← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 173

Sashe 96

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya shiga cikin gidan ya gaishe da mahaifansa, matan sarki sannan ya wuce faɗar mai-martaba. Be same shi a faɗar ba, hakan ya tabbatar masa da yana can turakarsa yana hutawa, tun da yaga motocinsa a waje balle yayi tunanin ko ya fita. Ta faɗar ya bi ya shiga turakar Mai-Martaba, a falon farko ya same shi zaune yana duba air conditioner da ake kan saka masa. Faɗawan na ganin Abdool duk suka faɗi suna ɗiban gaisuwa, shi dai hannu kawai ya ɗaga musu dan baya son irin gaisuwar nan da suke masa, ya fi gane a tsara masa ko a maƙe idan an ganshi. Da murmushi ya zube gaban mahaifinsa yana ɗiban gaisuwa.
Kallonsa Mai-Martaba yake da mamakin zuwan ba zata ta, sai kuma ya kai mafeshin Peacock dake hannunsa ya shafi ka ɗansa da shi. He didn't say a word dan baya son magana da Abdool a gaban faɗawansa ko baboro, yafi son sai ya keɓance yadda zai dake da shi kamar ba ɗansa ba.
   Ko ba komai nuna tsantsar ƙaunar da kake wani daga cikin ƴaƴansa babban laifi ne kuma ya kan haddasa ƙiyayah, sai dai hakan be hana familynsa depending ya fi son Abdool da kowa ba, dan abu ne da ko ya ɓoye sai dai ya ɓoye mai yawan ka buɗe kaɗan.

Yana unƙurawa zai miƙe tsaye sai faɗawansa suka zo da sauri suka tara rigunansu, suna masa kirari har ya miƙe tsaye sannan suka rufa masa baya suna masa fita.
   Hannu kawai ya ɗaga musu suka fahimci baya buƙatar su raka shi har can, sai kawai suka juyo gurin Abdool suna masa nasa kirarin. Be tsaya jinsun ba ma balle ya nuna masu jindaɗin abunda suke masa sai kawai ya bi bayan Mai-Martaba hannayensa laƙƙame a baya yana tafi guda-guda kamar mai takewa President baya.

Sai da suka wuce falon biyu da na uku, suka wuce garden ɗin Mai-martaba sannan Mai Martaba ya ƙarasa a wata ƴar ƙaramar rumfa mai kyau da ɗaukar hankali ya zauna, shi kuma Abdool ya zauna ƙasa complain ɗin kiraren da suke masa.
  Ɗan murmushi Mai-Martaba yayi irin na na manyan sarakuna, yana kallon ɗan nasa cikin farinciki da jindaɗi.

“Wata rana kai Sarki Abdool, irin wannan kalaman be kamata yana fita daga bakin ka ba”

“Haba Mai -Martaba ta ya zan zama sarki bayan Ina da yaya? Kuma ni wannan sarautar sam ba burgeni take ba”

Mai-martaba ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora akan ɗayar yana murmushin ƙasaita.

“Har gobe Babana baka san Sarauta ba, saboda ka guje mu a lokacin daya kamata acr ka zauna ka karanci komai na gidan nan, baka san jidaɗin sarauta ba, shiyasa kake wannan furuci, na kan lura da yanayin ka sam baka sakin jiki a harkokin sarautar gidan nan, balle na wani gurin, abu kake kamar ba ɗan sarki ba, ai yanzu kuɗi da milki su ake ɗubi abawa mutum sarauta balle kuma kai da ka cancanta dan kana da natsuwa da hankali ga tarbiya”

“Mai martaba wannan sarautar fa dai ku. Ina fatar na samu sarki cikin ƙoshin lafiya”

“Yareema ya samu Mai Martaba cikin ƙoshin lafiya da walwala, ya aka yi ka yi mana zuwan ba zata? Gashi ba ko wane abinci kake so ba balle na ce a ɗibo maka”

“Na samu hutu ne jiya, shiyasa na dawo gida as surprise kasan turawa sun ce surprise is better than disappointed”

