← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 173

Sashe 37

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu suka nufi ɗakin suna ihu da murna.
Kamar zasu ɓalla ɗakin haka suka tura ƙofar ɗakin Kalsoom suka shiga suna mata sannu da zuwa. Yanayin yadda suka ga Kalsoom tayi musu da fuska yasa suka yi tsaye cirko-cirko suna kallonta.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

                            Website
www.khadeejacandy.com.ng

Meaning of POV. Point of view: used especially in describing a method of shooting a scene or film that expresses the attitude of the director or writer toward the material or of a character in a scene.

*PAGE - 28*

NOT EDITED ⚠️

“Bana ce ku daina shiga ɗaki da gudu ba? Ban hana ku ban kar ƙofa ba? Sai kace ball”

Duk kama kunnensu suka yi kamar yadda ta koya musu.

“Auntie we sorry”

“Sorry for yourselves, aya kowa ya riƙe ƙafarsa ɗaya”

Duk dariya suka saka suka rumgume.

“Allah kuwa ba zamu sake ba, Auntie da baki nan Ulfah tace Dady ya siyo mata takeaway”

Ezzah ta faɗa tana zare idon, sai murƙususu take kamar ta shige jikin Kalsoom.

“Ke kuma kika yi faɗa da wata a School”

“Eyye 2+2 kowa taje ta kama ƙafarta na ce”

“A'a ai kince ba zaki sake mana horon dare ba, yau mun yi missing ɗin ki Auntie ina kika je?”

“Wani guri na je”

Ta faɗa tana jan hancin Ulfah, har ga Allah tana son yaran, haka take jin su kamar itace ta haifi su, sam basa sakewa da Mamarsu kamar yadda suke sakewa da ita, saboda ta kan basu lokacin ta.

“Aje a kwanta gobe akwai makaranta, kar a makara”

“Okay Auntie”

Duk kiss suka mata a gefen fuska sannan ta shafa kan su.

“Idan za a kwanta a yi alwalah, Ezzah ki yi addu'ah sai kiyi ma Ulfah, ke kuma Ulfah kiyi ma Rafiq, kuma zan shigo na ga wanda ya kwanta ba dai-dai gobe akwai kama ƙafa”

Ulfah ta tsuke baki ta girgiza kai

“A'a bana so yawunta be da tsarki”

Dariyar Hilal ce ta ɗago ta duka hankalinsu izuwa garesu, ashe yana tsaye jikin ƙofa yana kallon su.
Kalsoom ta ɗan sha masa mur, irin har yanzu fa fushi nake kai, ta kalli yaranta.

“Good night sweethearts”

“Good night Sweet Auntie”

“Ku saka kayan bachi, sauran ku watsar da wannan kayan idan kun cire”

Dariya kawai suka yi, suka je suka ma Daddyn u sai da safe suka fice. Shi kuma ya mai da ƙofar ɗakin ya rufe ya nufo ta yana murmushi.

“Yanzu shi kenan, daga fitar su sai kuma ki ɗaure min fuska, ni da su waya fi cancanta da far'ar nan naki?”

“Su kasan ana canja miji ba a canja ƴaƴa ba”

Dariya yayi ya rumgumota.

“Haba ni da nazo miki da albishir kuma”

Ta tsire baki tana ƙoƙarin zamewa daga jikinsa.

“Wallahi da gaske na ke, nayi shawara zan fara baki 50k duk month, tun da ita Rashida aiki take, ina ganin kamar ban yi adalci ba idan na bar ki haka”

“Dan Allah da gaske”

Ta tambaya cikin murna da jindaɗi, sai kawai ta saki jiki ta rumgume shi.

