← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 173

Sashe 73

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin data fara shan rubutun da Hajiya tasa aka mata, sai ta fara jin sauyi a jikinta, sai mafarkai take wasu ma har bata san kansu ba.
Natsuwar da take ji a yanzu, yana kan tunatar da ita rayuwar rikicin da ta yi a ƴan watanin nan, sai yanzu take mamakin kanta duk wacan abun da ta yi sai ya zama matar kamar mafarki.
Lallai a yanzu ta tabbatar da ta yi wasa da addu'ah, dan bata iya addu'ah safe balle kuma ta yamma da take gani kamar ba komai ba ce. Sai dai har yanzu bata jin ƙarfin yin addu'ah kuma jinin be ɗauke mata ba, amman dai ta dawo normal kamar yadda take, ba kamar baya ba da take jin abu na mata yawo cikin kai kamar tsutsa.

Da wuri ta tashi ta shirya musu abun karyawa, sannan ta tashi yaran duka tayi musu wanka da kanta, Izzah ce kawai bata bari anyi mata ba, sai wani cika take tana batsewa kamar wata babbar mace, ada tana yi a dole dan Rashida na sa, amman a yanzu kan na gaske take dan har cikin zuciyarta take jin tsanar Kalsoom bayan kuma bata mata komai ba, sai dai laifinta da take gani na kore musu uwa da ta yi, sannan tana ganim yadda komai ta yi musu Daddy su ba ya magana.

Sai da Kalsoom ta shirya su tsab sannan ya tura su gurin motar Daddy su ta shiga ɗan ta tashi mijinta.

A bakin ƙofar ɗakinsa ta tsaya ta buɗe maɓallin rigarta sannan ta kunna kai cikin ɗakin. Hannunta tasa cikin gashin kansa tana wasa da shi, amman be motsa ba, badan kuma be farka ba, sai dan daɗin da yake ji akan abunda take masa. Ganin be farka ba yasa ta kwantowa jikinsa ta zira halshenta cikin kunnensa. Still be motsa ba amman fuskarsa da murmushi alamar idonsa biyu kenan.

Hannu tasa ta matse masa hancin iya ƙarfinta, sai ya tashi ba shiri yana kallonta.

“K.e...”

Maganarsa ta maƙale lokacin da yayi arba da rigar bachinta dake buɗe. Rabon da ta masa irin haka har ya manta, Kullum sai dai ya haɗe mata yawu, yau ma yasan haka ne tun da jinin har yanzu be tsaya mata ba. Hannu ya kai ya laƙamo wuyanta.

“Let us enjoy ourselves...”

“No way, yara suna waje suna jiran ka”

Ya dafe kansa.

“Ya Subhanallah, gaskiya I'm tired of driving them to school”

Ta wara ido

“Then teach me how to drive!”

“No, ba zan bari ki yi driving ba, wani zai ganemin wannan kyakkyawar fuskar ba, sai dai na nemo direbe, idan kin san inda zamunsamu direba mai natsuwa ki nemo mana”

Ya yaye bedsheet ɗin dake samansa yaja kumatunta, ya sauka saman gadon ya shiga bathroom. Bakinsa ya wanke da fuskarsa sannan ya fito. Tsaye ya same ta jikin bathroom ɗin tana jiransa.
Ya ɗan risina kaɗan yayi mata kiss a baki.

“My Happiness”

Ta moɗe bakin tana hararsa irin na ma'auratan nan masu cike da shauƙin so.

“Ni kike harara?”

Ya kama kunnenta

“Ouuuch Doc it hurt”

Yana janye hannunsa ita tayi masa yadda yayi mata, ta fito falo da gudu shima ya biyota yana murmushi.

Ganin Asmee yasa dik suka tsaya cak, musamman ita dake ƙoƙarin gyara rigarta.
Be ce da ita komai ba, har sai da ita tabfara gaishe shi sannan ya amsa ya nufi ƙofar fita.
Kalsoom kuma ta koma ta ɗauki hijab tasa sannan ta fito falon cike da mamakin sammakon da Asmee ta yi musu haka kamar mai biyar bashi.

Ita kanta taji kunyar kanta, ga kuma baƙinciki ganin da tayi suna cikin walwala, dan tana taya ƙawarta kishi ne.

“Na doko muku sammako, kuna sha'aninku”

Kalsoom ta yi dariya.

“A'a nace dai Allah yasa ba bashin ki muka ci ba”

“A'a wallahi an kwana biyu ban zo ba shine nace bari na leƙo ki ban sirrin da kika bawa mijin ki ya kori Rashida”

Kalsoom ta rufe baki

“A'a sirri kuma? Ai duk wanda kika ga ta bar gidan mijinta inda akan rashin ladabi da biyayya ne to ita ce ta fitar da kan ta”

“Hmmm ba son ba mu sirrin dai ko, kin ga nima daman yara na kai scul shine nace bari na leƙo na gan ki”

“Aiko kin kyauta, an kwana biyu a a gaisa ba”

“To ai ƙara ni ke ba ko zuwa kike ba”

“Ba ya bari ne, cewa yake baya son ina yawan fita”

“Aikam baya son ki yi nisa da shi, kin ga bari na tashi na wuce sai kin zo”

Har gurin motarsa Kalsoom ta raka ta tana bata haƙurin rashin zuwa da ba ta yi ba, da kuma cewar zata zo idan Hilal ya barta.

ASIM POV.

Ba laifi yau kan yayi wanka ya shirya kansa, ko dan yana jumma'ah ne oho, da wanka ma be dame shi sai dai yayi kanta karya ya fita idan fita ta kama shi.
Bayan sun sauko daga sallah jumma'ah ya nufi gurin aikinsa yana mai jin haushin aikin nasa ace kullum sai ya yi zuga sannan ya samu ƴan kuɗin kashewa shi wannan aikin dik ya takura masa, sai jan tsaki yake yana maganganu shi kaɗai.

