← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 173

Sashe 97

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗan sunkuyar da kai.

“Hajiya na ce ko akwai abunda za'ayi miki?”

“A'a gaskiya yanzu kam babu sai dai zuwa anjima. Amman karka manta fa na faɗa maka za mu yi baƙo gobe zai zo daga garin ku, kuma dan kai kawai zai zo garin nan, ina fatar zaka ba shi haɗin kai, yana gida a nan idan ya zo a gidansa zaka je, zan baka maganin da zaka sha, kums ka tabbatar kana kallon videos dana tura maka ɗin dan kasan yadda zaka sarrafashi”

“Karki da mu inshallah ba za'a samu matsala ba”

“To yayi kyau haka na ke so, sai kuma a samu wata ƴar sana'a a riƙe gudun zargin mutane, ina ganin ma nan gaba kadan garin ku zai maida kai dan can yake”

“Nima ai zan fi jindaɗi dan akwai waɗanda na ke son su san nayi kuɗi dan sai na rama wulaƙancin da duk aka min”

“Allah dai ya taimaka, idan ka saki jiki ina faɗ Maka nan gaba kaɗan sai an saka ka a cikin matasan da suka fi kowa kuɗi a nigeria”

Wani kalar daɗi ne yaji marar misaltuwa. Kaɗan ya labarta mata irin gwargwarmayar da yayi da iyayen Namra sannan ya taso ya fito yana auna kansa a mizanin arziki.

Falonta ya dawo ya zauna, yana duba shafin facebook da sabuwar wayarsa. Yau ma ya tararda friend requests kamar wacan lokacin. Da kuma da kuma saƙon wata kyakkyawar yarinya ta tura masa dan katun ɗin nan na facebook mai cewa mutane Hi.

Reply yayi mata.

_“Hey How you darling”_

Sannan ya shiga profile ɗinta yana duba hotunanta.

“Wow wannan kan ba dai fari ba da kyau, irin wannan idan ka samu irinta ai ka huta”

Nan da nan yayi saving hotunanta, sai ya dawo inda taƴi masa reply yana ƙara amsa mata.

_i'm fine. By the way am Nabila Lawal Alƙali aka Pretty Nably. from Katsina living in Abuja_

_Nice to meet you dear, i'm Asim Ibrahim Sanusi aka Asim From Sokoto living in Katsina_

Bayan kamar minti ɗaya sai ta sake aiko masa wani.

_Wow which area in Katsina? I know Katsina in and out_

_Nasarawa road. Send me your number let's chat on whatsapp_

Cikin ƴan mintuna ta turo masa number. Sai da yayi saving sannan ya sauka daga kan facebook ɗin ya tashi ta fito ransa fari fes.
Motar daya saba shiga ya shiga, wacce ta zame masa kamar tasa.
Tun da ya doshi hanyar Nasarawa rayuwarsa ta soma baci, sai faman jan tsaki yake yana nasalta yadda zai tararda Namra.

“That's why i hate baƙar mace, da sun kwana biyu zaka ga sun lalace babu ko kyau kallo, ji jikinta dan Allah duk ta bi ta zube sai ƙassa me zaka kallo a jikinta ma ka yi sha'awa, mtsssss”

Be ji zai shiga da motar cikin gida ɗan haka ya faka ta a ƙofar gidan ya shiga yana wani yatsinar fuska, kamar bada aka yi rayuwa a gidan ba.

Zaune ya hango ta tana ta faman wanki tufafinta. Tana jin sawon tafiyarsa amman ta ƙi ta ɗaga kai ta kalleshi dan be yi sallama ba, kuma tasan abunda ya kawo shi a gidan be wuce abunda take zargi ba.
Zaunawa kawai yayi kusa da ita yana mata wani kallo kamar ba matarsa ba.

‘Ai dole na yi aure a ina zaka nuna wannan ka ce matar ka ce? Abu busasai haka’

Furucin da yayi a zuciyarsa kenan, a fili kuma sai ya ce.

“Sannu da aiki”

“Yauwa”

Ta amsa ba tare data kalleshi.

“Kin koma asibitin ne?”

“Bana da kuɗin hoto”

“To ma ba wannan ba, wace shawara kika yanke ne?”

Kallonsa tayi sai hawayen dake maƙale a idonta suka zubo

“Yanzu abunda kake min ka min adalci kenan? Shikenan kai babu ruwanka da danuwata kullum ni kaɗai nake kwana a cikin gidan nan idan ma wani zai shigo yayi min fyaɗe ko ya kashe ni sai dai ya zo? Asim miyasa kake min haka ne? Ka mayarda ni kamar karya marar amfani”

Hannu ya kai yana shafa ta, dan har ga Allah yayi missing ɗin jikinta.

“Ba haka bane Namra, sai da muka xauna da ke muka yi magana kan aikin nan kika ce kin yarda sai kuma yanzu ki fara complain ko dai ki shi kike ne?”

“Kishin me?”

“Kin ga zan yi kuɗi mana”

Ya faɗa da ƴar dariya, ita kuma sai tayi masa wani kallo.

“Ka min ka yi kuɗi Asim, dubun ka sun yi, wasu sun mutu sun bar kuɗin, wasu kuma kuɗin sun guɗu sun bar su. Kamin ka sanya rigar dubu goma, sai da nasa ɗan kunnen biliyan biyu da rabi na zinari, dan haka kuɗin da zaka yi basa burge ni balle na yi ƙyashinka”

Wata dariyar rainin wayo yayi.

