← Book details Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 173

Sashe 83

Zagon Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A baki take furucin zuciyarta cike da yaƙinin ita ɗin zata iya, shi kansa Asim yaga hka idonta sai dai babu abinda zuciyarsa ta ayyana masa sai aljanu, ganin yake aljanun Namra ne suka taso cikin daren nan. Nan da nan marar ta cika da fitsari, be nuna tsoro a fuska ba, amman a zuci tsoron har yayi masa yawa, ala-ala yake kar aljanun su caka masa wukar, dan shi dai yasan Namra da kanta ba zata iya masa haka ba.
Uffan be ƙara cewa ba, sai kawai ya ɗauki tabarma da filo da abin rufa ya koma waje ya kwanta, dan baya jin zai iya kwana ɗakin karya kasheshi cikin dare.

A wajen ma sai ya koma can nesa da ƙofar ɗakin sannan ya shinfiɗa ya kwanta. Duk bayan minti ɗaya biyu yake farkawa ya tofe kansa da addu'a sannan ya sake komawa. Kamin safiya ta qaye har ya matsu. Yana fita salla asuba, yai fitar gaba ɗaya.

*AMIRA POV*

Tana jin parking ɗin mota, ta ayyana a ranta cewar Abdool. Da sauri ta ƙarasa shafa hodar da take ta ɗauki ɗankwalinta ta yafa saman kai ta biyo sawun kannensa dake masa oyoyo.

Amal ce taje da gudu ta rumgume shi, Ummi da sauran ƙannensa kuma suka tsaya a jikin ƙofar falo suna jiran ya ƙaraso. Hannu Amal ya riƙa suka nufo falon hularsa a hannu yana murmushin data ƙayata kyausa.
Ɗan risinawa ya yi lokacin daya kawo bakin ƙofar falon, ya gasheta da Ummi kamar yadda ya saba. Sai ta amsa masa murmushi tana faɗin.

“Mu duk mun ɗauka jirgi zaka biyo fa”

“Wallahi haka kawai naji ina buƙatar driving da kai na”

“Amman ka biyo haka babu kp ƴan rakiya Abdallah abinda Mai Martaba yayi ta maka magana akai kenan, kana da maƙiya fa ya kamata kana bawa kan ka tsoro mana”

Murmushi yayi ya lanƙama Ummi suka shiga falon tana faɗin.

“Abinda Allah ya bututa babu mahani”

Amira bata jidaɗin yadda ya wuce ta ba, sai yayi kamar be ganta ba. Ba kuma dan be ganta ba ɗin sai dai rashin kular da yake nuna mata, dan shi sam bata burge shi.

Saman kujera ya zauna tare da Mahaifiyarsa yana dariyar yadda take masa faɗan ya take masa na zuwan da yayi ba tare da bodyguards ɗinsa ba.

“Haba ummi bodygrsd zasu tsare ni ko Allah?”

“Ni ba wani wa'azi na ce ka min ba”

Ya ɗaga hannayensa sama yana dariya. Kallonsa kawai Amira take cike da shauƙi, bata zaci yana dariya haka ba.

Ruwan sanyi Amal ta kawo masa tare da kofi, ya sha ruwan sosai ya jiƙa maƙoshinsa. Sannan ya tashi ya fice daga part ɗin ya nufi part ɗinsa. Tuɓewa yai ya ɗaura tawul ya shiga banɗaki yai wanka tare da alwala, sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan tufafin daman sune tufafin daya fi so inda a gida yake. Sai da ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito. Ya nufi masallacin gidansu yai salla azahar, bayan ya gama ya gaisa da wasu mutanen unguwar tare da sojojin da suke gadin gidan. Be fita da komai a aljihunsa ba shi kuma mutum ne mai alheri baya jindaɗin ya ganka be baka komai ba, sai dai kam akwai zuciya dan baya ɗaukar raini. Tsayar da mutanen yayi ya dawo cikin gida ya ɗauki kuɗi masu ɗan yawa ya miƙawa wani soja yace ya raba masu. Aiko har da waɗanda ba su yi salla a masallacin ba sai sheƙowa suke suna samun nasu rabo.

