← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 173

Sashe 88

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya kwana da nishaɗin da be san ta ina yake xo masa ba balle dalilinsa ba. Shi dai baya iya faɗin abunda ɗaya ta san ya shi ne silar farincikinsa tun jiya har zuwa yau.
Yau zai koma abuja ko ba komai dole yayi sammakon tashi, balle kuma Namra tace masa da safe ake samun mijinta.

Be tsaya wani karin kirki ba, dan a tunaninsa kamar idan ya daɗe ba zai samu mijin nata ba
Ko da bakwai tayi yana ƙofar gidan, sai dai be shiga ba sai da ya buga gate ɗin, ganin babu wanda ya fito yasa ya tura gate ɗin ya shiga cikin, black suit ne jikinsa yayi mugun masa kyau kamar balarabe.

Nesa da bq ɗin ya tsaya yayi sallama cikin muryarsa mai sanyin da daɗin saurora, da ace ma'aikatan sa zasu ganshi a yanzu da sun rantse wannan muryar arota yayi.
Asim ne ya fara fitowa yana samawa, daman tun da yaji sallamar ya raya a ransa cewar masu gidan ne. Sai dai yayi mamakin ganin mutuen duk da be san sunansa amman yasan shi ne ya biyo Namra asibiti. Ƙarasowa Asim ya yi yana masa wani kallo da shi kaɗai ya san fassararsa.

Hannu Abdool ya miƙa masa.

“Sunana Abdallah Ahmad Mai-doki, na zo ne a kan maganar wannan gidan, matarka na ciki?”

Be masa hannun nasa ba sai kawai ya ce

“Eh miye haɗin ka da matata?”

Abdool ya ɗan wara ido tare da taɓe baki haɗi da ɗaga kafaɗu.

“Nothing, jiya na zo akan maganar gidan nan ne sai take roƙo na akan dan Allah na taimaka na bar su a bq su zauna dan basu da gurin zama, so shiyasa na yi ƙoƙarin mai da gidan mallakin ku gaba ɗaya”

Asim ya washe baki, tare da miƙa masa hannu

“Mashallah Allah ya saka maka da alheri”

Daga nan da yake ya ƙwalama Namra kira. Sai gata ta fito cikin hijabi, kamin ta ƙaraso gurin asim fuskar Abdool kawai yake kallo ya gani idan ya kalli Namra. Babu abinda yake rayawa a zuciyarsa sai munafurcin da Namra take masa, wai shi za a maida wawa ya kawo mata gida ya ce ya basu dan tasan idan ya bata ita kaɗai dole za a gane abunda yake tsakanin su. A fili kuma murmushi yake kamar gaske yana kallon Namra da take gaishe da Abdool. Kallo ɗaya Abdool yayi mata ya ɗauke kai ya ciro takardar dake aljihunsa ya miƙawa Asim

“Daga yau wannan gidan ya zama na ku, ba zaku sake biyan kuɗin haya ba balle ace ku tashi”

Hannu biyu Asim yasa ya riƙe hannunsa yana masa godiya kamar zai shige cikinsa. Namra kan mamaki ya hana ta tace komai balle har ta yi godiya.
Sai Asim ne yake ta zuba masa godiya yana murna baka da zuci dan yasan shi zai mori gidan ba Namra ba.

“Mun gode sosai Allah ƙara arziki ya ƙara wadata jazakallahu khairan”

“Amin”

Ya faɗa sannan ya juya ya nufi gate, yana ƙara kallon gidan. Har cikin ransa yaji addu'ar da Namra tayi masa. Sai da ya wuce sannan Asim ya juyo ya shigo gida zuciyarsa cike da zarge zarge. Sam be nunawa Namra ya gane shi ba, sai kawai ya nuna mata ya fi kowa farinciki abinda yayi musu duk da zucin ma farinciki ne dan yasam shine zai ci amfanin abun.

