← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 173

Sashe 74

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe shida suke tashi daga gurin da yake aikin, amman baya dawowa gida sai goma ta gota na dare, zaman majalisa yake irin zaman nan da baya amfanar da komai sai zunubi da hassada, zaman zagin wane da wace, zaman matar wane tafi matar wane, wacce aure ya mutu wacce biyar maza take. Kusan ma shine yaro a cikin masu zaman majalisar dan duk sun girme shi dukansu magidanta ne.

Kicin-kicin ya shigo gidan baya ƙaunar kallon Namra, idan akwai wata maƙiyiyarsa yanzu a duniya to Namra ce. Ita kam idan sabo ta saba dan yanzu ba kasafai take ganin rahamar fuskarsa ba.
Tufafin jikinsa ya kwaɓe ya jefar saman katifar ya ɗauki wata guntuwar jalabiya ya saka yazo ya zauna tsakar ɗakin yana kallon kyanɗir ɗin dake hasken ɗakin

“Ina abinci na?”

Ko rufe baki be yi ba ta dire masa abincin gabansa da ruwan sha, sannan ta ɗauko mafeci tana masa fita, sai murmushi take tana masa fira dan kawar mata da ɓacin ran dake tare da shi. Har ya gama cin tuwon ya sha ruwa be kula taba balle ya tanka ta a firar da take.

Tsabar ƙazanta da rainin wayo cikin kwanon daya gama cin abinci ya wanke mata hannu. Ita kuma ta ɗauka ta kai waje ta aje. Sai gata ta dawo ɗakin da gudu jin wayarta na ringing.

Da murna ta ɗauka ganin number Anty daman haka take kullum kamar ba jiya tayi magana da ita ba, zaka rantse kace ta shekara ba ta yi magana da ita ba.

Bayan sun gaisa Anty take faɗa mata za a kawo lefen Maryam cikin weekend ɗin nan mai ƙarewa, ta kuma nuna mata tana son ta shigo ko dan kwana biyu da suka yi ba su ganta ba, kwanki babu yadda Anty ba tayi akan ta zo amman Namra ta nuna mata karta zo yanzu ta bari har gaba.

Da fargaba ta aje wayar dan tasan ba lallai bane Asim ya bar ta taje, amman a haka ta sake fuska tana faɗa masa Anty ce ta kira.

“Okay”

Kawai ya faɗa irin ina ruwan ɗin nan. Ya hau saman katifa ya kwanta yana mata wani kallo da ita kaɗai ta san kiran da yake mata.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *50*

AMIRA POV.

Har suka isa katsina babu abinda take tunani sai Abdool saƙe-saƙe kawai take a zuciyarta na yadda zata sace zuciyarsa da kuma iyalansa.
Babu abinda take annawa a zuciyarta sai sabuwar rayuwar da za ta shimfiɗa na kanta.

Duk irin yadda take misalta arzikin gidan su Abdool sai ya ci gaban tunaninta, ya sha banban da abinda take tsamani. Haka ta zaka kamar ba wacce ta fito daga garin Abuja ba. Idonta ya biɗe sosai lokacin da motar da take ciki ta kunna kai cikin gida.
Ga matakan tsaron daya shimfiɗa ma gidan kamar masaukin shigaban ƙasa. Part biyu ta gani a gidan sai dai part ɗin da suka sauka ya fi girma da tsaruwa, hakan ya tabbatar mata da wacan ɗin part ɗin Abbansa ne ko kuma nasa.
Tana fitowa motar idonta ya sauka kan wani ƙaton Garden dake gefen part ɗin, babu abinda kake ji sai sautin kukan tsuntsaye, ga wani swimming pool da tafi ɗaukar hankalin a hangen nata, daga ruwan swimming pool ɗin har itacen da suke gurin komai kore ne. Peacocks sai kai da kawo suke a bakin Garden ɗin.