Sai da ya tabbatar kowa ya samu sannan ya juyo ya dawo cikin gida. Part ɗin Ummi ya nufa dan cin abincinsa na rana.
Duka ƙanensa suna dinning har Ummi suna cin abinci, Amira ma ta maida hankalinta sai cin abincin take kamar bata ga shigowarsa ba, Amal ce kawai ta kawarda kai tana yamutsa fuska kamar mai ƙyanƙyami.

Kujerarsa yaja ya zauna yana naɗe hannun T-shirt ɗinsa yana rabon ido, dan be san wane abinci zai fara ci ba.

“Dude don't..!”

Amal ta faɗa tana yarfar da hannu.

“Why?”

“All these things wannan yarinyar ce ta girka”

Ta faɗa tana nuna Amira. Daga Ummi har Abdool ɗin da kansa be jidaɗin abinda Amal tayi ba. Ɗan murmushi Amira ta yi, irin murmushin na rashin jidaɗi ta tashi daga cin abincin da take ta nufi ɗakin Amal ɗin wanda yanzu ya zame mata kamar ɗakinta a yanzu.

Sai ta ta shige sannan Ummi ta kalli Amal cikin xafin rai tace

“Dan ta girki abinci kike cewa karya ci ita ba mutum bace? Bata taimake ku ba? Bata fiye muku wannan inyamurar da take girka muku abinci ba? Miyasa kika ɗauki rayuwa da zafi ne Amal, ke dai baki rayu da babanki ba, balle na ce shine ya koya miki, wannan sam sam ba ɗabi'ar ƙwarai ba ce, ɗan 'adam ba abun wulaƙamtawa be ne”

Fashewa Amal.tayi da kuka ta tashi da gudu ta shiga ɗakin Meesha. Abdool ya zuba abinci ya soma ci yana faɗin

“Ummi you shouldn't talk to her that way marainiya ce”

“Ai daman kai kake buɗe mata ƙofar yin abinda duk take so, babu dama ayi ama Amal faɗa a gidan nan, duk abinda take yi hundred percent kai kake supporting ɗinta”

“Ummi ba haka bane, Amal itace ƙarama a cikin mu, kuma yarinyar nan ko da ta yashi bata san mahaifinta ba, ya kamata ace tana jin sanyi wani gurin”

Ummi tayi shiru tana cigaba da cin abinci. Tasna abinda Abdool yake faɗa gaskiya ne da acw mahaifin su an nan da ko hararsu Ummi bata isa tayi ba, dan game da yaransa ba shi da kyau babu mai taɓa masa komai kusancinsa da kai, musamman Amal da yake jin ta kamar ransa. Sai dan tana marainiya ba zai bata damar wulaƙanta kowa ba, Ummi bata da wannan halin daman can halin mahaifinsu baya burgeta, Amal ce ta kwashe halin gaba ɗaya, sai kuma Meesha dake ko-in-kula da mutane.

“Amman shi kenan, dan tana marainiya sai ta riƙa irin wannan halin? Dubi ka ga yarinyar nan wai har warin mutane take ji haba wannan iskanci ai har yayi yawa”

Abdool ya yi dariya

“Ƙurciya ne zata daina nan gaba kaɗan”

“Allah yasa”

“Amin”

Yaja tissue ya goge bakinsa, sannan yaja kujerar ta yi baya, ya miƙe tsaye ya nufi ɗakin da Amira take.

Kife ya tarar da ita saman gadon tana kuka. Sai ya zauna a kujerar dake ɗakin yana ƙarema ɗakin kallo kamar baƙonsa.