“Amman ai kyau abu akan gashi a ƙasa, da muka yi aure mi Babanki ya kawo mana?”

“Me zai kawo maka, bayan yasan ka auri ƴarsa saboda abun hannunsa ne? Ai shi ba lurasari ba ne, irin Mama mai nuna sun abun duniyarta a fili”

Ya nunata da yatsa.

“Karki sake uwata a maganar ki wallahi”

“Nima karka sake saka ubana, dan cin mutunci ba gado bane kowa ya iya”

“Dube ki dan Allah ni in ban da kaɗɗara ma mi zan yi da irin ki?”

“Lallai kam kaɗɗara ce Asim da nima babu abunda zan yi da irin ka, dacan baka san da haka ba, sai yanzu? Dan kana jin nera ta fara keta wuyanka? Ko da yake hausawa sun ce ɗan talaka be iya samun guri ba”

Tasssss ya wanke mata fuska da mari. Ita kuma ta ɗauki bokitin da take wanki da shi ta juye masa ruwan wanki ta jeɗa masa bokinta. Zuciyarta ta kawo sosai ita kanta a yanzu ta san ba kuka take da buƙata ba, dan ta fahimcin idai har ta ƙyale Asim zai iya hallakata.

“Karka sake kuskuren taɓa min jiki dan ni ba baiwa ba ce kuma ba jaka ta siyo ba”

“Ni kika jiƙe da wannan ruwan? Wallahi sai kin raina kan ki dan sai jikinki ya gaya miki, ba ke fa wallahi yanzu ko ubanki nafi ƙarfinsa balle ke, banza a banza, kuma wallahi kije a zubar da cikin nan ko yanzu ki yi gidan ubanki wallahi, dole ki zaɓa”

“Wallahi ba zan zubar ba. Sai dai ka sake ni amman ba zan zubar da wannan cikin ba”

“Haka kika ce?”

“Haka nace kuma haka na zaɓa”

“To kije gidan ku na sakeki sa..ki ...ɗaya.... Idan kin zubar ki dawo zan maiyar da ke”

Kamar an sako duwatsu haka Namra taji saukar furucin Asim da bata tsammaci zai mata shi da gaske ba. Zubewa ta yi ƙasan guiwowinta tana masa kallon mafarki.

“Da gaske Asim ka sake ni?”

“Na sake ki mana, ba kin zaɓi abunda be isa aka masa numfashi ba balle ma har ya zo duniya ba, sama da ni”

Kai ta ɗaga masa wasu hawaye masu zafi suna bin kumatunta tace

“Na zaɓe shi sama kai, kamar yadda na zaɓe ka sama da iyaye na acan baya, na zaɓi ka sama da karatu na, na zaɓe ka sama da jindaɗi da arzikin da yake gidan mu, na zaɓe ka sama da samarin da suka yi so na, na biyo ka garin da ban san kowa ba sabida kai. Amman yau ni ka yi watsawa ƙasa a ido, lallai kai butulu ne Asim, ka tabbata ɗan bushiya. Duniya ce Asim wanda be zo ba ma ta shiriya masa balle wanda yake cikinta, ka taka a sannu dan duniya ƴar ɗauka da ajewa ce...”

Tsaki kawai yaja ya ɗauki keys motarsa da suke gurin ya juya ya fice cikin fushi. Da kallo Namra ta bishi wani irin abu ya soma zillo yana neman numfashinta.

*Best regards 🌺*
*Khadeeja Candy ♥*
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: Akwai inda na yi mistake jiya nasa ɗan kunnen biliyan biyu da rabi, miliyan biyu da rabi na ke nufi typing errors ne kuma ban yi editing ba.

*61*

NAMRA POV

Kwance tayi a gurin tana ɗaukar numfashi, sai lumshe ido take tana buɗewa, abu ya zo ya tsaya mata a zuciya kamar ƙashi kamar dutse.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Allahumma ajirna fi musibati wa'kalif ni khairan min ha”

Shine abunda take ta maimatawa tana yaƙi da zuciyarta, tana ji tana gani idonnuwanta suka fara nuna mata ba haka, sai dinshi-dishi take gani, kalmar sakin da Asim ya furta mata ne yake ta mata yawo a ƙwaƙwalwa. She just can't believe Asim ya sake ta, ina zata je? Minene a fita a gareta yanzu bata sani ba.

Hango kanta take a cikin gidansu Abbah yana korarsu ita da Anty. A ɗayan ɓangaren tana tunanin abubuwan da mutane zasu faɗa idan har aka ji aurenta ya mutu, duk wanda be son aurenta da Asim zai mata dariya idan ya ji aurensu ya mutu. Duka yaushe aka yi auren da har za'ace auren ya mutu, gashi duk ta lalace ta koma wata iri? Ciwon da yake jikinta za a ce sai da ta kwashi ciki da ciwon mahaifa sannan ta dawo gida.

“Azzalumi ma cuci Allah ya isa tsakani na da kai, Allah ya bi min haƙƙina”

Daga kwance da take tayi furucin tana kuka mai taɓa zuciya. Bata san inda zata je, tun da taƙi ta bi Anty Amarya tun da farko, yanzu kuma tace mata me?
Haka ta kwanta a gurin jikinta ya ɗige gaba ɗaya, kamar an zuba kayan wanki.
Chapter 97 · 0% Book details