“Kin gani ko yanzu kan alheri ya fara shigo mu, yanzu duk wannan gidan na mu ne kai Alhamdulillah Allah”

Namra tayi murmushi dan ita tun ɗazu mamaki take da tunanin dalili kyautar gidan da Abdool yayi mata, bayan acan baya ya taɓa binta yace yana sonta, ko dai akwai biyu a kyautar ne? Bata bar Asim ya gane abunda yake ranta ba, gudun karya zargenta, ko kuma yayi wani tunanin na daban daman can ya taɓa zarginta.

Dumamen shimkafar da tayi ne ya zuba masa, ya ci sannan ta kai masa ruwan wanka yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin data wanke masa. Sannan ya fito waje ya ciro ɗari biyar ya miƙa mata.

“Gashi ayi cefane”

Hannu biyu tasa ta karɓa tana muryar yau mijinta yyi abun kai

“To Allah amfana”

“Amin sai na dawo”

“Allah ya tsare”

Ya nufi gate zuciyarsa cike da ƙunar cin amanar da Namra take masa, abun har ya fara wuce gurin har ana kai ga kyauta gida.

“Hmm Lallai ma wannan matar wai har ni za a rainawa hankali, bari na zama Asim ɗi na na ƙwarai ki ga yadda zan yi da ke, ku yi ta abun ku yanzu na ba ku dama”

Ya filin yake maganar ya miƙe hanyar data zata kai shii babban titi, sai dai hanyar gidan su Mardiya ce, da gangan ya bi dan ya ganta.
Ya ko yi nasarar angota da ɗaura gaba tana tsaye ƙofar gida tana ciniki a warwaro da mai tutu-rutu, ƙirjinta kawai yake kallo yana siffantawa kansa ita, har ta kawo kusa da inda take.

“Barka da safiya Asim”

“Yauwa barka Mardiya ya gida?”

“Lafiya ƙalau, ina Namra?”

Ya ɗan ƙara washe baki dan be yi tunanin zata kawo maganar Namra a yanzu ba.

“Tana nan ba kin guje mu ba”

“A ni na isa ku ne dai kuka guje ni”

Dariya yayi ya ƙarasa gaban mai ɗan kunnen yana kallon kayan

“Me aka siya?”

“A warwaro ne da ɗan kunne”

Babu ko kunya take masa magana kamar bata sam ɗaura gaba ne a jikinta ba. 1k ya ciro ya miƙa mata

“To a siya da yawa”

Hannu tasa ta karɓa.

“Na gode sosai Allah kawo wa su, ayi irin mu huɗu”

Dariya yyi kamar ba shi ba ya amsa da amin yana tsayardar mai okada. Sai da ya hau sannan ya faɗa masa inda zai kai sa.
Hajiya Sadiya tayi mamakin ganinsa sosai dan a ƴan kwanakin daya ɗauka ta zata ko ba zai dawo ba ne, ruwa ta kawo masa da abinci, sai wani ƴauƙi take kamar ta ga mijinta. Shi kuma ya sake jikin sosai kamar gidansa, baya kallonta idan tana kallonsa ko taɓa gabansa sai ta bada baya yake kallonta.

“Baka buƙatar kwaso kayan ka ko wani abu, akwai komai da zaka buƙata a ɗakin da za a sauke ka, ni na ɗauka ma ba zaka dawo ba”

“Me zai hana? Mutum ya bar samu?”

Dariya...

“Aiko dai, ina kallon lokacin da kake ta ciwon nan kamar ba zaka tashi ba”

Gabansa ya faɗi dan be yi tunanin ko ta san shi ba, se dai be gama saƙe saƙensa ba ta cigaba.

“Lokacin da muƙa ɗauko ka daga asibitin Funtua zuwa nan katsina, lokacin kana cikin ciwo ba zaka gane ba, amman na san kana da mata ka ɓoye min ne kawai”

Ido cikin ido yake kallonta dan tantance abinda take faɗa.

