← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 173

Sashe 42

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kasa yarda, mamaki yake har yanzu, shi dai yasan yana yawan gwada kansa every 6 months da kuma iyalansa, kuma lokacin da aka auna jinin Kalsoom be nuna haka ba, why Rashida?
Gani yake mistake ne suka yi, sai dai baya jin zai iya koma ya tambayesu, abunda kawai zai iya, shine ya sake ɗibar jinin nata, da na ƴaƴansa da kuma na Kalsoom ya kai ward ɗin da ake gwajin cutar, dan tabbatar da zarginsa, idan har da gaske ne ai zai nuna yadda ta samu ciwon da kuma daɗewarsa a jikinta.

Be iya ƙarasa aikin ba ya haɗa kayansa ya ɗauki ƙaramin box ɗinsa ya cire labcoat ya riƙe a hannu ya fice, ba tare daya tsaya kulle office ɗin ba.

Ko da ya isa gida kansa har wani zafi yake kamar an kunna masa wuta, gaba ɗaya kalar idonsa, da fuskarsa ta canja irin kana kallonsa kasan yana cikin damuwa.
Rashida na zaune falo riƙe da plate tana cin abinci, ba laifi yanzu kan ta ɗan samu sauƙi dan ita ma tayi girkin sa kanta. A bakin ƙofar falon ya tsaya yana kallonta wani tausayinta yaji ya lulluɓe shi har idonsa suka cika da ƙwallah.

Ita kuma ta ɗan kalle shi kaɗan ta kauce kai, ba dan bata son kallon nasa ba, sai dan baƙin kishi daya rufe mata ido, gani take yanzu ai ba ita kaɗai ce da shi ba.

Yana sako ƙafarsa a first step ɗin falon, sai ta tashi ta nufi ɗakinta. Shi kuma ya tsaya a gurin ya bita da kallo zuciyarsa cike da tausayinta.

______________________________________________
Assalamu alaikum Habibaties 🌺
Ina fatar kuna cikin koshin lafiya? Allah yasa haka Amin
My dear readers idan Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya, idan na yi page 35 tau ZAGON ƘASA na Khadeeja Candy ya koma na siyarwa, daga bakin Page 35 har zuwa karshe na kudi ne, daga page 1 zuwa 35 free ne. Nasan zaku ga chanji yazo muku ba ta yadda kuka zata ba, ku yi hakuri ku min uzuri, haka sauyin ya zo. Kuma ina fatar zaku goya min baya, fiye da yadda kuke min a da, soyayyar ku da haɗin kan ku, shi na ke fata a kullum, Allah yasa ku min kyakkyawar fahimta. 😊👌

Ga waɗanda suke sha'awa. Naira ɗari biyu ₦200 zaku turo ta wannan account ɗin 0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.
Ga wanɗanda basa da account kuma za su iya turo katin waya na line mtn na dari biyu da hansin ₦250 ta wannan number 08036126660

Idan kun tura. Sai ku turo da shaidar biyan kudin wato screenshot ta wannan number 08036126660.

NA GODE 😊

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                             Website
         www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 32*

NOT EDITED ⚠️

Ɗakinsa ya wuce ya aje kayan da suke hannunsa,  sannan ya fito ya shiga ɗakinta. Zaune ya same tana taunar naman abincin data gama ci, kusa da ita ya zauna yayi mata ƙuri da ido, kamar mai tunanin abunda zai faɗa mata.

“What?”

Ta tambaya shi sam be san ta lura da kallon da yake mata ba har sai da tayi magana.

“Bana da ikon kallon ki ne?”

Ya faɗa yana murmushin ƙarfin hali.

