← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 173

Sashe 146

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba komai daman ni dai burina na ganka, kuma na ganka, take care of yourself”

“I will my love, ke ma ki kula min da kan ki, bari ma saukeki gida ko?”

“No da mota na na zo”

Sai da yaje ya biya kuɗi sannan suka jero suka fito tare, har gurin motarta ya rakata ta kama hannunta ya riƙa ya ɗan murza, yana mai jin tausayinta a ransa, sai dai kuma idan ta tuna Mama sai yaji babu wani tausayi a zuciyarsa. Sai da ta kama hanya sannan ya nufi motarsa ya shiga.

SORRY MY FAN'S🙏
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *84*

*Shafin na ku ne ƴan ZAGON ƘASA CONVERSATION I HEART YOU ALL*

Wani irin taku Abdallah yake mai ɗaukar hankali da burge duk wata mace mai kallonsa. Ko da wasa be kalli gurin da Lamido yake ba, yayi kamar ma be san da shi a gurin ba.

“Surprise...”

Namra ta faɗa tana tare hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata. Ɗaya daga cikin murmushinsa mai tsadar nan ya ɗauka ya miƙa mata, yana kallonta cike da shauƙi dan ta masa kyau sosai.

“Surprise is better than disappointed, haka naji turawa na faɗa, faɗa min wanda ya saka idon nan nawa kumbura, na hukuntasa”

Ya faɗa dai-dai lokacin da ya ɗoro ƙafarsa saman matattakar balcony ɗin da suke tsaye. Kallon mamaki na musamman Namra ta yi masa.

“Idon ka ko nawa?”

“Idon ki ai nawa ne”

Ya bata amsa kai tsaye, and yana acting like akwai wani abu a tsakaninsu. Saurin kawar da maganar tare da cewa.

“Meet my Brother. Lamido meet Abdallah”

Lamido ya danne abunda ke zuciyarsa, na kalaman da ya ji Abdallah yayi a yanzu, ya miƙa masa hannu.

“Am Aliyu Adam Lamido”

Wani kallo Abdallah ya watsa masa irin like sai a yanzu ma ya lura da shi, sai kuma ya tsaya kallon hannun kamar mai karantar abu a jikin hannun. Sai kawai ya zuba hannayensa duka biyu a aljihunsa yana ɗaga masa.

“Nice to meet you Lamido”

Ɗan murmushin ƙarfin hali Lamido yayi ya janye hannunsa, abunda be yi ma Namra daɗi ba.

“Baka ga ne shi ba ne? Lamido ne fa wanda...”

“Na gane shi *ABNAM* let talk something important”

New name ɗin da Abdool ya bata ya bata mamaki yana abu kamar su ɗin daman can masoyana, a ɗayan ɓangaren kuma bata jidaɗin kalmarsa ta ƙarshe da ya furta akan Lamido ba. Sai kawai ta kalli Lamido ta ce

“Zan kawo maka keys ɗin kaje ka duba”

Kai kawai ya iya ɗaga mata, fuskarsa na nuna rashin jindaɗin da ke zuciyarsa. Saukowa ta yi saman balcony ɗin ita da Abdool suka nufi ɓangare Abbah gurin da yake sauke baƙinsa.

“Faɗa abunda yasa ki kuka mana Abnan”

“Abun farinciki ne da tsoro da mamaki a lokaci ɗaya”

“Kamar...”

Ajiyar zuciyarta ta sauke ta kai hannu ta tura ƙofar falon.

“Bismillah”

“Thank you”

Ya faɗa sannan ya saka ƙafafunsa cikin falon, sai da ya shiga sannan ita ta shiga ta maida ƙofar ta rufe, sai ta nufi wata ƙofar da zata sadata da part Anty Amarya.

Bata samu kowa a falon Anty ba, sai kawai ta nufi ɗakinta dan labarta mata zuwan Abdallah nan ma sai ta samu bata nan, ɗakin Aisha ta shiga.

“Ke Anty ta shigo nan?”