“Ban gane ba”

“Hmmm Asim ko? Ni ce na ɗauko ka da mota na na kawo ka Asibitin katsina na biya kuɗin gado da magani, amman nasan ba zaka iya tunawa kancewar lokacin kana cikin ciwo”

“Eh...eh..ha...k...a..ne.... Ashe kin san ni”

“Na san ka nima farko ban gane ka ba sai daga bayan lokacin da nasa ayi min bincike akan ka”

“Bincike kuma?”

“Eh mana ai duk wanda xaka xauna da shi kana da bikatar sanin ko waye shi, gudun abinda zai je ya dawo amman miyasa kace min baka da mata bayan kana da ita?”

Ya ɗan sosa kansa yana cire hannunsa daga abincin daya fita ransa.

“Wallahi Hajiya naga kamar ba ki son mai matar ne shiyasa, ni kuma bana son na rasa wannan aiki na ki”

Tayi murmushin ƙasaita.

“Ba mai mata ne bana so ba, yadda nake son a min spending time ne nasan mai mata ba zai iya ba”

“Zan iya wallahi dan ni na fi ƙarfin matana na, duk abinda kike so zan miki”

“Hakan yana da kyau, namijin duniya irin ka na ke so”

Ya jidaɗi sosai.

“Anything for you Hajiya”

“Gobe aikin ka xai fara, yanzu idan ka gama, sai kaje gurin mai gadi ya nuna maka wasu abubuwan”

“Hajiya ai ni na gama ma”

“Ka daina kirana da Hajiya ka kira ni Sadiya na”

“Ai da nauyi sai dai ko nace Anty Sadiya”

Wata harara ta watsa masa.

“Na yi maka kama da Antyn ka ne?”

Kallonta yayi a zahiri kam tayi yi, dan wannan yasan ba sa'arsa bace sai dai kuma bata isa haihuwarsa ba.

“A'a Sunan ne ba zan biya faɗi a fili ba”

“To ka riƙa ce min Sadiya Babe, amman idam cikin mutane ne ka riƙa kirana da Hajiya na”

“To am gama na gode”

Har ya juya tace

“Kuma bana son sa ido, kar ka damu da baƙina ko ƴaƴan 'uwan da suke zuwa gidan nan kai dai kawai ka yi aikin ka”

“Inshallah ba zaki same ni mai tsaɓa uwarnin ki ba”

“Albashin ka 100k per month”

Da sauri ya kalleta fuskarsa ƙarara da mamaki, sai gashi kurfane ƙasa yana mata godiya.

“Allah ya ƙara miki arziki Allah yayi miki yadda kika min”

“Amin kai dai ka cigaba da biyayya kawai zaka iya samun fiye da haka ma”

“Inshallah”

“You can go, sai ya nuna ma ɗakinka da kuma aikin ka”

Ya juya ya fice yana jin wani irin nishaɗi da be taɓa jin irinsa sai yau.

*ABDOOL POV*

Ko da ya isa gida duka ƙanensa sun wuce scul Ummi ce kawai a dinning sai Amira suna karƴawa. Tun daga nesa Ummi ta hango nishaɗin dake fuskar ɗanta. Har ya ƙaraso kusa da su ya zauna a kujera daya saba zama.

“Ina ka je da safen nan haka?”

Be son maganar gaban Amira, sai kawai yayi murmushi ya ɗauki kofi ya soma haɗa ma kansa tea.

“Good Morning Yaya”

“How are you dear..”

_Dear_ taji kalmar har cikin ranta, shi kuma ya amsa mata ne da murmushi kuma ba tare da wata manufa ba.

“Ummi yau zan koma fa”

“Yeah i know i just want to know the secret of your smile?”

Shi kansa be san yana murmushi sai yanzu da Ummi ta yi magana. Yayi saurin kawar da murmushin

“Nothing”

Ya miƙe tsaye yana kallon agogon hannunsa.

“Around 9: za mu tashi”
Chapter 88 · 0% Book details