“Let's go Madam”

Ɗaya daga cikin sojan da suke tarar a gurin ya faɗa yana nuna mata ƙatuwar ƙofar shiga falon, wacce ta kasance abun kallo, idan ba wanda ya sani ba sai kan rantse kace da zinari aka ƙerata.

A hankali ta cira ƙafarta ta fara takawa, zuwa gurin ƙofar dake kashe mata ido saboda kyawonta. Hannu ta kai zata buɗe ƙofar lokacin data ƙarasa sai kawai ta ga sojan ya danna wasu numbers, sannan ya matsa gaban wata ƴar ƙaramar severity camera yayi magana. Bayan kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe da kanta.
Ƙofar kawai ya nuna mata ya juya ya wuce.
Tun kamin ta saka ƙafarta falon wani irin ƙamshi da sanye suka fara mata lale marhabun. Taku ɗaya ta yi a ɗan ƙaramin downstairs dake ƙarasar da mutun cikin falon, zuwa na biyu na uku ta tashi zamewa saboda sulɓi da kuma tsantsin da tiles ɗin yake da shi.
Haleema ta yi gaggawar riƙeta

“Be careful”

Amira na kallonta ta san ƙanwar Abdool ce dan ga kamanin Abdool nan shimfiɗe a fuskarta. Ita ta taimaka mata ta sauko saman stairs ɗin, tana riƙe da hannunta har suka ƙarasa tsakiyar falon gurin da sauran ƴan'uwanta suke zaune.

“Welcome Sister”

Fauza ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta ga Amira, Meesha kan aikin dannar waya kawai take ko inda Amira take zaune bata kalla ba. Amal ce ta karkace fuska tana mata kallon ƙyama ɗin nan, daman ita ta fi uban kowa wulaƙanci a gidan, cikin ma tana tsoron Ummi da Abdool dan sam basa son wulaƙanta ɗan'adam.

Haleema da kanta ta zaunar Amira a ɗayar kujerun da suke gurin, dan falon ya kasance mai part biyu ko kuma a'ce uku, idan a ka haɗa da dinning area.
Bayan ta zauna Meesha ta ɗaga kai ta kalleta tare da miƙa mata hannunta.

“Hey Sis Welcome, my name is Aisha aka Meesha, ke ce Amira ko?”

Amira ta ɗan ɗaga kai tana murmushin mai nuna tsantsan ladabi da kunya, da kuma sanin kai, kana ta miƙa mata nata hannun ita ma.

“Eh ni ce nice to meet you Meesha”

“Nice to meet you too”

Ta ɗan sakar mata murmushi kaɗan, sannan ta tashi ta nufi ɗakinta, till idonta na kan waya.
Tsire baki Amal tayi ta tashi ta nufi ɗakin Ummi.

“Shukura....”

Fauza ta ƙwala mata kira tana kallon tv kamar ba ita ce tayi kiran ba. Da gudu wata baƙar mace ta fito da gudu daga wani ɓangare na falon ta zo haban Fauza ta tsaya.

“Hasiya ga ni”

“Ba ki ga mun yi baƙuwa ba? A kawo mata abin sha mana”

Wacce aka kira da Shukura ta kalli Amira tana washe baki.

“A'a baiko na mu ne ta zo, sennu sennu, sennu da zuwa, bari ya kawo miki abinse yanzu, ahh sennu baiko”

Ta juya da sauri ta nufi kitchen. Yanayin shigarta da kuma maganar ya tabbar ma da Amira bayarabiya ce. Ƙasa ƙasa Amira take kallon tsarin falon tun daga kujerun har labulayen da flowers da aka ƙawata falon da su komai maroon color ne har center carpet ɗin.
Ga wasu golden gulob da aka ƙawata falon da su, wanda Amira bata taɓa ganin irinsu ba iya tsawon rayuwarta.

Fitowar Ummi ne yasa Amira ta karkata tana kallon yadda Ummi ta doso gun da take tana murmushi. Babu shaka wannan Mahaifiyar Abdool ce dan ga kamaninsa nan sak a fuskarta, dakakkar shaddar dake jikinta ta haske ta sosai, kamar wata sarauniya, hauru makka guda biyu dake a bakinta sun haska fuskarta sosai.