“Yauwa yanzu da kika ji maganar kuɗi sai na samu rumguma ko? Ko kunya baki ji ba”

Ta rufe kanta cikin ƙirjinsa tana dariya.
Duk wannan maganar da Hilal yake Rashida ya tsaye jikin ƙofa tana jinsa, wani ƙashin baƙinciki ne ya taso ya zo yayi mata tsaye a wuya, har ta kasa jurar tsayi a gurin ta wuce ɗakinta.
Har ta cire tufafin da suke jikinta, tsanar Kalsoom sai ƙaruwa yake a ranta, gani take duk ta zo cikin gida ta hana ta tsukuni ta ƙauce mata miji. Tawul ta ɗauka ta shiga bathdroom tayi wankan tsarki sannan tayi na sabulu ta ɗora da alwalah ta fito. Ta rama sallah magariba sannan ta yi na Isha'i.

Sai kusan goma saura Hilal ya leƙa ɗakinta. Ƙiri-ƙiri tayi kamar bata ganshi ba, ta cigaba da chatin ɗin da take a waya. Shi kuma ya tsaya a kanta.

“Bayan kin dawo aiki sai kika sake fita baki faɗa min”

“Amman ai kasan idan ba aiki ba, babu abunda zai sake fitar da ni ko? Kuma na ga kai ka bani damar nayi aikin, ita wacan da yake ƴar gatan ka ce ai sai ka hanka mata albashi tana zaune a gida ko?”

Murmushi yayi mai sauti.

“Kalsoom bata nufin komai dake sai alheri, ki duba kiga yadda take kula da yaran nan, ke kanki baki kula da su haka, a ganin ki kema kan ki be ci ace kin yanka mata albashi ba, naga ke kina aikin ai”

“Ƙwarai aikin kam yanzu na fara saboda abunda mahaifina ya koya min kenan, be nuna min na zauna a nema a bani ba nima na san Freedom ɗina”

“Good of you, amman idan har aikin yana da rana a gare ki be kamata ki saka hannu ki ɗaukar min dubu ɗari uku ba ba tare da sani ba, bayan kuma babu nauyin da ban ɗauke ba na cikin gidan nan, kin san iya abunda na aikata a rashin ganin kuɗin nan?”

Cikinsa tayi da masifa tana kuka.

“Ka yi min duk abunda zaka yi Hilal, ka kira ni da ko wane irin suna ka siffanta ni da duk sunan da yayi maka a duniyar nan, saboda kayi amarya, daman haka halin ku yake a duk lokacin da kuka aure mune abun wulaƙantawa, mune banza mune wofi”

Kallonta yake har ta gama faɗan ta koma gefen gado ta zauna tana cigaba da kuka. Sai ya sassauta zuciyarsa, duk wani abu da yake ji sai ya aje shi gefe, ya zauna kusa da ita ya jata ya rumgume.

“Bana da niyar wulaƙanta ki dan na yi aure Rashida, i love you so much”

Ƙara narkewa tayi.

“Hilal ina kishin ka, ina kishin ka kwana da wata Mace ba ni ba, Hilal i can't deny it and i can't take it, please divorce her Hilal”

“I can't and won't, ita amana iyayenta suka bani, son da nake miki ba zai sa na rabu da ita ba a kan ki, ke ma kuma ba zan miki haka ba, so karki yaudari kan ki”

Ganin ba zata daina kukan ba, yasa ya ɗaga ta ɗaga jikinsa, ya tashi cikin rashin daɗin rai ya nufi ɗakin Kalsoom.

NAMRA POV.

Sun yi sa'ar samun likitan har ya duba ta, ya sanar mata ciki ne amman ta samu miscarriage, ya rubuta mata gani da allurai sannan ya bata gado. Sai bata yarda ya kwanta ba sai tace mishi sai taje ya faɗawa mijinta. A cikin asibitin ta siye wasu maganin nikan.
A bakin gate ɗin suka samu Napep, Namra kamar jira take, suna shiga ta fara kuka. Ita sam bata jidaɗin ɓarewar cikin ba, gashi har yanzu zugi mararta take mata.

