu ne bata da shi ba, abunda kake yi baka kyautawa Alhaji, musulunci be ce haka ba, shikenan dan kawai ta auri wanda take so sai abu ya zama ɗan zane”

“Ai daman duk abunda take da goyon bayanki take yinsa, ke kika goya nata baya”

“Ni nake goya mata baya, ai daman ka saba faɗar haka, komai nice, daman na san ba ƴata ce baka so ba, ni ce baka so, ita Hajiya da take ƴar'uwarka ai baka mata haka ba balle ƴaƴanta, sai ni da ka auro bare, nice abar wulaƙantawa ni da ƴaƴana, ko kuma saboda ni ban haifi ƴaƴa maza ba shiyasa kake min haka”

Cikin faɗa da kuka Anty Amarya tayi maganar. Sai Abbah yayi mata wani kallo na mamaki.

“Subhanallahi, ai ƴaƴa maza da mata duka ɗaya ne a gurin Allah”

“Amman kai a gurin ka ba ɗaya bane, tun da gashi kana nuna min banbanci, idan baka da rai a yau babu wanda zan kallah na ji sanyi sai ƴaƴaka, haka nima idan bana da rai babu wanda zaka kalla ka tuna da ni ko kaji sanyi sai ƴaƴana, to dan me zasu zama abun wulaƙantawa a gareka, ashe wata rana idan bana da rai abunda zaka ma ƴar ciki sai yafi wannan tun da kayi mata haka ina raye, kai da ƴan'uwanka kun sa Namra a gaba, kamar ta kashe muku wani, daman ni ce ba ku so ba ita ba”

Ta juya ta fita tana wani irin kuka kamar ta faɗi ƙasa. Har cikin ransa Abbah yake jin kukan Anty Amarya, kalamanta sun ɓata masa rai, sai kuma sun fi taɓa masa zuciya sosai har sun sa ya sauko daga fushin da yake.
Ɗakinsa ya koma ya ɗan kimtsa sannan ya fito ya nufi gurin da aka saba aje masa motocinsa.

Da kuka Anty Amarya ta shiga part ɗinta, duk hankalin Maryam sai ya tashi, kasancewar ita kaɗaice ke falon, ganin mahaifiyarta na kuka, yasa ita ta fashe da kuka ba tare da tasan dalilin kukan na Anty ba.

“Anty me ya faru?”

“Wallahi yai ba zan kwanan a gidan nan ba, babu abunda zai sa na kwana gidan da za a hana ƴata shigosa, yafi son ta je can ta zauna inda za a riƙa zaginta ana tseguminta”

“Be yarda ta zauna, ban san munafukin daya faɗa masa ba”

“Anty kiyi haƙuri, zai sauko yana cikin fushi ne”

Aisha ce ta fito daga ɗakinsu ita da Hindatu suka nufo gurin da Anty Amarya take, suna tambayar ba'asi, dan basu san abunda yake faruwa ba, suna can ɗaki suna karatun exam.

“Lafiya miya faru”

Aisha ta tambaya tana dafa Anty.

“Abbah ne yace wai Namra ba zata shigo masa gida ba”

Maryam ta faɗa tana kuka. Hindatu ta kalleta da mamaki tace

“Amman yanzu Abbah ya kira wayar Aisha yace ta faɗa niki kije ki zo da Namra”

Anty Amarya tayi saurin kallon Hindatu tana share hawayenta.

“Da gaske? Yanzu ya kira ki?”

“Eh Wallahi”

Anty Amarya ta tashi da sauri ta nufi part ɗin Abbah, kamin ta ƙarasa ta hangoshi jikin mota, yana jiran direbansa ya tashi motar.
Gurin ta ƙarasa ta tsaya masa a gaba.

“Kai kace azo da Namra?”

“Amman sati ɗaya na yarda ta yi”

Haka kawai ya faɗa ba tare daya kalleta ba, ya buɗe motar ya shiga. Sai ga Anty ta dawo falon da far'ah tana cewa Maryam da Aisha su je su taho da ita.

RASHIDA POV.
Chapter 60 · 0% Book details