“Aiko kayi tsara kan gaɓa, daman akwai ɗaurin auren Abubakar Saturday, daman kai na ke son ka walkice ni, kuma daman can Abubakar ɗin nan abokin ka ne”

Abdool ya shafa kai

“Wai har auren ya tashi ne ? Kwanaki wani friend na mu yake ce min an kai masa kaya”

“Kai ma ai naka yana kusa, mun soma duba maka na dangi kamin mu fita waje, tun ka bamu zaɓi”

Ko be tambaya ba yasan Ummi ce tayi wannan maganar, on behalf of him. Ɗan murmushi yayi ya ce

“Ina za'ayi ɗaurin auren?”

“Zariya, ƴar sakin Zazzauce zai aura, Saturday nan”

“Okay zan je inshallah”

“Ba wai zaka je ɗin ba, ka tabbatar an ganka, zan haɗa tawagar da za kuje daga nan, kuma zaka je ne cikin shigar sarauta, sadauki zai naɗa maka rawani idan kunje can”

Ƙure yayi ma Mai martaba da ido yana kallonsa. Mai martaba yasan waye ɗansa kuma ya san kallon da yake masa.

“Kar ma ka soma, kai shikenan baka son shiga mutane? Ƴaƴan saraku irinka amman baka son shiga cikin su? Rabon ka da rawani tun a hawan salla, ni wannan rayuwar ta ka bata min Yareema, wasu ma basu kao darajarka ba basu kai muƙamin ka ba, sannan sarautar ta su ƙarama ce amman su yi ta tinƙaho suna nuna isa balle ka!”

Yayi tsuntsun da kai, yana murmushi, dan yasan Mai Martaba ya kamo tasharsa.

“Ai ban ce komai ba Mai martaba”

“Na san zaka ce ɗin ne. Tashi ga ruwa can ɗauko ka sha, kar kaje ka ce wa uwarka baka ci komai gidan Mai Martaba ba”

Ya tashi yana murmushi ya nufi wani ɓangare na gurin da aka jera freezer biyar a gurin dan shan ruwa kawai da lemu.

Be bar gidan ba sai da Mai- Martaba yasa aka daba masa wani abu ya ci. Bayan yayi  la'asar, yayi ma Mai Martaba sallama sannan ya nufo gida gurin Umminsa.
Gaisuwar ban girma da tadabi sojojin gida suka masa suna masa maraba da zuwa.
   Har zai wuce part ɗinsa sai kuma yaji ba zai iya ba har sai ya saka mahaifiyarsa a ido. Da far'ah da zumuɗi ya nufi part ɗinta.

  Tun daga yanayin yadda yaga falon zuciyarsa ta raya masa Ummi bata cikin gidan. Sai ya ɗauki remote ya kashe plasma ɗake falon sannan ya nufi ɗakin Ummi dan tabbatarwa. Haleema ya gani kwance saman gado Amira kuma na gurin tufafinta tana gyarawa.

“What nonsense is this?”

Ya faɗa a tsawaci. Daga Haleema har Amira zuyowa suka yi suka kalleshi dan babu wanda yasan da shigowarsa. Da sauri Amira ta zube ƙasa tana miƙa masa gaisuwa zuciya na bugawa da ƙarfi, haka kawai ta samu kanta tana mai tsantsar kunyarsa.

Be amsa gaisuwar ba sai kawai ya watsawa Haleema harara, ita kaɗai tasan abunda Hararar tasa take nufi sai ta sauka saman gadon da sauri ta kama hannu Amira suka fice.

Sai ya ƙofar ɗakin ya rufe da key, ya cire keys ɗin ya nufi part ɗinsa da shi. Yana shiga ya cire tufafin jikinsa ya ɗaura tawul ya shiga Bathroom. 

Ya ɗauki kusan mintuna arba'in a banɗakin yana cuɗa jikinsa kamar wanda zai canja fatarsa. Bayan ya gama wanka ya ƙarasa gaban madubi yana ƙara gyara  gemensa da babu komai a gurin.