Ko kallonta Aisha bata yi hankalinta yana kan computer ta, ta kaɗa mata biro alamar no. Namra ta janyo ƙofar ɗakin, ta nufi freezer tana ta tunanin abunda zata haɗa masa, ya zo mata a bazata, bata shirya masa komai ba, Lamido ma bata masa komai ba, su biyu ɗin sun zame mata ƴan uwa babu na wulaƙantawa a cikinsu. Hannu tasa ta dafe kanta kamin ta kai hannu ta buɗe firiza ta ɗauko fruits ta haɗa masa fruit salad, sannan ta haɗa tea da coffee ko wane one cup sai kuma ta ɗauki ƙaton ture ta ɗora kayan sama. Wani tunani ya zo mata na ta canja tufafin da ke jikinta, kar kuma ya ɗauka dan ta ganshi ta canja kaya he may think otherwise. Kai ta girgiza sai kawai ta ɗauki turen ta nufi part ɗin Abbah.

Zaune ta same shi ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana kallon tv, sam ta manta ma bata kunna masa tv ba. Ta dire turen gabansa tana faɗin.

“Na manta ban kunna maka kallon ba”

“Ai na kunna ni ba baƙo ba ne”

Yayi maganar cikin wata kalar murya.

“Ka zo unexpected, ba a shirya maka komai ba”

Ta faɗa tana ɗora fruit salad ɗin da Drink a saman wani ƙaramin tebur da ta janyo ta aje gabansa.

“Tea or coffee?”

Ya daɗe yana kallon gashin kanta da ya buɗe kamar ba zai ce komai ba.

“Da rana”

“Ban san abunda zan kawo maka ba ne... Wai ka ɗan ci kamin na girka maka abinci”

Ta faɗa kamar wacce ta ji kunya.

“Ban zo dan ki girka min komai ba, i just come to see you, kuma na gan ki hankalina ya kwanta”

Ya koma saman kujera ta zauna tana murmushi. Ya sauko da ƙafafunsa ya ɗauki fruit salad ɗin ya fara sha, still idonsa na kan ta yace.

“Ba ni labari”

“Kamar na me...?”

“Komai da komai”

“Nothing new”

“Seriously! What bought Lamido here?”

“Oh... He's my new driver”

“Driver...?”

“Yep Abbah ya kawo min shi ɗazu, zan fara zuwa scul Monday shine Abbah ya samo min sabon direba”

“Nice”

Ya faɗa kamar ba komai. Wayarsa ya fiddo ya kashe flash camera sannan ya shiga ɗaukarta hoto ba tare da ta sani ba, dan yasan idan har yace zai ɗauke hoto ba zata bari ba, kuma sisters nasa da Ummi sun dame shi akan suna son ganinta.
Haka suka ɗauki dogon lokaci a falon ita da shi babu wanda ya iya sake cewa ɗan'uwansa wani abu, kowa da abunda yake tunani, Namra gaba ɗaya hankalinta ya tafi akan halin da Uzair yake ciki, shi kuma hankalinsa ya tafi gurin Lamido dan yana ganin kamar zai masa zagon ƙasa ne, taya zai zauna ya zuba mata ido shi ya riƙa driving ɗinta scul ya sace zuciyarsa shi ya bar shi a nan.

“Zamu iya gaisawa da Abbah?”

“Yeah Yeah yes, bari na kira shi”

Ya miƙe tsaye tana taɓa kanta dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi gurin wacan tunanin nata.

Ƙofar da zata sadata da ɗayan falon Abbah ta nufa, tana tura ƙofar falon ta jiyo muryar Abbah sai ruwan bala'i yake, shesshekar kuka na tashi, cike da faɗuwa gaba ta shiga ɗakin Abbah, sai ta samu Anty Amarya da Hajiya Barau zaune ƙasan carpet ko wannensu na kuka. Hajiya Barau ta rashi tana kuka ta fice daga falon, Anty Amarya ta kama ƙafafun Abbah ta riƙe tana kuka.