“Kallo na nawa kuma, ai na gaji da kallon nawa ne shiyasa kaje ka ɗauko wata, kuma ni ka faɗa mata ta daina zuwa min yawo da yara karta lalata su”

“Uhmm, Pyar ki daina sawo zance Kalsoom a gurin da muhallinta ba, ke da ita duka ɗaya kuke a guna, wani abun da kike faɗa akanta ba daɗe yake min ba, and you know what ita bata taɓa wani mugun furuci akan ki ba, balle kuma akan ki ba, sannan tana kula da ƴaƴanki”

Ta taɓe baki ta aje plate ɗin ƙasa.

“Wallahi duk son ƙarya ne, babu kishiyar data zata so ƴaƴan kishiryarta, wannan duk Zagon ƙasa ne”

Ya kai hannu ya riƙo hannunta.

“Naji pyar faɗa min when last nayi miki gwajin jini?”

“I can't remember, ba kai kake min ba?”

Ya ɗanyi shiru.

“Ina ganin anyi shekara biyu yanzu, saboda ba samun zama nake ba, miya faru?”

“Ba komai, zan sake ɗibar wani ne, wacan a mota ya ɓata fitsarin kawai na auna”

“Okay amman yau zaka ɗiba, dan gobe zan je aiki”

“Daga jin sauƙi sai kuma zuwa aiki?”

“Kasan matsalar banki tun yau ma aka so na koma”

Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta.

“Pyar i love you so much ki sa wannan a zuciyarki, mijinki yana son ki sosai”

“Yana son mu dai point of correction”

Ta faɗa tana wani yatsina fuska, shi kuma yayi murmushin da be kai zuci ba, ya tashi tsaye.

“Bari na yi wanka”

“As you wish”

Bayansa ta bi da kallo zuciyarta na mugun tafarfasa, duk yadda take so mijinta idan ta tuna da ba ita kaɗai yake so ba, sai ranta ya ɓace.

Sai da yamma lis sannan Kalsoom ta dawo, dan yau gidan su ta wuni ita da yara, daman duk ranar da ba'a zuwa makarantan ilamiya, ta kan yi amfani da lokacin ta koyar da su wani abu na rayuwa ko kuma addini, sai ya kasance yau kan tana buƙatar zuwa gida gaida du Momy, shiyasa ta kwashi yaran duka suka je gidan.
    Tayi mamakin ganin Rashida tayi abinci a yau bayan kuma jiya ta gama koken bata da lafiya, kusan kwana biyu nan ma har cewa take ita ba zata iya cin komai ba.

Ta san yau Doc ba a ɗakinta yake ba, hakan yasa bata damu da dole sai ta ganshi, dan ko da suka dawo, baya gidan Rashida ce kawai, kuma har dare be dawo ba.
Da wuri yaran suka yi bachi saboda gajiya, sai ya rage ita kaɗaice a falon sai tv tada tisa a gaba tana kallo. Saman kanta Rashida ta zo ta tsaya sai wani yauƙi take kamar ance mata Doc ne a gurin zaune.

“Ammyn Rafiq ya idan zaki fita da yara ki riƙa faɗawa Dadyn su, yazo nan yana ta min faɗa wai shi baya son yawo kar a lalata masa yara”

Kalsoom ta ɗago kai ta kalleta tana murmushi

“Ai ni kaina ban fita ba, sai da na nemi izininsa, balle kuma na ƴaƴansa, I'm friendly Rashida feel free to tell me baki son ina fita da yaran ki, is okay sai na tura su duk inda nake so”

Bata tsaya jiran abunda zata sake cewa ba, ta aje remote ɗin dake hannunta, ta tashi ta bar mata falon.
Da wani mugun kallo Rashida ta bita ji take kamar ta tashi taje ta maƙareta, bata san tana kishinta ba ma sai a yanzu data kwana biyu nan a gida, ita dai gani take Kalsoom ta tare mata guri.