Tun daga nesa yake kallon wata makekiyar mota data faka gefen gurin da suke aiki, yana ayyanata a cikin jerin motocin da zai siya idan yayi kuɗi, dan kyawon motar ya ɗauki hankalinsa sosai.

Yana buɗe shagon da suke aikin, mai motar ta zoƙe gilashin motarta tana masa sallama.

“Assalamu alaikum samari”

‘Tab ashe ma mace ce’

Ya faɗa a ransa, a fili kuma sai ya amsa mata baki har kunne.

“Wa'alaikissalam Hajiya ina wuni?”

“Lafiya ƙalau, dan Allah masu aikin nan gurin nake nema za a gyara min gate ɗina ne”

Ta faɗa cikin yauƙi da rangwaɗa kamar ba babbar mace ba.

“Mu ne ai muke aikin Hajiya, ina gate ɗin na ki yake?”

“Kai ...?!”

Ta faɗa tana nunasa da hannunta, mamaki ne ya isheta, yanzu tsalelen saurayi kamar wannan ace aikin ƙira yake, dubi ko shigarsa fa.

“Okay ga kt na idan kun tashi aikin sai kuje gida ku yi min, gate ɗin be ɓalle bane duka rabi ne za'a gyara min”

Ta miƙa nasa katin. Yasa hannu biyu ya karɓa cikin girmamawa kamar wata uwarsa.

“To Hajiya da zarar abokan aikina sun iso zamu je muyi aikin, sai dai baki bamu time ba”

“Ga number waya na nan a jiki kamin ku zo sai ku kira ni”

“To Hajiya za mu zo inshallah”

Ya miƙa masa 5k

“Ga wannan asha ruwa”

Yayi taku tare da nuna kamar ba zai karɓa ba.

“A'a Hajiya ki bar shi”

“Bana mai da kuɗi idan ya fito jakana, so ka karɓa kawai idan ma watsarwa za kayi sai ka watsar”

Yasa hannu ya karɓa yana mata godiya. Ita kuma ta tashi motarta ta kama hanya. Sai da ta wuce ya kalli jikinsa.

“Ita kan ta ta ga ban yi mata kama da talaka ba, wallahi ni babban mutum ne”

Ya juya ya cigaba da buɗe shagon farinciki fal a ransa.

RASHIDA POV.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye tun lokacin da Asmee ta labarta mata irin rayuwar jindaɗin da Kalsoom take da Hilal. Kenan ita sun manta da duniyarta? Hilal ya manta labarinta?

“Ina ba za'a shafe ni a tarihim rayuwarsa, ba zai rayu da wata ba sai ni, wata bata isa ta mallake min miji ba. Amman malamin nan ko dai yaudara yake ne? Dan me zai ce min magani yayi alhalin be yi ba”

Tayi shiru tana nazari, wata ƙila ita ma Kalsoom tana shige-shige shiyasa ta shafe ta a zuciyar Hilal gaba ɗaya. Daman idan kana yin abu gani kake kowa ma haka yake.
Wayarta ta janyo ta kira lamanin dan bata jin zuwa can inda yake a yau tun da ko aikin dake gabanta bata gama ba ma, balle ta yi tunanin fita, kuma tasan ko ta fita kamin taje ta dawo dare yayi sosai.

Kiran farko be ɗauka ba, haka na biyu zuwa na uku, amman bata sarara masa ba, har sai da ta jera masa kira kusan 10+ sai da yayi picking sannan hankalinta ya kwanta.

Sama-sama ta gaisa ta shi sai ta koro masa da bayaninsa

“Ina zuwa bari na binciki ƙasa”

Jimmm yayo shiru na ɗan lokaci sannan ya yi gyaran murya yace

“Lallai wannan matar ta sha gaban ki, ta fiki shiga bokaye, shiyasa wannan aikin be yi wani dogon tasiri a gareta ba”

“Kana nufin aikin be kamata ba?”

“Ya kamata amman yana ƙoƙarin fita jikinta”

“Amman idan har ya kamata ai dole Hilal.zai damu, dan bashi da wata mata sai ita kuma har yanzu ban ji ance sun samu saɓani ba”

“Amman ƙasa ta nuna mana an samu tsaɓani, sai dai idan kece baki sani ba”

“Yanzu malam miye abun yi?”

“Abu ɗaya ya kamata daman na faɗa miki, idan wannan be yi ba sai na biyu zuwa na uku, dole ne mu haukatata idan kuma be yi ba sai mu yi mata halbin kasko”

Ta rufe baki. Rashin imaninta be kai can ba.

“Malam babu wata hanyar ne?”

“Gaskiya wannan ce kawai mafita indai kina son mijin ki, idan ta bar gida sai ki samo sperm mu hada miki wanda Mijinki zai maida ke gidan sa dan dole”

“Zan yi tunani a kai”

“To yayi kyau”

Ta aje wayar tana busar da iskar bakinta.

NAMRA POV.

Yau kam basu fara karatun da wuri ba, hakan yasa har suka wuce goma na dare basu tashi ba. Amman shigowar Asim yasa ta yi addu'ah ta sallami ɗaliban nata da mafi yawansu matan aure ne.
Har gobe ba zata daina girmama Asim ba, tana bashi haƙƙinsa a matsayinsa na mijinta, dan ta karanta ta gani, ta san irin girman da miji yake da shi ga matarsa, ita dai kam ta kan yi ƙoƙarin ganin ta bashi dukanin haƙƙinsa dan tasan ko mutuwa tayi sai dai idan shine ya cuce acan Allah ya yi musu hisabi.
Chapter 73 · 0% Book details