Ba karamin ƙarfin hali Mardiya tayi ba, wajen bata haƙuri dan ita gaba ɗaya hankalinta ya tattara ya koma gida, zuciyarta sai yaye yaye take mata. Ita kanta tana jin bata kyauta ba idan har gidan Namra ya ƙone, sai dai bata da mafita sai wannan.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ”

Ta furta a razane lokacin da mai Napep ya sauke su cikin jama'ar da suke gurin. Da sauri Namra ta buɗe idonta dake rufe ta fito daga Napep ɗin ta nufi gida a ruɗe.
Mardiya ce ta sallami mai Napep ɗin ta rufa mata baya, tana ta innalillahi. Haka Namra ta ƙira kusa mutane da suke tsastsaye suna kallon wutar, har ta shiga cikin gidan. Da sauri wani daga cikin yan fire service ya tare ta sai matan unguwar suka zo da gudu suka riƙe ta.
Wani irin fisge-fisge take take tana son ta kuɓuce ta shiga cikin wuta, sai ɗakinta take nuna musu tana wani irin kuka mai ban tausayi.

Wani irin tuma take tana direwa ƙasa, kamar sabuwar mahaukaciya. Sai kuma ta koma can gefe ta rumgume kanta, jikinta sai rawa yake kamar mai sabon fever.

“Allah na gode maka Allah, mijina ya kare, cikina ya ɓare yanzu kuma gidana ya ƙone, Allah ka sassauta min haka nan Allah, Allah ka yafe min na san ni mai yawan zunubi ce mai yawan saɓa maka Allah”

Wani irin ajiyar zuciya ta sauke sai jiri ya kwasheta, ta soma ganin mutane biyu-biyu sai ta jinginar da kanta, tana numfashi a hankali. Mardiya na can gefe tana kuka sosai, kamar gidan nata ne ya ƙone, idonta har ya kumbura ya daina hawaye.
Haka wutar ta ci ta cinye, ba a samu nasarar kasheta ba, sai da ta ƙone ilahirin gidan gaba ɗaya, ya rage saura BQ kawai. Har kuma lokacin Namra sama-sama take ganin mutane, komai ya zame mata kamar mafarki, yanzu kam bata da gabas bata da yamma, bata da madafa, bata da mafita sai ta Allah. Gashi babu abunda ya fita nata sai tufafin da suke jikinta.
A tunaninta kuɗin da Dillaliya ta kawo mata ya ƙone, ga sarƙarta ga tufafinta kayan ɗakinta da kayan kallo freezer da sauran kayan kitchen, yanzu bata da komai sai rai, gashi lafiyar jikinta ma bata isheta ba.

Mutane sun yi ta bata haƙuri suna nuna mata yarda da ƙaddara, da mata fatan Allah mai da alheri, a gidansu Mardiya ta kwana, ba kuma dan kwanan bachi ba, dan a zaune ta kwana, tana jinjina lamarin Ubangiji.
Da safe Mahaifiyar Mardiya ta siyo mata koko da ƙosai, Namra ta kasa sha, ta aika a siyo mata tea shima ta kasa sha. Sai tayi zaune jigum, tunani ya taru yayi mata tsaye a rai.

Tunanin yadda zatayi da Dillaliya, da kuma yadda zata faɗawa Asim gidansu ya ƙone, bata tunanin faɗawa Anty Amarya, saboda a ganinta sun juya mata baya, ita kuma ta ɗauki alƙawrin ba zata sake nuna musu tana buƙatar wani abu ba.

Sallamar Dillaliya sata ta razana sosai, kamar ance mata ga baƙon mutuwa. Sumi-sumi Dillaliya ta shigo ɗakin fuskarta ɗauke da damuwa da kuma tausayi.

“Allah sarki Baiwar Allah, haka Allah ka kawo miki wannan ƙaddarar ke kuma?”

Ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa. Idon Namra ya cika da ƙwallah.

“Kin dai gani, duk abunda Allah ya kawo ba a iya guje mishi, Wallahi komai ya ƙone”

“Haka na ji ƴar nan, ai ni jikina duk yayi sanyi na haɗa ɗan jarin na miƙa miki har da kuɗin mutane gashi komai ya ƙone”
Chapter 37 · 0% Book details