‘Ni ban ga abunda matar nan ta fini da shi ba, yaje ya kwaso ta, mace sai baƙin munafurci, Wallahi kin yi kuskuren auren mijina dan mijina mijin Rashida ne ƙadai ba dawata macen ba’

Ƙwafa tayi tana wani huci kamar maciji, ta juya ta koma ɗakinta. Saman gado ta zauna tana sauraren yadda zuciyarta take mata zafi, kishin Mijinta take ji sosai, sai a yanzu take gane abunda wasu ƴan grps nata na whatsapp suke faɗa mata akan kishiya, ya karɓe mata ƴaƴa, yanzu kuma tana ƙoƙarin karɓe mata miji, gashi Hajiya ma tafi son Kalsoom da ita.

Wayarta ta ɗauko ta aika ma da Asmee kira, sai da ta mata two missed calls sannan tayi picking.

“Ina ta kira hala baki kusa?”

“Eh Wallahi ya gida?”

“Gida ƙalau, ni dai ce hankali ba kwance kuma ban ji kin kira ni, Asmee idan mukayi sake fa matar nan ƙwace min miji zata yi”

“Wallahi ban samu naje bane, bana jindaɗi sosai, amman inshallah gobe zan je”

“Ayyah me ke damun ki?”

“Ina jin ƙiba ne sai kuma Infection ya shiga ciki”

“Indai Infection ne ki nemi ɗayyar citta da tafarnuwa ki feraye cittar ki ki jiƙa su, su jiƙu sai ki riƙa sha ko kuma ki nemi maganin nan Cantin yana yi sosai. Na rage tumbi ko kiba kuma ki samu ganyen guava guda bakwai ki tafasa with one liter of water kisha for seven day's mrng before breakfast da kuma last thing kafin kwanciya, shi Momy take kuma wallahi na sauka ta rage ƙiba sosai cikin satina ɗaya yayi mata aiki wallahi, masu ulcer ma zasuyi yana maganinsa, irin wannan yafi na asibitin dan shi ba shida side effect. Allah ya baki lafiya”

“Amin na gode sai kin ji ni”

Daga haka sukayi sallama, Rashida ta aje wayarta tana faɗin

“Garin kwashe kwashen ki dai sai kin kwasowa kan ki, ba ko wane malami bane zai haɗe yawunsa akan ki, ni ko zan yarda ai ba zan malaman ƙauye ba ƙazamai”

Ta ƙarasa maganar da tsire baki, duniyar tunaninta na son dawo mata.
A gogon ɗakin ta sakarwa ido daga seconds zuwa minutes take ƙirgawa har ya kai ga hours, Doc be dawo gida ba, haka ta gaji ta kwanta saman gado idonta a ƙafe, babu abunda take tunani sai Rashida.
Yadda ta shiga cikin gidan da kuma irin rawar data taka tun daga shigowarta zuwa yanzu, bata ankara hawaye suka silalo mata.
Sai yanzu take jin yadda ɗacin zuciya yake, sai yanzu take jin son Hilal na haƙiƙa a zuciyarta, sai yanzu take gane ta tabka kuskure da tabar shi ya ƙara aure, yanzu haka zata kasance ita da wata a cikin gida? Haka itama zata gina nata rayuwar ta karɓe mata kowa?

Tafiyar daƙiƙa biyar zuwa shida numfashinta yayi kamin ya dawo izuwa gareta har ta ankaro da duniya take, ta samu damar amsa sallamar mai gidan nata.

“Wa'alaikassam”

Sautin muryarta ya isar masa da saƙon damuwarta, ga kuma hawaye dake kwance a fuska. Ledar dake hannunsa ya aje ya zauna kusa da ita gabansa na faɗuwa, har zuciyarsa ta fara raya masa wani abun na dabam.

“Miya faru kike kuka?”

“Kawai ina tunanin rayuwa ne, da kuma irin sakamakon da kayi min, bayan nayi maka dukan hallacin”

Masauki yayi mata a ƙirjinsa, ya kai hannu ya dafa cikinta, zuciyarsa na hasaso masa wani tunanin na daban.
Chapter 42 · 0% Book details