“Funny you indai akan Amal zaki riƙa kuka zaki ƙarar da hawayen ki ne kawai baki gama kukan ba, the more Amal knowing you are crying for her the more she will do something to insult you, haka rayuwarta take akwai ƙuruciya a cikin ta sosai”

Daga lokacin da kalaman Abdool suka fara shiga kunnenta sai ta ji duka kukanta ya yanke, sautin muryarsa da take ji sai tsigar jikinta ta tashi. Tashi tayi zaune ta share hawayenta, ɗaga kanta da zatayi caraf cikin idanuwansa. Eyeball to eyeball suke kallon juna ita da shi, kowa da irin abunda yake tsaƙawa a zuciyarsa. Ita ta riga kawar da nata idon saboda kwarjinin da yayi mata, sai ta kawarda fuskarta gefe. Tana murmushi a zuci.

“Sorri for what Amal did to you”

“Never mind”

Miƙewa yayi tsaye ya fice ɗaga ɗakin ya nufi ɗakin Meesha inda Amal take. Ita ma lallaɓata yayi har tayi shiru sannan ya fito ya koma part ɗinsa ya canja kaya ya nufi gurin Mai Martaba.

Ba shi ya dawo ba sai da dare ya raba, daman duk yaje gurin Mai Martaba ko da rana ne sai ya daɗe balle ya je late. A falo ya sami Ummi Amal na saman ƙafafunta tana bachi, murmushi yayi ya zauna kusa da su yana kallon Amal ɗin.

“Har kun shirya”

“Ta ya za'ayi uwa da ƴa, ita ta kawo kanta tace min ta daina”

“Hmmm Amal kenan wannan ɗabi'ace kawai ta ɗan adam, amman idan kin lura har ƴan'uwanta bata bari ba”

“Jiya ma haka suka yai ita da Haleema akan Amirar nan”

“Ai tana gama wannan makararar ƙasar waje zan kai ta tayi karatu a can a huta”

“Ta dai ƙara lalacewa”

Dariya yayi ya miƙe tsaye.

“Ummi good night”

“Aha night, Abdallah yaushe zaka koma?”

“Jibi, akwai aiki a gaban mu abuja”

“Ai kai Allah be raba ka da aiki ba, ni dai kamin ka koma ina son kaje gidan nan na Haleema ka duba mana shi, yadda gyaran zai kasance sai ka kira yaron nan Isma'il ka faɗa masa, dan kasan gidan marayune ƙara a gyara idan ma wasu ƴan hayar za a zuba sai”

“Okay zaje gobe inshallah dan gobe babu inda zan je, a ina ne gidan ya ke? Tun da akayi gobarar nan ma ban je na duba shi ba”

“Yana nan Nasarawa na can wajen gidan action kuɗi ƙasa, kasan irin abubuwan nan sai maza, ni mace wano abu sai dai na ɗaga ƙafa”

“Inshallah gobe zanje”

“Allah ya kai mu”

“Sai da safe”

Yana hamma ya fice daga part ɗin dan duk ya gaji sosai.

*HILAL POV*

Lokacin daya isa asibitin be wuce ɗakin da Rafiq yake ba sai da ya biya ya karɓo hoton da akayi ma Rafiq ɗazun. Sai dai ba iya ya buɗe hoton ba har ya koma office saboda fargaba, sai yanzu ya gane irin abunda majinya suke ji idan wani nasu aka ce yana da wani ciwon ko kuma za ayi masa aiki.

Zamansa kenan a office, sai ga Alhaji Bashir ya shigo cikin mayan tufafin na shadda, tun kamin Hilal yayi masa uwarnin zama ya zauna yana nuna alhininsa akan abinda ya faru.

“Ɗazu nake jin labari babu daɗi ban samu na shigo ba sai yanzu”

Ya faɗa yana miƙawa Hilal hannu su gaisa. Hilal ya maiyarda Hoton gefe ya aje yana sosa kansa yace

“Ƙaddarori ne”

“Wallahi shiyasa kaga bana son ƙara auren nan dan rigima ce kawai ko wacce da kalar matsalar da take zuwa da ita, yanzu miye abin na sawa yaro guba”

“Babu tabbacin ita tasa Bashir, amman dai ita kaɗai ce a gidan”
Chapter 83 · 0% Book details