“Dan Allah karka aikata abunda zaka dawo kana nadama a lokacin da bata da amfani, dukanninmu ƴan'adam ne kuma ajizai masu yawan laifi da kuskure”

“Idan baki daina saka min baki a lamarin gidana ba, ke ma zaki haɗu da ɓacin rai na...”

Juyawa Namra ta yi ta koma jikinta a sanyaye, ba tare da ta kalleshi ba tace.

“Maybe idan ka sake dawowa zaku gaisa”

“Why...?”

“Abbah is not in the mood now”

Hawayen dake idonsa ya zubo muryarta kuma ya soma rawa alamar kuka yana tare da ita. Da sauri Abdool ya taso ya nufo inda take tsaye.

“Faɗa min Abnam, minene? You can't hide the truth”

“Mutumen da na taɓa baka labarin yace ƴana so na kuma ɗan luwaɗi ne, yanzu haka yana asibiti cikin mawuyancin hali, kuma ɗazu ya tara mu ya faɗi gaskiyar duk abunda yayi, ciki har da asirin da ya haɗa kai da Aminiyata Amira yayi min akan na gudu na bar gida, sai gashi asirin be kama ni sai ya kama Amirar Amiyar tawa ita ta gudu ta bar gidansu bata dawo ba sai ranar da na dawo garin nan...”

Ta ƙarasa cikin kuka.

‘Amira...’

Ya maimaita sunan a zuciyarsa, yana kallon zubar hawayen gimbiyarsa.

“Wannan ba abun kuka ba ne abun dariya ne da murna, amman komai daren daɗewa sai gaskiya ta bayyana kuma mai haƙuri mawadaci”

“Aminiyata ce fa, ace ta min irin wannan aikin ai dole na yi kuka, babu yadda ƴan'uwana ba su yi ba akan na rabu da ita amman na ƙi”

“Kin share hawayen ki, shiga ciki ki canja kamin na dawo, zan nuna miki wani abu”

“A'a Abbah ba zai bari ba”

“Zai bari just go”

Be jira amsarta ba, ya juya ya fice yana danna wayarsa.

MANAGE IT PLEASE 🙏
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *83*

Cikin nishaɗi da walwalah ta isa gida, tana faka Motarta Hajiya Sadiya ta fito hankalinta a tashe ta nufi inda take tsaye ta riƙa ta.

“Daga ina kike Nabila?”

“Mun ɗan fita ne da Asim, Lafiya”

“Na kira wayarki a kashe, ina kika je ne?”

“Munje cin abinci ne”

“Me kuka ci? Talk to me”

Ta riƙa fuskarta tana girgizawa. Itakam mamaki duk ya cika ta tashin hankalin da ta gani a fuskar Mahaifiyarta ta ruɗa ta.

“Miyasa kika tambaya?”

Hannunta ta riƙa ta jata suka nufi cikin falon sannan ta zaunar da ita saman kujera itama ta zauna fuskarta da damuwa ta ce.

“Ina tsoron kar ya baki wani abun ne, kin san mutane ba abun yarda ba ne”

“Hmmm Momi Asim ba irin mutanen da kike tunani ba ne, yana da kirki sosai”

“Ba daga nan take ba, Nabila ina fatar be baki Apple kin ci ba?”

“Ya bani apple kam kuma shi ma ya ci”

Ta dafa kanta ta sauko ƙasa ta riƙa hannayen Nably tana kuka.

“Wane irin apple ya ba ki? Na shiga uku na lalace, ya kai ki ya baro Nabila shi kenan, tawa ta ƙare”

“Momi me ke damunki ne?”

Kuka ta yi sosai har hankalin Nably ta tashi sannan ta labarta mata abunda ta shekara da shekaru tana aikatawa. Kuka Nabila ta saka zuciyarta ta cika da baƙinciki.

“Asim yayi daidai idan har da gaske ya bani apple ɗin na ci, na cancanci mutuwa a yanzu, ke ba uwa ba ce Momi, kin shirya kashe wata saboda tsiratar da ƴarki, kin shirya aikata komai saboda duniyarki”
Chapter 146 · 0% Book details