Zubewa Amira ta yi ƙasa tana gaishe ta. Ummi ta dafata tana mai jindaɗin yadda Amira ta bata girma.

“Tashi tashi ƴata”

Wannan furucin da tayi ya faranta ran Amira sosai, cikin kuzari ta tashi amman bata zauna a kujerar ba sai ta zauna ƙasa ta nutsar da kai.
Ummi ta ture Amal da ke riƙe da hannunta tana zuba mata shagwaɓa ta shafa kan Amira.

“Sannu ƴa ta ya hanya?”

“Alhamdulillah”

Ummi ta kalli Haleema tana ɗan zare ido.

“Miyasa ba a kawo mata komai ba?”

Haleema ta juyar da babban yatsanta tana nunawa Ummi kitchen. Sai fmga Shukura ta fito ɗauke da ture da kayan ciye-ciye niƙe-niƙi a saman turen. Har zata dire turen gaban Amira sai Ummi ta girgiza mata kai.

“No kai mata ɗakin Amal”

“Tau Mama Ummie”

Shukura ta faɗa ta nufi ɗakin Amal ɗin.

“Tashi ki bita ki shiga ciki ki yi wanka sai ki ci abincin”

“To”

Amira ta unƙura ta tashi ta bi bayan Shukura tana ƙarema ɗayan ɓangaren na falon kallo.
Sai da ta shige ɗakin sannan Amal ta fashe da kuka kamar wata ƴar shekara uku ta narke a jikin Ummi har da kuka.

»“Ummi za ki ce ta je ɗakina ni warinta na ƙe ji”

“That's why na ce ta je ɗakin ki, ba kece mai jin warin mutane ba? Wannan wane irin iskanci ne zaki ce kina jin warin mutane, dan iskanci”

“Wallahi Ummi mutane wari suke”

“Tau yayi kyau, kullum ina rabaki da wannan halin kina ƙarawa ko? Wannan dai baƙuwar Yarima ce idan kika wulaƙanta ta Dude ɗin ki kuka wulaƙanta”

Ta ƙara ɓare baki tana kuka, sai duk ƴan'uwan suka sa mata dariya, especially Haleema data fi kowa raina ta. Ummi kan tashi ta yi ta bar mata falon ta nufi kitchen.

RASHIDA POV.

Duk yadda take misalta yadda zata rayu ba tare da Hilal ba sai ta farka daga mafarkin da take, bata san son da take ma Hilal yayi yawa a zuciyarta ba sai yanzu, ta take ƙoƙorin lallasar zuciyarta ta haƙuri da rashinsa.
Saka wayarta da ya yi a blacklist ya dame ta sosai, tun da ko text ɗinta ba ya iya karantawa a yanzu. Gashi yayi blocking ɗinta a facebook da whatsapp duk inda take iya ganinsa ta samu sanyin zuciya bata ganinsa a yanzu.

Yau weekend ne ba ta zuwa aiki, amman kwata-kwata ta kwacewa abinci da kuma zaman falon da take ɗan yi dan ragewa kanta damuwa.

Bata fito ba sai da ta ji motsin ƴaƴan ƴar'uwarta Ummul Faisak, da suka zo weekend, sannan ta fito dan bata son kowa ya gane damuwarta.
Tayi ƙoƙarin yin far'ah dan da ɓoye damuwarta, amman hakan be hana Momy yi mata magana ba.

“Yau yanzu aka fito”

Ta zauna kusa da ƙanwarta tana sotsar kanta.

“Bana jindaɗi ne”

“Ai kullum ba za ki taɓa jindaɗi ba matuƙar baki cire Hilal a zuciyarki ba, ai mutumen be mana hallaci ba kuma ya ci amana”

Ta yi ƙasa da kanta hawaye na mata zuba, sai ta shiga murza yatsun hannunta. Ummu ta dafa ta
Chapter 74 · 0% Book details