Sallamar da yaji ana ta dokawa ne yasa ya wanke fuskarsa ya fito. Ya nufo falonsa. Amira ya samu tsaye a gurin hannunta riƙe da cup ɗayan hannun kuma riƙe da wasu dinner set an rufe su da ɗayansu.
Tana kallonsa gabanta yayi mummunan faɗuwa, bodybuilding ɗinsa ne ya tashi hankalinta, yadda aka tsara jikinsa da faffanɗan ƙirjinsa, ga fararen idon nan kamar an watsa masa madara tabbas shine irin mijin da take so.

“How may i help you?”

Ya tambaya ganin yadda take kallonsa kamar bata san da shi a gurin ba. Sai da ta gyara tsayuwarta gudun faɗuwa sannan ta miƙa masa duka abunda yake hannunsa.

“Coffee and fruits, tuwo ne aka yi kuma Haleema tace ba ka son tuwo, shine na haɗa maka wannan”

“Thanks i'm not a coffee drinker”

Fruits ɗin kawai ya karɓa ya aje saman kujera ya bar mata coffee. Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleta

“By the way bana son texts ɗin nan da kike tura min, ki daina please”

Kai ta ɗaga masa idonta na son cika da hawaye.

“Note”

“You may go”

“Thank you”

Jikin sanyi jiki ta juya ta fice, hawaye na bin fuskarta. A yadda ta fahimta kamar bata burge Abdool kwata-kwata irin ɗan sakewar nan ma baya mata shi.

Haleema na gani hawayenta tasan ba lafiya ba, daman kuma tasan za'a rina indai Abdool ne.

“Wani abun ya ce miki ne?”

“A'a kawai ina ganin kamar bana gabansa, kwata-kwata bana burgeshi”

“Daman ai shi namiji ba zai so ki lokaci ɗaya ba, komai a sannu yake zuwa, ni yanzu abinda nake so ki yi ta yin abinda zai ja hankalinsa gareki, har shi da kansa ya furta yana son ki, dan naji Ummi na maganar wai Mahaifinsa yayi masa mata”

Amira ta kalleta da sauri.

“Da gaske?”

“Wallahi amman kin ga idan shi da kansa ya ce ke yake so kin ga dole ki a ƙyale”

“Amman me kike ganin zai sa ya so ni?”

“Irin wannan ladabin da kike cigaba, kuma ki riƙa shige masa ki riƙa haɗa masa abu ko da be buƙata ba, sannan idan da hali ki koma gidanku, saboda zama a gaban iyaye yana da muhimmanci, sosai Ummi ma da kanta zata fi ganin darajarki idan kina zaune a gidan ku”

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah ita kanta tana son komawa a gurin iyayenta amman ba hali bata iyawa, bata san yadda zata yi ba.

“Zan yi ƙoƙarin yin hakan inshallah”

“Allah ya taimaka nima ina son ki auri Yaya Wallahi”

Amira tayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwarta.

*ASIM POV.*

Tun ranar daya bar gidan Namra be sake leƙawa ba, duk jin yake ya tsane ta ma, daman can baya akan cilas ne yake zaune da ita yanzu kuma yaji zai iya auren wata. Sannan yana ganin haihuwa a yanzu zata iya kawo masa matsala, dan haka shi be shirya haihuwa a yanzu ba.

Yau ma kamar kullum da tea da kwai yayi breakfast, sai da ys ci yayi nas sannan ya tashi yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin wasu tufafin masu kyau da tsada ya shiga sashen uwar ɗakinsa dan gaisheta.
Be same ta a falo ba, sai kawai ya wuce har ƙurƴar ɗakinta dan ta daɗe da bashi damar hakan matuƙar ba mutanr ya tarar a gidan ba. Bedsheet ya tarar tana gyara jikinta sanye da kayan bachi.

Yana ganinsa ta zauna saman gadon tana murnushi.

“Asim an tashi?”

“Eh Hajiya ina kwana?”

“Lafiya ƙalau Alhamdullah, ka yi kyau mashallah”
Chapter 96 · 0% Book details